Showing 3001 words to 6000 words out of 85666 words

Chapter 2 - BAZAWARA CE ITA COMPLETEHAUSA NOVELS BY .txt

ita kwata-kwata batama sanda mutani agunba, kallon mamaki tashiga yimusu tabud'i baki dazummar yin magana,karaf suka had'a ido aiko tamurgud'a masa baki tareda wasa masa harara,tamike tsaye

Aunty Rukayya dake tsaye agefe tace "him waikingaji watakilanma fad'a kikanimo kikecewani wai kingaji,

buga kafa akasa tashiga yi tareda yarfe hannayenta tanafad'an Ya Al'ameen kagantako saikuma tasaki kuka.

Yace"ke Rukayya inarunki aina kikaganta tayi fad'an?
Yishiru abinki jekihuta kinji'

Kai tagyad'a sanna tajuya tahaura step anan tabar kayanda tawatsar dasu.

Haushi da bakin cikine yaturnike zuciyar MAHFUS aransa yace ashedai tsiyar asali tasamo yaja guntun tsaki afili,

Saiyanzu Sadeeq yadawo daga tafiyar wucin gadin dayayi azaune agun, yadawo dakallonsa kan MAHFUS wanda yahade rai kamar an aikomasa da bakin labari, saiya maida dubansa ga Ya Al'ameen

Yace" Al'ameen wannafa ya akayi naganta anan?

Ya Al'ameen yace "wa waikananufin shalele?

Yace "Eh..Eh hakadai naji kakira sunanta bantab'a ganinta anan bane,

Dariya Ya Al'ameen yy yace"Kai Sadeeq JUHAIFAH ce bakasaniba,

Zama Sadeeq yagyara yace wata JUHAIFAH kana nufin JUHAIFAH dana sani..............




*Slm* *masoyana* *inamaisanardakucewa* *wanna* *littafin* *nasayarwane* *gamaibukatarsaya* *saiya* *tuntubi* *wanna* *number* *08034690723* *naira* 300 *kacal* *aturakatin* *mtn* *tawanna* *number* *08034690723* *kokumata* *asusun* *banki* *tawanna* *number*
*Sunusi* *yufuf* *Aliyu*
*0421042738*
*GT* *Bank*
SAI KA/KI TURA SHAIDAR BIYA TAWANNAN NUMBER 08034690723


Mommyn twins ceFollow this link to join my WhatsApp group: https://cha🌺 BAZAURACE' ITA!🌺



بسم الله الرحمن الرحيم

___________________________________


🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION🤝🏻
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________🌺 BAZAURACE' ITA!🌺


By✍🏻
Rasheeda S Director




~Free~ ~page~


*Wanna* *littafin* *nasayarwane* *gamai* *bukatar* *saya* *naira* *300* *kacal* *saika* *tura* *katin* *mtn* *tawanna* *number* *08034690723* *kokumata* *ta asusun*
*banki*
*Sunusi* *yusuf* *Aliyu*
*0421042738*
*GT* *Bank*
SAI KI/KA TURA SHAIDAR BIYA TAWANNA NUMBER
08034690723


🅿️2



Ya Al'ameen yace "itacedai,

Sadeeq yakuma washe baki yanafad'in "Kai lallai girma bawuya yaushene JUHAIFAH tagirma haka,kasanfa ni rabona da ita tun wani hutun dana taho daga india,Kuma lokacin tana yar piciciya,

MAHFUS dayacika harwuya, ganin yanda Sadeeq yaketa wani zakewa, yamike tsaye tareda zura hannayensa cikin aljuhun wandonsa, ganin haka yasanya Sadeeq mikewa shima

Sadeeq Yace "to bari mutafi saiwani lokaci kuma,

Ya Al'ameen yace "to mungode fa sosai.

Sadeeq yayiwa Aunty Rukayya sallama Ya Al'ameen yayimu SU rakiya hargurin mota harsanda sukafita agidan kafin yakoma ciki.

Amota kuwa Sadeeq saizuba masa surutu yake,yanafad'in gaskiya girman yarinyarna yabani mamaki,yaran na yaushe aka haifesu amma wai harsufimu baki, saiyakuma tunsuriwa da dariyar shakiyyanci yace "wlh harnatuna diramarku nad'azu Kai abin yabada kala.

Duk surutun da Sadeeq yake,azahiri jinsa yake abad'ili kuwa hankalinsa bayagun,dankuwa yayi zurfi acikin duniyar tunanin daya tafi,wacce tazame masa jiki,
Akoda yaushe idan yatuna sai hankalinsa yayi mummunar tashi saidai tashin hankalinsa nayau yafi nakullum ,dafe kansa yayi wacce keyimasa masifaffen tsarawa,
Cikin hatsala yace "ya isheka haka Sadeeq!.

Kunshe bakinsa Sadeeq yayi baikuma cewa komaiba

Saida sukayi nisa sosai sanna Sadeeq yajuyo yasaci kallonsa har alokacin fuskarsa ad'aure take,kiris yake jira yafashe, aransa yace him wanna mutumin idan yahad'e rai nikaina shakkar yimasa magana nake dan suffarsa gabad'aya canzawa take,

Ganin sunata tafiya baikuma San inda zai saukeshiba yasashi fad'in

"Man, gidanka zan kaika ko gidan Mommy?.

Shiru yy masa saida yad'au tsawon 10min kafin yace
"gidan Mommy .
Sadeeq yajuya akalar tafiyar tasu izuwa gidan Mommy dake Maitama

Wata tamfatsetsiyar gida Sadeeq yadanna hancin motarsa ciki,Kai Fan's tsayuwar fad'amuku irin girma da tsaruwan gidanma bata lokacine,Dan saina cika page d'aya bangama kwararo muku bayaniba,akarshedai zancemuku kuhasasho dakanku.

Ko parking baijira yakarasaba yabud'e marfin motar yafita,
Cikin salon zolaya Sadeeq yace "mutumin babu ko 'yar sallamar nanma, baikulashiba yayi shigewarsa.
Shiko yaja mutarsa yayigaba.

Asannu ya'isa jikin wata glass yad'aura hannusa ajiki saiga glass d'in taware gidabiyu,yashige ciki, katafaren parlour ne wacce tsaruwansa yawuci misali,bakajin komai sai tashin sanyi maihad'eda daddad'an kamshi ketashi,har ya'isa sakiyar parlour yanakokarin ketare cikinta saiyaji ance, "Kai MAHFUS.

Dasauri yajuyo danjin muryar mahaifinsa,yayi mamakin ganin mahaifan nasa zaune acikin parlour Amma haryawuce baigansuba,
Yajuyo ahankali ya isa inda suke tareda zama saman kafet kusa dakafan Daddynsa,

Yace"sorry Daddy banlura daku bane,

Daddy yatsura masa ido danson nazartar yanayin dayake ciki,daga bisani yy gyaran murya, yace"MAHFUS meke damunka?.

Saurin d'agowa yayi yace "wani abun kagani ne daddy?.

Daddy yace "sosaima kuwa tunda harka iya wucewa batareda kasan munacin parlourn nan ba. Mommy tace "gaskiya kam.

Murmushi yy yace "Daddy kawaidai bacci ne yacikamin ido ga gajiya, Sadeeq ne yad'ibeni yarikayawo Dani duk yagajiyar dani.

Daddy yace "ato tashi maza kajeka wasa ruwa saikaji dad'in yin baccin,

Toyace tareda mikewa yahaura sama inda zai sadashi da part insa dake cikin gidan.

Yanashiga bedroom yafad'asaman lafiyeyyen gadonsa wacce Tasha gyara saikamshi ketashi, yad'au tsawon mintuna kwance sanna daga bisani yamike zaune,asannu yashiga kwab'e kayan jikinsa,yarage dagashi sai boxer yafad'a bathroom yasakarwa kansa ruwa maisanyi batareda yacire boxer jikinsaba,rumsa idanunsa yayi dakarfi lokacinda ruwan kesauka azakiyar kansa, yacusa hannayensa cikin gashin kansa tareda yamusashi,cikin wata irin yanayi yataune lips d'insa nakasa,dogon tsaki yaja yacire hannaYensa akansa, yadunkule hannunsa tareda naushin d'aya hnnunsa,aransa yace "meyasa zuciya zaki d'auramin damuwa akan abunda baishafeniba?.afili yakuma furta, meyasa?meyasa?meyasa!?.yafad'a cikin karaji,Wanda saida ilahirin bathroom d'in yad'auka amon muryarsa.

Yajima sosai kafin yafito daure da towel akugunsa wardrobe yabud'e yaciro farar jallabiya yasaka sanna yahaye saman bed bajimawa bacci yad'aukeshi.



Numfashi Mommy tasauke tace "Alhj ni lamarin yaronnafa yafara isata kai bakaga saiwani sussunkuyar dakai yakeba, waidan karmu had'a ido dansabo nayimasa magana akan aure,harsai yaushene zaisan yagirma,
Sa'o'insafa daga mai yara ukune saibiyu, hatta kannensa Wanda yagirme musu duk sunyi aure harda yaransu,mu harsai yaushene zamuga jikokinmu?.

Zama Daddy yagyara yace "him ai bake kad'ai abun kedamunkiba, musamman idan nadubi kaina yanzu shekaru sunfara ja,yakama ta kam ace zuwa wanna lokacin ya'ajiye iyali,
Kwanaki danayi masa zancen, sainazamo surukinsa dazarar yaganni saiya nimi boyewa haka yarika wasan buya dani,

Mommy tace"to ai nima kwanaki danayi masa zancen guduwa yayi yabar kasar baki d'aya,baikuma dawowaba saiwanna karon.

Dariya Daddy yayi yace" Son Kenan d'anrigima, ammadai kidaina masa masa da maganar dayawa, adai bishi ahankali harya fidda matar dayakeso.

"Haba Alhj goyamasa baya kake?, to idan mukaci gaba da sakamasa ido ay saiyaji dad'in cigaba dazamansa ba matar,

Daddy yace "bawai inanufin azuba masa ido kwata-kwata bane,kinsan shi ba mai yawanson damuwa bane, so kada yawan yi masa maganar yasakashi shiga da uwa, so kisan yadda zakirika yimasa maganar bawai koda yausheba, ay yamallaki hankalinsa yasan dai-dai da rashinsa,lokacine kawai baiyiba idan lokaci yayi saikiga komai yawuce.

Hmm kawai Mommy tace dantasan dama bagoya mata baya zaiyi amaganarba, saidai yabi bayan d'an nasa.

Daddy irin iyayennan ne masu matukar son 'ya'ya amma son nasu baya hanasa yimusu tarbiya dai-dai gwargwadon yadda addini ya shar'anta..


Barcinta take cikin kwanciyar hankali, firget tamike kamar an zabureta,sanye take da doguwar rigar bacci pink, takalli agogon dake d'aure akan dorowa 2:00pm,
mika tayi tareda yin salati,
tamike tsaye tashiga bathroom, brush tafara yi kafin tagudanar da wanka, sanna
tad'auro alaula tafito,tashinfid'a sallaya tagabatar da sallah,koda ta'idar gaban miro tazauna,mayuka tashiga shafawa ilahirin jikinta masu sanyin kamshi,sanna tayi simple makeup, Masha Allah kyawun ta saiyadad'a baiyana,ta isa gaban wardrobe taciro riga da sket na atamfa d'inkin opin shoulda tasaka, bakaramar daukar fatarta yayiba, tafito parlour babu kowa saitawuce saman dinning,tashiga bubbud'e tarin kulolin dake jere asaman dinning d'in, yamusa fuska tayi saitakuma janyo wata kula tabud'e. had'ad'd'iyar chips ne wacce taji kayan masarufi kala-kala, tazubashi cikin plt sanna tahad'a tea a cup,tanaci tana kurb'ar tea d'in bawani mai yawa taciba,tamike tasauka asaman dinning d'in,fita tayi acikin part d'in gabad'aya, tanufi part 1.

Tundaga kofar shiga part d'in tafarajin hayaniya,sauri takara Dan jin sautin muryoyin dake tashi acikin parlour,da sassarfa tashige cikin parlour, tana fad'in "oyo yo my brother's.
Saikuma taja tatsaya tareda hard'e hannayenta akirji tawani turo baki gaba, gabad'aya hankalin 'yan cikin parlour yadawo kanta,dasauri wasu maza guda biyu suka taso suka rungumeta
Tareda fad'in
Oyo yo my shalele saiyanzu aka tashi abaccin?.

Cikin muryar shagwab'a tace "ay ni baruwana daku tunda yanzu kundaina sona,Ya Al'ameen ne kad'ai da Abbana sai Ammee na da Baby twins d'ina kad'ai kesona yanzu.

Ido suka ware dukansu biyu suka had'a baki wajen cewa "waya fad'amiki mun daina sonki!? Suka karasa maganar tareda lankwasa Kai cikin santsar so dakaunar kanwar tasu. Hassan da Husain dasuke cinyar Ammee suka mike aguje sukazo inda su JUHAIFAH suke tsaye,Husain yace "uncle muma kundaina sonmune?
Hassan yace "Eh basu kawomana chocolate ba sundaina son mu.

Gabad'aya parlour yad'auki dariya Ya Mujaheet yace "lalala wane mu chocolate d'inku yana nan a ajiye namancene ban ciro muku ajakaba, dagudu suka koma jikin Ammee suna fad'i yee uncles suna son mu.

Hannayensu tarike, tad'ago Kai takalli d'ayan dake gifen damanta tace " Ya Mujaheet,sanna tajuya d'aya gefen tace "Ya Jabeer, tomeyasa dakukazo baku nemeniba?.
Takarasa maganar tareda bubbuga kafa akasa tana mitar shagwab'a

Ya Mujaheet yace "mun isa muzo bamu nimi shalele JUHAIFAH ba,ai muna sauka d'akinki muka fara shiga mun taddaki kina bacci ne shine muka zonan Dan mubarki kiyi barcinki mai dad'i.

Ya Jabeer yace "kwarai kuwa Dan bamaso mukatse miki baccinki shiyasa,

Tace "au to shikenan zan hakura Amma da sharad'i,

sukace "to muna jinki.

Tace "to sai Ya Jabeer yamin faretinsu na sojoji tukun,

Ya Mujaheet yace "to Jabeer yimaza kafara,

Ya Jabeer ko yadaddage yarika zabga fareti asakiyan parlour,itako sai dariya take da salle kamar Baby, su Hassan da Husain suka rika tayata,idan ya ce ya isa?.saitace bai isaba yakara.

Abba dayaga abin bana kare bane, sai yace "taho nan Mamana kibar yayan naki yahuta haka.tace "to. tajuya zata gun Abba saita washe baki dafad'in laa Aunty Nuwaira dama dake akazo ay bangankiba?.

Nuwaira takalli mijinta wato Ya Mujaheet, sanna tamaida kallonta ga JUHAIFAH

Tace "inakuwa za kiganni bayan yayun naki sun lullub'eki,aranta kuwa cewa take lallai JUHAIFAH tanaganin kauna da soyayya agun wanna family.

taje kusa da Abba tazauna,nan shima tashiga zuba masa shagwab'a,yayinda dukansu suka biyemata,

Hira sosai suka bud'e har saida lokacin sallar la'asar yayi kafin, Abba da Ya Al'ameen Ya Mujaheet Ya Jabeer,sukanufi masallaci, Ammee tashige ciki itama dan gudanar dasallan, Aunty Rukayya takoma part 3 part inta kenan,Aunty Nuwaira itama tatafi part 2 wanda yake part intane idan sunzo hotu da mijinta.JUHAIFAH ko, kin tafiya tayi, anan toilet in parlour tayi alaula takuma yi sallan acikin parlour, nan suka dawo suka sameta,sanna suka d'aura daga inda suka tsaya, lokacin sallace kad'ai ketadasu, har karfe 11 dare suna gun,saida Abba yace dasu kowa yaje yakwanta saida safe Kuma. kafin taron ta watse..



Shirin barin kasar yake tayi Dan hutunsa yakare,kuma ayaune jirginsu zai d'aga dakarfe 12 nadare izuwa kasar Canada zaune yake abakin gado yana shirya kaya acikin a kwati,Mommy taturo kofa dasalla,ya Amsa tareda rufe akwatin yaturashi gefe, ta'isa tazauna kusa dashi,

Yace "barka da dare Mommyna.

murmushi tayi tace "yauwa Son, anakan Shirin kenan?

Kwantar da kansa yy akafad'arta sanna yace "Eh Mommy,Allah ni nama rasa meda me zansa acikin jakarna, Mommy kinfasan ban iya shirya kayaba, gashiyau kinki shiryamin,

Goshinsa tadungure tareda fad'in "ay ko bazan sake shirya makaba Dan yanzu kagirma,saika koya dakanka,

Yace "to Mommy yazanyi na iya bayan bansaba yiba,

"To basaika aje wacce zata rikayimakaba, dan nikam narigada na sallameka saidai naji dana autana Zahara"

"To nikuma yaushe zan d'auki 'yar ay ki dannasan bazama ta iya yanda Mommyna takeyimin ba,ko acanma idan JC yagyaramin d'aki sainasashi yakuma harsau uku,Amma baya tab'a yin kyau kamar naki,

Mommy tace "ay ko bazai tab'a yin kyauba danku gyaran gida sai mace,macenma na musamman,

Shiru yayi danjin zancen Mommy yafara canza salo, aransa yace " to Mommy zata kawo wata zancen kuma, bai idda zancen zucin dayakeba yaji tace

"MAHFUS har idan kuwa kanaso arika yimaka gyaran dakakeso tokuwa saika aje matar aurenka agida,daganan zaka rika samun duk abinda kakeso,

cikin ko inkula yace "to Mommy menanima narasa dahar saina aje wata kafin nasamu? inada iyaye gata gakuma dukiya tome yaragemin Kuma,

tace "banason shiririta Dan bashi yakawoniba, nazone akan zancen wanna yarinyar fareeda dan banaso katafi batareda naji wata kwakkwara bayaniba,kadaisan tana sonka, inason hutun dazaka Kuma dawowa yazamana shine lokacin aurenka da ita,Dan wanna karon banaso kakuma wasamin kasa a ido, Dan munrigada mun gama magana da mom inta.

Shiru yy batareda yace komaiba,itama shirun tayi,tareda tunani iri da kala acikin zuciyarta,
zuwa can yace

"Mommy abar maganar fareedar nan Dan Allah nifa basonta nakeba,

Cikin hasala Mommy tace "gayamin wakakeso fad'amin nace!?wlh MAHFUS kaji tsoron duniya kada rud'inta tad'ebeka takaika tabaroka,kaduba tulin shekarunka Amma ace bakada mata,yanzu kahaura shekara 30 fa,kada kasa duniya tafara zarginka, MAHFUS! mekeyimaka dad'ine a irin wanna rayuwar?,yau kimanin shekaru biyar kenan kullum akan abu d'aya ake, mata biyar aka nima maka harsai ansa ranar aurenku kace Kai kafasa.saikuma tasassauta muryarta,kanaso har saimun mutune kafin kayi auren?

Tunda tafara maganar shiru yayi batareda yace komaiba sai tsura mata ido dayayi aransa yace "wato Mommy tana zargin ina mu'amala da mata awajene shiyasa take wanna zancen,murmushi yy tareda riko hannunta yace" Allah yahuci zuciyarki Mommyna in Allah ya yarda idan nadawo zan kawo miki matar dazan aura,

Tace "idan baka kawo bama wanna karon babu gudu baja dabaya aure kuwa ba fashi dakoma waye,

tamike tafita ad'akin ,

Ciccusa kayan yayi acikin akwatin yarufe, sanna yashiga bathroom yayi wanka tareda yin alaula yafito,shafa'i da wutiri yy sanna yashirya saf cikin kananan kaya, yayi shar dashi kamar wani tauraru,yakalli agogon dake d'aure ahannunsa lokacin saura minti 30 jirginsu yad'aga,
yajanyo jakarsa yafito parlour,
anan yatadda Daddy zaune yana kallon labarai a TV,Mommy nazaune agefensa tana had'a masa coffee,

Daddy yace "yauwa yanzu kuwa nake kan zancenka kagafa saura mintunane jirgin yatashi, kayi hanzari kada kab'ata lokaci,

yace "to Daddy,

Sukayi masa fatan alkhairi yafita, yanafita farfajiyar gidan cikin hanzari ya'u driver yataho ya amshi jakarsa yasashi amota sanna yabud'e masa gidan baya, yashiga,sanna yazaga yashiga mazaunin driver yaja motar sukabar gidan, suna isa airport batareda b'ata lokaciba jirginsu tad'aga, ya'u driver kuma yakomo gida,

Tunda MAHFUS yatafi baikara waiwayo Nigeria ba haryashafe kimanin wata 5,duk sanda sukayi waya da Mommy saiyace mata zaizo acikin satinna, Mommy data gaji dasa mata rana dayake saita madaina kiransa, waiko dun zaiji wani abu akan hakan yadawo,shiko dad'ima yaji data daina kiransan,

Mommy kam babu irin tunanin dabatayi akansa,waya tad'aga takira abokinsa Sadeeq, tace yazo tana nomanshe,bareda b'ata lokaciba Sadeeq yazo gidan kasancewar masu gadin gidan sun sanshi haka bai bashi wahalar shiga gidanba,a parlour ya iske Mommy cikin girmamawa yarisina yagaisheta,ta ammasa cikin sakin fuska tareda tanbayarsa ya mutan gidansu?yace "lfy lau.tace"to madalla,

"Sadeeq.takira sunansa,

yace "na'am Mommy,

Tace "Sadeeq inaso nayimaka wata tanbayace,Amma kadubi girman Allah kafad'amin sakanin ka da Allah, kada karage koka boyemin wani abu, kasani idan kaboyemin bafa zaka boyewa Allah ba!.

Yace "insha Allahu bazan boyemiki ko narage miki daga abinda nasaniba,

"To madalla,

"Sadeeq inaso kasanar Dani abunda bansaniba nagame da abokinka,

Sadeeq yace "Mommy banfahim cekiba,

Tace "inaso nasan da wasu irin mata MAHFUS yake huld'a dasu awaje, wanda har yakejin baya sha'awar yin aure,

Sadeeq yace "subhanallahi Mommy wayafad'a miki wanna kazamin zancen,

Mommy tace "bafad'amin akayiba ,ninake zargin hakan,to inba hakaba maizaisashi kinyin aure awanna shekarun nasa,

Murmushi Sadeeq yy tareda fad'in oh Mommy shekarun nasa sunkai hamsin ne da har akafara kwatance dasu, akwai wad'anda suka fishi shekaru sunanan kuma haryanzu basuyi aureba,

Tace "au kaima shiriritar zakayimin irin nashi,shiyasa kaima kakenan kunsaya garin shiririta kun kasa fidda mata ku aura,tanbayarka nayi kabani amsa,

Zamansa yagyara tareda tankwashe kafarsa,yace wlh tunda nakeda MAHFUS bantab'a ganinsa tsaye dawata dasunan soyayya ba, bare har wani alaka tashiga sakaninsu ba,wlh Mommy ina fad'amiki zancenna ne harcikin raina,

Numfashi tasauke tace "toko bashida lfy ne?

Yace "todai gaskiya wanna amsar saishi dakansa,

Tace "katabbata abinda kafad'amin gaskiyace?.

Yace "wlh Mommy duk abinda nafad'amiki babu karya cikinta, harcikin raina iya gaskiyar kenan.

"To shikenan zaka iya tafiya,

Yayi mata sallama yatafi.komawa tayi tajingana dajikin kujera,"tabbas idan kuwa MAHFUS baya niman mata awaje,to yatabba bashida lfy kena,taja numfashi tasauke tad'aura dafad'in to Amma kuwa yayi wauta dahar yabar irin wanna cutar ajikinsa batareda yasanar mana mu iyayensa mutai maka masaba. tajima sosai zaune da tunane-tunane acikin ranta har Daddy yadawo daga gun ay ki, sannu da dawowa tayimishi tareda karb'ar jakar ahannusa tashigar ciki,tawuce bathroom tahad'a masa ruwan wanka sanna tafito tace dashi yaje yawasa ruwa,kafin fitowarsa tad'auko abincinsa daga saman dinning tasauko dasu sakiyar parlour,
bayan yayi wanka yashirya yafito parlour nan yatadda Mommy zaune,zama yy tazuba masa abinci,yanaci suna d'an tab'a hira,harya kammala.
Tahad'a kayakin takira hanne mai aiki takwashi kwanukan takaisu mawanki.

Shiru gurin yad'auka bawanda yakuma magana acikinsu, yayinda Daddy yakafe TV da ido yana kallon labaran da ake, Mommy tanisa cikin raunanniyar murya,tace"Daddy!. Juyowa yy yana fuskan tarta,kacokam yamaida hankalinsa gareta,Dan jin sunar data kirashi dashi,duk sanda takirashi da sunan da yaransa suke kiransa dashi to lallai wanna rana tana cikin damuwa ko maka mancin haka,tana kuma bukatar tai makonsa,tun shigowarsa yalura da akwai wani abunda kedamunta, cikin nuna kulawa
Yace "ya'akayine Mommyn MAHFUS da Zahara?mata agidan Alhj Tukur Shali Daddyn MAHFUS da Zahara,murmushi tayi danjin kirarin da yayimata, shiyake yimata aduk sanda yafahimci tana cikin damuwa,

Tace "akan batun yaronnane,kamardai yanda kasanida,yanzu watannisa shida datafiya,duk sanda nakirashi saiyacemin zai dawo asatinna,
Ni inaganin d'anna bayada cikakkiyar lfy ne,shiyasa baya da sha'awar yin aure, har yaushene zai aje iyali,su biyu Allah yabani,akoda yaushe ina addu'ar subiyunna suzamo sanadin ninkuwar zuri'a,takarasa maganar cikin rauni.

Kai ya jinjina cikeda tausayin matar tashi,yasan tana matukar son haihuwa da yawa,Amma Allah daya tashi bata saiyaba 'ya'ya biyu rak, cikin tattausar lafazi maicikeda kwantar da hankali, yace"amma kuwa MAHFUS yy wauta ace cuta nadaminka baza kafad'a atareshi tunda wuriba, ki kwantar dahan kalinki indai akan wannane kada kidamu,nida kaina zansashi yadawo sanna munima masa magani,inya warke saiyayi aurensa,kinga daganan saiki samu 'yan jikokinki.

Atake agon yad'aga waya yakirasa, bugu biyu yad'aga tareda yin sallama,Daddy yace "Son ya'aikin dai?, yace lfy lau Daddy komai natafiya normal,yace "madallah.
Son yaushene kake free inaso kazone mud'an tattauna.
Yace " week inna ina free,sai last week zanshiga UK.
Ok to saika zo Dan muyi maganar,
Yace "toh
Harsunyi sallama yy saurin cewa "yauwa Daddy Mommy tayi tafiyar datace zatayinna kuwa?.
Daddy yakalli gefen datake saiya ga takafeshe da ido,saiyayi murmushi tareda fad'in a'a ammadai zatayi inaga ko gobe ko jibi idan Allah yakaimu,
Yace "to nizanzo gata,
Daddy yace " Allah yakaimu,sukayi sallama yakashe wayar.

Mommy tace"him wato harma tanbaya yake kona tafi saboda bayaso yazo yasameni, dan inagayamasa gaskiya.
Daddy yace"haba kada kifassarashi dawani nufi mana,tunda yace zaixo to bashikenanba,Kuma ay balaifinsa bane ciwonne kesashi wanna guje-guje da b'oye-b'oyen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login