Showing 27001 words to 30000 words out of 85666 words

Chapter 10 - BAZAWARA CE ITA COMPLETEHAUSA NOVELS BY .txt

wardrobe Tamika mata tana fad'in "kisaka ina zuwa".ta amshi kayan itakuma tafice,tamike asannu tashiga saka kayan bayan data saka takoma tazauna tareda rafka uban tagumi, talula duniyar tunani,har Mommyn Jos tashigo tadire plt d'in abinci gabanta bata saniba tazauna kusa da ita tareda dafa kafad'ar ta,d'an zabura tayi tasauke numfashi,
Mommyn Jos takura mata ido saitace "JUHAIFAH meke damun ki? Kuma dai daga gida kkfito dai ko?".
Afirgice tad'ago tana fad'in "Babu komai,Eh daga gida nafito".
Mommyn Jos tayi murmushi irin nasu na manya tace "akwai abunda ke damun ki JUHAIFAH Dan ni asanina ba JUHAIFAH Dana sani dacan ba bace agabana JUHAIFAH danasani dacan ban tab'a ganinta cikin irin wanna yanayinba".
sai tad'anyi shitu da zancen ta sanna taci gaba "JUHAIFAH meyasa bazaki yi hakuri kizauna agidan mijin kiba karki mancefa Sulaiman d'an uwan kine inada tabbacin wanna fitar nakima babu Wanda yasani, sanna Kuma wace irin mota kk shigo dazaki iso garinna awanna lokacin ko kwana kukayi kuna tafiyar?".
Shiru tayi batare da tace komai ba,
Tace "JUHAIFAH ina tanbayar ki kwana kukayi kuna tafiyar?".
Tagir giza kai alamar a'a,tace to "agarinna kk kwana?".
Saurin kawar da zancen tayi dafad'in "nifa Mommyn Jos bana son shi shima Kuma yasani Amma sai yarika zuwamin d'aki Kuma nafad'a masa yadaina zuwamin Amma yaki' shine jiya yashigo ina bacci kawai ya..shiru tayi tana wasa da 'yan yatsun ta batareda ta karasa maganar ba sai hawayen dayafara gan garo wa idonta,
Mommyn Jos ma ido takura mata aranta tace "kenan yazo da bukatarsa taki shine yamata nakarfi harya jimata ciwo.afili Kuma tace
"To inbanda abunki JUHAIFAH meye wani abun tada han kali anan ai kowata mace dakika gani gidan mijin ta ahaka take rayuwar ta idan kkyi hakuri sai kiga komai yawuce kibi kisaba abunki,Kuma abunda yasa kkga yake shiga miki d'aki Dan yasan shid'in mijin kine' lokacin da bai zama mijin kiba koyaje gidan ku kinga Yana shiga d'akin naki bare haryaje da wata bukatar sa? JUHAIFAH yakamata kinutsu kisan meyadace yanzu ace duk watannin dakikayi agidan sa Yana hakuri dake ahaka batareda yanimi hakkin saba' ace Rana d'aya yabukaci hakan kibiji re masa idan kk mutu awanna lokacin mezaki cewa uban giji?,kinsan girman hakkin miji akan matarsa kuwa?tomeye amfanin hakan yanimi hakkinsa kikaki yakuma biki da karfi yanzu bagashi an barki da jinya ba".

Wani irin kuka ne yataho mata lokacin da Mommyn Jos tafurta bagashi an barki da Jin yaba takifa kanta acinyar ta tana wani irin kuka mai tsuma rai "Allah kasakamin kada kabar wancan katon azzalumin haka daya tozar tani tozarci mafi muni arayuwa ta ko Ya Sulaiman dayake mijina beyimin irin abunda kayimin ba wlh bazan yafe makaba' sakayyata tundaga Nan duniya zata bika".tafad'a acikin ranta tareda Kuma kara sautin kukan ta,
Lallashin ta Mommyn Jos tarika yi dakyar tasamu tayi shiru Mommyn Jos ita duk azaton ta tuno yanda Sulaiman in yamatane dakuma zafin ciwon yasata kukan, haka tarika lallashin ta da bata baki harta samu tayi shiru tasata taci abincin data kawo matan,bayan tagama ci tace da ita takwanta tahuta'
Batabar d'akin ba harsan da taga bacci yad'au keta.


A, Abuja kuwa
ana idar da salla Sulaiman Yakomo gida direct bedroom d'inta yanufo Dan ganin yanda takwana Koda yashiga ya iske bata d'akin sai yy zoton tana bathroom ne Dan haka yajuya yatafi bedroom d'insa bai Kuma fitaba har saida gari yy haske sosai kasan cewar ranar Saturday ne Yana gida,Koda yafito dinning yanufa yaja kujera yazau na yashiga bud'e kulolin abin cin da Umma ta turo musu, Jim yy ganin babu alamar an tab'a abincin mikewa yy Yana fad'in "kenan batama fitoba bare taci abin cin.yatura kofarta yashiga waige-waige yashiga yi ganin bai gantaba yamatso jikin kofar bathroom yad'aura hannunsa da niyyar yin Knocking sai yaga kofarma abud'e take yy saurin tura kofar yashige ciki dasauri yajuya ganin bata'aciki yafito Yana fad'in "JUHAIFAH! JUHAIFAH!! JUHAIFAH!!! hankali tashe yanufi part d'in Umma Rabi tundaga bakin kofar yake kwad'a mata Kira haryashiga ciki,dasauri Umma Rabi tafito daga cikin d'aki tana fad'in "ina JUHAIFAHn take kk wanna kwad'a mata Kiran haka?".
"Umma bata nanne?ban ganta acikin d'akin tabane".
Yafad'a Yana kwaigen cikin parlourn,
Tace "a'a bata Nan tun jiya dakuka koma part d'inku bamukuma gamuwa ba,anyako kaduba dakyau kuwa? kodai tana band'aki ne".
Yace "Umma batanan ko ina naduba har cikin bathroom in ma nashiga bata ciki".
Tace "mudaije nagane wa idona da kai na Amma inane zataje da safiyar Nan".
Tayi gaba Yana biye da ita tana cigaba da fad'in "bakadai dubata da kyau ba Amma inane zataje da safiyar nan".
Koda suka shiga parlour Kiran sunanta tashiga yi har suka shige bedroom bata fasa Kiran sunan nataba,har bathroom tashiga taleka tafito, tako ina a part d'in saida tabi talelleka Amma Babu alamar ta, tadawo parlour tana maida numfashi ta kalli Sulaiman Wanda ke zaune yarafka uban tagumi tace "kai Sulaiman tun yaushe kafahim ci bata gidan?".
Yace " Umma yanzu Dana fito nashiga d'akin ta".
Shiru tayi Nan take abunda Abba yafad'a mata ranar daya kawo JUHAIFAH dakansa gidan yafad'o mata, dayake cewa "Rabi banga amfanin kiba acin gidan nan ace kina gidan har yarin yarnan tasa kafa tafita acewai baki saniba".
Takalli Sulaiman tana fad'in "zama bai kamaniba taso maza kakaini gidan yaya gara naje dakaina naduba ko tanan can".
Yamike suka fito dasauri tashiga part d'inta tad'auko mayafi tafito tashige mota yaja suka nufi gidan su JUHAIFAH,
Koda suka isa tafito acikin motar dasauri tanufi part d'in Abba Sulaiman yabiyo ta shima da sauri da sallama suka shiga parlour Ammee da Abba nazaune cikin parlour suka amsa sallamar suka karaso Umma Rabi tazauna saman kujera Sulaiman Kuma yazauna akasa Nan suka shiga gaisawa,bayan sun gama gai sawa Abba yakallesu yace "lafidai naganku da safennan?".
Umma Rabi tagyara zama sanna tace "Yaya d'azunne Sulaiman yashigo yake saidamin wai baiga JUHAIFAH ad'akin taba todai daya fad'amin ban yarda ba saida naje naduba ta dakaina kafin natab batar da batanan' kagafar ceni Yaya wlh duk wata kula inayi akanta Dan ganin bata Kuma sakafa tafita ba amma..saurin d'aga mata hannu Abba yy batareda yabari takarasa maganar ba Yace "ya'isa Rabi, tun yaushe tatafin?".
Sulaiman yace "Abba da safennan ne".
Abba yy shiru tareda tunani daban-daban aransa,Ammee kam hannu tashiga tafawa tana fad'in "kai jama'a wai yaushene 'yarnan tadawo hakane kam Ashe duk barazadar da akayi mata abanza saida takuma sa kafa tafita".
Abba yadubi Umma Rabi yace "kukoma gida za'a nemeta.
Umma Rabi tamike jiki bakwari shima Sulaiman ab'an garensa hakan take haka suka koma gida Babu walwala tattere dasu,


Abba yakira Ya Al'ameen yace yazo Yana niman shi batareda b'ata lokaciba Ya Al'ameen ya'amsa Kiran Abba Abba yadubesa yace..................



08034690723



Mommyn Twins ce


*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association




By
Rasheeda S Director



🅿️9


~Free~ ~page~




Abba yace "Al'ameen kaje kanimo Mamana Dan takuma fita ba'asan inda take ba."
Abba yy maganar cikin raunanenniyar murya,Mai nuna tsantsar damuwa da tashin hankali,
Ya Al'ameen yad'ago dasauri cikin kid'ima Yana fad'in "Abba takuma fita?to ina taje?."
Abba yace "shine yanzu nake son sani kaje kanimo inda take Amma kada kabuga waya a Yelwa yanzu harsai mun tabbatar da bata cikin garinnan."
Abba na kaiwa nan yamike yanufi d'akin sa.
cikin han zari Ya Al'ameen yamike yafita mota yashiga Mai gadi yabud'e masa get yafita,duk gidajen dayake zaton tanacan yaje Amma batanan, haka yagama yawon sa har yagaji Yakomo gida
Jiki bakwari
yashai dawa Abba,Abba yy shiru lokacin tashin hankalinsa yakuma tsananta haka kawai yakejin zuciyarsa nabugawa,tsoro yalullub'e zuciyarsa,tarasa tan tance wani irin yanayi yakeji acikin zuciyar tashi.
Shuru sukayi kowa da abunda yake sakawa aran sa,Ya Al'ameen yanisa yace "Abba wata kila yanzu ma Yelwa takuma zuwa dadai an tanbaye su ko tana can d'in."
Abba yace "a'a Al'ameen ba yanzu ba sai mun dad'a tabbatar da bata cikin garinnan kafin mukira mutanen Yalwan."
Ya Al'ameen yace "to shikena fatan mudai Allah yasa tana cikin koshin lfy."
Abba yace "Allah yasa."
Ya Al'ameen yamike yafita,
Zuciyarsa Babu dad'i kwata-kwata baimaga amfanin wannan aureba, gashinan kanwarsu mace tilo rayuwarta nakokarin salwanta.
Abu kamar wasa har yamma tayi,Babu wani labari.
Ammee tayi sallama d'akin Abba Yana zaune abakin gado kallo d'aya zakayi masa gane Yana cikin damuwa, ta'isa tazauna kusa dashi yad'ago Yana kallon ta,
itama ab'an garen ta hakan take saidai ita takanyi iya bakin kokarin ta wajen boye damuwar ta,
Tad'an kwakulo murmushi tace "barka da yamma Alhj."
numfashi yasauke tareda fad'in "yauwa."
Ammee tanisa tace "Alhj har yanzu ba'a sami labarin yarin yarnan bako?."
Abba yajinjina Kai cikeda damuwa
Yace "haryanzu babu wata labari, Amma kin kirawo kawayen kin danace kikira kitan baya ko tayi tagidan sun?."
Ammee
tace "duk kawaye na danasan natab'a zuwa da ita gidan su nakira natan bayesu bataje gurin suba."
Abba yace "to wad'an da baki kirasun ba bakya tunanin ko zata iya zuwa gurinsu?."
Ammee tace
"Mutum d'ayace Haj Kubura matar Alhj Tukur Shali Kuma kasan yanzu kawan cenmu da ita a'iya waya muke yinta ban tab'a zuwa da ita gidan ta ba, bance Kuma tasan gidan ba gaskiya,Amma ni inaganin mukira mutanen Yelwan mutan baye sun kawai da akan muzauna muyita kokonton ko tana can gara mutabbatar."
Abba yace "yanzu dakika ganni azau nennan nakira Hadiza nace mata taje taduba gidan Yaya Salihu Amma kar tasake tafad'a masa abunda ke faru yanzudai zaman jirar isarta nake."
"To Allah yasa muji alkhari." cewar Ammee Abba yace "amin."
Karar wayar Abba yasanyasu d'agowa dukan su dasauri,
ganin sunan Hadiza yabaiyana akan fuskar wayar yasa Abba saurin picking na call d'in,
Abba nakara wayar akunnen sa yace "Hadiza tana gidan Yayan ko?."
Gaggo Hadiza tace "wlh naje batanan na tanbayi batar Yaya Salihun ma tacemin wlh batazo ba Kuma nace mata Dan Allah kada tafad'a mishi takuma yimin alkawarin bazata fad'a mishi ba."

Shiru Abba yy tareda kashe wayar,dasauri Ammee tace "yadai Abban Ameen? tanacan d'in ko?."
Kallonta yy arau nane yace "bataje cand'in ba."
Ammee tace "innalillahi wa inna 'ilaihirraji'un
Allahumma ahjirni fi musibati."
muryar Ammee narawa tacigaba da fad'in Abban Ameen tsoro nakeji wlh inajin tsoro."
Abba cikin dakiya yace "in Sha Allahu Babu komai Allah zai tsareta aduk inda take."


Abba hankalin sa yatashi matuka 'yarsa mace d'aya tilo rayuwar ta nakokarin salwanta har yafara da nasanin yimata dole yad'auki duk laifin yad'aurawa kansa, Ya Mujaheed da Ya Jabeer baro gurin aikin su sukayi sukazo gida basuyi wata wataba suka baza cigiyarta, takafafin sadarwa irinsu gidajen radio gidan TV da mujallu da yanar gizo,
Zuwa yanzu labarin batar JUHAIFAH yazagaye ko ina, Koda Baba Salihu yasami labarin shiru yy batareda yace komai ba,
Abba kuwa na zaune da Shirin sa Dan yasan Baba Salihu shirun sama maganace.


Fitowarsa kenan daga bathroom d'aure da towel a kugun sa sai wata karama dake rike a hannunsa Yana tsame gashin kansa, ya isa gaban mirror yazauna yarataye towel d'in hannunsa agefen mirror shiru yy Yana sauraran cigiyar da ake acikin TV, asannu yajuyo yakurawa TV ido dai-dai lokacin aka hasko hoton ta zunbur yamike tsaye Yana cigaba da kallon hoton, ji yayi zuciyarsa nayi masa wani irin rad'ad'i cikin han zari ya isa gon TV yaka sheta gaba d'aya,tun ranarda yadawo gida zuciyarsa takasa barin sa yahuta aduk mintuna kalinan sai ya tuno yanayinda yasame ta lokacin da d'an fashinnan yy mata fyad'e, sai yarika ganin kamar alokacin abun yafaru,
Duk sanda yatunu kuwa saiyaji gaba d'aya kyamarta yalullub'e shi,haka yarika fama da zuciyarsa yayita kokarin yakace hakan azuciyar sa, har yad'an samu sassauci,
ganin ta nayanzu kuwa sai yakuma dawo masa da abun sabo afi azuciyarsa,
Afili yafurta "yamayar da ita Kazan ta!.
Yajuya da sauri yanufi wardrobe yabud'e yaciro kaya yasaka yad'auki makullin mota yafita yabar gidan gabad'aya..


A Jos kuwa
Yanzu jikin JUHAIFAH yayi sauki Dan bakaramin kula take samu agun Mommyn Jos ba, yanzu tafiyar ta yayi normal saidai duk wanda yasan ta Dazarar yaganta zai fahimci sauyin datayi, haskenta yaragu ga uban ramar datayi.
Zaune suke a d'aki JUHAIFAH da Mommyn Jos sai Zulaihat babban 'yar Mommyn Jos Hira suke asaka nin su, Zulaihat ko nata aikin latsa wayarta ido taware kan wayar sai kuma tamike zaune daga kwancen datake dasauri tace "Mommy kalla kigani ai wanna JUHAIFAH ce
Aketa pasting nata wai ana nemanta kallafa kigani ga hoton ta itace wlh."
dasauri Mommyn Jos takarb'i wayar tana kalla hoton da Zulaihat ke nuna Mata,
dasauri JUHAIFAH tamike tazo taleka wayar,
Mommyn Jos tace "tabbas itace sumhanallah wlh nayi ragon azanci da ban sanarwa Yaya da wuri ba, waiso nake JUHAIFAH tawarke tukun, nakuma mance da halin dazasu shiga lokacin dazasu gane batanan, mikomin wayata gatacan Zulaihat." tanuna mata inda wayar tata take.
Zulaihat Tamika mata wayar talalub'o number Abba,



su Abba suna zaune acikin parlour kamar kullum tun zuwansu Ya Mujaheed sai yazamo kullum suna tare acikin parlour, kamar masu zaman makoki,kwananin JUHAIFAH goma kenan suko gani suke kamar shekaru goma, fuskokin su kuwa Babu abunda yake nunawa sai tsantsar damuwa da tashin hankali,
Karar wayar Abba ne yasan yasu d'agowa gaba ki d'ayan su, Abba yad'au wayar tareda duba Mai Kiran nasa sunan Hauwa'u yabayyana afuskar wayar Abba yad'au ka tareda yin sallama,Mommyn Jos ta amsa tana fad'in "ina wuni Yaya."
Abba yace "lfy Lau yagida da yaran?."
Tace "duk muna lfy,
Yace "to madalla sai yanzu kk sami labarin b'arta Maman nawa? nayi takiran wayarki bata shiga."
Mommyn Jos tace "wlh Yaya wayar tawace tab'ata yau kwana biyu kenan dayin welcome back shiyasa' to ai muna ma tareda JUHAIFAH d'in
Wlh kwata-kwata nagama sha'afane bansanar dawuriba."
dasauri Abba yamike tsaye Yana fad'in "kuna tareda JUHAIFAH?."
Tace "Eh."
Abba yace "Alhmdllh.
Hayaniyar da parlour yakace me dashine yasa Abba sauke wayar yadakatar da Ya Jabeer daya mike nafad'in "brothers kutashi mutafi Jos."
Abba yace "a'a bayanzu da yamman Nan ba tunda Allah yasa munji inda take to sai mugode wa Allah daya bayyana mana ita yasa tafad'a hannun nagida Allah mun gode maka. murna gunsu yau ba'a magana har d'an wani karamar liyafa suka had'a asakanin su,Nan aka shiga shai dawa 'yan'uwa da abokan arziki. Sulaiman daya samu labarin yy farin ciki sosai haka Umma Rabi,Koda mutanen Yelwa suka Sami labarin suma sunyi murna sosai han kalinsu yakwan ta, koda labari yaiso kunnen Baba Salihu shima yaji dad'in lamarin dama ko sau d'aya bai tab'a Kiran Abba akan batun b'atar JUHAIFAH ba Dan bakaramin kullatar Abban yy ba,Baba Salihu aikawa yy yace Akira masa Goggo Hadiza Koda tazo yace mata "kitan bayi mijin ki idan Allah yakai mu gobe zamu tafi Abuja."
Goggo Hadiza tace "to Allah yakai mu."
Bayan tafiyar Goggo Hadiza Baba Salihu yakira Mommyn Jos awaya bayan sun gaisa yace "idan Allah yakaimu gobe akwai mitten dazamuyi na gaggawa ki tanbayi mijin ki sai muhad'u acan Abujan Amma kada kizo da JUHAIFAH sai bayan mitten d'in inyaso sai ta koma gida."
Mommyn Jos tace "to Yaya."
tayi Mamakin dataji Baba Salihu yace kada taje da JUHAIFAH sai ta sha-shan tar,
adaren naran tafara shiri

Washegari dasafe suka d'au hanyar Abuja Mommyn Jos tariga su isa kasan cewar tafiyar tasu tafi nata nisa Amma dake sammako sukayi sai isar tasu takusa zamo atare, suna shiga Abuja Baba Salihu yakira Umma Rabi yace "kuzo gidan Yahaya keda d'anki yanzunnan."
Umma Rabi saida taji gaban kirjinta yabuga jin abunda Baba Salihun yafad'a,
Saita amsa da toh.

isowar su gida yakaca me da murna musamman dasukaga Mommyn Jos sai sukayi zaton tareda da JUHAIFAH take,
Su Ya Mujaheed kam kasa hakuri sukayi suka shiga tan bayarta ina Shalele JUHAIFAH, dariya kad'ai tabisu dashi batareda tabasu amsa ba, koda suka matsa mata sai cemusu tayi "tana hanya.ana cikin haka su Umma Rabi suka shigo itada Sulaiman Nan parlourn yakacame da gaishe-gaishe da jajan tawa juna had'eda taya juna murnan bayyanar JUHAIFAH.
Aunty Rukayya da Aunty Nuwaira suka shiga kiching d'in Ammee suka shiga kokarin had'a abincin da ba'i zasuci batareda bata lokaci ba suka had'a lafiyayyen abinci, suka d'auko suka direshi a parlour suka zubawa kowa suka kaiwa Baba Salihu da Abba nasu a can parlourn Abba,
Bayan sun gaggama cin abin cin kowa yatashi danyin sallar azahar su Ya Al'ameen dasu Abba suka wuce masallaci,
su Aunty Nuwaira suka tafi part d'in su.
Koda aka idar da sallah su Ya Al'ameen suka shigo atareda da su Abba,
Baba Salihu yakalli su Ya Mujaheed yace
"kutashi kufita zamuyi magana."
Ya Jabeer yy kasa da murya yace "ashedai hali nanan."
Ya Al'ameen yad'an dun gureshi Dan yasan Baba Salihu kun nensa da iya Jin magana komai kan kancin sa,
Ya Al'ameen yamike Yana fad'in "kutashi muje"
suka mike harda Sulaiman,
"A'a ban dakai."
cewar Baba Salihu Yana duban Sulaiman,
Sulaiman yace "ni?."
Baba Salihu yace "Eh kai."
Ahankali yakoma yazauna yayinda zuciyarsa ke bugawa da karfi, sukuma suka fita.

Shiru parlourn yadauka Baba Salihu yy gyaran murya tareda yin salati wa Annabi S.A.W. kana yad'aura dafad'in "Alhmdllh Allah mun gode maka daka nuna mana wanna rana muna masu rai da lfy, bakomai ne yasani taraku anan ba saidun inaso mugyara wata b'arakar datake ta yawo sakanin mu,
Kuma in Sha Allahu yau Zan kawo karshenta,yakallesu d'aya bayan d'aya yace "meyasa kuka fiye son kanka
dayawa haka?,
shin bakwa tunani yin hakan zai iya jefa wani cikin matsala ko damuwa?.
Kallon junansu sukayi kowa yafara shiga tai tayin sa dan sun tabbata muhimmin magana ce,
Baba Salihu yaci gaba "son kanku da kuka nuna shiya jefa d'iyarku cikin damuwa taketa gudu takasa zama guri guda,
waiku kunyi hakanne saboda kara dankon zumunci baku sani ba so kuke kubada kofa wajen ruguje war zumun cin,
waishin sai tahanyar had'a aure ne kad'ai zumun ci ke karuwa
ko dad'a dun kulewa guri guda?
Wato a She baza ku iya cikawa mahai fanmu burin su haka kawai ba har sai kun b'ullo dawata tsigar nadaban?
shin ashe zumun cin' namu naboge ne kawai yanzunne muke kokarin had'ata dole dakarfi tahanyar had'a 'ya'yan mu aure."
yadubi Abba yaci gaba da fad'in "yanzu kai hakan yy maka dad'i d'iyarka tarika yawo akan titi saboda wata dalilin ka dabata da ma'ana,
baka tunanin idan hakan yaci gaba da faruwa zata iya fad'awa mummunar hali kota fad'a hannun miyagun mutane kokuma
tashiga duniyar ma baki d'aya?
shin hakan gata kayi mata koko son kanka kanuna?."
Shiru Abba yy tareda sunkuyar da kansa kasa, yynda maganar Baba Salihun ke yimasa yawo acikin kwa-kwal.


Baba Salihu
Yamaida dubansa ga Umma Rabi yace
"Rabi."
tayi saurin dawowa daga duniyar tunanin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login