Showing 1 words to 3000 words out of 85666 words

Chapter 1 - BAZAWARA CE ITA COMPLETEHAUSA NOVELS BY .txt

🌺 BAZAURACE' ITA!🌺



بسم الله الرحمن الرحيم

___________________________________


🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION🤝🏻
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________



By✍🏻
Rasheeda S Director

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DQ7frDuB7TjJ9gta4R2mte






INAYIWA UBANGIJI GODIYA DAYA KUMA ARAMIN LOKACI NAKUMA DAWOWA DAWANI SABON LITTAFINA MAISUNA🌺BAZAURACE' ITA🌺
INAROKON ALLAH YABANI DAMAR FADAR ALKHAIRI ACIKINTA YASARKAKEMIN ZUCIYATA CIKINTA DAWAJENTA👏🏻

😭ALLA KAJIKAN BABY KHAIRAT KASA MAICETONE👏🏻😭

free page

🅿️1


Ahankali take sauka daga matattakalar bene,kacokam hankalinta yakoma kan wayarda ke rike ahannunta,yarinyace da baza tawuce 'yar shekara 19 ba farace soll irin fari maikyanna,kyakyawace nakarshe,tanada tsawonta daidai kwarkwado baza'akirata doguwaba sannakuma bagajeruwa bace" tsawonta daidai,tanada manyan nonuwa ga uwa uba hips,duk d'aga kafarta dazatayi sai ilahirin jikinta yamotsa"irin motsinda duk lafiyayyen namiji idan yayi tozali dashi saiyawun bakinsa yatsinke.

asannu ta idda sauka, ta'isacikin katafaren parlour wanda yaji kayan'alatu dana more rayuwa,parlour ne babba yakayatu iya kayatuwa"

Asannu ta'isa cikin parlourn tazauna bisakan d'ayadagacikin, lafiyayyun kujerun da kejere acikin parlourn, har'alokacin idanunta nakan wayan,
lokaci zuwa lokaci saita saki murmushi mai matukar karawa fuskarta kyau,

"takai tsawon 20min a zaune tana aikin latsa wayar,sanna tamike tsaye,tajuya takalli gefenta tasauke manyan idanunta saman dinning, saita yamusa fuska tareda jan d'an karamin tsaki,asannu tafara d'aga kafarta ahankali tanufi wata kofar dake gefe dacikin parlour tanafadin "Aunty Rukayya! Aunty Rukayya!.
dai-dai lokacin tatura kofar, takusa kanta ciki,
masha Allah ranb'a she-shen kitchen ne mai matukar kyau danko yatsaru yaji kayan duniya,

wata 'yar matashiyar matace wacce akalla shekarunta zasukai 27 tsaye acikin kitchen d'in tana d'auraye kwanukan datayi amfani dasu, tajuyo tanafad'in "yaya lfy da irin wanna kiran haka?.
baki taturo gaba
tace "Aunty Rukayya kinsan bazaki iya yin aiki ked'aiba kikace bakya bukatar 'yar aiki,
duba kigani 2:00pm amma ace haryanzu ba'a kammala abinciba nifa kinsan bana jurar yunwa,tund'azu nashirya zanfita kuma yanzu haka Aysha jirata take zamutafi shopping saikirata take nafito mutafi yunwa tahanani fita,
wlh zan fad'awa Ya Al'ameen kawai ad'auko 'yar aiki dan mutun yarikacin abinci dawuri,dansaboda kishinki kikoramana 'yar aiki gashi yanzu komai mutum wai saidai yayi dakansa.

murmushi Aunty Rukayya tayi, tace "toh aini kena taimaka danki juri yin aiki dakanki koda ace kinje gidan mijinkine aiki bazai baki wuyaba dan kinrigada kinsaba,kinga tunda kinason cin abinci dawuri saikirika zuwa munayin aikin tare,kinga kekanki zaki karu dawani abun,

Tace, "lallaima cemiki akayi ban'iya aikinba?.

Aunty Rukayya tace "nasan kin'iya amma kikara akan iyawarki.

tace "Allah ni bazan wani iyayin aiki ba nidai bari Ya Al'ameen yadawo me aiki za a d'auko,
Aunty Rukayya tace "to ay laifin Yayan nakine tunda shi yasani yin girki har kala hud'u wai zaiyi bako,da ace girki d'aya zuwa biyune danajima dagamawa.

baki tatab'e tagota tagefen Aunty Rukayya tad'au plt tabubbud'e kulolin datashirya girkin aciki,manyan idanunta tawaro tareda bud'e baki cikeda mamakin ganin yanda tatsara girke-girke na musamman har kala hud'u,tajuyo takalli Aunty Rukayya "tace duk wanna girkin nabakonne? saikace wani Minister ne zaizo.
"to wayasani ko Minister ne"cewar Aunty Rukayya,yamusa fuska tayi tareda kawar dakanta gefe tana fad'in "cankuma tamatse muku kuda bakon naku, akanshi azauna ab'atawa mutane lokaci,Aunty Rukayya dai dariya kawai tayi dan tasan halin ta da tsiwar tsiya bata kyale kowaba,tad'ibi abincin tafito parlour
takoma kan kujerar data tashi tazauna,

Turo kopar parlour akayi tareda sallama,ta'ammsa sallamar tareda turo baki gaba takuma ture plt d'in abincin tareda kwabe fuska, tayi rau-rau da ido,asannu Wanda yayi sallamar ya'iso inda take,yanafad'in "subhanallahi! Wayatabaki shalele?. Tamatse idanu da karfi saiga hawaye shar-shar harda jan hanci,cikin muryar kuka

tace "ba Aunty Rukayya bace,


Yace "Rukayya to me Rukayyan tayimiki!?.baijira amsartaba yashiga kwallawa Rukayya Kira,dasauri tafito daga cikin kiching,
Cikin d'aga murya yace "mekikayi mata!?,yafad'a tareda nunata da yatsa,

binsu da ido dukansu tayi,kana tace"toni mekuma zanyi mata?.cikin Kuma d'aga murya yace "ba'abun da natan bayeki bakenan amsa nakeso kibani.
Sunkuyar dakanta tayi tana alhenin yanda, Ya Al'ameen yake goyawa kanwar tasa baya kodakuwa itace batada gaskiya, bama shikad'aiba duk family su,katse mata tunani yayi dafadin,dake nakefa,
D'ago kanta tayi

tace "wlh ni ba abinda nayi mata kawaidai akan girkine tamayar masa yanda sukayi,
Yajuyo yakalleta,

Yace"wai hakane?.

Kai ta gyad'a tanaci gaba da masar kwalla, numfashi yasauke tareda susa bayan keyarsa,shi kwata-kwata ma yakan mance da halin kanwar tasa sonta yakan mantar dashi,
Gyaran murya yayi yaceda Aunty Rukayya

"jeki cigaba da ay kinki,yasunkuyo yadau plt d'in yamaida mata gabanta,yace"ci maza abinki shalele laifinane da bance afara yimiki girkinki kafin na bakon ba,kiyiwa yayanki afwa, kai tagyad'a tareda goge y'ar guntun hawayen fuskarta,
ahankali tafara cin abincin kamar bazataciba,shiko mikewa yayi yabi bayan Aunty Rukayya,


korabin abincin bataciba tature plt d'in gefe.
tamike tsaye
tana lallasa waya takarashi akunne,

hello fito mutafi. tafad'a taredad'au kar
gyalenta da da 'yar karamar Jakarta
dake hannu kujera,
tanufi kofar fita daga parlour tafito farfajiyar gidan.

Ya Al'ameen nashiga kiching d'in yatadda Aunty Rukayya tsaye ya'isa inda take yarungume ta tabaya numfashi tasauke tad'ago hannu tashafo gefen fuskarsa,ahankali tafurta "kagaji ko?.saida yalumshe idanunsa yakuma bud'ewa sannan

yace
"sorry My Ruky kinsan yarinyarna karamar yarinyace kinsan shikuma yaro d'an lallamine ki..saurin juyowa tayi batareda tabari yakarasa zancen nasaba, Dan tasan kullum kalmar nasa baiwuce kiyi hakuri yarintace ke damunta ba, ita yanzu harta saba da halin kanwar tasa danshi baya tab'a ganin laifinta,kullum ayarinta take.


Tace"taho muje kad'an watsaruwa saikafi jindad'i.
Tajanyo hannunsa suka fito.


Tamfasetsen gidane maid'aukeda part uku,asannu tanufi d'aya daga cikin part biyu dasuke jere,ahankali take d'aga kafarta tana haurawa bisa steps d'in dazai sadata dakofar shiga cikin part d'in,
dasallama tashiga cikin parlour,wata dattijuwar mata ce wacce akalla shekarunta zasukai 50 years tanazaune acikin parlour dawasu yara biyu 'yan kanana shekarunsu baiwuce 3 years ba,
dagudu yaran suka mike ajikin matar suka taho suka rungumeta,
"oyoyo Mamy
yaran sukafad'a sunad'ada rungumeta,
murmushi tayi tadad'a janyosu jikinta tareda shafa kansu,
tasunkuyo dai-dai tsawonsu ta sunbaci goshinsu da
kumatunsu,

tace " Hi
Guy's kuna lfy?

cikin maganarsu dabata gama nuna abakinsuba,
sukace

"Eh, "Mamy zakije damu?

ido tad'an waro saita d'aura hannunta a kumatunta tadafa tad'an juya idonunta sama kamar maiyin nazarin wani abu,suko yaran yanda tayin haka suma sukayi,
d'ayanda ke gefen damanta yasauke hannunsa a kumatunsa, yaja hannuta dak'ekan fuskarta

yace, "Mamy tachi mutafi,saiyariko hannun d'ayan yanafad'in
" Hussain jomupita.
mikewa tayi tana murmushi, tace "Hassan Hussaini,kuzauna yau badaku zantafiba kujirani yanzu zan dawo bajimawa zanyiba zankawo muku tsarabarku kunji?,
kai suka gyad'a mata,


tace " yauwa good boy's,
tariko hannunsu takarasa cikin parlour inda matar nan take,tazauna kusa da ita,
yaran suka zame ahannunta suka koma kafar dattijuwar,kunnuwarsu tarike tana fad'in

"nikutashimin anan sarakunan yawo,kukenan duk inda za'aje saikunce zaku,kodashike laifin uwar takuce data maidaku kamar jaka duk inda zata saitaje daku,

baki taturo gaba tace "Ammee sud'inne jakkar? dankawai sunce zasubini,

Ammee tace

" Ai su wad'annama sunfi jakka ni kid'ibesuma kutafi sun'isheni dama dashegen surutun nan nasu.

tace "Ammee keda kanki zakije nimansu anjima,dan dai yau bada mota zanfitaba napep zamushiga da Aysha kuma banaso sud'ibi kurar hanya datare zamu tafi,Ammee kikula dasu sosai.

Ammee tace" to masu 'ya'ya,dadai kin d'ebesu kuntafi da wanna dokokin da ake gindayamin akansu,

Murmushi tayi tamike tsaye
Tace "Ammee kidai kulamin dasu Allah idan bahakaba kuka zanyi tayimiki kuma bazan tab'a yin shiruba harsai Abba yadawo yararrasheni dakansa, dan yau ko Ya Al'ameen da Ya mujaheet da Ya jabeer ne suka rarrasheni bazan tab'a yin shiruba,

Dakuwa Ammee tayi mata,
Tace "kinci gidanku ja'irar yarinya kawai,yoni kansuzo ay na nakad'a miki dukan tsiya kinga sazo suyimiki lallashin da tushi,

Bubbuga kafa tashiga yi tareda matse idanu,

Dasauri Ammee tace
"Ya'isa shikenan jeki zan kular mikidasu.

Saida takuma sunbatar yaran agoshi kafin tafi,
Tanafita direct bakin get tanufa, dasauri wani dake goge d'aya dagacikin motocin dake jere a parking lot yayi saurin isa inda take,kamar zai durkusa kasa tsabar girmamawa,

Yace
"Ranki shidad'e wata motar za'afito da ita?

Yayi maganar kansa asunkuye,

Hannu tad'aga masa batareda tace dashi komaiba,
Ganin hakan kuwa yasashi saurin jadabaya dan yafahimci abinda take nufin,dan har idan kuwa yana bukatar cigaba da ay kinsa tokuwa kada yakuma tanbaya nabiyu, ay bashiri yayi saurin barin gurin,

Tunkan ta'isa jikin get d'in mai gadi yayi hanzarin bud'e mata karamin kofa,takusa kai tafice acikin gidan.

Shiru unguwar babu motsin kowa,lafiyayyun gine-gine ne tareda shinfe d'ed'd'iyar titi wacce aka kawatata da koyayen wuta da furanni masu matukar kyau da kyalli da d'aukar ido.

Bakajin motsin komai sai iska mai fidda sassanyan kamshi mai matukar dad'i ke ketashi,Wuse Kenan.

Asannu talumshe idanunta tareda shakar daddad'ar kamshinda ke yawo asassanyan iskar dake kad'awa.

Gadukkan alamu tana matukar jin dad'in yanayin,sai murmushi take tana dad'a jefa kafarta akan shin fid'ed'iyar titin,

Abin mamaki duk dakuwa girman titinna Amma ba'alamar ababen hawa ko guda, hasalima shiru gurin yad'auka.

Kofar wani get tatsurawa ido wacce kedaga can sallaken titin,saita ja tsaki afili tafurta,

"Amma kincika 'yarrainin wayo sokike ni najiraki kenan?
Tayi maganar tareda d'ago wayarta talallasa takara akunnenta anad'agawa

Tace
"Kinfasan banajira,

Aysha dake biye dakiran
tace
"Sorry tawan gani dafda bakin get zanfito,

Yamusa fuska tayi cikin salonta nako oho tasauke wayar, dai-dai nan ta'iso tsakiyar titin.

Damugun gudu wata mota tasharo kwana,
cikin razana dafirgicin ganinta atsakiyar hanya, gakuma mota gadan-gadan yanufota da mugun gudu,idan tace zatakoma dabaya tofa motar zata iya karasowa gareta hakama idan tayi gaba,
Kara takwalla tareda kankame idanunta,arazane yataka wanin wawan burki,

"inanlillahi'wa'inna'ilaihirraji'un' yafurta amatukar tsorace,

Dasauri yab'alle marfin motar yafito, yataho inda take durkushe sai kakkarwa take har alokacin idanunta narufe,

Hannusa narawa yamika yariko hannuta yad'agota tsaye,

"Waiyo Allah, Kai Allah nagode maka daka tsayar iya haka ay ni nayi zatonma nabigeki gaba d'aya, kaigaskiya na auna arziki.
Cewar mutumin dake Jan motar,yacigaba

"Kiyi hakurifa wlh ban lura da mutun na tahowaba,Allah dai yasa bakiji ciwo ko kad'anba dan naga kinata matse hannuki,

Yafad'a yana kokarin riko hannun nata, sai asanna tabud'e idanunta jin bugun zuciyarta ya dai-daita, tayi saurin sake hannuta batareda ta bari yasami damar rikeshiba,
tazabga masa wani uban harara tareda jan dogon tsaki,

Tace
"wlh Allah yayimaka babban taimako daka bigeni da wlh yau kayi bankwana da farin ciki, kana tuki kamar baka gani duba kagani yanda kashafamin datti ajiki ni wlh Allah bayarda zanyiba,yaza'ayi karika tuki sonranka saikace anyimaka titin kaikad'aine.

Yace "Kiyi hakuri wlh bada gan-gan
nayiba nayi kokarin kauce miki amma saidad'a kusawa kikayi, babu yanda zanyine kingama ay Allah yatakaita kiyi hakuri.


Sosai tadage tarika surfeshi dayimasa tsiwa ita adole kawai shine bashida gaskiya,shiko hakuri yarika bata darokonta akan tayi hakuri tatafi.

Ahankali yakoma yajinginu dajikin sit in motar, yalumshe idanunsa alokaci guda yabude,saiyaja guntun tsaki, yakalli kayataccen agogon da ke d'aure ahannunsa,akalla yakai tsawon 20min azaune acikin motar,shibawai rikicin dasuke bane yadameshi ba,barinshi da'akayi zaune acikin mota kuma ana batamasa lokacinsa akan wani shirmen banza, yakai dubansa kan titin har alokacin tananan tana zuba tsiwa, nanma wani tsakin yakumaja, idan ransa yayi dubu to yabaci,

Cikin zafin nama yab'alle marfin motar yafita ,

Wow Masha Allah

"Allah yayi halitta anan,

Inda suke yanufa yana fad'in "wanna wace irin rashin mutuncine Sadeeq? yazaka barni zaune acikin mota kazo katsaya yin wani shirmen banza.

Yajuyo gareta yanunata da d'an yatsa

Yace
"Kewaye daza azauna baki hakuri kina fad'in bazaki hakuraba!?

Wlh inda ni nake driving inna da bigeki zanyi inbige banza inga mai zai faru,kifito kan titi kina tafiya kamar titin na ubankine,harza'a tsaya ana baki hakuri kitsaya kinayiwa mutane rashin kunya,

Yamaida dubansa ga Sadeeq

Yace
"Kaikuma banza mara aikinyi katsaya batamin lokaci akan wani banzan Abu kazauna saibata hakuri kake kamar wata uwarka,

Sadeeq dai murmushi yy
Yace
"Komadai me yanzudai tahakura muje.

Ido taware cikeda masifa
Tace
"Waya fad'amaka nahakura ay wlh tunda yazageni yajawa kansa musifa, dakuma kakecewa wai titin na ubanane inda Kai kake tukin daka bigeni,aiko dakayi bankwana dafarin ciki,rayuwarka kuwa zatakare a firizin kaid'in titin na tsohonka ne dazaku rika gudu son ranku.

Takarashe maganar cikeda tsiwa tanayi tana ware manya idanunta tareda kad'asu cikin wani irin salo namusamman.

Azafafe yad'aga hannu zai kaimata mari Sadeeq yayi saurin rike hannunsa,
Yace
"Haba Man mezaka buga anan kadubetafa du-du nawa take wanna ay batafi sa'arsu Zahara ba,baikamata mu mubiye mataba,

Kallon Sadeeq yy
Yace
"Zaginanafa tayi,
Wlh saina koyawa yarinyarna hankali wawuya kawai.

Sadeey yace
"To ay kai babbane saikayi hakuri,

Sadeeq yarika bashi hakuri da tausasaki yajanyo hannusa yamaidashi cikin mota,

Aysha dake tsaye duk abinda yafaru akan idonta yafaru,tajinjina kai tana mai mamakin hali irin nakawar tata ita babu wanda takyale daga nagidan har nawajen tagirgiza takaraso inda take.

Sadeeq sanda yatabbatar daya zauna kafin yarufe marfe motar,yazago gefen sa yashiga yaja motar sukayi gaba.

Aysha tace "taho mutafi,kamar jira take tajuyo cikin masifa,

Tace
"Ay wlh saiyasan waya zaga idan yasaba wulakanta mata yashare tokuwa yau zaisan yataba gamonsa.

Saikuma tasaki kuka tana bubbuga kafa akasa cikin muryar kuka had'eda shagwab'a

Tace
"Allah bazan kyaleka kaci banzaba saina nuna maka ni 'yargatace gaba da baya.

Aysha tace "kidaiyi hakuri kingama suntafi abinsu bakuma saninsu kikayiba bare kinuna masan.

Dakyardai Aysha tasamu ta lallab'ata sukatafi,

Tuki Sadeeq yake Amma hankalinsa naga abokin nasa ganin yadda yahad'e rai sai'aikin jan tsaki yake tareda taunar lips d'insa nakasa,

Numfashi Sadeeq yasauke saikuma yasaki 'yar karamar dariya,
yace
"Kai wlh Allah yataimakemu dayarabamu da wanna rikicacciyar yarinyar, kai kaji yarinya da rikici ko,
Ammadai gaskiya taburgeni,ni tana maganarma gabad'aya jikina b'ari yake dan gaskiya yarinyarfa tahad'u idan tajuya idanunta kamar naruga aguje haka nakeji,saiyakuma sakin dariya,

Yace
"waikai Man baka lura dahakan bane? Wlh yarinyan tahad'a komai gaskiya taji kayan had'ifa sosai,

harara yagurga masa yace "banza namamajo kace dama duk wulakancin datayimin kaika shirya,shiyasa kad'aukoni wai nayimaka rakiya zuwa gidan abokinka, daka barni agida abina da banzo nahad'u da bacin ran waccan banzanba, to saime inta had'un zaka iya maidani gida saikaje gurinta.

Sadeeq yace "yihakuri mutumina aini nad'aukokane dankaga gari kai kenan duk sanda kazo hutu kasarna saidai kakarici zamanka agida bazaka fita kad'an yawataba,kuma ay ni duk son matana bazance inason waccan yarinyarba dan tafi karfina, dankuwa da matan manya tafi kama,kamar irinsu governor minister dadai sauransu,
Saikuma irinku manyan kusoshin Nigeria.

Azafafe yajuyo yace wad'in ni Allah yasawake ai ko mata sun kare aduniya bazan tab'a auren waccan wawuyar yarinyarba,

"Kanaji ko Sadeeq?

Sadeeq yace "inajinka

Yace"idan zakarika yin kwatancenka kadaina misaltawa dani.

Dariyar shakiyyanci Sadeeq yayi yace "to ranka shidad'e.

Daidai nan suka iso bakin get yadanna hon maigadi yawangale musu get suka kusa cikin gidan, Sadeeq yadaidaita parking yafito shiko nahakimce acikin motar,saida Sadeeq yazago gefensa

Yace
"Fito mushiga mana,

Kamar bazai fitaba saikuma yazuro kafarsa waje yamike tsaye, kallo d'aya yayiwa gidan yad'auke ido,

tsayuwarsu yayi daidai dashigowar wata mota,direban yagyara parking ajerin motocin dasuke cikin parking lot,dasauri yafito yazaga yabod'e marfen baya cikin girmamawa yad'an jadabaya dan nacikin yasamu damar fita, wani farin dattijo ne yafito daga cikin motar akalla shekarunsa zasukai 60 cikin shigarsa na kamala da dattako.

Dasauri Sadeeq yamaso inda yake cikeda girmawa yace
"barka da dadawowa Abba.

Abba yafad'ad'a fuskarsa da murmushi
yace "yauwa Sadiku kuna lfy daiko?

Sadeeq yaritsina yashiga gaidashi

Daga inda yake tsaye yad'an ritsina yace "barka da rana,

Abba yakuma fad'ad'a murmushinsa yace "yauwa wanake gani kamar

*MAHFUS* Tukur Shali kodai kamace?.

Sadeeq yace "shinedai Abba bakamaba.

Abba yace "toh lallai marabanku, Kai Sadiku abokin naka baisan dazuwan na kubane?

Sadeeq yace "yasani Abba.

Abba yace "toshikenan ni bari nashiga ciki.

Abba nashigewa
Sadeeq yaciro wayarsa ya daddan yakara akunnensa "hello mun iso.

Ya Al'ameen dake zaune a parlour yamike tsaye yanafad'in naji kace kun iso, au bakai d'aya bane?

Sadeeq yace "Eh nida mutumina ne,

Ya Al'ameen yace "wani mutumin naka?

Sadeeq yace "kafito mana zakaganshi ay.

Dawayar rike akunnensa yafito, da mamaki yake kallon wanda Sadeeq yazo dashi,dankuwa bai tab'a sammanin hakanba, yayi mamakin ganin wanna fuskar anan, dukda kuwa yasan cewa abokinsa Sadeeq yana abokantaka dashi sosai, Amma kasan cewarsa babban mutum wacce duniya tasanshi take Kuma burin cigaba darayuwarsa acikinta baiyi zaton ganinsa haka dasaukiba,dukda kuwa hakan bazai iyabashi wuya wajen ganin nasaba kasancewar suma duniyar tasansu Amma sanin da akayiwa MAHFUS Tukur Shali yagirmi sanin nasu.

Ya Al'ameen cikin sakin fuska yamikawa MAHFUS hannu,shimadai bayabo bafallasa yamiko nasa hannu sukayi musabaha,sanna yayi musu jagora zuwa cikin part d'inshi,

Cikin katafaren parlour sa yayi musu masauki,
Hira suka bude, Sadeeq sai zuba surutu yake shiko MAHFUS wayarsa yaciro yashiga latsawa batareda yasanya musu baki acikin hirar tasuba,

Aunty Rukayya tafito suka gaisa itama tayi mamakin ganin MAHFUS d'in, taje takawo musu kayan ci dana sha wandatashirya
tacikasu dashi,

Sadeeq yawashe baki yace"Kai amarya Kuma uwargida duk wanna namune?

Tayi murmushi tace "duk nakune idan bai isabama sai akaro,

Ato lallai mungode kinga dama yunwa nakeji rabondanaci abincin kirki tun daren jiya shimad'in sanda nashiga gurin hajiyata naci.

Ya Al'ameen yace "ay tunda rawar ido kasa gaba kakasa tsayar da mace guda ka aura ay kuwa kaida samun nutsuwa kaci abinci yadda kakeso cikin kwanciyar hankali babushi,dubekafa harkafara zama tuzuro"

dariya Sadeeq yatuntsire dashi yakalli gefenda MAHFUS yake saiyakuma fashewa da dariya,cikin muryar dariya

yace
"Todai badani kakeba yanzukam kanayi Dana gefen daman kane Dan naga alama soyake yamutu tuzuru,yakarashe maganar tareda kuma shekewa da dariyan shakiyyanci kad'an yarage yashake da loman abincin dayakai bakinsa.


Ya Al'ameen yace"ay garashi kaifa ba yarinyar dazaka gani bakace kanasoba Amma haryau kakasa fidda guda cikinsu,

Yace"saurin me kake kunkusa kusha biki dankuwa yanzu nafidda matar aure Abida zan aura,

Ya Al'ameen yace "Allah dai yasa dagaskene bayaudararta itama zakayiba,

Duk hirar dasuke d'inna MAHFUS baice dasu kalaba abincin da Aunty Rukayya tazubamasa ko kallonsa baiyiba,
Ya Al'ameen yalura dahakan sai yace dashi "Bismillah tareda nunamasa plt d'in abincin gabansa,

Kallo d'aya yayiwa abincin yad'auke ido batareda yace kalaba, har Sadeeq yagama cikin abincinsa shiko drink bai kurb'aba,

Sadeeq ko yasan hali shiyasama baice dashi komaiba,

Adaidaita ne ya'ajesu abakin get, koda suka fito kosallama batayiwa Aysha ba tayi wucewarta ciki, Aysha ko baki tabud'e tana binta da kallo daga bisani taketare titi tashiga gidansu,

Direct part 3 tanufa dasallama tatura kofar parlour, takusa kanta ciki tana isa tsakiyar parlour, tawurgarda jakar hannunta da bag d'inda talodo shopping inta aciki, tacire mayafin kanta da d'ankwalinta da takallimin kafarta duk tayi wurgi dasu atsakiyar parlour,

Jin karar wurga abu yasanyasu kallon inda karar ke tashi,sananin mamaki yacika shi

" itacefa shin wanna mutunce ko aljana to mekuma yakawota nan?yy tanbayar aransa saiyaji ransa gabad'aya yab'aci,

Murmushi Ya Al'ameen yy yace "shalele har andawo kenan?

baki taturo gaba tayarfe hannu cike da shagob'a

tace "Allah Ya nagaji tafad'a tareda zama hannun kujerar dayake,

Yace"badole kigajiba bayan ba'a mota kika tafiba duk kind'ibi kurar titi,

Sadeeq kam baki da hanci yabud'e yana kallon ikon Allah

Ya Al'ameen yakallita tareda yin murmushi yace "shalele bakiga ba'i ba kigaidasu.

tad'ago takalli inda yake nuna matan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login