Showing 36001 words to 39000 words out of 85666 words

Chapter 13 - BAZAWARA CE ITA COMPLETEHAUSA NOVELS BY .txt

idan tadawo gida alokacin Abba duka zaiyi mata,Amma lokacin data shigo gidan sai yanuna tausayinsa akanta haryake lallamin ta. Nan take wa'azin malam nad'azu yakuma ziyarci kwakwalwar ta,kalmar sa nakarshe daya Rika nanatawa,inda yake fad'in "yake wannan amarya kizamo mairike sirrinki,karkizamo Mai fallasa sirrin gidanki ko namijinki,tundaga kan yau da kk zamo matarsa,kirike sirriku nakune kedashi kada kiyarda kisako wani cikin lamuranku."
Kodatakai karshen tunanin nata sai tasinci kanta cikin wani irin sabon yanayi, tad'ago kanta tasaci kallon Abba taga harlokacin idonsa nakanta, ahankali tagyad'a kanta alamar Eh tana sonshi.
Abba baisan sanda murmushi yasub'uce masaba,hamdala tayi acikin zuciyarta
Tabbas yau tasan tafaran tawa Abbanta Wanda harya gaza boye farin cikin sa.
Baba Salihu yace "to alhmdllh Allah yy Miki albarka yadauwamar da farin ciki arayuwar aurenki.yacigaba da fad'in "JUHAIFAH kizamo Mai hakuri da biyayya wa mijinki,sai kinyi hakuri zakiga ribar rayuwa,kada kizamo d'aya daga cikin matan da basud'auki aure abakin komaiba Kuma ita aure babbar abuce yanda kk numfashi haka itama take,kiyi biyayya wa mijinki, kiyi biyayya wa mijinki."
Natsiha sosai Baba Salihu yarika yimata maishiga jiki,daga karshe yabita da fatan alkhairi,
Yacewa Mommyn Jos "Hauwa'u kukaita d'akinta."
Mommyn Jos tariko hannunta suka nufi d'akin' Ammee,
I'tamadai nasihan tayima sosai inda nasihar Ammeen yafi karkata akan,kada takuma aikata abunda ta aikata abaya idan tanason farin cikin su dakuma albarka yadauwama arayuwar ta,sannan tayita sanya mata albarka da nimamata fatan nasara azaman aurenta agun Allah.
Mommyn Jos takuma ruko hannunta suka nufi part d'in Ya Al'ameen a parlourn sa sukasameshi shidasu Ya Mujaheed,
Tunkan sukaraso cikin parlour suka kafeta da ido,itako saurin share hawayenta tayi cikin dabara ta'in'da bazasu fahimci hakanba,
Suka isa cikin parlour
Mommyn Jos tace "ga kanwar ku kuyi mata naku nasihar Dan awuce da'ita d'akinta."
Zama tayi atsakiyarsu,
Ya Al'ameen yadubeta Yana fad'in Shalele yau bakukane?."
Kwakulo murmushi tayi,muryarta narawa tace "Dan Allah yayuna kuyimin addu'a wannan karon nasharewa mahaifin mu hawayensa zanje nazauna agidan aurena dan nasama masa farin ciki."muryarta yafara hard'ewa tashiga kokarin danne kukan dayake kokarin kwace mata,
Ya Mujaheed yad'aura yatsarsa agefen odon ta inda hawaye yafara gangara yashare matashi,
Tabbas girma yafara shigar kanwar tasu tunda hartasan tayi wannan tunani.

Ya Al'ameen yarike hannunta
Yace "Shalele Allah yabaki ikon samarwa mahaifin mu farin ciki,
Muma hankalinmu zai kwantane idan kika nutsu guri guda,
Shalele farin cikinki shine namu."
Saiyanzu Ya Jabeer yy magana' cikin salon kwantarwa da kanwar tasu hankali yace "Shalele yau bazakice nayimiki faretin bane kosainazo gidanki kafin."
Cikin muryar shagwab'a had'ida kuka da dariya tace "a'a nidai yanzu zakamin."
Yace "to angama."
Yamike tsaye yashiga zabga fareti,
Wannan karon JUHAIFAH batayi sallen murna aduk sanda Ya Jabeer yafara yimata faretin ba,mekewa tsaye tayi tarungumeshi tareda fashewa da kuka, shima rungumetan yy,yayinda hawaye yashiga gangarowa kan fuskarsa,saikuma yasaketa' tareda rike kafad'arta, ahankali yashiga furta "Shalele kizauna agidan mijikin ki kinji? ida kk zauna ke zakirika yimin tarun kayan aurena."
Dariya Mai had'ada kuka takumayi tace "Ya Jabeer tarema zamuje musiyo kayan ko?."
Yace "sosaima kuwa,ai kezaki zab'i kalar Wanda za'asawa amaryar acikin akwatin ma."
Baki takuma washewa hawaye na gangara kan fuskarta.
Yad'aura hannunsa yashare mata tareda girgiza mata Kai alamar tabar kukan,
gyad'a kanta tayi,
Ya Mujaheed da Ya Al'ameen suka mike sukazo inda suke tsayen,
Ya Al'ameen yadafa kafad'arta yace "Shalele inkinje kiyi hakuri kinji ko,Kuma karkirikayin kukannan fa."
Tace "tom."
Mommyn Jos tashare guntun hawayen idonta,
Tabbas tautsayin yaran yakamata
Ganin yanda suke nunawa junansu zarlar kauna da tausayawa kanwar tasu.
Tace "to zomuje munbar mutane zaune sunata jiran mu."
Ya Mujaheed yace "to mujenku." Yafad'a tareda d'aukar makullin motarsa asaman kujera,
"Mommyn Jos tace to kukuma Ina zaku?."
Ya Jabeer yace "ai mu zamu kaita, brother ban makullin."
Ya Mujaheed yamika masa makullin,
Ya Al'ameen yaruko hannunta sukayi gaba harsun Kai kafa.
Hassan da Husain dayanzu saukowarsu daga sama,suka karaso cikin parlour aguje suka rungume JUHAIFAH,suna fad'in Mamy "munata nimanki."
Juyowa tayi inda suke tace "Yauwa kuzo muje nima inata nemanku tun d'azu."
Husain yace
"Mamy wai cabon gida jaki koma inji Ummi kumawai bataye damu jaki tafiba."
Yy maganar Yana kallon Aunty Rukayya datafito rikesa mayafi ahannu,
JUHAIFAH tace "wasa Ummi take muku tare zamu tafi kunji."
tsalle sukashiga yi sunafad'in "yee jamu koma cabon gida."
Dasauri suka shige gaba.

Wasu motocine masu tarin yawa suka yi parking acan wajen get Dan bahalin shigowa gidan, farfajiyar gidan cike yake dam da motoci da mutane,
Motar Sadeeq nad'aya dagacikin motocin dasuka faka awaje,yafito daga cikin motar yashigo cikin gidan,

Yanashiga kuwa yahango su Zulaihat sunfito daga part in Ammee, duk dakuwa cewa darene Amma tako Ina hasken wuta ya haske,daga inda yake yarika yimusu hannu Allah yataima Aysha tahangoshi,tanunawa Zulaihat shi suka nufi inda yake.
Yace "Sannun kufa ya hidimar dai."
"Lfy lau wlh hirima kam gashinan yau kafarmu kamar zata sinke."
Cewar Zulaihat, Aysha tace "kedai bari yau innan sai mun Nemo angon Nan irin wanna wahalar damuke tayi musu shida matar tasa Amma ko godi babu."
Sadeeq yy dariya tareda fad'in "bari nawakil ceshi mun gode mun gode sosai sannun kufa da kokari."sukayi dariya,
Aysha tace "mu nabakin angon muke so."
Aransa yace "ilaiko angonnan zaimuku wuyar ganuwa.
Afilikuma cewa yy "yanxudai muje gamotar kucan."
Sukace to yajuya sukabi bayan sa.

Acan gunsu JUHAIFAH kuwa Ya Al'ameen narike da hannunta suka fito lokacin jama sunfara raguwa Dan wasu motocin dasuka zo walima sun d'ibi wasu daga cikin jama'ar suntafi dasu gidan amarya,
Ya Jabeer dasauri yanufi parking lot yashe motar Ya Mujaheed yafito da ita yazo kusada su,
Cikeda mamaki had'eda sha'awa mutane suke kallon su, yauga ikon Allah maza zasukai amarya,
Saikuma kallo yadawo kansu,
Ya Al'ameen yabud'e gidan baya yace "shiga Shalele."
Tashiga shima yashiga yazauna gefen ta,Ya Mujaheed shima yazaga d'aya gefen yashiga suka sata atsakiya, ihu Hassan da Husain suka saka suna fad'in "Mamy jamu piki."
Ya Al'ameen yace "kuje ga Ummin ku can zatashige waccan motar kuje kushiga."
Dasauri Ya Mujaheed yabud'e gefensa yace "zoku shiga."
Aiko dagudu sukazo suka shiga,Hassan yazauna kafar JUHAIFAH Husain Kuma yazauna kafar Ya Mujaheed.
Mommyn Jos Kuma tashiga gaba gefen Mai zaman banza,
Ya Jabeer yywa motar key tareda dannan hon Dan motocin dasuke gabansu su yi gaba suma susamu sufita.

Kodasuka fito waje,motarsu JUHAIFAH ce akasata atsakiya ahankali motocin suke tafiya,bakajin komai sai sautin karar motocin ketashi, suka nufi Maitama.
Suna isa unguwar sukad'au hanyar layin dazai sadasuda gidan Alj Tukur Shali,kasan cewar Nan za'afara kaita kafin washegari a'kaita d'akinta.
Koda suka iso kofar gidan maigadi yawan gale musu get,haka motocin sukarika shiga suna parking,duk tulin motocin Nan Amma kaf saida suka shige cikin gidan.

Mommyn Jos tabud'e motar tafito,Umma Rabi da goggo Hadiza dawasu kannen Ammee guda biyu suka matso jikin motar da JUHAIFAH take,Umma Rabi taleko cikin motar tana fad'in Al'ameen "sauko Dan tasamu tafito."
Kuka tafashe dashi tareda rirrike Ya Al'ameen d'in tana fad'in 'Ya Al'ameen kada kasauka nidan nafasa zaman auren mukoma gida kawai."takuma fashewa dawa kukan.
Ya Al'ameen cikin dauriya da ganin halin da kanwar tasa tashiga yanzu,yace "haba Shalele JUHAIFAH bamuyi haka dake bafa,kenan kinfasa farantawa Abban mu ran nasa Kenan?."
Tagirgiza Kai cikin muryar kuka tace "a'a nidai Ya Al'ameen bazan iya rabuwa daku bane."
Ya Al'ameen yace " wayafad'a Miki mun rabu bazaki Rika zuwa gidaba muma Kuma zamu Rika zuwa dubaki."
Tace "kullum zakurika zuwa?."
Shiru Ya Al'ameen yy,dasauri Ya Mujaheed yace "Eh kullum zamu Rika zuwa ammafa inkin Mana alkawarin Zakisa Abba farin ciki tahanyar Zama agidan mijin ki."
Tace "namuku alkawari."
Tace "Ya Jabeer inadai baka fasa bani ajiye kayan auren kaba."
Ya Jabeer yace "waneni ai yaza dole Shalele ce zata aje kayan aurennan."
Tayi murmushi tareda share hawayenta,
Ya Al'ameen yasauka itama razuro kafafunta kasa,Ya Mujaheed da Ya Jabeer ma suka fito,
Cikin zolaya Ya Jabeer yace "um su Shalele JUHAIFAH anzamo babba harda tarun kayan lefe."
Dariya tayi tareda mikamasa hannu suka tafa
Tamikawa Ya Al'ameen hannu shima suka tafa,Ya Mujaheed ma suka tafa,
Sukarika zolayarta wai tagirma yanzu harzata fara tarun lefe yanzu itacema yayan Jabeer d'in,
Itako dariya tarikayi wai Dan sunce yanzu itace yayar Ya Jabeer.
Umma Rabi tariko hannunta tareda Jan mayafinta tarufe fuskarta,Mommyn Jos tatsaya d'aya gefenta suka sata tsakiya,
Goggo Hadiza Kuma takamo hannun Hassan da Husain suka nufi cikin gidan,asannu tafara d'aga kafarta tayi takun yakai goma sai tatsaya cak tareda juyowa takalli yayun nata, har lokacin suna Nan tsaye jikin mota,jitayi kamar takoma gunsu,haka' suma sukaji kamar sud'auketa sumai data gida.
Umma Rabi ta janyota suka shige cikin katafaren parlour gidan,

Suna shiga aka fara feshesu da tura ruka had'eda rangad'a guda.
Akayi musu jagora zuwa d'akin' da'aka tanadawa amarya suka isa da ita ciki,Nan suka tadda Aysha da Zulaihat Umma Rabi tazaunar da ita bakin gado,suma suka zazzauna,mutane suka Rika shigowa suna daz'in Ina amaryar Ina amaryar,
Wasu Mata guda biyu farare kyawawa suka shigo Zahra nabiye dasu suka karaso cikin d'akin, d'aya matar tamaso kusa da JUHAIFAH tana fad'in "amarya bud'e idanunki nagani da 'akecewa wai kin fine kyau."
Zahra tace "Allah Aunty Na'ima tafiki kyau."
Wacce aka Kira da Na'ima tawaro ido tace "todai kice nafasa kashe auren nawa nazauna da habibina kawai,
tunda Wanda zan kashe dominsa yasami wacce tafini kyau shikenan nabar Miki shi."
Zahra tace "um yanzudai bakida bakin cewa bazai Sami matar data kaiki kyauba gadaishi Nan yasamo wacce tafikin ma."
Na'ima tace "um nifa banyarda ba inba tsoronba tabud'e fuskarta nagani Mana."
JUHAIFAH dai sun kuyar da kanta tadad'ayi acikin mayafinta.
Na'ima tazuge zip d'in Jakarta tazaro kud'i ta'aje kan cinyar JUHAIFAH tace "gashi nasiyi bakin saura Kuma kije kikuma amsar Mana kud'in d'an uwa,
Yauwa karkuma kiji dad'i Dan nace nabar Miki shi,har in natabbatar da bakifini kyauba tofa nafasa barin Miki shid'in."
Suka juya suka fita suna dariya.
Su goggo Hadiza ma dariya sukayi Dan sunfahimci abokiyar wasan su Zaharan ce.

Suna fita su Umma Rabi suka shiga yimata nasiha, daga bisani suka mike,goggo Hadiza tace "kuzo mutafi ko." Tafad'a tana dubansu Hassan dasuka rakub'e gifen JUHAIFAH,
Yaran suka fara kokarin yin kuka,
JUHAIFAH tace "Dan Allah goggo kubarsu anan."
Aunty Rukayya tayi saurin cewa "a'a JUHAIFAH bazai yuwu abarsu anan ba, kidai bari idan kk kwana biyu akai mikisu can gidan naki."
Raurau tayi da ido za'tayi kuka,
Mommyn Jos tace "abarsu anan d'in sukwana inyaso gobe saisu koma dasu Zulaihat."
Aunty Rukayya tace "toshikenan."
Suka fita sukabarta itada su Zulaihat,
Koda suka fita can suka tadda
Su Ya Al'ameen har lokacin suna tsaye jikin motarsu
Sadeeq yad'ibi su amotarsa,
Su Ya Al'ameen kuma suka shige mota jiki bakwari sukabar gidan.

Amasaukin amare kuwa bayan fitarsu Umma Rabi Aysha tamike taje tarufe kofar suka rage kayan jikin su,
Zulaihat tabud'e d'an madai daicin akwatin dasuka rukowa JUHAIFAH, taciro Mata doguwar rigar bacci,
Tace "JUHAIFAH ga rigar bacci kitub'e kayan nauyinnan haka kihuta,wanna sabuwar kunyar da'aka yafuta itama acire yanzu kowa yatafi saura marainan Dan gankinne suka rage."
Aysha tace "aikam kidai bud'e kanki Kisha iska."
Tacire mayafin kanta tana binsu da harara, Zulaihat tashe da dariya tanafad'an "har kincire kunyar kenan."
Komai batace musuba sai mikewa datayi tashige bathroom tawasa tareda yin alawala tafito tarama sallar da ake binta,
Suma alawalar sukayo sukazo sukayi sallah.
Tana idarwa tatub'e kasaka rigar baccin,ta isa bakin gado tagyarawa su Hassan kwan ciyarsu Wanda tun d'azu sukayi bacci,itama takwanta kusa dasu.

Bajimawa kuwa bacci yad'auketa,
Su Aysha ko Hira suka bud'e awaya da samarukan su,sai wajen karfe 12 kafin suka kwanta.
Kiran sallar asuba yatadata tamike tashiga bayi tayi alawala tafi tayi sallah Koda ta'idar tahayo gadon tashiga bubbuga su Aysha tana fad'in "da Alla kutashi da wanine Yace karkuyi bacci da wuri."
Zulaihat tagyara kwan ciyarta cikin muryar bacci tace "ko salla ba'a kiraba kikama tada mutane."
JUHAIFAH takuma d'aka Mata duka acinya tana fad'in "in ba sokike Rana tayi kafin kiyi sarrar bakam Kiran salla Kuma saina gobe."
Aysha kam tuni tadaddauri tamike tayo alawala tatada sallah,itama Zulaihat d'in tadaure tatashi.
JUHAIFAH tazauna bakin gadon har suka idar da salla sukazo suka sameta,zuwacan su Hassan suka farka takaisu bayi tayimu wanka tazo tamaida musu kayan data ciremusun,itama taje tayi wankan tashirya tsaf cikin riga da zani na atamfa bawani kwalliya tayiba Mai da fauda sai man baki kad'ai tashafa Amma tayi bala'in kyau,
Kafin gari yagama haske duk suka shirya tsaf dasu.


Zulaihat namakale da waya akunne tanata soyewa,Aysha da JUHAIFAH Kuma suna d'an tab'a Hira.
Akayi knocking na kofar dasauri JUHAIFAH tayanyo mayafinta tarufe fuskarta tareda kwanciya tabawa kofa baya................




08034690723




Mommyn Twins ce


🅿️12



JUHAIFAH tayi saurin janyo mayafinta tarufe fuskarta tareda Kwanciya tabawa kofa baya,
Aysha tamike taje tabud'e kofar,wasumata suka shigo d'aukeda kuloli harguda biyar suka direshi cikin d'akin',
Su Zulaihat suka gaishesu,
Suka amsa suna tanbayarsu "yakwanan bakunta.
Sukace "lfy lau. Sai suka juya suka fita zuwa can suka Kuma shigowa d'aukeda flas da cup da plt da cokula,suka aje sukafice tareda jamusu kofar,bayan fitan matan
Zulaihat takalli JUHAIFAH data wani dukun kune cikin mayafi sai taku kallon Aysha sai suka sheke da dari.
Zulaihat tace "ikon Allah ashedai JUHAIFAH kinada kunya wlh banyi zaton hakanba."
Mikewa zaune tayi tareda Jan mayafin yasauko kafad'arta
Harararsu tayi baki d'aya saitaja guntun tsaki,
Tajanyo Husain daketa faman nuna kulolin da akashigo dashin yana cewa "Mamy aci."
Tashafa cikin yaron Dan tasan zuwa yanzu sunfara Jin yunwa,Dan ko agidane ana idar da sallar asuba suke farawa da tea kafin gari yy haske sud'aura da Mai nauyi.
Tace dashi "zakaci?."
Tagyad'a Mata Kai alamar Eh,Kai tagirgiza sannan tadubi su Aysha daketa famar zolayarta tace "to banzaye marasa aikin yi kutashi kuhad'awa yara abun Kari."
Zulaihat tamike tana fad'in "Kai nimafa irin yaranne yasin dawuri nake karyawa."
Tasauka tashiga bod'e kulolin,wani irin masifaffen daddad'an kamshine yagarwaye d'akin'
Kowani kula nau'in abincin cikin sa dabanne,
tea tahad'a wa yaran tazuba musu chips a plt tadubesu tareda fad'in "to kusauko Nan kuci."
Suka sauko kasan tamikawa kowa nashi yafara ciki.
Zulaihat tace "Aysha in zuba Miki yanzu ko sai anjima."
Aysha tace "gaskiya yanzun zanci Nima irinta yaranne."
"Aikam Nima hakan take."
cewar Zulaihat,
Takalli JUHAIFAH tana cigaba dafad'in
"Ginbiyar kam nasan bayanzuba,Dan ko lokacin datayi godun hijira zuwa Jos sai rana tad'au zafi take baiwa cikinta hakkinsa."
JUHAIFAH tab'e baki tayi tareda kawar da kanta daga kallonsu.
Suna kamla break d'in suka had'e cup da plt d'in dasukayi amfani dashi guri guda
Suka koma sukaci gaba da hirarsu.

Sai wajen 11:30 kafin JUHAIFAH tacewa Aysha tazuba Mata abinci zataci, tana kammalawa takuma komawa gadon,
Wayar Aysha ce yy Kara alamar shigowar Kira takalli Zulaihat dake kusa da wayar tace "Dan Allah mikomin wayar."
Zulaihat tad'au wayar tana fad'in "ke mutumin kine Sadeeq, nifa bangane wani kallon kasa-kasa da kukeyiwa juna jiyannan bafa."
Aysha tace "Dan Allah bani wayar karkisa Kiran takatse."
Zulaihat Tamika Mata wayar tana fad'in "idan tayi wari maji."
Aysha tayi picking call d'in takoma tajin ginu dajikin pillow,tareda yin sallama,
Sadeeq dake biye dakiran ya Amsa sallamar' tareda fad'in "ranki shidad'e ya gajin zirga-zirgan jiyadai?."
Tace "um gashinan kam haryanzu bai gama sakemuba."
Yace "wayyo Allah ammadai Ina ba inda yake yimike ciwo gajiyar ce kawa?."
Tace "Eh ba inda yakemin ciwo gajiyar ce wai."
Yace "Kai harnaji hankalina yakwanta insha Allah zuwa anjima Zaki nimi gajiyarma kirasa idan kika koma gida,Amma Babu damuwa muma zasu rama Mana wahalarmu Nan bada jimawa bawa."
Murmushi tayi tareda rufe fuskarta,
Ab'an garensa shima murmushin yy sannan yace "bakice komai ba."
Tayi kasa da murya ahankali tace "um yaushe kenan?."
Yace "alokacin hidimar bikin mu."
Rufe fuskarta tayi datafin hannunta tana 'yar dariya kasa-kasa
Dasauri taciro wayar akunnenta takatse Kiran,tana cigaba da karamar dariyarta.
Zulaihat datun farin wayar nasu takafeta da ido ganin yanda take ta wani dariya da rurrufe ido sai itama tafashe da dariyar taredafad'in "kaji sabon shigar love."
Fad'awa tayi jikin Zulaihat tace "Kai haka abun yake da dad'i."
Zulaihat tace "ai ita soyayya tazarce zuma Zaki,idan kk fad'a cikin ta tofa mantar da komai take' Dan rufe ido gabad'aya take."
JUHAIFAH tabisu da ido tareda yimusu wani kollon shekeke,
Zulaihat tad'aga Mata gira tace "yes idan tazago kanki zakiyi bayani,Dan irinku mugun kamu take yimuku."
JUHAIFAH tace "Allah yasawake kudai kutafama dakuka d'aurawa kanku."
Zulaihat tace "Him wlh Ina mugun tausayin ki JUHAIFAH lokacin da soyayya za'tayi Miki dirar mikiya,Hhhh wayaga su JUHAIFAH anfad'a kogin love."
JUHAIFAH
Taharareta taredafad'in "kekika sani."
Aysha tace "gaskiya abun akwai dad'i Allah jiya bakuji yadda nayi bacci cikin Jin dad'in ba."
Dariya sukayi tareda tafawa.
JUHAIFAH kam ido tazuba musu tana sauraran hirar tasu wacce tad'aukeshi amatsayin shirme,
Dan ita batasan meye dad'in soyayya ba,sau d'aya tatab'a yinsa Kuma shimad'in tun tana aji biyar a primary School,dawani d'an ajinsu,
Kuma tunda tabar makarantar ma tashafe babinsa.


Ab'angaren MAHFUS kuwa tun jiya daya shige d'akinsa baikuma fitaba,koda lokacin sallar magriba datayi,yy alawala yatafi masallaci bai shigo gidanba harsaida yy sallar isha, Koda yashigo gidan ya'iske mutane cikin motoci nashirin zuwa d'auko Amarya,
Saiyaji kamar yakori mutanen Dan bakin ciki,yabita hanyar baya yashege d'akinsa.
Yana shiga yad'au makullin motarsa yafito,
Lokacinda yafito har motocin sun tafi,yanufi parking lot yashiga motarsa yaja yabar gidan.
Tunda yafita baidawo gidanba saida dare yy nisa sosai.yashige d'akinsa yanajan tsaki ganin yanda harlokacin hayaniyar mutane natashi acikin gidan.
Washegari ma tunda yafita sallar asuba yy zamansa amasallaci bai komo gidanba harsaida gari yyhaske,Koda yakoma d'akinsa bathroom yashiga yy wanka,yafito yashirya saf yad'au keyn motarsa yanufa parking lot yashiga motarsa yabar gidan.

Ab'an garensu JUHAIFAH kuwa sunan cikin d'akin' da akayi musu masauki,hirarsu sukacigaba dayi sallace kad'ai kitadasu kokuma cin abinci.
damisalin karfe biyar na yamma dukkaninsu sukakuma wanka,
Suka sake sabon shiga.wannan karon JUHAIFAH daguwar riga tasaka.

Acan gidan Abba kuwa, dawowar su Mommyn Jos Kenan daga gidan MAHFUS inda suka dad'a shiryawa JUHAIFAH kayanta dakuma akwatunanta dasuka tafi Mata dashi.
Suka baje a parlour kowa nafad'in albarkacin bakinsa gamida tsaruwan gidan MAHFUS ko ince JUHAIFAH d'n.
goggo Hadiza tace "Kai Masha Allah gidan JUHAIFAH kamar ba'a Nigeria yakeba,itakam saita fito waje tasan cewa a Nigeria take."
Mommyn Jos tace "kedai bari gidafa yatsarukam bakarya."
Ammee kam bud'e kunnuwanta tayi tana saurararsu, yayinda zuciyarta yacika da farin ciki,
Addu'ar zaman lfy tashiga yiwa d'iyar tata acikin zuciyarta.
Mommyn Jos tace yamma tayi yanzu yakamata ace su Zulaihat sudawo."
Tad'au wayarta tadanna numbern Zulaihat,
Zulaihat tad'au wayar taredayin sallama,
Mommyn Jos ta amsa tanafad'an "mekuke jira haryanzun baku dawoba?."
Zulaihat tace "Mommy fa bamurakata gidantaba tukun."
Mommyn Jos tace "a'a kudawo baga mijintaba shizai d'auki matarsa sutafi,kudai kudawo kada dare yy,Kuma kud'auko su Hassan da Husain kudawo dasu."
Zulaihat tace "to."
Tareda sauke wayar akunnen ta.
Ido JUHAIFAH takura mata, Zulaihat tafahimce kallon da takematan saita kawar da kanta.
Tadubi Aysha tace "wai mukoma gida yanzu kada dare yy."
Aysha tace "to,bari nakira Sadeeq dama yace idan zamu koma nakirasa sai yamaidamu."
Tad'au wayarta tareda lalub'o numbern Sadeeq,tadanna Kira.

Ab'angaren Sadeeq kuwa shigowarsa Kenan gidansu MAHFUS d'in yana
kokarin dai-daita parking,
Kiran Aysha yashigo wayarsa,
Koda yaga itace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login