Showing 12001 words to 15000 words out of 85666 words
Chapter 5 - BAZAWARA CE ITA COMPLETEHAUSA NOVELS BY .txt
dani?lallai akwai babban abunda yasani game dani tabbaas,innalillahi wa inna ilaihirraji un,takuma furtawa,
Dafe kirjinta tayi dasauri Jin yadda yake tsarawa,ta janyo pillow ta dukun kune ajikin sa ta rufe idanunta da karfe,tajima sosai ahaka kana tacire pillow ajikinta tamike tsaye dasauri,lokacin aka turo kofa Aunty Rukayya ce tashigo tana fad'in "JUHAIFAH har yanzu baki tashiba naga yau bakifito da wuri ba duba karfe 11 yanzu Allah dai yasa lfy."
Kallon agogon da Aunty Rukayya tanuna tayi,tayi mamakin ganin
yanda lokaci yaja har haka,komawa tayi tazauna bakin gadon,
"Sub hanallahi JUHAIFAH meyasa meki?kardai ince kwana kuka kikayi? meyasa kike son d'aurawa kanki da muwa haka?.Aunty Rukayya tafad'a tareda zama kusa da ita,
Ruko hannun Aunty Rukayya tayi saikuma ta fashe da kuka cikin muryar kuka tace "Aunty Rukayya bana sonshi bana sonshi."
"Yihakuri JUHAIFAH kidaina kukan haka ya isa duba kiga yadda jikinki yafara zafi,kiyi hakuri kid'auka hakan kaddarar kice ki run gumeta amasayin kaddarar sai Allah yakawo miki sassauci acikin ta."
"Aunty Rukayya bazan iyaba wanna mutumin yafara bani tsoro."
Tayi Mamakin Jin kalmar tsoro daga bakin JUHAIFAH tunda take da ita bata tab'a Jin tafurta cewa tana Jin tsoron waniba, tasan JUHAIFAH mai tsiwa ne dakuma neman fad'a makoma waye duk Wanda yy mata Abu takan iya tsayar masa bata shayin kowa Amma saigashi yau da bakinta take furta wai tanajin tsoron wani lallai wanna lamari da ban mamaki yake.
Tace "kina tsoronsa JUHAIFAH?."
"Eh Aunty Rukayya tsoro yake bani." takuma kan kame hannun ta,
Tace "JUHAIFAH kinutsu yanzudai kici abinci tukuna sai muyi magana kinji?."
kuka tasaka mata tana Shure kafa tareda fad'in wlh ni bana son shi,duk lallashin da Aunty Rukayya takeyi mata abanza domin kuwa tuburewa tayi tarika shushshure kafa tana cigaba da fad'in ita bata son shi wlh bata son auren saitakuma kara volume in kukan ta,ganin haka yasanya Aunty Rukayya fita dasauri takira Ya Al'amee
Dasaurinsa yashigo d'akin ya taddata tana Shure kafafu,zama yy bakin gadon yariko hannunta yace "Shalele kiyishiru kibar kukanna haka ya isa ai tunda kk ce baki son shi to kuwa muma bama son shi,munyi magana da Mujaheet da Jabeer suma sunce tunda fa baki amin ceba to sumafa basu amin ceba Dan haka baza mutab'a bari ayi wanna aureba Dan bazamu sake ganin abunda zai cutar dake mukyale ba yarigada yakare yanzu Dan haka ki kwantar da han kalinki kidaina wanna kukan nafad'a miki tunjiya ki kwantar da han kalinki kinji?."Kai ta gyad'a masa alamar toh, yajuyo yace "Rukayya je maza ki kawo mata abinci."
yarika tau sasata har tad'an samu taji sanyen wani abun,kana Aunty Rukayya tafita takawo mata breakfast
Ya Al'amee yasata gaba har saida yaga tad'anci abincin kafin suka fita.
Koda su Ya Al'ameen suka fita wanka tayi tashirya tsaf da ita tayi d'odar dukda kuwa yar ramar datayi acikin 'yan kwana kinna,tana zaune gaban mirror takumajin karar wayarta alamar shigowar sako,ji tayi gaban kirjinta yabuga,lallai ko ba afad'aba tasan shine yakuma turo mata,wanna karon kin d'aukar wayarma tayi gaba d'aya,numfashi tasauke sakamakon tunano sakonsa nayau da asuba,afili tafurta lallai wanna mutumin yasan wani babban al'amari game Dani,zunbur tamike tad'au wayarta,batareda ta duba sakon daya kuma turo mataba tayi delete inshi,
tashiga contact ta lalub'o numbern Ya Mujaheet bugu biyu yad'aga yana fad'in "hello Shalele."
Kuka tasaka mishi cikin muryar shagwab'a tace "Ya Mujaheed.
Saikuma tayi shiru tareda kara sautin kukan ta' "na'am JUHAIFAH menene?kiyi shiru ki fad'amin kinajina ko ? gobe idan Allah yakaimu munanan zuwa kar kidamu babu wanda ya isa yy miki dole,kinajina daiko?."
kashe wayar tayi batareda tace komaiba tamike tafita ad'akin tashigo parlour babu kowa ciki sai tawuce tafita tanufi part d'in Ammee.
a parlour ta iske Ammee nazaune tazube kan cinyarta tareda sakin kuka,
Ammee tace "ke JUHAIFAH wainikam kuka yazamo miki abin cine?kid'aga hankalinki kid'aga nawasu,wlh kishiga han kalinki kinji nafad'a miki kena,yanzu dakika d'agawa su yayunki nacan hankali to me kkyi kena,suma dake sun fiki hauka ai dole subaro aikin su suzo Dan shir men ke,
to wlh ina mai shaidar miki kinutsu ki kama kanki ke kinfiso kicigaba da zama agida ne, duk wata mace da kikaganta burinta bai wuce gidan aureba,Amma ke bansan wace iri bace."
Cikin muryar kuka tace "to kicewa Abba yafasa auren sai in daina kukan."
"Ai ko saidai in bazaki dai nanba dankuwa babu abunda zaisa afasa wanna aure,wata macene kk tab'a ganin anbarta haka batayi aureba?ba atab'a ba Kuma baza afara akankiba."
"Ammee ni nafiso nayi rayuwata ahaka nibana so nazamo akar kashin ikon wani."
"ke sha sha-shace idan da ace haka akeyi dake nan bakizo duniyaba, haryanzu ke yarin yace sai nan gaba zaki gane gata muke son yi miki."
JUHAIFAH tace "ai dama nasan keda Abba yanzu kun daina sona."
Ammee tace"ni kinbi kin cikamin kunne kitashi kibani guri."
cikin salon shagwab'a tamike ajikinta tana bubbuga kafa akasa tafice a parlour
Washe gari kamar yanda Ya Mujaheed yafad'a karfe 4:30 yamusu agarin Abuja,a parlour Ammee sukayi masauki kamar yanda suka saba,bayan sun gaida iyayennasu,hira suka bud'e nabayan rabuwa,bayan wani d'an lokaci Abba yy gyaran murya yace
"inafatadai lfy naganku awanna lokacin Dan nasan lokacin zuwanku bai yiba."
Ya Mujaheed yace "to lfyn kenan Abba munzone akan maganar auren JUHAIFAH."
"kwarai kuwa.
cewar Ya Jabeer,Abba yakalli Ya Al'ameen daya kawar da kansa gefe saiya girgiza Kai Dan yasan duk shirinsa ne,
Yace "to ina jinku wani abunne yafaru akan auren nata?."
Ya Mujaheed ya gyara zama yace "Abba nasan baka mance abunda yafaru abaya lokacin wancan aurenta ba,yakamata ace yanzu ita zata zab'arwa kanta miji Abba tunda tace bata son shi to kawai ajanje maganar auren abarta tazab'i Wanda takeso sai a aura mata."
Ya Jabeer yakarb'i zancen yad'aura dafad'in "Kuma gashi tana fad'in har idan akayi auren zata kuma guduwa Abba Dan Allah abar yarin yarna tunda yanzu hankalinta yakwanta kada akuma tada matashi abarta tafidda Wanda takeso."
Ya Al'ameen yajuyo dasauri yace "wlh baku ga yanda take kwana kuka ba abun tausaye duk tarame."
Tunda suka fara maganan Abba ya zubamusu ido harsanda sukakai karshen zancensu,sannan ya girgiza kai kana yace "duk naji zancenku amma kusani bazantaba yiwa JUHAIFAH abunda zai cutar da itaba, idan baku bada koyon baya akan tayi aureba bazaku hana yin auren ba,yau shekaru nawa tana zaune agida ko sau d'aya ban tab'a yi mata zancen aureba nayi hakanne badun komaiba saidun tahuta tasamu nutsuwa da kwanciyar hankali ta mance da abunda yafaru abaya shiyasa,dakuma lokaci da baiyiba Amma yanzu da lokaci yy fa?yakamata kubada goyon baya akan haka' baku nuna rashin goyon bayankuba, kun nunamin cewa ko bayan ba raina bazaku d'aura kanwar ku kwalli d'aya ahanyar kwaraiba saidai duk abinda taso ko maikyau ko mara kyau agunku dai-dai ne,yanda kuke son ta haka Nima nake son nata zan iya cewama son Dana keyi mata ma yafi naku,Amma son bazai tab'a rufemin ido har nakasa aiwatar da abunda yadace akantaba."
Ya Al'ameen yace "Abba mu bamuna nufin hana JUHAIFAH aure bane a'a mu muna maganane akan abarta tazab'i Wanda takeso tunda tace bata son shi wanna da za ahad'a su dashid'i."
Abba yace "toyanzu kunaso nace na janye auren kenan indai hakane da tunda fari dasuka zo neman auren da ban aminceba, sai yanzunne da aure yazo saura kwanaki kalilan nace najanye? kunga ai banyiwa kaina adalciba'dan haka kuduba wannan lamari da kyau,yanzu misali idan d'aya daga cikin ku hakan yafaru dashi yazakuji?yanzu abunda yakamata muyi shine muyi mata addu'an zaman lafiya agidanta banaso kukara cewa komai akan wanna maganar sai yamike yabar parlour."
JUHAIFAH da yanzu shugowanta parlour tatsinci zancan Abba asama sai kawai tazube tsakiyar parlour tafashi da kuka nanfa su Ya Jabeer suka d'ungumo kanta kowa dakalar rarrashin dayake yi mata haka suka ringa rarrashinta dakyar suka shawo kanta tayi shiru, sannan suka fice
waje.
Acan bakin get suka yada zangonsu,Nan suka fara niman hanyarda zasubi Dan susamawa kanwarsu mafita,daga bisani sai ya Jabeer yanisa yace "yanzu meyakamata muyi tunda ga abunda Abba yace Kuma gashi JUHAIFAH bata so?."
Ya Mujaheed yace "yanzu kawai muje musami Daddynsa." Ya Al'ameen yace " " a'a karmu tinkari Daddynsa, musamu shi MAHFUS d'in dai tunda har kunji Abba yace babu batun janyewa to sai musan matakin dazamu d'auka. suka tsara yadda abunzai kasance.
Zaune yake a bedroom yatasa laptop gaba yayinda waya ke kare akunnensa gadukkan alamu magana mai muhim manci yake,zuwacan yasauke wayar tareda rufe laptop d'in,yamike tsaye yanufi kofa har ya rike handle sai yaji wayarsa tafara tsuwa alamar shigowar Kira ahankali yasaki handle d'in yajuya ya koma inda wayar take,yad'au ka kallon number daketa yawo akan screen d'in wayar yy Dan bai tab'a ganin taba,sai yawurga wayar saman bed batareda yad'au kaba yajuya haryakai sakiyar d'akin saikuma yakuma dawowa lokacin Kira nafarko takatse Yana zuwa inda wayar take Kira nabiyu yakuma shigowa yad'au wayar tareda d'aukar Kiran yakara wayar akunne,daga cikin wayar yaji anyi sallama ya amsa sai kuma yayi shiru da sauraran mekiran, ahankali yaji ance
"nasan baka sanniba sunana Mujaheed yayan JUHAIFAH nakirakane domin mudanyi wani shawari game da aurenku ina fatan kana jina?idan kaduba yarinyarnan batasun aurennan sannan kuma kamar yadda bata so haka muma bama so domin duk abunda takeso muma shi mukeso domin itad'in farincikinmune amma tunda mahaifinmu yanuna amincewarsa babu yadda muka iya saidai ina mekara shaida maka JUHAIFAH farincikinmune idan aka bata mata kamar anbata manane ina fata zaka kiyaye." shiru yayi batare da yace komaiba,Jin shiru ba'akuma cewa komaiba yasashi ciro wayar a kunnensa bin wayar yy da kallo,mamaki yacikashi waishin dagaske Kiran nashi akayine ake Kuma yimasa gar gad'i akanta?,yy tanbayar acikin ransa, girgiza Kai yayi tare yin murmushin jefen baki,zama yayi abakin gadon yafara neman numbern ta yadanna kira.
tana kwance akan gado kira yashigo wayanta kallo daya tayi wa number tagane numbern sane kindauka taki har wayan takatse yakira yakai miss call biyar bata dagaba cansai taji massage yashiga nanma bata duba,minti biyu sakani wata sakon takuma shigowa,zunbur tamike zaune tad'au wayar tabud'e sakon,asannu tafara karantawa.
_"Kamata_ _yy_ _kafin_ _sufarayimin_ _gargad'i_ _Susan_ _ko_ _wacece_ _kan_ _warsu_ _domin_ _kuwa_ _kanwarsu_ _ba_ _kowa_ _bace_ _face_ _saura_ _mara_ _amfani_ _zan_ _taimakane_ _abisa_ _umurnin_ _Daddyna_ _nazauna_ _da_ _rageggeyar_ _kanwarsu_ _bazaura_ _Kuma_ _sauran_ _wasu_ _inadad'a_ _jad_ _dada_ _miki_ _bazaura_ _ko_ _kyauta_ _akabani_ _banas musamman_ _ke_.
Jitayi zuciyarta na tafar fasa wurgi da wayar tayi takwanta ruf daciki ta kifa fuskarta ajikin katifa,sosai kirjinta ke harbawa yayinda zuciyarta tashiga tuna nomata abunda yawuce tun shekaru hud'u dasuka shud'e.............
Waishin wacece JUHAIFAH? Menene da lilin dayasa MAHFUS yake jifanta da muggan kalamai?dama can yatab'a sanin tane?
MUDAIJE ZUWA DANJIN YADDA ZATA KASANCE
DOMIN JIN CIGABAN LABARIN SAI KABIYA NAIRA 300 KACAL KITURA KATIN MTN TAWANNA NUMBER
08034690723
KOKUMA TA ASUSUN BANKI
SUNUSI YUSUF ALIYU
0421042738
GT BANK
Mommyn twins ceFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/IFwQqToBiiCHVosgNITJ4q
IDAN KINSAN BASIYA ZAKIYA BA DAN ALLAH KADA KIYI JOIN KIKARAN TA FREE INKI KWAI😂AWUCE GURIN
IDAN KUMA SIYA ZAKIYI SAI KIYI JOIN DAN SAMUN KARIN BAYANI SAI KONZO🤝🏻🌺 BAZAURACE' ITA!🌺
بسم الله الرحمن الرحيم
___________________________________
🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION🤝🏻
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
By✍🏻
Rasheeda S Director
PLS IDAN KINSAN BASAYA ZAKIYIBA DAN ALLAH KADA KIYI JOIN D'IN GROUP D'INNA IDAN BAKI SHIRYA SAYABA IDAN KUMA SAYA ZAKIYI TO KIYI JOIN DOMIN SAMUN KARIN BAYANE SAI NAJIKU MASOYANA NGD🤝🏻
~Free~ ~page~
🅿️5
Wacece JUHAIFAH?
Alhaji Yahaya asalinsa d'an jahar Plateau ne awani gari da ake Kira Yalwan shandam, su biyarne agun mahai finsu wato Malan Adamu, su uku cikin su d'aya, Alhj Yahaya sai kannensa biyu mata Hadiza wacce akekira da Goggo Hadiza,tana aure acikin Yelwa sai Hauwa'u wacce akekira da Mommyn Jos itakuma tana da aure acikin garin Jos,
Sai wad'anda suke uba d'aya Baba Salihu da Umma Rabi Baba Salihu Yana zaune da iyalinsa acikin garin Yelwa, itakuma Umma Rabi tana Abuja acan tayi auren ta da 'ya'aynta duk suna can.
Baba Salihu shine babban su duka, sai Alhj Yahaya kebinsa sai Umma Rabi Mommyn Jos kebin Umma Rabi sai Goggo Hadiza itace karamar su,
Suna rayuwar su gwanin ban sha'awa idan kagansu zaka rantse cikin su d'aya ne saboda tsabar had'in kansu da kawazucin junan su, basa nuna banban ci asakanin su kokad'an,Koda mahaifan su suka rasu sai Baba Salihu yazame musu tamkar uba dukda kuwa alokacin kowa nagidan mijin sa,duk abunda zasuyi kuwa sai sun nimi Sha warin sa,yatabbata yazame musu garkuwa.
Alhj Yahaya
d'an kasuwa acikin kwaryar Nigeria ayanzu Yana zaune ne da iyalan sa a wuse, dake cikin birnin taraiya Abuja, Alhj Yahaya mutumin kirkine yanada matarsa d'aya Hjiya Halima auren dangine a sakanin su, Haj Halima 'yar kanin Mln Adumu ne wato mahaifin su Alhj Yahaya, sunada yaransu guda hud'u
Al'ameen shine babba sai mebimasa Mujaheed sai Jabeer,saikuma autarsu Hafsat,Hafsat taci sunan kakansu ce wato sunan mahai fiyar Abba sai ake kiranta da JUHAIFAH,
JUHAIFAH tatashi cikin gata da soyayyar iyayenta da kuma yayunta,basa kaunar abunda zai b'ata mata rai kokad'an musamman yayunta afili suke nuna tsantsar kaunar dasuke yimata,yayinda itako take shuka siyarta son ranta danko shagwab'a babu kalar wacce bata iyaba suko biye mata suke' tayi son ranta. JUHAIFAH yarinya ce mai tsiwar gaske Dan haka bata ragawa kowa, ta sana dayyar ta ansha korin masu aiki agidan Dan kuskure kad'an idan sukayi mata saita daka salle tadire tace bata yarba haka za akoresu abakin aikinsu,akwai wata ranar datasa kaf aka kori yan aikinsu tunda ga kan driver mai gadi mai baiwa fulawa ruwa batareda wani kwakkwarar da liliba. akasake kawo wasu sabbi,ko fad'a tanemo tofa itace mai gaskiya danko bata laifi ko kad'an agurinsu.yanzu duk wani kasu wancin Abba Al'ameen da Mujaheed tare suke gudanar wa,
Ya Al'ameen yana zaune da matarsa Rukayya acikin gidan,Ya Mujaheed ma yayi aure sunar matarsa Nuwaira,suna zaune damarsa a Kaduna Dan shike rikeda ragamar kasuwan cin Abba na jahar Kaduna.Ya Jabeer Kuma shi Soja ne haryan zu baiyi aureba shima yana Kaduna acan yake aikin sa,alokacin JUHAIFAH tanada shekaru 15,duk sanda suka sami lokaci Ya Jabeer da Ya Mujaheed tare suke zuwa Abuja.
***********
Yau Monday dasauri tafito sanye da uniform Ya Al'ameen nabiye da ita rikeda School bag d'inta,wani motane yashigo ya gyara parking wani matashine yafito daga cikin motar yanufo su da murmushi d'auke akan fuskarsa yakaraso inda suke yace "barka da safiya Ya Al'ameen."
Ya Al'ameen yace "Yauwa Sulaiman antashi lfy?."
Yace "lfy lau."
yajuyo inda JUHAIFAH take Yana fad'in "madam ba gaisuwane?."
Harararsa tayi tareda Jan guntun tsaki takawar da kanta gefe,
Ya Al'ameen yace "yauwa Sulaiman in kashiga yanzu zaka fito ne?."
"Eh yanzu zan fita su Abba kawai Zan gaisar."
"Ok to yi maza kafito sai kasauke JUHAIFAH a School."
Dasauri tajuyo tace "Allah idan shi zai kaini gara nafasa zuwa School d'in."
"Murmushi Ya Al'ameen yy Dan yasan dama dakamar wuya tayarda yakaitan,Yace "to Shalele bari driver yakai ki, kin gani Abba najirana zamu fita.
Kafa tashi ga babbuga wa akasa tana faf'in "nidai Kai zaka kaini kokuma infasa zuwa School in."
Yace " a'a baza ma kifasa ba kidaiyi hakuri driver yakaiki gobe ni saina kaiki." Dakyar yasamu ya lallab'ata ta amince driver yakaita.
Sulaiman yawuce ciki a parlour ya iske Abba da Ammee cikeda gir mama wa yatsu gunna yagai shesu,Ammee tace "Sulaiman ya Mamar taka tana lfy dai ko?."
"Lfyrta lau Ammee tace ma nagai daku."
"Ato madalla. cewar Abba,
d'an shiru yy tareda sun kuyar da kansa kasa,
Abba yakalle sa yace "kun gamu da JUHAIFAH kuwa Dan yanzunna tafita zuwa makaranta."
"Eh Abba mun had'u acan waje."
sai ya mike tsaye Yana fad'ain "dama gurin aiki zani nace bari nabiyo nagai daku."
"to mun gode sosai Allah yayi albarka." cewar Ammee,yy musu sallama yatafi.
Bayan akwa 9
Abba da yanzu dawu wansa daga gurin aiki nazaune a parlour shida Ammee yakalli agogo yace "kash lokacin tashin su Mmn yy gashi na aiki Isa driver bari nakira Al'ameen yaje yad'au kota."
Ammee tace "ai kam in ba hakaba yau sai tahana kowa sakat da kuka akan ba'a d'aukota da wuri ba."
Abba yad'au wayarsa yakira numbern Ya Al'ameen sai akayi rashin sa'a bata shiga ba, yasauke wayar ya daddan numbern Sulaiman Yana d'agawa yace "kaje kad'auko JUHAIFAH a makarnta.
"toh."
yace,
Abba yasauke wayar,
Ammee ta dubi Abba tace "Alhj Sulaiman katura d'auko yarin yarna baka ganin zata iya nemansa da fad'a kasan halinta sairai bafa shiri suke ba."
Abba yace "to ai ni sonake surika kasan cewa tare Dan taha kanne kad'ai zasu saba da junansu har sufara Shirin' kinga daga Nan shikena sai atsayar da maganar auren nasu."
Numfashi Ammee tasauke tace "hakane kam to Allah yatab batar mana da alkhairi."
Ameen cewar Abba,
Sulaiman d'an kanwar Abba ne Wanda suke uba d'aya,wato Umma Rabi Yana son JUHAIFAH duk family bawanda baisan da zan cenba har yakaiga manya sun shigo ciki,Abba kuwa ya Amin ce dan yabawar da yy dahan kalin Sulaiman d'in yakuma d'au al kawarin aura masa ita idan takammala karatun ta. JUHAIFAH kuwa babu Wanda tafi tsana kamar Sulaiman Dan tun ranar dace Yana sonta ta d'auki tsanar duniyar na ta d'aura masa,rashin kunya da rashin mutunci duk bawanda Bata masa Amma yakafe yace yaji yagani.
Tana tsaye abakin get d'in makaran tar tundaga can tahan go motar sa kallo d'aya tamasa tad'auke Kai, kusa da ita yafaka motar yafito
yakaraso inda take yace
"Madam Bismillah." yafad'ad tareda nuna mata motar,
Ko kallon sa bata yiba bare abunda yake nuna matan, hasalima juyawa tayi zata bar gurin,yy saurin cewa
"Taho mutafi mana kinga yanma nayi."
Cikin hatsala tajuyo tarike kugu tace "Kai haba malam kabi kacikani da surutu ina ruwanka Dani da can Kai kaka woni bare kadamu da koma wata gida? tom Babu ruwanka Dani nafad'a maka kena taja tsaki."
Tajuya Dagaske zata wuce shi yy saurin ciro wayarsa yadan na numbern Abba yasaka a amsa kuwa Yana d'agawa yace "Abba kafad'a mata Kai katuroni na d'auko ta."
Abba yace "Mmn shiga motar yakawo ki gida yayanki baya gidane driver ma na aikeshi kinga kan su dawo za a ab'ata lokaci."
Daga inda take tsayen tanajin duk abunda