Showing 57001 words to 60000 words out of 95354 words
Chapter 20 - BUGUN ZUCIYA Hausa Novels Complete by Fadila Lamido.txt
komawa gidan ummi suka hau shiri, duk da cewa alhaji bashir yace karsu dauki komai amman deeni saida ya kwashe wukaken shi tas"
Cikin takaice tare da dana sani alhaji bashir ya kalli deeni sannan yace"
Me kuma zakayi da wukake haka, bafa nason wannan dabi'ar yanzun ba da bane"
Ummi ce tace auta kabarsu anan karka tafi dashi"
A'a ummi akwai abin da zanyi dashi ummi, kisan zama be ganni ba, bazan barwa Jamal asma'u ba, dole zan nemesa duk inda yake, yabani kayata, wlh wlh ummi matsawar inna nunfashi bazan barwa Jamal asma'u ba' daga
ranan da nasamu nasara asma'u ta dawo gareni zan aje makami na"
Sakatoto Alhaji Bashir yayi da baki yana kallon deeni zuwa can yace"
Saratu wacece Asma'u?
Ahankali ummi ta warwarewa masa komai"
Shiru yayi na wasu lokaci zuwa can ya dafa deeni tare da fadin"
Ka kwantar da hankalin ka, indai kudi na magani zaka Aure asma'u ka neme shi, ko nawa yake so zan bashi, bukatata kawai ya saketa"
Take wani dadi ya ziyarci zuciyan deeni, bakin abban sa dayake gani ya goge tas"
Karfe goma da rabi na dare suka isa Abuja, saida suka sauke deeni agidan daddy sannan suka wuce giida"
Tunda deeni ya dawo kullum saiya fita neman ma'u, yayi dakon jiran kiranta harya gaji"
Damuwa ya fara shiga, Allah yasa Asma'u lfy take, dan yasan inda lfy take bazata bari har akwashe kwanakin nan bata kirashi ba"
Babu laifi yanzun deeni ya natsu, kulum da safe yake zuwa ya gaida daddy da momy"
Nafisa ko bata gajiya da kallon deeni, akulum tana cikin satan kallon shi"
Duk da cewa daya kalleta yake galla mata harara"
Yauma kamar kullum, deeni na zaune afalo shida daddy da nafisa"
Babu abin da deeni ke yi banda tunanin ma'u, yana takaicin wai kamar asma,u ace babu waya ahannunta, tsaki yaja kadan sannan ya dauko wayar shi"
No da ma'u ta kirashi kwanaki ya gani, ji yayi kamar ya kira, sai kuma ya tuna tace mishi na kanwar Jamal ne karya kira"
Gani yayi bazai iya hakuri ba dan wannan ce damar data rage mai danna no yayi tare da karawa akunen sa"
Dai dai lokacin wayar nafisa dake gefe ta fara kuka"
Daukan wayar tayi ta danna tare da fadin hello"
Cikin sauri deeni ya kashe wayar tare da kallon nafisa"
Itama sauke wayar tayi tare da jan tsaki"
Kara duba no deeni yayi, tabass itace dan yariga ma ya haddace no din"
Kira ya kara dannawa, wayar nafisa ta sake kara
Cikin mamaki deeni yake kallon nafisa yaya akayi haka"
Tunawa yayi da lokacin da daddy yace gashi jamaludeeni bayanan da kunje tare, take wani gumi ya fara karyo mai"
Mikewa yayi tsaye cikin matsanancin tashin hankali, juyawa yayi ya kalli daddy yace"
Daddy jamaludeen yana da mata ne?
Cikin murmushi daddy yace kardai kace min baku taba gaisawa da asma'u?
Wani irin mummunan faduwa gaban deeni yayi, take idon shi ya kada yayi jawur, wasu jijiyoyi ne suka tasomai kamar zasu tsintsinke, jikin shi na wani irin rawa"
Daddy ne ya kalle shi yace yadai?
Ajiyan zuciya ya sauke sannan ya daki bango tare da fadin, ina, billahillazi la'ila ha'illahuwa bazata sabo ba"
Daga daddy har nafisa mikewa sukayi, daddy ne ya karaso ya dafah kafadar deeni tare da fadin menene ya faru?
Babu komai ya fada yana kokarin fita afalon"
Koda ya koma dakinsa bangon ya sake duka, zuwa can ya share gumin da ya karyo mai sannan yace"
Wannan dama ce babba nasamu, da wannan damar zanyi amfani innunawa Jamal kuskuren Sa, da wannan damar ne zan turamai takaicin da sanda ma zai saketa be sani ba"
Kwashewa yayi da dariya saida yayi me isarsa sannan ya sarara"
Gurin megadi ya nufa domin yanason yasan unguwar da gidan Jamal yake"
Mamaki yayi sosai dayaji cewa wai asma'u anan cikin gidan take, dan haka ya yake shawaran da dare zaikai mata ziyara"
1:32am Nafisa da Asma'u ne kwance akan gadon dakin nafisa"
Gaba dayan su bacci suke duk su bararraje"
Ahankali deeni ya turo kofar ya shigo dagashi sai gajeren wando"
Kallon yabi gadon dashi, daga can gefe ya hango ma'u"
Takawa yayi yakai saitinta sannan ya tsaya, kurama mata idon yayi na wasu lukuta, ahankali ya aje ajiyen zuciya sannan ya tsuguna agabanta"
Gani yayi tayi fari tare da kiba kadan, ahankali yace Allah yasa baki bashi furata ba"
Murmushi yayi kadan daya tuna yadda ma'u take nonamai kyauna"
Ahankali yasa bakin shi saitin fuskanta yana hura mata isa"
Kara runtse idonta tayi sannan ta dada gyara kwanciyan ta"
Ahankali yasa dan yatsan shi awuyanta ya fara mata tafiyan tsutsa......
Heat Beat
*Mmn Yazeed*
[24/01, 11:04 a.m.] โช+234 906 689 6652โฌ: ๐๐๐๐
โ*BUGUN ZUCIYA*โ
( โHeartbeatโ)
๐๐๐
๐
๐๐๐
โByโ
๐
โโ*Fadeela Lamido*
*@AMยฃยฃNCI WRITER'S ASSOCIATION๐ค*
โ
Dedicated๐๐ป
*Beebee Isa*
Cikin bacci taji taji kamar wani abu na mata yawo ajiki"
Hannu ta fara mikewa ta shafa gurin"
Jitayi kamar ta rike hannun mutum, ahankali ta fara bude idanuwanta"
Fuskan deeni ta gani yana mata murmushi, kara mutsuke idonta tayi, sannan tasa hannu ta murza idon ta sake budewa"
Yana nan dai ayadda taganshi dazun, dan haka afirgice ta fara kokararin tashi, tare da mika hannun domin tashi nafisa"
Hannun ya daga mata alamar kul, cikin sauri ta janye hannunta tare da kara tsareshi da ido"
Da hannun ya sake mata alama ta sakko"
Batai musu ba, dan tarasa metakeyi mafarki ne, ko da gske ne"
Ahankali ta sakko deeni yana gaba tana binshi abaya, har zuka fita dakin
Jatayi ta tsaya bakinta ya kasa furta komai"
Zuwa can tayi ta mazata tace deeni kai ne? Ko kuma mafarki nake yi"
Ni ne asma,u, nine ba mafarki kikeyi ba"
Kara zero ido tayi sannan tace, yaya akayi kazo nan, deeni ta ina kashigo, dan Allah dan darajan annabi ka rufamin asiri ka tafi, dasafe zan kiraka awaya zamuyi mgn"
Ganin inda jikinta ke rawa yasa yayi dariya sannan ya fara takowa ya dafa kafadarta tare da fadin ki kwantar da hankalin ki, nasan kina da lbrn bakon da kukayi agidan nan, bakowa bane nine shamsudeen"
Cikin mamaki tare da zubuwar hawaye tace"
Yaya akayi haka ta faru"
Ahankali ya shiga warware mata komai"
Cikin sanyi taja da baya ta manne ajikin bango, tare da fadin, ina lillahi wa inna ilaihir raju,un"
Hannun deeni yasaKe dagawa yakai bakinshi, ya mata nuni datai shiru tare da waigawa ya kalli bayan shi sannan ya matsa ya dafa kafadanta"
Da saurinta tasa hannu ta zame hannun deeni daga jikinta"
Hannun da ma'u ta sauke ya kallah sannan ya daga idon sa ya kalle ta yace"
Asma'u nine fah?
Sunkuyar da kanta tayi kasa ahankali tace nasani deeni"
Hunnuwanta ya sake jawowa ya fara tafiya da ita zuwa dakin sa"
Deeni ina zaka kaini?
Dakina, akwai mgnr da zamuyi domin mu samar ma kanmu mafita"
Cikin sauri ta girgiza kai sannan tace"
Haba deeni baka tunanin wani ya ganmu, akwai fa Aure akaina, duk wadda ya ganmu tare da wannan lokacin bazai mana uzuri ba, karashi mgnr tayi cikin zubowan hawaye"
Ido deeni ya zuba mata tare da fadin me kike nufi da wannan maganar ?
Shiru tayi zuwa can tace ina nufin ka bari da safe zan kiraka awaya saimu yi mgnr"
Kallo ya sake binta dashi cikin jajayen idon sa da suka kuma jawur yace"
Asma,u kardai kice min kin fara son jamal idan kikamin haka nima bazan miki uzuri ba, wani abo ya shiga tsakanin ku ne?
Girgiza kai tayi batare da ta dago kai ta kalleshi ba"
Hannun shi yasa ya dago kanta sannan yace"
Gaya min meye matsayi na azuciyar ki?
Cikin rada tace deen kana nan a inda kake, babu abin da ya canza"
Karya ne, ada bakimin musu, yau ko nagani acikin idon ki, kina nema ne kimin taurin kai"
Bata bari ya rufe baki ba' tace yanzun da daba daya bane deen, yanzun fah agidan mijina na nake, kuma ina tare da iya.....
Batakai ga karasawa ba taji deen ya make mata baki, cikin sauri tasa hannunta ta dafe bakin, sabo da tsabar zafi sai takeji kamar hakurinta ya zubo"
Cikin fada tare da daga muryan shi sama yace"
Ni kike cewa agidan Mijin ki kike, kinsan yadda nake jin sonki acikin zuciyata kuwa? Da kin sani bazaki furta gidan mijinki agabana ba"
Ganin inda ta dafe bakinta yasashi saurin kai hannun fuskanta tare da fadin Allah yasa banji miki ciwoba, yi hakuri raina ne ya bacci, bazan iya juran ganin ki kina taraya dawani namiji bani ba, jeki ki kwanta, amman gobe da safe ki fito falo inason ganin ki ko bazamu yi mgn ba"
Har bakin dakin nafisa ya rakata sanna ya juya yana waigenta, jiyake kamar ya makaleta ajikin shi ta tayashi kwana"
Ya wuce tsakiyan falo yana daf da fita momy tafito"
Daidai lokacin da deeni ya taba kofar zai fita"
Shamsudeen Momy ta fada cikin matsanancin mamakin ganin shi wannan lokacin"
Cikin dakiya yace na'am momy sannan ya waigo yana kallonta"
Agogo ta kallah karfe 3:34am dan haka ta juyo takalshi tace"
Shamsundeen me kakeyi cikin daren nan afalo tun dazon nakejin motsi"
Murmushi yayi tare da shafa keya sannan yace"
Momy waya nayi"
Oh tafada sannan tayi murmushi ta juya daki"
Ma'u ko tana shiga daki ta samo nafisa zaune abakin gado, jitayi gaban ta ya fadi"
Wani irin kallo nafisa ta mata sannan tace ina kikaje kuma?
Toilet ta fada tana kokarin hawa gado"
Cikin mamaki nafisa ta bita da kallo, zuwa can tace Amman ga toilet adaki me zaikai ki waje?
Jawo bargo tayi tare da fadin kofar ce taki buduwa"
Nafisa batakara cewa komai ba ta haye gado ta kwanta"
Ma,u ko bata iya runtsawa ba tunaninta ta wacce hanya zata bollowa lamuran ta, hakika ayanzun tana neman shawara sai dai babu wadda zata iya tunkara da wannan zancen"
Kuma tana tunanin kar mutuncinta ya zube a idon duniya, tasani deeni ba abun kunya bane awajen shi, dan angan su tare, amman ita tasani ganin su tare masifa zai janyo mata babba tare da bakin fetin da batasan ranar fitanshi ba, wata kila abba da mama su tsine min duniya ma zata zageni, da auren wani akaina kuma ina sauraran wani, babu wadda zai fahimce ni, koda bawani abu muke aikatawa"
Cikin hawaye cabe cabe take,cikin zuciyarta tace Allah ka kawo min mafita, Allah kasa nafi karfin zuciyata, inason deen kuma akwai aure akaina"
Washegari tashi tayi bakinta ya kunbura, saboda dukan da deeni yayiwa bakinta, idonta maha sakamakon kukan da takwana yi"
Nafisa ko kallon ma'u kawai take amman acikin zuciyarta bata yarda da zancen ma'u ba, gashi yadda taga fuskanta ya nuna mata akwai matsala, dan haka tunda safe taje ta kira momy"
Yadda momy taga fuskan ma'u abin ya bata tsoro, dagota tayi tana kara kallon fuskanta"
Asma'u menene ya sameki abaki?
Bugewa nayi cikin dare na tashi zani bayi shine ban sani ba nabige"
Shiru momy tayi tana kallon asma'u zuwa can tace toh idonki fah?, naga duk kinci kuka ga dukkan alama bakiyi bacci ba, kuma begewa ai bazaisa ki kuka haka ba, wani abu na damun ki ne?
A'a
Toh ko kina tunanin mijinki ne?
A'a ta sake fada da saurinta"
Toh ki gayamin abun da ke damun ki idan ba hakaba to tunanin Jamal kike"
Shiru tayi kanta akasa domin bazata iya gayawa momy abonda ke damunta ba gara aje atunanin Jamal din take"
Momy bata kara cewa komai ba kallon ma'u kawai take tana girgiza kai, zuwa can tace"
Asma'u ki kwantar da hankalin ki kamar yau ne zakigan shi ya dawo, kodan kinga har yanzun be kira bane hankalin ki ya tashi?, nima da hankali na ya tashi amman daga baya daddyn ku yaje Office dinsu dakenan Abuja antabatar mai suna nan lfy gurin da suke ne babu service"
Duk da ba haka bane azuciyar ma'u taji daddin jin lbrn Jamal yana lfy"
Haka momy taita lallashin ma'u hartaga kaman hankalinta ya kwanta sannan ta tafi"
Momy na fita nafisa ta fara dariya saida tayi me isarta sannan tace"
Ashe dai yaya jamal nada matsaye, amman kuke nuna kamar baku damu da junan ku ba"
Mikewa ma'u tayi ta nufi toilet batare da ta kalli inda Nafisa take ba"
Wunin ranan ma'u ta kasa fita falo, dan gudun kar wani ya fahinta dan tasan halin deeni"
Shiko deeni afalo ya yuwuni, sallah kadai ke fiddashi, har momy ta fahinci kamar akwai abin da yake jira dan motsi kadan yake jan tsaki tare da kallon hanya"
7:30pm ma'u na zaune daki ta takure guri guda, ga abinci da nafisa ta kawo mata agefe ta kasa ci, hawaye ne yake zubo mata ta gefen idonta, bakomai ke tada mata hankali ba illah gudun bacin sunanta ta tabbata deeni zai iya dawowa adaren yau, dan haka dole ta nemi mafita"
Nafisa ce ta shigo ta tabi ma'u da kallo tare da fadin"
Lallai abin naki babba ne, saboda tunanin yaya kike kin cin abinci"
Tsaki taja kadan sannan tace"
Wai nafisa meyasa ba'a rufe dakin nan?, nifa gaskiya tsoro nakeji"
Mikewa nafisa tayi tare da fashewa da dariya sannan tace"
Bana kullewa, kuma ni ba yaya bane bare kimin shagwaba"
Fita tayi tabar ma'u dabin bayanta da kallo, sanna ta share hawayen da ya gangaro ma"
Nisa tayi da tunani zuwa can ta yake shawaran kiran deeni domin tasan indai bata kirashi ba, babu abinda zai hanashi dawowa yau"
Bugu 2 ya dauka tare da fadin"
Asma'u sai yanzun kikaga damar kira na?
Cikin sanyin jiki tace yau banajin dadi ne"
Meke damunki? Koda yake ma barshi Anjima zanzo indubaki tunda kinki zuwa na ganki.....
A,a deeni dan Allah karkazo, koma meye kabari sai yaya jamal ya dawo, tunda yace bazai zauna dani ba, dan Allah deeni kayi hakuri nasan bakaji dadin mgnta ba, kafin yaya Jamal ya tafi yamin gargadi sosai tare da nunamin karnamai wasa da Aure"
Wani kara ma'u taji alamun deeni ya daki wani abu, cikin fada yace"
Ni kike gayawa Jamal ya baki umarni?, atunanin ki ni zan saurari umarnin sa ? Yaci uwassa dan uban sa, me kike nufi kina nufin kinason Jamal yanzun kuma zakibi umarnin sa?
Hawaye ta share sannan tace"
Bahaka bane deeni, narasa inda zansa kaina, inajin tsoron fushin uban gijina, wannan mgnr da mukeyi yanzun haramun ne, deeni kar akamani da wani laifi ayanzun abba zai tsine min duniya zata kalleni abaibai, dan Allah kayi hakuri mubi komai ahankali"
Asma'u kin daina sona ne?
A'a haryanzu kana nan inda kake amman kabari mubi komai ahankali"
Ajiyan zuciya yayi sannan yace"
Asma'u dan Allah karki gujeni idan kika gujeni bansan inda zan saka kaina ba, sonki acikin jinina yake, daga ranan da kika gujeni zuciyata zata iya bugawa, wata kila na rasa rayuwata, asma'u duk abinda kikaga nayi ba laifina bane laifin son da nake miki ne, sonki ya shigeni batare da yayi shawara dani ba"
Ahankali tace deeni?
Na'am asma'u
Nace mezai hana muruki Allah idan alheri ne atsakanin mu ya kawo mana mafuta, idan ba alheri ya canza mana da mafi alheri"
Jiya yayi gaban shi ya