Showing 66001 words to 69000 words out of 85666 words
Chapter 23 - BAZAWARA CE ITA COMPLETEHAUSA NOVELS BY .txt
yahad'esu da jikin motar yadanne cikin
kasa da murya yace
"Doka da nuna ikona akanki ba'a iya cikin gidana kad'ai yatsaya ba aduk inda kk afad'in duniyar Nan,idan da kinayin abunda kkga dama to yanzu baki'isa kiyishiba Dan yanzu da Aurena akanki Baki Isa kirika sa wad'annan kayan kina yawo dasu harki Rika fitowa wad'ancan gardayen suna ganin kiba."
Yanuna ma'aitakan gidan,
Saikuma yasaki hannun ta Yana bin jikinta da kallo asannu yad'aga hannunsa yad'an janye mayafin data rufa jikinta dai dai sakiyar kirjinta nonuwanta ta sama duk abud'e suke yakai hannu yana kokarin sau kewa kansu saita...............
Mommyn Twins ce
🅿️27
Saita ture hannunsa tazame jikinta tagefe tafita daga inda yamatse tan tayi saurin masawa can gefe sai Kuma tajuya dasauri tanufi ciki,aranta take fad'in duk maza 'yan iskane.
Asannu yajuya yabi bayanta da kallo rumtsa idanunsa yy da karfe yakoma yajin Ginu dajikin mota asannu yabud'e idanunsa yamike daga Jin ginen dayake yashige motar yy hon Maigadi yabud'e Masa get cikin sanyin jiki yafice agidan.
Washegari da safe yakuma tafiya gidan yatura Mai gadi yakira Masa ita Taki fita Dan kansa daya gaji yaja motarsa yakoma gida direct d'akin Mommy yanufa tana zaune bakin gada yashigo d'akin da sallama ta amsa, yakaraso cikin d'akin yazauna kusa da'ita yace "barka da safiya Mommy."
Tace "yauwa."
Tadubesa cikin kulawa tace "Son kayi breakfast kuwa? Tun d'azu nashirya maka yana can Kan dinning".
"Banajin yunwa." Yafad'a atakaice, sai yajuyo yana fuskantar Mommyn yace "Mommy kice Hafsat tadawo dan ni ban Bata izinin fitaba ban yarda ba."
Shiru
Mommy tayi batareda tace komai ba ganin Mommy tayi shiru saiya mike yafita,
Bin bayansa tayi da kallo a'yan kwanakin Nan duk yasauya sarai tasan Yana zuwa gidansu JUHAIFAH taji dad'in hakan bakad'an ba. yakoma d'akinsa kwanciya yy yad'au wayarsa yakira layinta har alokacin Yana kulle, saiya mike dasauri yasauko agadon yafito daga cikin d'akin yanufi d'akin mommy,
tana zaune a'inda yabarta kalonsa tayi ganin yanzu fitarsa yasake shigowa d'akin.
yajinginu da jikin garu yahard'e kafafunsa,
d'agowa Mommy tayi da zummar yimasa magana sai yarigata
yace "mommy kisa tadawo mommy kiyi magana dan Allah
kisa Hafsat tadawo mommy kidainayin shurunnan
Dan Allah mommy kiyi magana mommy kice wani abu".
kallonsa tayi sai kuma tamai da kallonta kan wayarta tafara lasawa tace "to mekakeso nace dakai MAHFUS? nifa bani nace tatafiba bare kuma nace tadawo
ita tayi ra'ayin kanta tatafi,
bani dawani ikon dazance tadawo nibani da wani abunda zance."
yace "
Mommy bakida ikon dazakiyi magana kullum sai naje gidansu duk sanda naje bata fitowa nasan idan kky magana zata dawo." damamaki mommy take kallonsa bakaramin dad'in jin hakan tayiba aranta,
Tabbas yanzu burinta yacika tunda har yatsaya gabanta yake fad'a mata wanna maganar
Da iya gaskiyarsa,
sai kuma tabasar tace "to tunda bata fitowa basaika bartaba."
da sauri yace "what! mommy da auren nawa akanta zakice nabarta." tace "to tunda bazaka bartaba nibansan yanda zanyiba ni banada wani abunda zan iyayi."
shiru yy saikuma yajuya cikin hanzari yabar d'akin.
'yar karamar dariya Mommy tayi tace "ba duka ba zagi ba mummunar magana jiki magayi, abunda nake gani cikin idon ka game da'ita shikad'ai ya'ishe ka wannan Kuma shine hukun cinka."
Takuma yin murmushi tareda girgiza Kai.
Koda yakoma bedroom insa makullin mota yad'auka yafita yana fita direct yayi airport dan dama jiya yashirya akan zaibar kasar gaba d'aya garin ta'isheshi, yanazuwa airport yakira direba yace yazo airport yad'au mota.
Koda Mommy tawayi gari bata gansaba sai takirasa awaya dataji numbern sa na Nigeria bai shigaba saitayi murmushi Dan
sanin dabbas saiya bar kasar tunda bata nuna damuwa
akan lamarinba,
layin kasar datakeda tabbacin Yana can takira
bugu biyu yad'aga
Bayan sun gaisa tace "Son yaushe zaka dawo?."
Yace "Babu Rana."
Tace "to Allah yanuna Mana ranar."
Takashe wayar.
Aban JUHAIFAH kuwa kwance take akan gadon
dawaya kare a kunnenta tana fad'in "wlhy ni bantab'a ganin marakunyan amarya irinkiba
wai dakanki kike yayata aurenki,
waihar kinafad'a wa Ya Al'ameen date in Auren d'azu inaji kina fad'a masa ai kai wallahi Allah yashiryeki Zulaihat bakida kunya."
Zulaihat da ke biye da wayar tace
"iye dan nafad'i date in Aurena shine sabon Abu wlhy zanfada ni wlhy baki masan yanda namasu ayi ayi aurennan ba,
ai danaso natai makawa goron yayan kinnan Jabeer
naso nataimaka masa shiyayiwa kansa ai nace ya'aje bindiga muyi aure yaki dayanzu nataimaka masa."
JUHAIFAH tace "ya taima kamiki dai wai wani kitaimaka mishi ai saidai shi ya taimaka miki Dan duk ba sa'annin aurenki cikinsu."
Zulaihat tace
"Tab ai gara d'aya daga cikinsuma Al'ameen ko Mujaheed dai danwanna goron naga halaman ba aure zaiyi nankusaba saidai yakare da rikon bindiga,
nikuma banason mai mata Mujaheed da Al'ameen suna da mata dama Mujaheed ne naso natai
makamai sainaga bazan iya da matarsa Nuwaira ba."
JUHAIFAH tace kai gaskiya bakida kunya dasunan su zaki ringa kiransu bazakice dasu yayaba."
tace "Allah yasawake kije ki tanbayesu suma sunsan duk na girme musu."
JUHAIFAH tace "toma mezasuyi dake saidai kijecan wanda kikasamu d'in yalallaba ayi Auren,keni kinma dameni sai anjima."
Zulaihat tayi saurin cewa
"Tun ana saura satifa zakuzo keda Aysha Dan mutsara yanda shagulgulan bikin zasu gudana,yanzu zan turo muku ashoben daza'ayi saiku siya kinfasan saura kwana 22 ne yanzu bb wani lokaci sosai."
JUHAIFAH dai kashe wayar tayi batareda tabata amsaba.
Kamar yadda Zulaihat tafad'awa JUHAIFAH kuwa haka akayi tana kashe wayar ta tutturo Mata da kalar ashoben dazasuyi har kala biyar,da yamma JUHAIFAH tashirya taje gidansu Aysha tanuna Mata kalar ankon.
Acikin 'yan kwananin suka gama siyayyan kayakin harda d'inki.
★★★★★★★★
Bayan sati uku
★★★★★★★★
Hakan yy dai-dai da saura kwana d'aya d'aurin Auren Zulaihat.
Su Ammee nahango tsaye jikin mota Abba yakalli Ammee yace "wai me yarinyar Nan take da har yanzu bata fitoba? Wani irin tafiya ce zakuyi yanzufa karfe 1 harda Rabi idan bata gamaba kutafi gobe mazo da ita."
Ammee tadubi Aysha da yanzu shigowar ta tace
"Aysha je maza ki kirawo ta in bata gamaba mutafi tazo da Abban gobe."
Aysha ta'amsa da tom tanufi part in Ya Al'ameen tana shiga tahangota tana sauka daga step sai tatsaya takaraso suka fito tare.
Lokacin dasuka fito har su Ammee da Aunty Rukayya sun shige mota,
Hassan da Hussain suna gaba suna ganinta sukace Sam saidai tashigo gaban suzauna tare sabida yaran tashiga Dan ita bata fiye son zaman gaban mota ba, Aysha tashiga baya gurinsu Ammee direba yaja Abba da Ya Al'ameen suna d'aga musu hannu su sai gobe zasuzo d'aurin Aure.
Kasan cewar basu tashi da wuriba Basu suka isa cikin garin Jos ba sai bayan sallar magriba,
Agajiye suka iso gidan Mommyn Jos bayan sunyi sallah dasu cin abinci dasauran su akafara gaishe-gaishe da 'yan uwa acan suka Sami mutanen Yalwa harsun rigada sun iso,
Tuni JUHAIFAH da Aysha sukayi d'akin amarya Zulaihat Nan suka tadda Ameera da Walida 'ya'yan Baba Salihu suka bud'e shafin Hira,hirarsu sukai sosai kafin sukayi bacci.
Washegari bayan sallar juha'a aka d'aura Auren Zulaihat da angonta Mansur.
bayan shagulgular biki da'akayisu da Rana har kala biyu damisalin karfe takwas nadare Kuma aka tsara yin party awannan lokaci.
Amare sun Sha kwalliya sai sheki suke duk Wanda kagansa fa tabarakallah Masha Allah, can nahango JUHAIFAH wacce take zaune can gefe idan kaganta zaka rantse itace Amaryar gaba d'aya tahaska su.
Babu jimawa motocin dazasu d'ibi mutane zuwa gun party suka iso kofar gidan,
Moton ango da amarya itace gaba saina kawaye sauran Kuma na 'yan'uwa da abokan Arziki.
JUHAIFAH dai kin shiga motar kawaye tayi bb yanda ba'ayi da'itaba tace ita bazata shigaba sunzo da motarsu a motarsu zata tafi,
tace direba yakaisu itada Aunty Aysha sukabi bayan sauran motocin.
Taro yy taro hall yacika makil da mutane bakajin komai sai sautin kid'aya
'yanmata da samari sai Kai komo suke.
Batareda b'ata lokaciba akafara gudanar da biki MC yagayyato amarya da ango suka fito fili sukad'an girgije bayan amarya da ango sun koma mazau ninsu sai yakuma gayyato kawayen amarya suka fito fili JUHAIFAH kuwa ko kallo Basu ishetaba Zulaihat tanata yimata alama da hannu akan tatashi tafito filin harara ta dalla Mata takawar da kanta daga kallonta.
wayarta ce tafara diri acikin jaka tayi saurin zuge zip in jakar taciroshi tad'aga wayar dazummar takaishi kunnen ta,karaf idanunta yasauka akan shi daidai lokacinda suka shigo hall in, dasauri tayi kasa da wayar tareda bud'e idanunta dakyau akan ahi,
Karaf kuwa idanunsu yahad'u da juna cikin mmk suke kallon junansu ko wannensu Yana Mamakin yadda akayi d'ayansu yazo nan,
Tamike tsaye cikeda b'acin Rai Dan ita atunaninta biyota yy Nan inma.
Dasauri ango yamike Yana washe Baki yasauko daga mazauninsa yazo inda su Sadeeq da MAHFUS suke yamika musu hannu suka tafa Yana fad'in "ashedai zakuzo da har nacire Rai da zuwan ku."
Sadeeq yace "Eh wlh bamu tashi dawuri bane ai da tuntune mun iso."
Cikin Jin dad'in ganinsu Mansur yaruko hannun MAHFUS Wanda gabad'aya hankalinsa baya kansu yace "mukarasa ciki."
Yafad'a Yana dariya sai lokacin MAHFUS yamaida hankalin sa gareshi.
Cikin hanzari JUHAIFAH tazaga tabayan gujeru tabi tabayansu batareda yagantaba tafice a Hall d'in,
Tana fita taga direban su tsaye dasauri tanufi inda motar take tashige ciki dasauri direba yabi bayanta ganin tashige cikin motar sai shima yashiga
Tace "kamaidani gidan damuka baro yanzunnan yace "to"
Cikin hanzari yaja motar suka bar gurin.
Yad'ago kansa da ga kallon Mansur yamayar inda yaganta d'azu sai bai gantaba waige waige yashiga yi yarika juya gefe da gefen sa Nan ma bb alamarta.
Aysha kuwa ganin tanda JUHAIFAH tafita da sauri yasata mikewa tabi bayan ta turus tayi ganinsu Sadeeq tsaye Baki tabud'e tana kallon Sadeeq shima bakin yabud'e yake kallon ta
Sadeeq yayi saurin cewa "meyaka woki Nan?".
Itama cewa tayi "meyakawo ka nan?".
dariya Sadeeq yy Jin tamayar Masa da tanbayar da yy Mata yace "ai bikin danake cemiki na abokin mu zamu Jos innan to ai wanna bikin ne."
Tace "toh lallai kam to ai bikin Zulaihat ne muma Kuma shi mukazo."
Sadeeq yakuma washe Baki yace "dagaske dama Zulaihat ne ka'aura Mansur."
Yafad'a Yana duban Mansur,
Mansur yy murmushi tareda girgiza Kai yace "itace dama ka santane?."
Sadeeq yace "ai 'yar uwan matan Man ce."
Mansur yadad'a rike hannun MAHFUS yace "Kai Amma abun yy dad'i." MAHFUS shidai gabad'aya hankalinsa baya kansu tunani yake to Ina tashiga ne. Aysha tajuya gefe takalli MAHFUS sai kuma tajuya gafe da gefen ta Sadeeq yace "yadai."
Yafad'a Yana duban Aysha tace"JUHAIFAH nabiyo yanzu naga fitanta shine nataso nabi bayanta harma tafita bansan ida zataba."
Dadauri MAHFUS yajuyo Yana kallon Aysha da fuskar tanbaya yace "tafita?".
Aysha ta gyad'a kanta alamar Eh cikin hanzari yajuya zai fita Sadeeq yy saurin cewa "ina kuma zaka?."
Kansa yashafa saiya koma yagyara tsayuwar sa.
Mansur yy musu jagora zuwa mazaunin da'aka tanada domin su suka zauna Nan aka cigaba da gudanar da party.
Gabad'aya hankalin MAHFUS Baya gurin shidai Yana zaune ne kawai Amma hankalinsa na kanta dakuma inda tatafi awannan daren agogon dake d'aure ahannunsa yakalla karfe 11 sai yamike tsaye ya Sadeeq yad'ago Yana tan bayarsa Ina zashi batareda yabashi amsaba yasauko daga mazaunin su yafice a Hall in.
Yashiga motar sa da yy niyyar acikin Daren sukoma Amma tunda yaganta saiya sauya ra'ayi yaja motar yanufi hotel inda suka sauka d'azu shigowarsu garin,
Sadeeq ganin MAHFUS yafita batareda yace dashi komaiba sai yakirasa awaya sai cemasa yy yasamesa a hotel.
Ba'a gama party ba sai wajen karfe biyun dare aka kwashi amarya da kawayenta akayi dasu gidan amarya.
Ab'angaren JUHAIFAH kuwa suna isa gida tashige d'aki tayi Kwan ciyarta washegari dasafe Aysha tahayo adaidaita yakawota gidan Mommyn Jos Koda ta'iso ad'aki ta iske JUHAIFAH tana kwance takaraso tazauna gefen ta tace
"Kai JUHAIFAH meyasa kk tafi jiya?."
JUHAIFAH tace "Ina ruwanki." Aysha tace "um abunda ba ruwanka dad'in ji."
Tafad'a tana kunshe dariyarta sarai tafahimci abunda yasa JUHAIFAH gudu jiya agun party.
Zulaihat takira wayar ta tarika had'ata da Allah akan tazo tace ita bb inda zata bacci zatayi dakyardai zulaihat tasamu tashawo kanta ta Amin ce zataje gidan nata.
JUHAIFAH tamike tashige bathroom wanka tayi sannan tafito tana fita Aysha ma tashiga tayi wankan,
JUHAIFAH tashirya cikin wani doguwar riga pink tayi simple makeup afuskarta sai gyalen rigar tasakashi akanta ta tattaroshi tasakoshi tagaba Masha Allah bakaramin kyau tayiba tazauna bakin gado tana latsa wayar ta, Aysha nagama shiri suka fito takarb'i makullin mota agun direba tashiga mazaunin direba Aysha ma tashiga gaba, JUHAIFAH taja su d'au hanyar unguwar suna Isa unguwar Aysha tarika nuna Mata hanyar dazatabi kasan cewar ita tasan gidan Koda suka iso get in gidan ganin motoci pake akofar gidan sai itama tasamu guri tafaka motar agun suka fito.
Tana sanya kafarta cikin gidan tayi tozali dawasu shinfi d'ad'd'iyar carpet manya guda biyu Masu matukar laushi, d'ayan angone da abokansa zaune akai d'ayan Kuma amaryace da kawayenta, gabad'aya hankalin jama'ar gun maza da Mata yadawo kansu
Jitayi kamar tajuya takoma ganin yanda mutane ke kallon su Aysha kuwa ganin haka saita ruko hannunta Dan tasan hali sarai saita iya juyawa takoma,
Asannu tarika d'aga kafarta harsuka karasa Kan carpet inda Mata suke zaune,duk jikinta ad'aure yake ita bata iya sakewa cikin jama'a irin haka,hakan Kuma wani al'adane dawasu daga cikin 'yan garin suke yi aduk sanda sukayi aure alokacinne abokan ango zasu siyi bakin amarya kowani aboki zai nuna bajin tarsa tahanyar zuba kud'i Masu yawa kafin kawaye zasu d'iba daganan Kuma saisu maida amarya d'akinta.itakuwa JUHAIFAH kwata-kwata zaman bai mataba.
turo kofar get akayi Nan kowa Yakima maida dubansa zuwaga kofar akasin JUHAIFAH da idanunta kekasa,
Jitayi wata dake kusa da'ita na fad'in "Kai gaskiya wanna gayen yahad'u." d'aya nakusa da'ita tace "d'ayan ba dogun cikin."
Asannu tad'ago kanta Dan ganin Wanda suketa kod'awan,
D'an zabura tayi ganinshi tsaye yahard'e hannu akirji yayinda yakeyiwa wani dayake yimasa magana murmushi.
Hannun Aysha tarike cikin kasa da murya tace
"Muje kinunamin d'akin Zulaihat fisari nakeji."
Aysha tace to suka mike suna shiga parlourn JUHAIFAH tace "to kikoma idan nagama zanzo."
Aysha nafita takarasa cikin parlourn tahaye Kan kujera takwanta tareda lumshe idanunta.
Kamar amafarki ta shaki kamshin turarensa dafda hancin ta,ahan Kali tabud'e idanunta cikin hanzari tawaro su kan fuskarsa daya kawoshi daf da fuskarta lokacin yasauke lip insa Kan goshin ta, cikin hanzari tamike zaune asannu yazauna gefenta daf da ita ido yakafeta da shi ahan Kali yafurta
"Yabaki sha'awa ko? har gashi kin kwanta cikin sa saidai Kuma banaki bane na meshine dole zuwa anjima kibar Mata gidan ta, kicire abunda kk ji acikin ranki nadama ace acikin gidanki kike kwance bana wataba."
Mikewa tayi tsaye tana yimasa kallon waye kai,
Cikin tsiwa had'eda masifa tace "wai meyasa kk niman takurawa rayuwa ta ne kam, meye gaminka dani? Dahar zaka Rika bibiyata".
Saikuma tajuya takarewa parlourn kallo sannan tamaida kallon ta kansa tace
"Inawani abun burgewa acikinsa da har kk saran hasashen ka zai zamo gaskiya, na tabbata kasan inda nake rayuwa bare kace wani kyalekyalen Nan zai dameni."
Murmushin gefen Baki yy yamiko hannu yafizgota tafad'o jikinsa yazagayeta da hannunsa
Yayinda fuskarsu ke daf da juna yace
"Aduk inda kk rayuwa Koda kuwa akan zinare kk rayuwarki dole hakan kkjishi acikin ranki yanzunnan."
Baki tabud'e za'tayi maga sai yy saurin sauke bakinsa kan nata ya..............
Mommyn Twins ce
🅿️28
Yadad'a gyara zaman sa sosai Saida yatsotsi bakinta na tsawon second biyar kafin yazare bakinsa Yana kallon fuskarta, tureshi tashiga yi tana kokarin mikewa ajikin sa
Shiko dad'a rungumota yy sosai yaman nata da jikinsa asannu yamosa lips insa yace
"Ban amince da fita da d'an wanna karamar mayafin ba dukda dai kayan Basu wani matse jikin ki sun fidda surar kiba, duk wanda yaganki da'irin wanna shigar zaiyi tunanin bakida aure,idan Kuma yafahim ci ke matar aurece to zai kalli mijinki amatsayin mara tunani daga yau banyarda kisake fita batareda hijjab ba wanna umurni nake Baki daga Kan yau hijjab Zaki ringa sawa dannin ba sakaran namiji bane nasan abunda nake bazai yuwu da Aurena kanki kirika yimin wasa dashiba."
Harararsa tayi tareda murgud'a Masa baki
Tace "da Allah sakeni malam karikeni kanayimin bitan abunda bazai zauna cikin kwakwal wata ba Kaya nawane haka jikin ma nawane duk sanda naga Daman sanu zan sa."
Hannunsa dake bayanta yaciro guda d'aya yasunsa biyu yad'aura Kan bakinta yakomo lips inta da yasun nasa yahad'a lips in yad'an matse su.
Juya Kai tayi alamar Jin zafin yadda yy matan taci gaba da yunkurin mikewa tana fad'in
"Allah idan kasake matsemin Baki bayarda zanyi ba kasake yimin mugunta kagani." maida d'aya hannunsa yy bayanta yariketa sosai tayadda bazata iye mikewa ajikin saba,
Jin abunda tafad'a saiya kuma d'ago hannun zaikuma kaiwa bakin nata Yana fad'in
"Bari nafasa bakin naga abunda zakiyi."
dasauri takifa fuskarta akirjinsa hannu yasaka Yana kokarin d'ago kanta,
Dad'a cusa fuskarta tayi cikin kirjinsa tana goga fuskar nata Kan shinfi d'ad'd'en kirjinsa,
Hakan datakeyi kuwa yasanyasa shiga wani irin yanayi duk juya Kan dazatayi sai yaji wani irin Abu yatsarga Masa asannu yy kasa da hannunsa yamaidashi bayanta yadad'a had'ata da jikinsa sosai, yakwantar da kansa jikin kujera asannu yalumshe idanunsa.
Acan waje kuwa Sadeeq yaga lokacin shigewarsa parlourn gashi yafi 10min baiga fitowar Saba sanin halin mutumin nasa yanada tabbacin har idan yasami hanya agun zai'iya tafiya yabarsa anan,
Sai yy saurin nufar hanyar dayaga yabi,
Mansur ma yaga shige warsa tabaya shikuma atunaninsa ko wani abun yake bukata sai yamike shima atare suka isa bakin kafar parlourn
Suna kusa kansu cikin parlourn sai sukaja suka tsaya Nan bakin kofar kallon juna Mansur da Sadeeq sukayi sai kuma suka Kuma kallon inda suke ido Sadeeq yawaro cikeda mamakin ganin abokin nasa rungume da wacce yafi tsana arayuwarsa Kuma washe Baki yy saikuma abun yabashi dariya da matukar shauki abun yamugun burgeshi bakad'an ba, yaji dad'in ganin abokin nasa ahaka yanada tabbacin yanzu abokin nasa yafara samun nutsuwa a'yan kwanakinnan yaga sauyi gameda MAHFUS in sai gashi Kuma yau Yakuma ganin wani babban sauyin.
Dariyace taso kufce wa Sadeeq ganin yadda MAHFUS yawani lumshe idanu gadukkan alamu Yana mugun Jin dad'in yanayin dasuke ciki,Sadeeq dariyace sosai takamashi yana tunanin abokin nasa da kalamansa na baya kai ikon Allah ashedai mace zata iya sauya MAHFUS.
Mansur yariko hannun Sadeeq yymasa alama dasufeta Dan kada su katse musu Jin dad'in yanayin dasuke ciki yanzu shiko Sadeeq duk toshe bakin dayake Saida dariya yasub'uce Masa,
Ahankali yabud'e idanunsa yasauke akansu cikin hanzari itama tad'ago kanta dasauri tamike ajikinsa shima saiya saketa tamike tsaye cikin