Showing 15001 words to 18000 words out of 95354 words

Chapter 6 - BUGUN ZUCIYA Hausa Novels Complete by Fadila Lamido.txt

29 Oct 2025

496

da duka"

Mama batace komai ba mikewa kawai tayi tabar dakin"

Nan ma,u ta kwanta tanajawowa *Jamal* Allah ya isa acikin zuciyarta"

Ko ina ajikin ma,u ciwo yake dan yau abin ya mata yawa ga wahalan da *Duna* ya bata gana wannan dan iskan abokin yayan"


*****


Washegari ma haka ta tashi batajin kwarin jikinta dan haka batace zata makaranta ba"

Misalin 11 tayi wanka ta danji dadin jikinta, falon Abba ta wuce acan ta samu mama"

Gaban abba ta zauna ta tankwashe kafa sannan ta fashe da kuka"

Nan danan hankalin Abba ya tashi, zaman shi ya gyara tare da kura mata ido sannan yace"

Mamana waye ya taba ki?

Cikn kukan tace ba yaya usman bane yacewa abokinshi wai banajin, shikuma kawai sai ya ciro bulala ya hau dokana"

Abokin nasa?

Eh Abba"

Duka fa kika ce mamana?

Xanin ta ta fara dagawa tare da fadin eh abba kagama gurin"

Babban mgn Abba ya fada bayan yaga inda jikin ma'u yai rudu2"

Mikewa yayi sosai sannnan ya daga waya ya kira usman"

Cikin Monti 15 suka iso, dukka su jallabiya ce ajikin su fara kar"

Tunkafin su zauna abbba yake fadin a'a wanake gani kaman *Jamal*"

Mumurshi kamal din ya saki yana shafa keya yake fadin nine abbba"

Bayan sun gaida abbba hira suka hauyi, dan haka ma'u ta Kule"

Mikewa tayi tana kokarin tafiya Abba ya dakatar da ita sannnan yace"

Mamana kinga wannnan sunan shi Jamal yayanki ne shima, nida mahaifin shi tare mukayi wasa, dan haka yadda usman yake da daman hukuntaki shima yana da dama kijji ko"

Tana barin falon ta fara kunkunai kai tsaye ta wuce dakin mama dan daman tuni ta bar musu falon, zama tayi tare da share guntun hawayenta sannan taci gaba da kunkunan ta"

Mama na gefe tanajinta jefi jefi tana tsintan abinda take cewa, zuwa can tace"

Kee!!!! Tashi kibani guri, haka kurun zakizo kisani agaba kinamin mita toh me kikeso nayi rama miki zanyi kome?, yariya banda fitsara ba abinda kikasa agaba ke wacece da baza'a dakeki ba?, to kici gaba kece zakisha wahala"

Dahaka mama ta fice tabarta adakin"

Itama mikewa tayi tabar dakin"

Tundaga ranan asmau bata sake zuwa makaranta ba har wani satin ya zagayo, gashi kewan deen ya dameta, dan tasan yanzun har ya gaji da zuba ido"


***



Yau ta kama asabar dan haka tunda wuri ma'u tayi sallama ta fito"

Saidai tana fitowa taci karo dasu yaya suna kokarin shigowa"

Dauke Kai tayi taja gefe sanan tace ina kwanan Ku murya ciki2"

Yaya usman ne kawai ya amsa amman jamal gaba yayi, harta kusa fita taji jamal na cewa usman, kunabin bayan yariyar nan Kuwa....

Daidai lokacin suka sha kwana dan haka bataji amsan da yaya usman ya bashi ba"

Tana tafiya tana waige dan gani take kaman Jamal zai biyo ta"

Hango deen akofar gida shine yasata ta manta komai tundaga nesa ya sakar mata murmushi itama mayar mai tayi tare da sunkuyar da kanta kasa"

Tana isa gaban shi taja ta tsaya tare da kara sunkuyar da kanta kasa"

Babu abinda deen yake banda kallonta acin tuhuma ya dago fuskanta sannan yace"

Me yasame ki kwana 2 ?

Shiru tayi tana kara tsurawa kafarta ido"

Girgiza kai yayi sannan ya cije lebensa na kasa Yasa ke daga ido ya kalleta cikin bacin rai yace"

Yayan kin yasake dukan ki ne?

Kanta na kasa ta girgixa kai"

Kanshi ya daga ya kalli sama sannan yace yasin zanyi rashin mutunci wlh, fuskanki ya nunamin an cuceki kuma kina cikin bacin rai wai wanene wannan yayan naki? a ina zan sameshi ?

Nan danan hawaye ya fara zubo mata dan bakaramin takaici takeji ba, haka kurun daga zuwan shi zaisa bulala ya zane ni"

Murya kasa2 tace ba yayana bane, abokin shi ne"

Abokin sa ? Idon shi daya ya rufe sannan ya karkata dayan yace dukan ki yayi?

Hannu tasa ta share hawayen daya zubo mata sannan tace eh"

Uban wanene ya bashi iznin ya dake ki?

Bata iya cewa komai ba illah kukanta daya karu"

OK shikenan dena kuka kingane?, ban ni dashi zan nuna masa daya tabaki gara yaje ya tari babban mota, haduwan mu bazaiyi kyauba naratse sai uwassa ta kasa gane shi"

Yana mgnr ne yana daga hannuwan shi tare da karkace baki"

Ganin inda yake fada yana tiriri yasa ma'u jin dadi ko banza tasamu wadda zai kwatan mata enci, amma tafison deen yayi abin cikin sirri ba baro baro ba dan batason kowa yasan shi arayuwar ta"

Dago kanta tayi sannan tace bari na shiga makaranta idan antashi zan shigo nagaida ummi....

Batajira me zaice ba ta fara tafiya tana jiyo muryan shi yana cigaba da babatu"

Ko a makaranta batayi karatun kirki ba, kawai tunanin hanyan daukan fansa take"

Zuwa can tunanin duna ya fado mata, tabas duna kadai ya ishi jamal amman idan deen ne duka zasu masa dan suma suna takama da karfi, karshema kila su kamashi, amman duna zai iya basu whl batare da sun san waye ya turoshi ba"

Kwashewa tayi da dariya sannan tace inama ina gurin inga ya zasu yi?

Takarda ta samu ta fara rubuta yadda takeson abin ya kasan ce, tana cikin rubutun aka tashi tsayawa tayi ta karasa sannan ta fito"

Lokacin da tafito babu sauran dalubi amakaranta duk sun fita"

Gabanta ne yayi mummunan faduwa sakamakon hango Jamal tsaye shida baba idi"

Batasan me suke cewa ba, tana kokarin fita taga jamal ya wuceta"

Abakin makarantar taga motar yaya usman, budewa Jamal yayi ya shiga, har sun tada mutar yaya usman yace shigo mutafi"

Wani haushi ne ya kamata, tasan duk shirin jamal ne, bayan ta zauna suka fara tafiya banda masifa babu abinda yaya usman ke yi, Jamal ko kauda kansa gefe yayi ya bude jarida"

Ma,u ko hankalinta yana kan dakalin da deen yake zama, yana nan zaune sai raba ido yake"

Suna zuwa daidai inda deen yake ta saka hannuta ta widow motar sannan ta wurgawa deen takardan data rubuta"

Akan jikin shi ya fada, tana kallon deen ya dauka sannan yabi motar da kallo"

Sun gota gurin kadan taga Jamal ya rufe jaridar hannun shi ya aje agefe, sannan ya cire glass din dake idon sa"

Waigowa yayi ya kalleta cikin ido sannan yace"

Usman koma baya....





Heart Beat
*Mmn Yazeed*​
[24/01, 11:03 a.m.] β€ͺ+234 906 689 6652‬: πŸ’—πŸ’πŸ’πŸ’—
​*BUGUN ZUCIYA*​
( ​Heartbeat​)

πŸ’“πŸ’πŸ’—
πŸ’—

πŸ’“πŸ’πŸ’—
​By​
πŸ’—
​​*Fadeela Lamido*




*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATION🀝*





1⃣9⃣ to 2⃣1⃣





πŸ“™πŸ“™ Ahankali usman ya koma baya, kusa da dakalin deeni Jamal yace yayi"

Hannu ya mika ya dauki glass din shi ya maida a idonshi sannan yace"

Ke! Sauka ki karbo dakardan da kikajefa"

Idanuwa ta fito dasu waje zufa taji yana karyo mata, kallo gurin tayi taga deen ya daga bakin shi sama yana fito"

Jamal ya sake cewa ko bakiji abinda nace ba?

Jikinta har rawa yake ta bude motar ta sauka, daga gefen dakalin duna ta hango wata takarda ko kallon inda deen yake batai ba ta tsuguna ta dauka, harta shiga motar tanajin fiton deeni"

Usman ne ya karbe ta kardan ya bude babu komai aciki, tsaki yaja sannan yace kai manga kana da matsala wlh"

Ko kallon shi beyi ba yace kaidai muje kawai, kaima ai matsalan gareka"

Itako ma',u tunda ta dauko tasan ba ita bace, har suka isa gida babu wadda yace uffan"

***

Da yamma tana zaune adakinta tunani ta shigayi ta yaya zata bullowa al amuranta"

Hakika deeni yana matukar burgeta kuma da bi'un shi suna sata nishadi, amman idan ta tuna abbanta gabanta na faduwa"

Koda atunanin ta bason deeni take ba, amman tana tsoron ranan da abba xaisan tana mgn da deen harma tana shiga gidan su, alhanin ya gargadeta daga makaranta ko gidan dada be amince taje ba"

Hawaye taji yana zubo mata hakika batason bacin ran abbanta kuma tanason ta masa biyayya amman kuma tanajin deen ajikinta kuma tanaso kasancewa dashi akoda yaushe, har tanaji inama su zauna gida daya taita kallon shi harta gaji"

Murmushi tayi lokaci da ta tuna yadda deen yayi data gaya mishi an begeta, tabas da zatabawa deeni dama da yayi banna komai girman mutum dan ya duramai zagi bawani abu bane, ji inda ya takarkare agabana yana cewa zaici uwar yaya, wata kila ya manta cewa uwarmu daya"

Wata zuciyar ce tace ke ba mantawa yayi ba yana sane ko kin manta yadda yayiwa dada?

Kwashewa tayi da dariya har tana rike ciki kai gsky dada matsuraciya ce, dagajin zance sara ta ware kafa amman da anyi mgn tace kafanta na ciwo*


Dariya take sosai har da hawaye, da karfi taji anturo kofar, mama ce kallo tabi ma'u dashi sannan tace toh wai kodai mahaukacin kare ya cijeki ne?, mutum shi kadai yaita dariya adaki"

Gintse dariyarta tayi sannan tace mama dada fah na tuna"

Dada ? Ke banason shashanci kinji ko, kiyi hankali da kanki ba kowa bane keson dariya dallah ni tashi ki kaiwa su yayki abinci'

Hade rai tayii sannnan tace mama ni gaskiya nagaji da ganin su agidan nan waishi yaya meyasa baazai kaishi gidan shiba??

Ke tashi kiji bansoo. Surutun banza

Mikewa tayi ta fara tafiya tana. tana mgn ahankali"

Binta da kallo. Mma
Sannan tace me kike cewa?

A,a mama daman cewa nayi kodai Anty fa'iza tayi yaji ne?

Cikin takaici mama tace bani da lbr amman idan kije kina iya tambayo shi"

Bata sake cewa komai ba ta juya ta fita dan tasan mama gatse ta mata"

Kwance ta same su afalon abba sunyi wani shabe shabe dasu, duk su biyun jikin su babu babu riga dan haka batace zata tsawaita kallon su ba"

Jarida ce ahannun Jamal kaman yadda ya saba yayin da usman ke rike da waya yana dannawa"

Ajiye abincin tayi ta juya zata tafi taji waya na kara

Harta kai bakin kofa taji Jamal yace Haba Momy kiyi hakuri wlh wani abu ne ya tsaidani, amman gobe da wuri zan taho"

Yadda Jamal ya kashe murya yana shagwaba abun yayi matukar bata mamaki dan haka taja ta tsaya tana jiran taji me zai sake cewa"

Muryan yaya usman taji yace ke me kike jira"

Azubure ta fice adakin"

Koda ta koma daki addu,a taitayi Allah yasa momyn shi ta matsamai ya tafi gobe, dan wannan bakon gundura ne"

Washegari da safe bayan tayi shirin makaranta ta fito ta samu mama sai hada wasu kaya take"

Cike da zumudi tace mama wannan kayan fa?

Idon mama akan kayan tace wlh Jamal ne be tashi gayamin zaitafi gida ba saiyau da safen nan, shine zan bashi turaren nan ko kyauta yayi dashi"

Kasa boye murnanta tayi tace ai gara ya tafi"

Mama batace mata kala ba harta fice"

Cikin farin ciki ta nufi mkrnt tanaji azuciyarta daga yau zaman kunci ya yaye"

Tana daf da isa kofar gidan su deeni ta hango karnuka guda 3 sai shawagi suke"

Ja tayi ta tsaya tare da dafa kirji, ido ta sake zuba musu manya2 karnuka ne amman duna duk ya fisu girma"

Ahankali ta fara takawa ta koma lungun da kawarta zainab take bi dan bakaramin tsoron duna take ba"

***


Shiko Jamal karfe 10:45 ya mike yacewa usman bari naje wani guri na dawo"

Cikin mamaki usman yace kadai CE natashi muje"

A'a bana bukatan rakiyan kowa, ni daya zani"

Mamaki ne yasake kama usman dan tunda yazo garin nan kusan satin shi 2 be taba cewa zai fita shi kadai ba sai yau"

Murmushi Usman yayi sannan yace toh adawo lfy Allah ya tsare, key din motar sa ya mika masa amman sai yaki karba yace da kafa zashi"


Makarantar su ma'u ya nufa yana tafe yana shirya muguntan dazai mata indai ya sameta da laifi"

Koda ya hango karnnuka na shawagi be kawo komai azuciyan shi ba, dan ya saba ganin karnuka iri2, dan haka kanshi tsaye yake tafeya tare da neman inda zai labe yaga wucewan ma'u idan ma wani abu take shiryawa yau zai gani"

Shiko deeni yana zaune kan dakalin da ya saba zama ya rufe ido tare da dage hanci sama"

Kan Jamal tsaye ya nufi bita tsakiyan karnukan yana daf da shiga cikin su yaga sun haukace kaman suna fada da junan su, duk idan yaso be ya wuce nan suke dawowa suna kawai junan su rikici"

Jamal be tsorata ba acikin zuciyan shi yace wadan nan wasu irin yan iskan karnuka ne"

Daure fuka yayi sosai yayi kansu gadan kadan tare da niyan idan suka kawo mai wargi zai kai masu duka"

Wata muyar yaji daga gefen tana cewa dan durin uwar mutun ya tabamin kayana yagani"

Juyawa yayi ya kalli gurin da yaji mgn mutun ne zaune kato meji da karfe Kuma daganin shi bayaji dan almun rashin ji sun bayana agareshi haka ne ya nunawa jamal shine mamallakin karnukan amman saidai kaman bashi ne yayi mgnr ba dan idon shi rufe yake"

Karnukan ya kara kallo har yanzun sunan a inda suke dan haka ya daga murya yace "

Ai sai kazo ka tattara kayan naka dan inason zan wuce"

Baki deeni yasake dagewa sama yafara fito" dan haka Jamal yasa kafar yayi ball da daya daga cikin karnukan"

Akuje duna ya taso ya yi kan jamal yana kaimai cizo tare da yakushi, saidai baya kawaiwa jikin Jamal din domin fada da kare ba sabon abo bene awajen shi, da duna ya kawo mai cizo yake kaimai duka"

Ana haka aka tashi yan mkrnt, suna ganin abinda ke faruwa suka watse wasun su sunbi lugu wasuko makarantar suka koma, mau ko wani logu ta rabe tana lekowa tana komawa acikin zuciyanta tace kai Jamal akwai maye"

Jikinta ne yayi sanyi lokacin da ta hango yadda jamal ke kaiwa duna duka, ga deen zaune ya rufe ido kaman me bacci hawaye taji yana zubu mata shikenan Jamal zai gama da duna ya dawo kan deeni tunda ciwon baccin shi ya motsa, jitayi kaman ta tashe shi dan tasan babu yadda za'ai idon shi 2 ya bari ana jamgar masa duna"


Kuka take sosai hawaye shabe2 zuwa yanzun ta fara tausayawa duna itace tajamai gashi Jamal zai kashe abanza"

Wani irin kuka duna ya fara almar yana shan wahala, yana fara kukan taji deeni yayi wani irin fito me kama da mgn, nan danan duna ya haukaci tare da wani irin haushi me firgitarwa yayi kan jamal akan damtsen shi ya kafa bakin shi saiga jini yana zuba"

Hannu Jamal yasa ya danne gurin hakan yaba duna daman cigaba da cizon Jamal akafan shi dole tasa Jamal ya sake uhun da be shirya ba, tare da kokarin guduwa"

Daidai lokacin ummi ta dawo daga cefane afirgece ta saki kanyan miyan sannan tayi kan duna tana kai! Kai!! Ja baya duna yayi amman har yanzun yana gurnani tare da kunbura wuya"

Ma,u ko banda dariya babu abinda take saidai taso ace duna yabi Jamal aguje"

Tana cikin wannan tunanin taji duna ya sakeyin fito aguje taga duna ya wuce sauran karnukan nabin shi abaya "

Sai alokacin mutanan unguwan suka fara fitowa, deen ko mikewa yayi ya shige gida"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login