Showing 42001 words to 45000 words out of 85666 words
Chapter 15 - BAZAWARA CE ITA COMPLETEHAUSA NOVELS BY .txt
jiya dazasuzo Mommy tasa Zahara takai Mata akwatinta da basket d'in motorsa,
"wato shine ajemin kayan agun inyaso koma me yasamesa shi baida asara tunda yasan wannan ba' akwatin daya siyan bane."
Tafad'a afile,tayi kwafa tareda juyawa tanufi kofa tabude tafito cikin parlour,lumshe idanunta tayi Jin wani daddad'an kamshin daya bugi hancinta,takuma bud'e idanunta acikin parlourn dayasha gyara sai fidda wata daddad'an kamshi yake da kyal-kyali,motsin dayajine yasanyata juyowa can tahango wani d'an matashi nata aikin goge steps,haryagangaro zuwa kasa,Yana d'agowa kuwa yaganta tsaye dasauri ya'aje Mopar dake hannunsa yy saurin isowa inda take,yasunkuya gefe da'ita yace "barka dafitowa hajiya inakwana."
Shiru tayi tana binsa da kallo kamar bazata amsaba saikuma tace "lfy lau."
D'an matashin yamuskuta yanafad'in,
"Hajiya
Sunana Liti, nima'aikacine Amma na'iya Eriyar Nan tundaga cikin wannan parlourn zuwa cikin bedroom and bathroom da kiching dakuma toilet dake cikin parlour,harzuwa sama shima da duk d'akunnan dake cikin ta,ninake gyarasu,sau uku nake gyaran arana,safe Rana yamma,shekaruna uku Ina aiki acikin gidannan."
Ido tazuba Masa tana saurarar yadda yake kwararo mata bayane kamar tatan bayeshi, watodai shi ma'aikacine yakuma gabatar Mata dakanshi. tab'e baki tayi tace "to sannunka da aiki."
Yace "Yauwa, Dama d'azu Dana shigo nagama gyaran cikin parlourn Nan shine nahaura sama ganin baki farba."
Saiya mike yanufi bedroom inta,domin cigaba da aikinsa.
Itakuma tajuyo tayi kofar fita daga parlourn tana jinjina maganar sa arai,"wato shekararsa uku yake aiki agidan bamutane ciki Amma yaketa aikin wahala.
Tana fita parking lot taje tad'auki 'yar karamar akwatinta da basket d'in,
Abakin kofar parlour wasu maza biyu suka tareta suma suka gabatar Mata dakansu,D'aya maigadi d'ayakuma maibaiwa fulawa ruwa dakuma share barfajiyar gidan.
Tajinjinawa Mai aikin sharar tsakar gidan Dan duba dagirmar cikin gidan Kuma harda lungu dasakon cikin gidan duk shi yake kula da tsaftarsu,saitajima ashedai Mai gyaran cikin nasa nafulace,
Suma sannunsu da aiki tayi musu,suka nimi karb'ar kayan hannunta, tace subarshi tawuce cikin parlour ta'aje basket d'in Nan cikin parlourn,tawuce da akwatinta cikin bedroom,Koda tashiga ta dadda haryagama gyaran cikin d'akin taji motsinsa Yana wanke bathroom.
Ta'aje akwatin tafito parlourn tad'auki basket d'in tanufi wasu kofofe guda biyu data gansu abud'e Wanda jiya batalura da zamansu agunba,sunacan tagefen step,daga inda take tana iya hango cikinsu,d'aya toilet ne d'ayan kuma kiching ne,gadukkan alamu yagama gyaransu ne bai rufesuba tukun ganin kofofin duk abud'e.
Tashiga cikin kiching d'in,Masha Allah katon kiching ne Wanda girmansa yakai girman bedroom D'aya,yaji kayan duni duk wata abun bukata antanadeshi aciki.
Tabud'i kular dakecikin basket d'in,gasassun kajine guda biyu aciki sunsha kayan yaji sai tashi dakamshi suke dak dakuwa sun kwana,Nan tashiga kiciniyar d'umasu,da girga ruwan dazata had'a tea dashi, Bata wani b'ata lokaciba tad'und'umasu, tad'au D'aya tasa a plt sanna tahad'a tea,tad'au plt d'in da cup d'in tea d'in tafita a kiching d'in takoma bedroom.
Aban garen MAHFUS kuwa
Yana fita gidan Mommy yanufa a parlour yatadda Mommy itada Zahara,yazauna saman kujera tareda gaida Mommy ta amsa tana fad'in "ya matar taka takwana?."
Wani irin bakin cikine yataso yatukare zuciyarsa,yatsani arika arika dangan tata dashi, bare har'ace wai matarsa.
Shiru yy batareda yabaiwa Mommy amsaba,Mommy ko idu takura mishi saikuma tamayar da kallonta kan abunda take.
Zahara tagaisheshi, "lfy." Ya'amsa atakaice.
Duban Mommyn yy yanafad'in "har Daddy yafi tane?."
Mommy take "Eh yafita."
Shafo cikinsa yy tareda duba agogon dake d'aure ahannunsa yace "Mommy haryanzufa ban yi break ba yunwa nakeji kisamin abinci."
Batareda takallesaba tace "kabaro gidanka kazonan kacemin kanajin yunwa?
To meye amfanin matar taka dabazaka zauna tagirkama abinci kaciba?,to mu harmun rigada mun cinye abincin mu,kakoma kaje gidanka kaci."
Dasauri yace "Mommy ita zata girkamin abincin dazanci."
Mommy tad'ago tace "au yanzu idan Bata girkama abinciba wazai girka makan,to kayi hanzarin komawa gidanka kaje kaci."
Mikewa yy ransa ab'ace indai ita zata girkamasa abincin dazaici to gara yatabbata da yunwan,fuuu yafice cikin parlour,Mommy tabibayansa da kallo, dasauri Zahara tamike tana fad'in "Ya MAHFUS tsaya nazubo maka abincin."
Tuni yarigada yafice,dasauri Zahara tasa kafa zata bibayansa Mommy tayi saurin dakatar da'ita "ke Zahara dawo kizauna kibarshi yatafi."
Mommy
Tafad'a tannuna wa Zahara gurin zaman datatashin.
Cikin marairaice fuska Zahara tace "ayya Mommy yunwafa yace yakeji,kumafa akwai abinci a kiching."
Mommy tace "nasa ai zokizauna nace."
Jiki asab'ule takoma tazauna yayinda tausayin Yayan nata yacikata.
Mommy tadubeta dakyau tace "Zahara ai nasan akwai abinci,Amma banaso yaci ananne nafiso yaje gidansa yaci acan.
Zahara tace "to ai Mommy yace yanajin yunwane watakila kafin yakoma gidan yunwan tayimasa yawa."
Mommy tace "Zahara wanna bahujja bace, sonake nanuna Masa muhimman cin Zama agidansa yarikacin abinci,yanzu misali kece zakiso mijinki yarika fita yanacin abinci awaje,bakya ganin ko Office Daddy'n ku yatafi inayin kirki akai masaba,haka' ko tafiya Daddy'n ku zaiyi saina girka Masa abincin dazaici ahanya,saidai idan ya'isa inda zashin bayanda za'ayi doleyakama yaci acan d'in, to danhaka haka nake bukatar matar MAHFUS takasance."
Zahara tajinjina Kai dagamsuwa da abunda Mommyn tafad'a.
Awata b'angaren zuciyar Mommy kuwa cewa take "idan banyimasa hakaba bazai tab'a nusar dahankalinsa guri guda harsu fahimci junaba.
Shiko Yana fita daga parlourn yashige motarsa yabar gidan,
Shi babu abunda yafi Kona Masa Rai kamar yadda Mommy tace wai ita zata girkamasa abincin dazaici,yaja kwafa taredafad'in "idan so suke nai Aman hanjina to naci abincin nata,da'ita da abincin nata ai duk kazantace."
Yawani yamusa fuska irin yanda mutum yaji kazantar Abu yakeyinnan.
Gurin cin abinci mafi kusa dasu yaje yasiyi abinci yawuce gida,Koda yashigo gidan a parlourn kasa yazauna yafara cin abincin,yad'anyi nisa dacin abincin nasa,yad'ebo abincin zaikuma kaiwa bakinsa,saiyatsaya tareda yin kasa da cokali tareda kurawa abincin cikin cokalin ido,dasauri yakai hannunsa yazaro gashin dayake gani kiri-Kiri acikin abincin cikin cokalin,
Dasauri yadire abincin kasa yamike cikin hanzari Yanufi toilet in cikin parlour,dasauri yakunna panpo Yana tarar ruwar Yana kaiwa bakinsa saiya kurkure yazubar,ji yy cikinsa nawani irin hausinawa kamar zaiyi amai,yad'au brush da makilin,yarika wanke bakinsa dashi.
Aban garen JUHAIFAH kuwa
Gasheshiyar kazarta taci tayi Kat sanna takara da tea,tana kammalawa tad'au plt in da cup tafito parlour,tunkan takaraso cikin parlourn tarikajin ana wani irin Abu haka kamar mutum nason kwakulo amai dole.
Dasauri takarasa cikin parlour tana fad'in "Liti Liti Liti."
Liti dayanzu shigowarsa rikeda zannuwan gado, yy hanzarin amsa Kiran nata,kallonsa tayi sannan tamaida dubanta kofar toilet d'in.tace "au bakai bane me kwakulo Aman Nan?."
Tayi tanbayar idonta nakan kofar toilet in,
Liti yace "a'a hajiya ni yanzu shigowata."
Tace "ok jeka."
Yajuya dasauri yahaura sama ya'aje zannuwan gadon yasauko,har lokacin tana tsaye,
Liti yazo yawuceta,
"Kai wlh Allah yasawake kazanta batayiba,wanna ai sai ad'agawa mutum zuciya."
Tafad'a tareda Jan tsaki tawuce kiching ta'aje plt da cup d'in hannunta,tanacigaba da yamusa fuska, ita dai tayi maganarne bawai kodun tasan Wanda kecikin toilet inba.
tana aje plt d'in tajuya tafito,turus tayi ganinsa tsaye atsakiyar parlourn,saikuma tacigaba datafiyarta tazo zata gotashi saiji tayi ya...............
Mommyn twins ce
🅿️14
Saijitayi ya angizata saman kujera,ya takarkare yazabga Mata Mari,agigice takwalla Kara tareda dafe gefen fuskarta,yamatso daf da'ita yad'aga kafarsa d'aya yatake katarta d'aya kafar tashi Kuma yad'aura saman kujerar datake Kai,Kara Takuma kwallawa Jin yadda yake murkushe kafar ta.
Yadubeta da kyau yace "waye kazamin?akwai kazantar dayawuce ke,BAZAWARA sauran wasu ke Kazan tace har idan naganki jinake kamar nayi amai."
Tadad'a kwalla Kara tareda fashewa da kuka Jin dadda yake dad'a murkushe kafarta arazane tamike tsaye tasa hannunta tana ture kirjinsa da iya karfinta,Amma ko gizau baiyiba,saima cigaba da murkushe kafar nata dayayi.
Jin yadda yake aikin murkushe kafar nata kamar zai balla Mata 'yanyasu,sai kawai tasulale kasa tarike kafar nata tana fad'in "wayyo Allah na zaiballa min kafa wayyo kafata."
Cikeda mugunta yajanye kafarsa akan kafarta,Yana binta da mugun kallo,
Dasauri tarike yatsun kafarta dasukayi ja Dan azaba takuma Kara sautin kukanta, yasunkuyo inda take zaunin yad'aura yatsarsa kan lips insa yace "shiiit,kidaina cikamin kunne menamiki?."mikewa tsaye yy yanacigaba dafad'in "idan kk ce Zaki dameni da wannan kukan nikuma zan yi maganinki." Yanakaiwa Nan yajuya yafara haurawa step.
Dakyar ta'iya mikewa tsaye,cikin d'aga murya tace " wlh Allah sai yasakamin mugu kawai, Kuma wlh zakasan Waka mara."
Gargiza kansa yy batareda yajuyoba, yad'aga hannunsa sama yagirgiza yatsarsa alamun zamu had'u.
jankafarta tayi tarika d'ingisa kafar hartashige bedroom. tana shiga tafad'a saman bed takuma fashewa dakuka,tajanyo wayarta ta lalub'o numbern Ya Al'ameen tadanna Kira, Nan take wa'azin malam yaziyarci kwa-kwalwar ta,afili tafurta "fad'ar abunda yymin d'in shima fallasa tsirrin gidan mijinne."
"Kwarai kuwa shima fallasa tsirrin zaman aurenkine."
Zuciyarta yabata amsa,
Saitayi sauri takatse kiran tareda kashe wayar gabad'aya.
Tashafa gefen fuskarta dake yimata zugi tarika girgiza kafarta shima dake matan zugin.acikin zuciyarta kuwa Allah ya'isa tarika jamasa,ahaka bacci yayigaba da'ita,kana ganin baccin kasan nawahane Dan sai sauke ajiyar zuciya take acikin baccin.
Tunda baccin yad'auketa Bata farkaba sai kusan sallar la'asar,Koda tafarkar saitaji zuginda kafarta da kafuskarta keyimata yadaina, taje tayi alawala tazo tayi sallar azahar,tana zaune akan sallayar aka Kira sallar la'asar,tamike tagabatar dashi bayan ta'idar taninke sallayar tatub'e hijjab inda tayi sallar,tanufi parlour Dan samawa cikinta abunda zata sakamishi,direct kiching tanufa,tsayuwa tayi tana nunanin mezata girka,ta'isa jikin kofar store dake cikin kiching d'in,tatura kofar,Masha Allah kayan abinci kala-kala gasunan birjik Nan idonta yasauka kan dankali tad'iba tad'ibi shinkafa ma dai-dai yadda zai isheta takoma kiching, nandanan taharhad'a duk abubuwan bukata,lafiyayyiyar jalop tagirka Wanda yahad'ada shinkafa da dankali da yankakkun nama kananu akai,sai kayan lanbu datadad'a kawatashi dashi,cikin kankanin lokaci kamshin girkinta yamamaye ilahirin gidan,tana kammalawa tazuba a plt tafito parlour,ta iske Liti yakammala gyaransa nayamma,ta aje plt in abincin a parlour takoma kiching tazubo Masa abinci takomo parlourn Koda tafito lokacin nashirin fita haryakai bakin kofa,tace "Liti ga'abinci kaci."
Washe baki yy Dan dama tun d'azu kamshin girkinnata yagama cikashi yawunsa gabad'aya yagama tsinkewa,yakaraso inda take yanafad'in "to hajiya ngd."
Yakarb'i abincin yanaci gaba dayimata godiya,Zama tayi saman kujera tajanyo plt d'in abincinta tasoma ci.
MAHFUS dayanzu shigowarsa gidan yafito dagacikin parking lot abakin kofar parlourn sukayi kiliya da Liti,dasauri Liti yadurkusa yanafad'in "barka da shigowa Alhj."
Binsa dakallo yy batareda ya'amsaba,saikuma yace "yau girkin naku acikine kukayi."
Dasauri Liti yace "a'a Alhj, hajiya ce tazubamin,mun Isa mushigo ciki muyi girki."
"Hajiya?."
MAHFUS yafad'a Yana dubansa.
Hannun Liti narawa yace "Eh ranka shidad'e."
yafad'a tareda nuna cikin parlourn,
Sakai yy yawuce batareda yakuma cewa Liti komaiba,Liti ma yy saurin barin gurin.
Yana Sakai cikin parlourn kamshin girkinnata yy Masa maraba,tanajin motai tayi saurin d'ago kanta ganin shine saitamayar dakanta tacigaba dacin abincinta,
Yawuce yahaura sama Yana shiga bedroom yatub'e kayan jikinsa yasaka 3qtr.da singlet,komai yiyake cikin dauriya Dan bakaramin yunwa yakejiba rabonsa da abinci tun Wanda yaci dasafe yaga gashi cikinnan shima Kuma bawani maiyawaba,shigowarsa yanzu kamshin girkintan yakuma d'ago Masa yunwan dayakeji,saidai bazai iya cin abincintaba har cikin ransa yakeji idan yaci zai'iyayin amai.
fita yy daga cikin bedroom insa yasauko kasa, harlokacin tana Nan zaune yazo yawuceta yashige kiching Dan bazai iya cigaba dazama da yunwaba dole yanimawa kansa abunda zaici. tsayuwa yy acikin kiching in Yana tunanin mezai girka,tunaninsa yasauka kan taliya Dan yaji anacewa tafi saurin nuna,yy murmushi tareda matsowa jikin na'urar girki yakunna yad'au tukunya yazuba ruwa cikinta yad'aura kan na'urar girkin, yad'auko d'anyen nama ya yayyanka yawanke yazuba cikin tukunyar,yad'au su Maggi mangyad'a da duk kayan d'and'ano yazuba cikin ruwan,yashiga store yad'auko taliyar yab'are yajuyeta atukunyar, ko zafin kirki ruwan batayiba bare asaran tautsarta,
yamommosa sannan yarufe sai murmushi yake,yaja kujera yazauna Nan cikin kiching in Yana jirar tanuna.
Baiwani Jima dazamanba yafara ganin tukunyar tafara fitar da hayaki alamar tafasa,mikewa yy yabud'e tukunyar yaga Yana tafasa sai yakuma yin murmushi taredafad'in "Yauwa yanzu zai nuna."
Yakoma yazauna, 5min yakara yakuma mikewa yabud'e tukunyar yad'au ludayi yad'ibo taliyar data canza kala tsabar taji kayan had'i,yatab'a ahannunsa yajita tanuna lukui,yad'au plt yazuba aciki yarufe sauran Mai uban yawa,yafito parlour Yana share gumin fuskarsa.
JUHAIFAH ko tuni tagama cin abincinta tanadai zaune tana lallatsa wayarta,can nesa da'ita yazauna,jin wani kamshin girki nadaban daya garwaye parlourn tayi saurin d'agowa ta hangoshi can zaune ga plt agabansa sai turiri yake, tab'e baki tayi tamayar da'idonta kan waya.
Saida abincin yad'an huce kad'an sannan yagyara zamansa yad'ibo taliyar yakai bakinsa,taunar farko dayayi saida yaji hanji cikinsa yahautsina dakyar yadaddage ya'iya had'iye nabakinsa,
Magice tayiyawa a'a gishirece karninine, kasa tantance kalar d'and'anon da abincin kebadawa yy,jiyaya gabad'aya ransa yab'aci,duk tulin wayalar dayasha kafin yayi girkinnan amma ace wai baiyi dad'iba, badun Yana zaune a kiching d'in har girkin yahoba dasai yace zuba Masa wani abun akayi aciki.
Dariya JUHAIFAH tayi cikeda jin dad'in chatting inda take.
Azafafe yajuyo Dan gani yake dashi take,
Ya Murtuke fuska yakalli inda take yace "ke tashi kibar cikin parlourn nan."
Kallon sama da kasa tayi mishi sanban tace "awani dalilin zakace nabar Nan bayan nikazo kasama aciki to NI Babu inda zani."
Yace "ke ni kikecewa haka na rantse saina murd'e harshenki idan kika karayimin gautsin baki,
kuma Bari kiji duk sanda nake cikin parlourn Nan kada kikuskura nakara ganki aciki,idan zaman zakiyin sai kibari saina fita kafin kishigo."
Shekeke take kallonsa tace "to dakyau wlh har idan Ina cikin gidannan to zaman parlour wajibi,kuma wlh kasakece zaka tab'ani kagani,haka kawai ni tunda nake agidanmu bawanda yatab'a d'aga hannu yasa ajikina dasunan duka,haka kawai kazo Rana asaka hardawani marina,narantse kasake yunkurin tab'ani kaga abunda zai farudakai.
Zubur yamike tsaye azafafe yanufota,tana ganin haka tayi wurgi dawayarta saman kujera tamike tsaye,Yana zuwa inda take yad'ago kafarsa zai take kafarta wani irin tsalle tayi tahaye saman kujera,fizgota yy tafad'o jikinsa yad'ago hannu nakokarin Kai Mata Mari,tayi saurin kifa fuskarta akirjinsa ta tukuikuyeshi tana ihu,duk inda yabi Dan yasamu yabigeta inda zataji zafi yakasa, Dan kuwa kanainayeshi tayi dagasken gaske tarika lilo ajikinsa tana zandara ihu,
cirota yy ajinsa dakarfi yy wurgi da'ita asaman kunera,saikuma yajuya dasauri yahaye sama.
🅿️15
Dafe bayanta tayi inda tabugu dajikin kujerar,tamike zaune tagyara zaman ta tana maida numfashi kamar wacce tayi tsere, mikewa tayi Jin wayarta nakara taje tad'auki wayar inda tawurgashi, Zulaihat tagani ke Kiran nata dasauri tayi picking na call d'in takara wayar akunne tace "hello Zulaihat."
Zulaihat tace "gamu akofar gidanki."
JUHAIFAH tace "to kushigoma."
Takashe wayar tamike cikin murna tafito farfajiyar gidan can tahango su Zulaihat bakin get suna tahowa,da sassarfa tanufesu suka rungume juna,sai kuma tajanye jikinta tahararesu tace "watoma saiyanzu zakuzo ko? tunda safe kuzo bakuzoba sai dayammacin Nan tukunna zakuzo."
Zulaihat tace "yihakuri Shalele wlh tunda safe mukaso zuwa Aysha ce suka b'atamin lokaci itada Sadeeq wai Saida yamma muzo wai karmuzo dawuri mukatse muku love inku." Zulaihat takarashe maganar da dariya,
Aysha tace "to karya mukayi yanzuma baga sainin ajikintaba dubi kayan jikinta yadda yayamutse, Zulaihat zo mukoma kada mushiga hakkin bawan Allahn Nan Yana rage zafi muzo mutakura Masa."
JUHAIFAH tabi Aysha da harara.
Zulaihat tace "to konima zanbi maganar tasuce Dan naga alamar kamshin gaskiya.
JUHAIFAH tace "indai dama cin mutunci kukazo min to kukuma kawai."
Tafad'a tareda juyawa tafara tafiya, bin bayanta sukayi suna dariya, suna isowa bakin kofar parlourn
Aysha tace "Zulaihat zo mukoma tunda korarrmu take agidanta."
Dasauri tajuyo tarirrike hannayensu tace "wlh ba'inda zaku."
Dariya sukakuma yimata suka shiga cikin parlour suka zazzauna.
Tamike taje tazubo musu abinci ta had'o musu da drink takawo musu,cin abincin suke suna hira,
Aysha tadubi JUHAIFAH tace "Kai Anya JUHAIFAH kekikayi girkinnan kuwa? Kodai Mai aikice tayi." JUHAIFAH tace "a'a kekikazo kikayimin 'yarrainin wayo."
Dariya Zulaihat tayi tana fad'in "Aysha kinkasa hakuri kenan Saida kikayi magana' nidai nahad'iye tawa maganar aciki.
JUHAIFAH tace "zakudaiji da gulmarku.
Suna gama cin abincin suka kwashi kwanukan sukai kiching,sannan suka dawo parlourn sukacigaba da hirarsu,
Har daf magriba suna Nan zaune cikin parlour.
Aysha tanisa tace "magriba yayi yakamata mutafi yanzufa Zulaihat."
Dasauri JUHAIFAH tace "au bakwana zakuyiba?."
Ido Zulaihat tawaro tace "mukwana a'ina wai anan gidan yanzu zamutafi wlh."
JUHAIFAH tace "haba kukuwa Dan Allah mukwana Mana."
Aysha tace "Kai haba bazaiyuwuba."
"To meyane idan kun kwanan?."JUHAIFAH tafad'a tana dubansu
Zulaihat tace "nifa gobe zamu wuce,kumama bama hakaba Taya zamuyi mukwana agidan amaryar kwanad'aya,kema kinsan hakan baiyuwuwa,bazamu zauna muganewa idanunmu abunda zai damemuba, gara mulallab'a rayuwarmu muma mu'isa gidajen mazajenmu lfy."
Aysha tace "aikam kinsan Sabin aurennan bahakuri sukedashiba,ga My love Sadeeq nakiranama inada yazo maidamu gidane."
Aysha tafad'a tareda
yin picking na call in takara wayar akunne.
Daga b'an garen Sadeeq yace gani nashigo gidan inafatadai kungama gaisawar."
Aysha tace "Eh mungama."
Yace "ok Man Yana cikine Dan nakira wayarsa batashigaba."
Aysha tace "wlh mudai tun shigowar mu bamu ganshiba."
Sadeeq yace ok Bari nashigo."
Tace "tom.
Takashe wayar,
Sadeeq yashigo parlourn da sallama,suka amsa yakaraso ciki Yana fad'in "Amarya barka dagida."
JUHAIFAH tad'anyi murmushin yake tace "sannun ka." Yace "Yauwa, angon nacikine?."
Shiru tayi kamar bataji abunda
yafad'aba, Aysha tatab'a tace "ana tanbayarki wai mijinki naci."
Kai kawai tagyad'a alamar Eh.
Yanufi step Yana fad'in Bari naduboshi.
Yana haurawa tajuyo gun Aysha tace "wlh zamu Sami masala dake idan Baki daina mun hakaba."
Aysha tace "to ai shi Zaki fad'amawa baniba."
Zulaihat tace "to wai dun menene za'asami matsalar?."tayi tanbayar tana d'an dariya kasa-kasa Dan tarigada tasan abunda yasa JUHAIFAH fad'ar hakan.
Aysha tace "Dan saboda ance mijinta ba, ko bamijin naki bane?karya akayi Mata oho."
Fuska tayamusa tareda kawar dakanta gefe.
direct bedroom in MAHFUS Sadeeq yashiga,zaune yataddashi da cup in tea agabansa, Sadeeq ya'isa yazauna saman kujerar dake fuskantar gado Yana fad'in "Man nayita kirar wayarka batashiga."
"Nakashe tane."
MAHFUS yafad'a atakaice.
Sadeeq yagirgiza Kai yakalleshi da kyau yakalli cup d'in tea in gabansa sannan yace "MAHFUS yanaganka haka ko bakada lfy ne? Dan naga yanayinka kamar bakada lfy."
MAHFUS yad'au cup in tea in yakurba sannan yamayar ya'aje batareda yakalli Sadeeq d'inba yace "kazo kasameni azaune kacewai banada lfy."
Sadeeq yace "to ai shi ciwo ba Wanda ke kwance kad'ai yake kamawaba har Wanda ketafiya da katarsa bai kyaleba, bare Kai dadanazo nasameka zaune."
MAHFUS yace "toni lfy ta Lau."
Sadeeq yace "to Allah yasa,ya angoncin dai? Da kamar bazamuzo yauba munso mubarku saikunci Amarci na kwana biyu tukun."
Mikewa tsaye MAHFUS yy yanafad'in "to mekuma yakawo kan yanzu?."
Yafad'a tareda shigewa cikin bathroom Dan lokacin anfara kiraye-kirayen sallar magriba,alawala yy yafito yazura jallabiya Yanufi kofa, Sadeeq yamike yabi bayansa suka sauko kasa.
Su JUHAIFAH suna Nan zaune cikin parlourn su MAHFUS suka sauko, suna sauka yy hanyar kofa, Zulaihat tayi saurin cewa "inayini."
Cak yatsaya Jin wata murya nadaban banataba Dan shi tunda yasauko ko kallon cikin parlourn baiyiba bare yasan suwaye aciki baimasan dazaman mutane agunba, "lfy Lau." ya'amsa tareda juyowa, Aysha ma tagai sheshi ya'amsa fuskarsa Babu yabo ba yallasa, tareda fad'in "kunzo lfy yy gida?." Sukace "lfy Lau."
Saiya juya yafice,
Sadeeq yadub'esu yace "kungama dai ko to kutashi mutafi."
Suka Mike harda JUHAIFAH,
Hargun mota yarakasu kamar za'tayi kuka tana tsaye harsaida taga tashinsu kafin takoma ciki.
Koda tashigo bedroom inta tawuce tashige bathroom tayi alawala tafito tagabatar da salla,Bata tashiba harsaida tamayar da isha'i,
Wanka taje tayi tafito tasanya sleeping dress tahaye
Gado,bajima bacci yy gaba da'ita.
Ab'angaren MAHFUS kuwa baishigo gidanba sai bayan sallar Isha, Yana shiga kiching yawuce yad'au cup yahad'a yafito yazauna Nan parlour kasa yasha tea