Showing 57001 words to 60000 words out of 85666 words

Chapter 20 - BAZAWARA CE ITA COMPLETEHAUSA NOVELS BY .txt

ba Saida yatabbatar da yasami bacci kafin yatafi,bayan fitar sa Jc yagyra cikin d'akin bayan yagama yafita tareda yaja Masa kofar.
Yajima sosai Yana baccin sai can da yamma yafarka lokacin zazzab'in yad'an sakesa ciwon cikin ma haka saidaifa marar nanan bb abunda yarago dagacikin ciwon marar,ahankali yasauko agadon yashige bathroom wanka yy tareda d'auro alawala yafi,
Yanafita yatadda Jc yakawo Masa tea,Saida yy salla kafin yazauna yad'an tab'a tea d'in yakuma komawa yakwanta.
Adaddafe yy sati biyu yakuma hayo jirgi yadawo Nigeria,
Su Mommy suna zaune sai ganin sa sukayi kamar an wurgosa,da mmk Mommy ke kallonsa Dan Bata tab'a sammaninsa a'irin wannan lokacin ba,ganin yanayinsa yansanya Mommy cewa "Kai MAHFUS daga Ina kk haka yanagan ka wani'iri."
Tafad'a tareda mikewa tazo inda yake tsaye tariko hannunsa taci gaba dafad'in
"Bakada lfy ne?wace irin ciwone yafiddaka cikin hayyaci haka".
Yace
"Banada lfy ne."
Yafad'a atakaice yajanye hannunsa dake rike ahannun Mommy yanufi bedroom insa.
tsaye Mommy tayi tana bin bayansa da kallo harya haura sama,saikuma tayi saurin bin bayansa tana shiga d'akin ta'iskeshi kwance akan gado,tazauna bakin gadon saiya bud'e idanunsa daya lumshe su, Mommyn takira sunansa tace "meke damunka?"
Ahan Kali yamosa lab'b'ansa yace "zazzab'ine".
Mommy tayi shiru tana nazartarsa saikuma tace "likita yadubaka?". "Eh" yace Mata saiya maida idanunsa yalumshe,ganin haka yasa Mommy mikewa tafita Dan tabarshi yahuta,
Kiching taje tagirka Masa Abu marar nauyi,tad'auka takai Masa d'akin ta'iske Yana bacci sai ta'aye Masa tadawo parlour.
Yau Kwanansa uku kullum Yana d'aki baya fita ko parlour,kullum Daddy Yana zuwa yaduba sa kafin yafita idan yadawo ma sai yashigo d'akin kafin yawuce d'akinsa.
Kullum sai Mommy tagirka Masa abinci takai Masa,idan takawo masan sai yace shi Lipton yakeso tagir ka Masa musamman ta'aje Masa flas kullum safe zatazo tad'auka taje takuma girka Masa wani Lipton in tazuba cikin flas d'in takawo Masa, duk sanda taje d'akin sai taga lemun tsami kusada flas in,
Ananne tagane matsalar nasa Dan tayi tayi yafad'a Mata da bakinsa yake.
Girgiza Kai kawai tayi tafice ad'akin.
Ranar jikinsa yad'an sakesa har ya'iya zuwa masallaci sallar magriba da Isha washe garima da asuba yafita yaje masallaci.

Zaune JUHAIFAH take a parlour Mommy tafito d'auke wata babbar barkar laida ta'iso inda take ta'aje laidar kusada ita tace
"JUHAIFAH wanna laidar yanzu tela zaizo yakarb'a,tund'azu yacemin gashi ahanya gashi har yanzu bai'isoba zan shiga sallah ko wata kila ya'iso Ina sallah,idan yazo zai Kira saiki d'auka kikai masa."
Mommy tafad'a tareda Mika Mata wayarta,
JUHAIFAH takarb'i wayar tana fad'in "tom"
Mommy takoma d'aki. Minti 5 bayan tafiyar Mommy Kira yashigo wayar,ganin sunan tela yabaiyana akan fuskar wayar yasa JUHAIFAH saurin d'aukawa daga cikin wayar akace "hajiya na'iso."JUHAIFAH tace "toh."
Tamike tad'au laidar tanufi waje,
Can tahango telan tsaye ta'isa inda yake Tamika Masa laidar tana fad'in "gashinan Mommy tace nabaka tana sallah ne."
Yace to yakarb'i laidar harta juya zata wuce yace "um d'antsaya kema yarinyar hajiya ce Amma dai ban tab'a ganinki agidannan ba sai yau kodai ke bakuwa ce."
Tace "Eh ni bakuwace."
Yace "naga alama da nad'auka ke yar Zahara ce sainaga haskenku ba'iri d'aya bace haskenku daban dabanne ke naki kalar hasken wani irin haskene."
Yanda yy maganar sai yabata dariya watoma kowani haske da kalarsa.
Sai tayi dariya.
MAHFUS nakwance kamar ansikare shi yamike tsaye yazo jikin window yajanye glass yaleko kasa karaf idanunsa yasauka kanta lokacinda takeyawa telan dariya daga inda yake Yana kallon bakin telan Yana motsi alamar magana Yana Kuma had'awa da dariya shima. dasauri yabar jikin window yanufi kofa.
Ganin maganar telan bana kare bane yasa JUHAIFAH juyawa tayi ciki abinta, tana shiga parlourn shikuma Yana karasa sauka gadan gadan yanufo inda take yamiko hannu zai kamota tayi saurin ja dabaya,dai-dai lokacin Mommy tafito daga bedroom inta ganin Yana yunkurin Kuma rukota yasa Mommy cewa
"Kai.kai dakata meye hakan metayi maka?."
Juyowa yy yakalli Mommy saikuma yamaida kallonsa ga JUHAIFAH Yana nunata da hannu Yana wani irin huci yace
"Mommy hirafa take dasaurayi awaje ranar tayi namata magana shine batajiba yauma takuma Kiran wani katon to Bari kiji ba'a kofar gidannan ba."
Mommy takalli JUHAIFAH dasauri JUHAIFAH tace
"Mommy ranarfa wani d'an ajinmune sukazo da Aysha shine nafita muka gaisa.
Mommy tajuya takalleshi tanafad'in
"Toyanzu da kk cewa wai Hira take nifa na'ai keta takawai tela kayan d'in kinmu."
Rai b'ace yace "to yanzu Mommy ita zata kaiwa tela kaya awaje?.'
Mommy tace "to ina ruwanka in takaiwa tela Kaya awajen meye damuwarka."
Kafad'a yad'aga alamun Babu ruwan nasa, saikuma yace
"To nidai nafad'a Miki idan maza Zaki Rika kawo Mana gida kitafi can gidan ku kirika kaisu can.
Yana kaiwa Nan yajuya yanufi step.
Cikin d'aga murya Mommy tace to basai kazo kad'au keta kamai data gidan nasuba tunda Kai kakawota.
Mommy tajuya takalli JUHAIFAH tace "wuce kitafi d'aki abinki."
Jiki asanyaye tashige d'aki..........




Mommyn Twins ce


πŸ…ΏοΈ22


Saida Mommy taga shigewar ta d'aki kafin itama Takoma d'akin ta.
Shirin fita Mommy tayi tafito tanufi d'akin JUHAIFAH kwance tasameta, JUHAIFAH naganinta tamike zaune Mommy takaraso ciki tace "JUHAIFAH zan fita yanzu balallai bane nadawo dawuri kiyi Mana girki kafin nadawo."
JUHAIFAH tace "tom"
Sannan tayi Mata adawo lfy tatafi.
Komawa tayi takwanta Dan lokacin d'aura abincin baiyiba,Kuma Zahara yanzu Bata zama bare tafita suje suyi Hira idan tatafi School tun safe sai yamma take dawowa gida. bayan sallar la'asar tafito tanufi kiching,awa uku bayan shigarta kiching tagama had'a lafiyayyen girki,tana cikin gyara inda tab'ata tajiyo muryarsa yanata kwad'awa Mommy Kira.
Ab'angaren MAHFUS in kuwa Jin Mommyn nasa Bata amsaba harya juya zai koma jin motsi a kiching yasashi tunanin ko Mommy ce a kiching sai yanufo kiching in dasauri Jin abar tasa tafara motsa Masa Yana cigaba da Kiran sunan ta,yakusa kansa ciki Yana fad'in "Mommy Lipton in fa yakare Baki girkamin waniba ." turus yy ganin ba Mommyn bace.
JUHAIFAH kuwa baya tabawa kofar kicking in tanajin shigowar sa da abunda yake fad'ar Amma ko juyowa batayi ba taci gaba da'abunda takeyin.
Bin bayanta yy da kallo saikuma yajuya da sauri jin yanda marar tawani tsiga Masa lokaci guda,Yana fita parlour Zahara nashigowa, ko gaisuwar datake yimasa bai amsaba yace "jeki girkamin Lipton yanzunnan."
Tace to ta'aje jakar makaran tarta saman kujera tawuce kiching shikuma yakoma d'akinsa adaddafe.
JUHAIFAH takalli Zahara dashigowar ta kiching in kenan tace "har'an dawo?"
Zahara tace "Eh,yanzu shigowa ta Ya MAHFUS yalikomin wata aikin."
JUHAIFAH dai murmushi kawai tayi takwashi girkin data shiryasu cikin kula takaisu saman dinning,sanna tawuce d'aki taje tayi wanka.
Cikin mintuna kacilan Zahara tagir kamasa Lipton in tajuye a cup takai Masa Yana kwance ruf daciki ta'aje saman durowar tafita, Koda Mommy tadawo ganin hardare bai fitoba saitaje d'akin nasa zaune ta taddashi akan gado yamike kafafunsa yahad'e su guri guda,kallo d'aya tayi Masa tagane cewa jikin nasane yamotsa,tayi Masa sannu sannan tad'au flas taje tazubo Masa Lipton takawo Masa yanda tafita tab'arshi haka tadawo tasa meshi, girgiza Kai kawai tayi tafita aranta tana fad'in "akwai randa Lipton da lemun tsami bazasu yimaka amfaniba.

β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…

JUHAIFAH tafito daga bedroom tasami Mommy zaune a parlour ta'isa inda take tazauna tareda yimata barka da war haka,Mommy ta amsa cikeda kulawa,d'an shiru JUHAIFAH tayi saikuma tanisa tace
" Mommy inaso naje shopping akwai abubuwan danake son siya."
Mommy tace "yakamata kam shikenan da yaushe zaki tafi sai direba yakai ki."
Mommy tamike tashiga d'aki bajimawa tafito tamikawa JUHAIFAH kud'i masu yawa tace "gashi nasan wad'annan kud'in zasu isheki."
JUHAIFAH tace "munyi magana da Ya Al'ameen yace zaizo yakawo min kud'i anjima."
Mommy tab'ata Rai takoma tazauna tana kallon JUHAIFAH,
tace "lallai JUHAIFAH kin kyauta wato yadda nad'au keki asheke bahaka kk d'au keniba?Dan zakije shopping saikin Kira gida akawo Miki kud'i gaskiya bakiyin adal ciba."
Sunkuyar dakai JUHAIFAH tayi sannan tace "kiyi hakuri Mommy wlh baha bane jiyane damuke gaisawa dashi shine nake fad'a Masa yau zanje shopping shine yace zai kawomin kud'in kada ad'aura Miki d'awai niya."
Mommy tasaki fuskarta,tace "Ashe hidimar da uwa zatayiwa d'iyarta d'awainiyace? To kice Masa injini nace yabar kud'insa bamason taimakon."
JUHAIFAH tayi murmushi cikeda jin dad'in abunda Mommyn tafad'a,sannan Mommy taci gaba dafad'in
"Idan kin shirya sai direba yakai ki".
JUHAIFAH tace " ngd Mommy."
Tamike takoma bedroom kasan cewar tarigada tayi wanka kaya kad'ai tasaka tad'au mayafinta tafito tace "Mommy natafi."
Mommy tace
"To nayiwa driver magana Yana kan jiranki yanzu haka."
Tace "tom.
Koda tafita lokacin driver har yafito da mota Yana jiranta tana Isa jikin motar yy saurin fita yabud'e Mata Baya tashiga shima yakoma mazau nensa yaja sukabar gidan.
Afarfajiyae I.B Nakowa shop, driver yafaka motar JUHAIFAH tafito tanufi ciki Nan ahankali tarika kusawa ciki tana duban abunta take bukata,tsayuwa tayi jikin wani dogon riga Wanda yy mugun tafiya da'ita, tad'aura hannunta jikin doguwar rigar tana kokarin ciroshi maganar dataji abayan tane yasata juyowa batareda tasauke hannunta ajikin rigiba,
Wani matashi tagani tsaye Yana fad'in "gaskiya kinsan kalarki idan kk d'auka saiki had'a da wancan."
Bin hannunsa tayi da kallo Dan ganin abunda yake nunawan,jakace da takalmi kalar rigar,matsowa yy kusa da'ita yad'aura hannunsa gefen nata yazaro rigar yamanna ajikin sa yana cigaba dafad'in
"Kalla kigani zaidace da jaka da takalmin can sannan Kuma zai dace da fatarki."
Murmushi tayi taresa juyowa,cak tahad'iye murmushin datake, da d'inbin mmk take kallonsa tacikin glass.
Abunda Bata saniba shine tun fitowarsu sukayi kiliya da shi ahanya kasan cewar glass in motar ba'a d'age takeba tanan ne yahangota cikin motar ganin daga ita sai driver,sai yabi bayansu ahanya gosulo tatsareshi sukuma suka wuce.
Ganin haurowa yake inda suke dasauri tabi gefen mutumin tabita bayan wasu kayaki tab'ulla tawani layin daban tana fitowa taganshi agaban ta kad'an yarage suyi karo ja dabaya tayi dasauri,Miko hannu yy yariko hannunta yajanyota yafita da'ita agun rike da hannunta kokarin janye hannunta take rikon da yy matan yasan yata kasa kwace hannun nata,Yana zuwa jikin motarsa yasaki hannunta Yabud'e gaba yakalleta Rai b'ace yy Mata nuni da hannu akan tashi,kallonsa tayi tana kokarin ja dabaya,yakuma tamke fuska yy magana cikin kakkausar murya yace
"Wuce kishiga nace!".
Yanayin yadda yy maganar Saida tazabura, dukda ta tsorata da yanayinsa Amma baihanata cewa "akan me zakace nashiga bayan bakai kakawoniba,sannan abunda nazo yin banyiba kace wai natafi to akan me meye ruwanka Dani?".
cikin tsawa yace "shiga tun ranki baib'aciba!!". Arazane tashige cikin motar Dan hatta hantar cikinta Saida yakad'a sanadin tsawan daya buga matan.
Zagawa yy yashiga gefen sa yaja motar da mugun gudu yafita aharabar wurin.
JUHAIFAH tarufe idanunta da karfi ganin yanda yake sharara gudu kamar zai tashi sama, cikin kankanin lokaci yakawosu gida ko gama dai-dai parking baiyiba yafito yazaga gefen datake yabud'e yariko hannunta tasako kafafunta kasa da sauri ganin yanda yafizgota kamar zai kifata kasa,
dakarfi yarike hannun nata harsaida tayi 'yar Kara,
yajanyota kamar zai tadata sama San sauri yanufi cikin parlour da'ita sai yasaki hannunta Yana binta da kallo Rai b'ace.
Mommy nazaune acikin parlourn sai ganinsa tayi rike da'ita dasauri Mommy tad'ago ganin yanda yatsare JUHAIFAH da'ido Yana wani huci, sai ta kawar da kanta kamar batasan dashigo warsuba.
MAHFUS yanuna ta da yatsa saikuma yagirgiza Kai yajuya fuuu yafice a parlourn.JUHAIFAH wani kuka ne yazo mata Dasauri ta toshe bakinta tajuya aguje tashige d'aki tazub'e kan gado tafashe da kuka,
Mommy tamike tabi bayanta ta'isa bakin gadon tazauna tadafa kafad'arta tace "JUHAIFAH tashi kizauna". Bamusu tamike zaune, Mommy tace "to share hawayen ki."
Taja gefen mayafinta tashare fuskarta, Mommy takuma dubanta tareda yin murmushi tace "to kada kisake yin kuka kinji?".
JUHAIFAH tagyad'a kai alamar taji.murmushi Mommy takuma yi tamike tsaye tafita ad'akin.
MAHFUS nafita yahango driver wanda shigo warsa kenan yanzu cikin zafin nama ya'isa inda yake Yana zuwa yashako kwalarsa cikin kakkausar murya yafara magana
"Waya baka izinin d'aukarta a mota har kafita da'ita wani gurin?".
Direba tsabar yaji shaka Saida idanunsa suka fiffito waje cikin azaba da miryarsa dayake fita da taritari yace "wlh ranka shidad'e hajiyace tace nakaita bayin kainaba".
MAHFUS yadad'a shakosa yace "daga yau kada kasake d'aukarta a mota,ai kinta kk acikin gidannan? duk inda zataje tatafi akafa kokuma a motar haya,duk randa hakan yakuma faruwa to kasani karasa ai kinka kenan har'aba...........




PLS KUYI HAKURI DAN ALLAH WLH YAU NAYI BA'INE BASU TAFIBA SAIDAF MAGRIBA SABODA BANASO NABARKU HAKA SHIYASA NAYI MUKU WANNAN D'AN KAD'AN IN DAFATAN ZAKUYIMIN UZIRIπŸ‘πŸ»


πŸ…ΏοΈ23


Sake kwalar rigarsa yy Yana binsa da mugun kallo sai Kuma yajuya dasauri yashiga motarsa yabar gidan.
Direba kuwa ana sakinsa yarika shafa wuyar sa inda MAHFUS yahad'a da rigarsa yashakure shi.
JUHAIFAH duk yanda taso zama ad'aki Mommy tahana,haka dole tafito. MAHFUS kuwa tunda yabar gidan baidawoba sai dare.
JUHAIFAH nazaune a parlour ita kad'ai tanajin sallamarsa tamike dasauri tana kokarin barin gurin kafin tayi wani yunkuri har ya'iso inda take yasha gabanta yad'aure fuskarsa tamau,cikin nuna Isa da takama yace "kada nakara gani kojin cewa driver yakaiki wani gurin,kekike biyansa kud'in aikinsa da duk inda kkso yakaiki zai kaiki?to dagayau idan Zaki tafi yawonki kisan Wanda zai kaiki Amma bashiba Dan ba'akawoshi Dan yy Miki aikiba,idan kinason fita yawonki kije akafa ko kisan yadda zakiyi ke Bari kijima idan yawo kk so to ba'a gidannan ba Dan Baki isaba."
Kallonsa tayi sama dakasa sannan tace "wannan Kuma Kai kasani Allah yatai maka kaima kasani ire-iren wad'annan ma'ai katan muma munadasu agidan mu badun hakaba bansan iya inda gurin naka zai tsayaba kada kaga Ina zaune agidanku kanima kawula kantani,
Dakake cewa ban isaba kaida ka'isa saika nuna isar taka nagani."
Tana kaiwa Nan tajuya zata wuce yariko hannunta tareda juyota yad'aura yatsunsa biyu kan lips inta yahad'a nasama da kasan yamatse, dasauri tayanye hannun ta dayarike dad'aya hannunsa d'aya hannunsa nakan bakinta tahad'a hannunta biyu tajanye hannunsa dake rike da lip inta tajuya kanta tareda yarfe hannunta Dan yanda yy matan Taji zafi.
Taja dabaya tana kallonsa saikuma tad'aura hannunta kan bakinta tayi raurau da'ido Dan sonyin kuka tuno abunda Mommy tafad'a Mata sai tajuya dasauri tashige d'aki.
Washe gari
Har tagama break tashiryasu kan dinning Mommy Bata fitoba Zahara tafito dashirin ta nazuwa makaranta tahayo kan dinning in tace "yauwa Aunty JUHAIFAH kinyi babban tai mako da da yunwa zantafi School ashedai ke kikayi Mana breakfast in."
JUHAIFAH tace "lallai ma bawa kowa nayiwaba,wa Mommy da Daddy kad'ai nayi,je kiching kikaib'i break inki fun Lami."
Zahara tayi dariya taredafad'in "adaiyi hakuri asakuramin acikin nasun ko kad'an to".
JUHAIFAH tace "to dai kinci albarkacin makaran ta inda agida kk da saidai kici na Lami." Zahara tad'au plt tazuba abincin tana fad'in "to ai nagode tunda har naci albarkacin makarantar in nazauna nace zanci anan zan makara amota ma zanci."
Tana gama d'iba tamike tacewa JUHAIFAH tatafi tayi Mata adawo lfy,
Zahara nafita JUHAIFAH tamike tasauko daga saman dinning in atsakiyar parlourn taganshi tsaye Kuma tahanyar dazata bi tashige d'aki komawa tayi tazauna saman kukerar dinning asannu yatako yazo inda take kallonta yake adakile yace "meyasa bakiyi maganar tun tuniba Saida kkga nafito,da Zahara kk ko Dani?".
Cikin rashin fahimta take kallonsa Dan Bata fahimci abunda yake nufin ba,saikuma takawar da kanta tana Yun kurin mikewa taji yasauke kafarsa kan nata,dukda kafar kad'ai yad'aura batareda ya murkushe ba Amma taji zafin hakan Dan akwai takalmi akafar nasa.tabi kafar nasa da kallo saitaji ranta yamugun b'aci wanna wula kancin ya'isheta haka yanzu wulakancin nasa yakai harda takalmi zai Rika takata lallai abun nasa yakai makura
Yace "harwani girki kk iya dahar kk gindaya wad'anda zasuci su Mommyn ma dahakuri sukeci bawai kodun dad'i ba,shiyasa wani lokaci abincin bayayin dad'i ashi dai kinasa hannu acikin girkin ne."
Ahankali yarika
janye kafarsa cikeda mugunda Yana zuwa karshen yatsunta yamurkushe su.
tsananin b'acin Rai had'eda bakin ciki yatasa kasa iya furta komai Yana sauke kafarsa tamike aguje tayi cikin d'aki,
tazauna bakin gado kasa danne kukan daya zo Mata tayi sai tafashe da kuka takifa fuskarta saman katifa tana kuka Mai tsuma zuciya Babu abunda yakai wanna kaskan ci da takalmin kafarsa zai take Mata kafa wai menene ma yazau nar da'ita agidannan har yanzu.kuma fashewa da kuka tayi aranta take fad'in "tunda su Abba basa Sona ai Baba Salihu shikam nasona tafiyata zanyi gurin sa."
Haka tarika kuka ahaka har bacci yad'au keta.

Yau kwana uku kenan kullom acikin Shirin barin garin take tanason fad'awa Mommy za'tayi tafiya Amma takasa, Dan batasan wani irin fassara Mommyn zatayiwa tafiyar nataba watakilama tace tabari tukun Dan Tasha cemata zataje gida tagaida su Ammee sai tace Mata tabari tukun,
Tunani tafarayi ko tatafine batareda sanin Mommyn ba Amma saitaga rashin dacewar hakan Kuma tasan bb yanda za'tayi tabar gidan batareda sanin mommyn ba,daga karshe dai tayanke hukun cin zuwa tasanar mata.
Mommy nazau a falo JUHAIFAH tafito tazau kusa da ita tare dayi mata barka da rana, Mommy ta amsa cike da kulawa tana dubanta domin acikin kwana kinnan talura akwai abunda yake damunta saidai yanayin ta alakantashi da tsaman dake sakaninsu da MAHFUS, JUHAIFAH tadan muskuta tad'anyi kasa da kanta,duk Mommy na lura da'isa Kuma yanayin nata nayanzu yanuna Mata akwai magana abakin ta,
Mommy tad'ago tana kallon ta tace "yayadai JUHAIFAH kamar akwai abunda kk son fad'a ko? Ina sauraran ki." JUHAIFAH takumayin kasa da kanta tana wasa da 'yan yasunta tabud'e Baki tafara magana dukda batada tabbacin Amin cewar Mommyn tace "Mommy dama iso naje Yalwa ne nagaida su Baba Salihu."
Mommy tace "hakan yana da kyau yakamata kan kije kigaidasu dan tunda akayi aurennan nasan bakijeba yanzu yaushene zakije?." mamakine yakamata dan batataba zatan Mommy zata amince da wuriba tasha mamakin yanda Mommy ta amince dawuri haka.
cikin muryan jindadi tace "gobe nakeson tafiya."
Mommy tace "to Allah yakaimu".
Cikeda zumud'i JUHAIFAH tace "amin."
tamike takoma d'aki cike da murna da jindadi nanta fara shirya kayanta, kaya maiyawa tasaka cikin akwati tarufe ta ajiye tana alla-alla dare yy gari ya waye.
Washegari gari tunda tayi sallar asuba Bata koma ta Kwan taba, taje tayi wanka tafito tafara shiri, yau ko Daman Taya Mommy aiki Bata samuba Dan shirin barin garin datake, koda Mommy tagama shirya break tashigo d'akinta tace tafito taci abinci, bawani abincin kirki taciba takomo d'akin karfe goma dai-dai tajanyo Jakarta tafito parlour,Mommy tadub'eta tace "har an anfito?".
tace "Eh Mommy."
Mommy tad'au kud'i agefenta Tamika Mata tace "idan kinje kice Ina gaidasu."
JUHAIFAH tace "to zasuji,amma Mommy kibar kud'in akwai Wanda kk bani nayin shopping innan sunanan."
Mommy tace "wancan daban ki ajesu kiyi shopping in dasu wad'annan Kuma kiyi amfani dasu wajen tafiyar sai kije driver yasau keki atasha."
JUHAIFAH takarb'a tareda yimata godiya taja akwatin ta tafita can tahango driver kusa da bakin get ta'isa har gurin,direba naganinta yy kokarin barin gurin dasauri

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login