Showing 18001 words to 21000 words out of 95354 words
Chapter 7 - BUGUN ZUCIYA Hausa Novels Complete by Fadila Lamido.txt
Allah wadai mutane suketayi da halin deeni yayin da wasu daga ciki suka rufan ma ummi da hayaniya cewa tajawa danta kunne"
Wasu dadtawa ne su 2 suka saka Jamal amota suka nufi asibiti dashi"
Cikin gida ummi ta nufa tana share hawaye, hakika babu dade ace danka bayaji tabbas ta sani duk unguwannan babu me irin dabi,un deeni kuma tasani kuskure ne da tayishi tun abaya ta manta cewa ice tun
yana danye ake tankwara shi, afili tace babu komai zanci gaba da addu'a Allah ya shirya min shi"
Koda tashiga gida batawa deen mgn ba wuceshi tayi tana cigaba da share hawaye"
Kallonta kawai yayi ya kyauda ido, daidai lokacin Asmau ta shigo fuskanta dauke da murmushi"
Shima murmushi yayi sannan yace zoki zauna"
Girgixa kai tayi tace sauri nake amman yaya akayi kasan Jamal?
Murmusawa yayi sannan yace ai jiya daku ka wuce na kare musu kallo na gane yayaki ne ta kama dake dana gani"
Shiru sukayi zuwa can tace yaya shamsundeen wai dan Allah meyasa kake bacci akofar gida?
Murmushi ya sakeyi sannan yace sabo da bana samon bacci da dadaddare"
Cikin mamaki tace toh meyake hanaka baccin?
Cikin sauri ya jawo hannunta ya hada da nashi sanan ya kafeta da ido yace tunanin Ki ke hanani sukuni harna kasa bacci
Tunani na kumaπ?, dama kaima kana tunani na?
Kema kina yin nawa ne?
Cikin sauri ta girgiza kai, tare da fadin a'a"
Karya kikeyi Asmau kinayi na tabbatar abinda nakeji kema kinaji"
Hannuta ta janye sannan tace zan tafi, kar aga na Dade"
Karajan hannuta yayi sannan yace toh wani tukuici zakibawa duna"
Shiru tayi zuwa can tace to ka fadamin abin da yake ci gobe na kawo masa"
A'a bayason abinci, goben idan kinzo zan nuna miki yadda zaki masa"
Aranan saida deeni ya rakota har kusa da gida, suna tafe suna hira , yau ma'u jitake kaman karsu rabo da deeni, koda suka rabo sai waiwayen shi take"
Shima kasa tafiya yayi yana jira wai sai ta shiga gida" darker suka hakura da kallon junan su"
Tana shiga gida tasamu mama hankalinta tashe ko tambayan ina ta tsaya batayi ba tace"
Asmau Jamal ne ya buguwa usman waya wai yayi hatsari tun dazun fah, gashi har yanzun basu dawo ba"
Cikinta cike da dariya tace hatsari kuma??
Kafin mama ta bude Baku suji tsayowan mota arude ummi tayi waje, yayin da asmau ta shige daki dan tasa bazata iya boye dariyarta ba"
*Mmn Yazeed*β
[24/01, 11:03 a.m.] βͺ+234 906 689 6652β¬: ππππ
β*BUGUN ZUCIYA*β
( βHeartbeatβ)
πππ
π
πππ
βByβ
π
ββ*Fadeela Lamido*
*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATIONπ€*
Dedication ππ»
*Firdausi Sodangi*π
2β£2β£ to 2β£4β£
ππ Tana shiga daki ta fashe da dariya bakin window taje ta tsaya tana kallon yadda Usman ke kokari tallafu Jamal"
Gajeren wando ne kawai ajikin Sa, kafan shi duk 2 nade suke da bandeji haka damtsen hannun shi na dama"
Saida taga shigowan su sannan ta koma bakin gado ta zauna taci gaba da dariya tare da share hawayen mugunta"
Bayan usman ya kwantar da jamal akan gadon dake dakin dake kusa dana abba, gefe gadon ya koma ya zauna sannan yace manga yaya akayi ka tsaya kare yacije ka?
Ido ya runtse dan babu halin bude jarida"
Binshi da kallo usman yayi sannan yace ina mgn kayi shiru"
Cikin fada yace dallah Malam karka dame ni"
Shiru usman yayi yana tunani zuwa can yace to kodai Karen daya tsare asmau ne ranan ?
Bansani ba, nace maka kabar mgn sai wani nanatawa kake kare2 salon wani yazo yaji kuma"
Toh meye idan anji uban waye yace ka tsaya kare ya cijeka, wlh ka bani mamaki Dan Allah ji inda ya maka kaca2"
Kaga usman banaso ka rabu dani kawai"
Mikewa usman yayi ya fice dan abin takaici yake bashi"
Mama ko tayi tayi da asmau taje ta gaishe da Jamal taki zuwa, tanajin yadda mama ta takarkare tana gayawa Abba wai yau Jamal ya auna arziki"
Dariya ce ta kwace mata taita tuntsurawa dan haka daga mama har Abba suka juyo suna kallon ta"
Cikin fada Abba yace wanne irin iskanci ne wannan?
Nan dan ta daure fuska tare da sukuyar da kanta kasa"
Abba ne yaci kaba da cewa kina hauka ne, yaya ana mgn Mutun yayi hatsari Ki kama dariya"
Mamace tace ai yanzun dabi'a data fara kenan ita kadai ma saikaga tana dariya, narasa gane kanta, Jamal ko Daman ta tsane shi wlh ina kula da ita tunda nace mata yayi hatsari annashuwa ta cika fuskanta"
Fada yaita mata tun yanayi cikin fada har ya dawo nasiha akarshe ya kara da lallashi"
Kwana 2 jamal ya fara samun sauki, dan haka yau Usman gida yake shirin tafiya dan matar sa ta dawa ta dawo tun ranan da abin ya faru"
Jamal na zaune akan kujera yayin da usman ke zaune agefen shi"
Usman ne ya kalli damtsen hannun jamal yace kai amman gsky karan nan ya iya tsiya toh wai ta bayanka ya biyo ?
Kwashe duk yadda akayi yayi ya gayawa usman sanna ya kara da cewa kasan Allah saina naga uban da ya tsayawa mishi"
Usman ne yace kana nufin karan yafi irin karnukan mu horo"
Guntun tsaki Jamal yaja sannan yace wannan fa umarni ake bashi kuma ni tunda nake bantaba ganin kare me zafi kalan shi ba, amman na dakeshi sosai na tabbatar inda nai jiya shima saiyayi jiya dan dukan dana mushi banzaci zai iya tashi ba bare har yamin wani abu, kuma ni fa bawai nabar mgn bane"
Aidama ko kanarta ni bazan bari ba abinda yasa ban daga mgn ba sabo da naga baka son asani"
Eh banaso"
Towai saboda me?
Haba usman ina Sonja aga kare yamin haka?
To ai tsautsayi ne ko?
Shiru yayi zuwa can yace nifa sabo da wannan yariyan ne banason asani, kartazo ta raina muta ne
Kallon shi usman yayi sannan yace au wai Asma'u?
Ita, kasan yariyar ba kunya kareta ba kuma akwai wani abu da nake nazari idan na tabbatar zan gaya maka"
***
Washegari ta kama alhamis dan haka yau babu makaranta ma'u na daki tana ninke kaya taji kiran mama"
Bayan taje mama fada taita mata akan kin zowa gaida Jamal datayi, haba asma'u wanne irin zuciya gareki ace mutun agidan ku yayi hadari Ki kasa zuwa ki gaida shi, haba asma'u ke bakiji dadi bama daya nuna yadamu da lamarin ki ?
Nan danan ta fara matso hawaye tare da fadin mama hakanan fah ya zanene saboda tsabar cin zalli wlh na tsane shi kuma idan Allah ya yarda bazai gama da duniya lfy ba"
Ah, ah ah babban mgn Asma'u kanki daya kuwa? Toh idan kece uwarshi saiki hanashi gamawa da duniyan lfy"
Wucewa mama tayi ta barta aguri, zama tayi taita kuka domin ita harga Allah bata kyaunar ganin Jamal, bata tabajin ta tsani wani ba kaman yadda ta tsaneshi"
Har yamma mama bata sake mata mgn ba koma ta mata bata amsawa
Ganin haka Yasa ta mike ta nufi dakin da Jamal yake tayi sallama"
Daker ya amsa bayan ta shiga ta dan rage tsayonta sannan tace sannu ya jiki?
Banza yayi da ita harta gaji da durkuson ta fara kokarin mikewa"
Haka ake gaisuwa sannan saiyau kikasan bani da lfy ?
Shiru tayi tare da turo baki"
Shiru shiru zuwa can ta waiga daga yana bacci , zabura tayi ta mike harta taba kofa yasake cewa idan kika fita ranki zai baci tambaya nayi kuma inason kibani amsa"
Shiru tayi taki mgn shikuma ya dage dole tayi mgn, ahaka Usman ya shigo ya same su"
Murmushi usman yayi sannan yace kona koma ne?
Hararan shi yayi sannan yace shigo mana"
Bayan usman ya zauna Jamal ya kalleshi yace wai yariyar nan ajinta nawa?
Usman ne ya waigo yace ke ajikin Ki nawa ?
5 tafada batare da ta kallesu ba
sauraki shekara daya kenan?
Eh ta fada tana share guntun hawaye"
Ganin inda take nuna alaman gajiya Yasa Jamal yace tashi ki tafi , wawiya dake kawai"
Tana fita Jamal yabi bayanta da kallo sannan ya juya yacewa usman usman wannan yariyar yaushe zaku mata Aure?
Shiru usman yayi yana nazari, zuwa can ya hada fuska sannna yace"
Munyi mgn da Abba kwanaki yace data yi sauka zaiyi mata Aure, kaga kenan bazai wuce nan da shekara 1 ba"
Kuna nufin bazata karasa karutunta na ban garen boko ba?
Eh gsky kozata karasa sai adakin mijinta, saboda wannan dalili dana gaya maka"
Shiru Jamal yayi zuwa can yace amman da kun bari ta karasa saboda yanzun zamani ya canza kuma bakowanne namiji bane zai yadda matarshi ta tafi makaranta, kaga kamarni bani da ra'ayin mace tana gida na kuma tanazuwa makaranta, saboda na sani inada kishi sosai"
Girgiza kai usman yayi sannan yace ina aiko ni bana goyon bayan Asma'u taje Jami'a idan mijin da zata aure be amince ba shikenan wadda ta samu Allah ya amfana"
Shiru Jamal yayi tare da rufe ido, ganin haka usman ma ya kwanta agefe, sun kwashe kusan minti 30 ahaka, Jamal ne ya kira usman batare da ya bude ido ba"
Waigawa usman yayi yayi ya kalleshi sannan yace yaya akayi ?
Daman tambayan ka zanyi kun mata miji ne?
Wani haushi ne ya kama usman nandanan ya hade rai sannan yace Eh ammata wani abu ne"
A'a tambaya ce kawai, jamal ya fada yana kokarin tashi, akwatin shi ya dauko ya fara hada kayan shi yana zuba kayan yana fadin gida zani gobe"
Gobe kabari mana sai ka kara warwarewa"
A'a ni gida zani mezan zauna nayi?
Dacan me kakeyi?
Cikin fada yace dalla gafara Malam karka dameni, ubana ne kai daxaka tareni da tambayoyi?
Mamaki ne ya kama usman, cikin shi cike da dariya yace Allah ya baka hakuri"
Jamal bece komai ba yaci gaba da hada kayan shi"
****
Washegari Jamal yayiwa su mama sallama, Abba yaso ya kara kwana biyu amman Jamal ya dage"
Tare da usman suka fito har sun shiga mota usman na kokarin tayarwa Jamal yace usman dan Tsaya...
Tsayawa usman yayi yana kallon jamal"
Basarwa Jamal din yayi sannan yace ko kuma muje kawai"
Usman bece komai ba ya tada motar har ya fara tafiya Jamal ya ja tsaki sannan yace wai *Husna* batanan ne ?
Sarai Usman ya gane wayake nufi amman saiyace wacece *Husna* kuma?
Cikin dakewa yace *Asma'u* nake nufi"
OK kasan dayake babu me kiranta da *Husna* sainaji abin yamin banbarakwai yana mgnr ne yana kara waya akunne, zuwa can yace mama dan Allah turo mana *Asma'u*"
Usman na sauke waya ya juya ya kalli jamal, sai wani daurewa yake yana wani basarwa, dariya ce taso kama usman Amman saiya cije yace ga *Husnar* nan zuwa"
OK Toh daman inaso ne nadan ja kunnen ta"
Daidai lokacin Asmau ta fito dan haka usman ya bude motar yana kokarin fita yace eh gsky haka yana dakyau"
Heart Beat
*Mmn Yazeed*β
[24/01, 11:04 a.m.] βͺ+234 906 689 6652β¬: ππππ
β*BUGUN ZUCIYA*β
( βHeartbeatβ)
πππ
π
πππ
βByβ
π
ββ*Fadeela Lamido*
*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATIONπ€*
2β£5β£ to 2β£7β£
ππ Gefe ya koma ya zauna, yana mamakin halin jamal
Itako Asamau fuskan nan murtuk ta tsaya agefen da jamal ke ciki sannan ta turo baki tace gani "
Daure fuska yayi murtuk kaman be taba dariya ba sannan yace ni sa'an wasanki ne zaki tsaya daga nesa kina cemin wani gaki ?
Bata rai tayi kamar zatai kuka sanna ta matsa kusa da widow motar tana cigaba da turo baki"
Fuskar shi adaurai yace nayi ciwo harman warke bakizo kika duba ni ba, yanzun gashi zan tafi bakizo muyi sallama ba ko?
Rasa inda mgnr shi ta nufa tayi dan haka tamai shiru tana wasa da hannunta"
Ajikinta taji kallonta yake cikin sauri ta dago ta kalle shi"
Sauri yayi ya dauke idon shi sannan yace *Husna* bazaki min mgn ba ?
Batace kala ba , ganin lokaci na tafiya Yasa Jamal yace shikenan nizan tafi gida ki kula da kanki, kuma ki rage son wasa, kinji ko?
Kai kawai ta daga mai"
Hannu yasa aljihun gaban rikar shi ya Ciro kudi ya kirga 20k ya mika mata"
Hannu buyu tasa ta karba dan ta kosa tabar wajen, juyawa tayi da nufin tafiya taji yace *Husna* nacewa Momy na kina gaisheta ?
Kaita sake dagawa sannan ta juya da sauri dan ta kosa ta daina jin muryan shi"
Usman na Ganin wucewan asmau yatashi ya koma, aguje ya tashi motar yabar gidan"
Asmau ko tana shiga gida ta mikawa mama kudin tace gashi nan yace nakawo miki"
Tunkafin ta rufe baki mama tace karya kikeyi aini yabani nawa".
Mama to nima na baki, ni banason komai nashi wlh yadda na tsaneshi haka na tsani duk wani abu daya shafe shi"
Kai asmau nikam al'amarin ki yana bani tsoro, kin fiye naci da mitan tsiya, dan Allah kiyi hakuri kibar mgn yanzun dauki kudinki ki wuce ina ce dazun kikace nabaki 3k ?
Em mama kibani amman ni wlh bazan bazanyi amfani da kudin shi ba"
Mikewa mama tayi tare da fadin Allah ya shirye ki"
***
Tunda Jamal ya tafi ma'u ta saki jikinta kulum da wuri take zuwa mkrnt , sai ta fara biyawa gidan su deeni sannan ta wuce makaranta"
Kuma da antashi break take kumawa sai kuma taji anbuga kararrawa sannan ta koma mkrnt"
Shakuwa sosai sukayi da deeni, baya zuwa ko ina sai ya jira anta she su akamakarata, zuwa wannan lokacin kawayen ta rahama da zainab sun fahimci halin da suke ciki tsakaninta da deeni, dan haka dukkan su tsoron mu'ammala suke da ita, duk da cewa basu taba taranta akan mgnr ba amman sun san soyayya suke yi"
Ahaka har suka kwashe tsoyon wata 8 zuwa wannan lokacin ma'u ta fahimci son deeni,
Take Dan haka shima deeni soyayyan asma'u yakeji sosai azuciyar shi, saidai babu fargaban komai azuciyan shi dan gani yake ko za azubar da jini saiya Aure asmau"
Itako asmau anata bangaren tana fargaban kaimai deeni a matsayin mijin da zata aure domin tasan mawuyacin Abu ne Abba ya yadda da zabin ta, dan haka ta fara shiga damuwa"
**
Abba ne zaune cikin mota akan hanyar su ta zuwa gidan dada"
Kallon asma' u yayi sosai yace mamana wai meke damunki kwana 2 ?
Karya ta shirya ahankali tace babu komai abba kawai karatu nake dan munkusa fara jarabawa ga kuma saukan mu na tahowa"
Har cikin zuciyan shi yaji dadi, fuskan shi dauke da murmushi yace"
Allah ya taimaka mamana, saura wata 2 ko?
Eh abba"
Murmushi yayi sannan yace kinga dakin gama sai Aure ko ??
Zuciyarta taji ta bugu cikin sanyin jiki tace um um Abba ba yanzun ba"
Kul mamana kar muyi haka dake, isha Allahu bazaki kara wata uku agida ba, Aure zakiyi mamana, meye amfanin zaman"