Showing 51001 words to 54000 words out of 95354 words

Chapter 18 - BUGUN ZUCIYA Hausa Novels Complete by Fadila Lamido.txt

29 Oct 2025

489

ta fice Jamal binta da kallo yake, sannan ya jigina kanshi jikin gado, runtse ido yayi idan na fahimci momy nufinta son husna nake, eh nasani tunda na daura husna a idona ban tajin wai basonta ba, inason ta amman bada Aure, sosai nakejin ta acikin zuciyata, dan haka nashige cikin lamarinta"

Haka yaita tunani daka karshe ya tashi ya bar gidan"

Momy ko koda ta koma gurin daddy mamakin halin Jamal taitayi, ita bataga amfanin mutum nason abu ba amman yaita wani kyauce kyauce, kwashe yadda sukayi da Jamal tayi ta fadawa daddy"

Dariya daddy yayi sosai tare da fadin tunda yana son kunshi daya fita kisa amata sabon design"

Itama momyn dariya ta sake yi, sannan tace"

Ni wlh mamaki ma abin yake bani, kofa kallonta baya yayi, amman kaji ashe idon sa ya gano masa kunshin ta"

Bayan fitan daddy momy kiran ma'u tayi, tace nafisa ta tsefe maki kai, anjima umma zata zo ta miki kitso"

Mgnr Jamal ce ta fado mata, take taji batason yin, kumshi kwata2, kanta tasa akasa sannan tace"

Momy abari sai gobe ne dan kaina yau ciwo yake min"

Shiru ummi tayi zuwa can tace toh Allah ya kaimo goben lfy, kin sha mgn ko?

Eh kawai tace, sannan ta mike zata fice"

Ahankali momy takira sunanta bayan ta dawa ta mika kofin dake gefenta tare da fadin shanye kiban kofin"

Karba tayi tana kara bin cikin kofin da kallo, ko ba'afada ba tasan maganin mata ne aciki, Karba tayi ta shanye azuciyanta tanajin ana gyarawa deeni ne"

Da yamma Jamal ya dawo gida jikin shi babu kwari, kallo daya yayi wa ma'u ya kyauda kai tare da Jan tsaki"

Kallon shi momy tayi tare da fadin lfyr ka?

Lfy lau yace ataika ce sannan ya mike ya fice"

Binshi da kallo momy tayi sannan ta juya ta kalli ma'u tace tashi ki wuce part din Ku"

Afalo ta wuce Jamal yana zaune ya zuba uban tagumi, kallon shi tayi alalace tashige daki"

Harta kwanta bacci bata sakejin motsin Jamal ba"

Shiko Jamal lokacin dayayi nufin zuwa daki ya kwanta kasa wucewa yayi, saida ya tura kofar ma'u ya gama lekenta sannan ya wuce"

*****


Washegari


8:00am Jamal ya fito cikin shirin tafiya aiki, falon daddy sa ya nufa, bayan ya zauna ya mika gaisuwa gurin daddy da momy"

Cikin natsowa yace fara gayawa iyayen sa antura shi kasar Somalia, sati me zuwa zasu wuce, karashe magar yayi cikin yanayin damuwa"

Addi'oi daddy da momy suka masa sosai"

Amsa musu kawai yake da ameen amman zuciyar shi babu dadi"

Daddy ne ya kula da sanyin jikin jamal dan haka yabishi da kallo sannan yace"

Jamal yadai ? naga kamar bakason tafiyan nan, tun da kake tafiya bantaba ganin jikin ka yayi sanyi haka ba"

Ya ke, yayi sannan yace a,a bakomai daddy kainane yake dan min ciwo"

Toh kasha magani ko?

Mikewa yayi tare da fadin idan nafita zan nemi magani"

Dahaka yayi sallama da iyayen Sa ya nufin office"


****



Deeni zaune agaban ummi nasiha take mai akan ya hakura da ma'u, amman ya dage yace inna sam asma'u kayan shi ce"

Dan haka wata dibara ta fado mata, tari tayi sannan ta juya tace"

Auta gawata jaka can kaje ka dauko min"

Mikewa yayi babu musu , bayan ya dako ya mika Mata"

Bude jakar tayi ta ciro kudi masu yawa ta mikawa deeni, sannan tace"

Kaga wannan kudin nabaka ne kayi kudin mota kaje garin baguma kaji ko suna da lbrn mahaifin ka"

Wani kallo deeni ya watsawa ummi sannan ya karkace baki yace"

Ummi aina gaya miki idona idonshi za'yi batacciya Allah wlh"

A'a auta koma me kakeji kayi hakuri, inason naganshi akwai maganar dazan gayamai, kuma kagani bani da lfy bazan iya zirga zirga amota ba"


Daker da sudin goshi deeni ya yadda zai tafi baguma"

Haka ko, washegari ta asubahi ya dauki hanya"

Da daddare ya isa kyauyen su, dan haka ba kowa ne yasan da zuwan nashi ba"

Tsofaffen kakannin shi yasamu kwance tsakar gida suna shan iska"

Sallamar shi yasa tshowa duduwa karo fitilan kwan dake gefenta"

Shima tsoho carbin shi ya rarumo yana fadin wanakeji kaman Shamsudeeni"

Shine ya fada atakaice"

Arude tsofaffin biyu sukayo kashi suna haska shi da fitila"

Tabass shamsudeeni ne murnace ta kamasu gaba dayan su"

Bayan sun natsu suka kawo masa abinci, yanacin abincin yana gaya musu yadda ya baro jikin ummi, tare da gaya musu dalilin zuwan nashi"

Duduwa ce tace muko muke da lbrn bashir, dan bashir ya dawo tuntuni, kuma yayi bakincin rashin samun ku anan"

Shiru duduwa tayi na dan wani lokaci dan haka deeni yace toh yanzun yana ina kenan"

Nigeria wani gari wai Abuja, bashir yayi kodi sosai bayan komawan shi Nigeria, tunda Allah ya hadasu da dan yayata Alhaji Muhammad Inuwa......


Deeni bebari ta karasa ba yace"

Ashe arziki ya tafi nema mu kuma ya bazatar damu, ya tafi yabar ummi cikin tashin hankali, ya manta da ita bare ma ya tuna dani, aina zan ganshi?

Ai ka baroshi abaya, mikewa tayi tare da fadin inzuwa"

Bata jima ba ta dawo ta mikamai wata takarda, Karba yayi ya duba address ne ajikin ta"

Dubawa yayi sannan ya mike tare da fadin zan koma, zanje innemeshi duk inda yake"

Be samu mota adaren ba dole tasa ya kwana atasha, da misalin karfe 6;00am motar su ta tashi,

Sai washegari ya iso Abuja cikin ikon Allah ya isa kofar gidan kaman
yadda adireshin ya nuna"

Saidai ganin gidan ya tsorata shi, sabo da tsaruwan sa, harya fara tunanin anya kuwa gidan ne, dan yafi kama da gida jen turawa"

Lokacin daya nufi shiga gidan fir megadi ya hanashi shiga, acewar sa ai ba'a sanar cewa wani bako zaizo ba"

Dakarfin tsiya deeni ya tura megadin ya shige tare da fadin ubanka yaci uwatarrr"

Megadi bekara cewa zai tare deeni ba dan ya gano kalla, uhu ya fara yana fadin ranka ya dade akwai Matsala"

Wani farin Alhaji ne ya fito cike da zafi, bayan shi wasu maza ne, da alama abokanshi ne"
Ganin deeni cikin sauri alhaji ya fara tako matakalar benen"

Tsayawa deeni yayi aharabar gidan yanawa alhaji wani mugun kallo"

Cikin sauri ya karaso ya kama kafadar sa, tare da fadin shamsudeeni kai ne"

Be tanka ba kuma har yanzun wani kallo yake watsa mishi"

Hannun shi alhaji bashir ya faraja yayi cikin gidan da shi"

Afalo yaga wata yariya zaune ta hakimce gefenta yara ne guda biyu suna wasa"

Harara ya watsa mata kardai wannan yariyar baban nasa ya aura"

Dakin baccin sa yakai deeni, cikin sauri ya jawo akwatin kayan sa ya aje agaban deeni, tare da fadin"

Shamsudeen ka bude akwatin nan ka zabi kaya, ka sauya, bana son abokai na suganka cikin wannan shigan, zaka bani kunya, zaka zubarmin da mutunci, inason kasan wani abu yanzun bada bane, mutane namin kallon mutunci bazan su ka zubar min da mutunci ba"

Bakin gadon deeni yaje ya zauna ya daura kafa daya kan daya yana fito"

Sororo alhaji bashir yayi yana kallon deeni, nadama ce ta shigeshi me tsanani"

Hannu yasa Aljihu ya ciro waya, ya danna sannan ya kara akunne, zuwa can ya fara fadin Alhaji inuwa yau Allah ya kawo shamsudeen har gida, gashi agabana sai dai yana nan da halin nan nasa wadda nagaya maka, ka......

Shiru yaji baban nasa yayi yana saurara, zuwa can ya miko ma deeni wayar tare da fadin ku gaisa da baban ka"

Tunda suka gaisa da deeni da alhaji inuwa suka shiga zuciyoyi junan su,"

Daga karshe alhaji inuwa yacewa deeni karyaje ko kofar insha Allahu jibi zaizo ya dauke su"


****

Abangaren deeni kuwa yau tafiyan shi saura kwana biyu duk yabi ya kara rikicewa, dan haka da safe dayaje gaida momy harya mike zai fice ta dakatar dashi"

Jamal wai meke damun ka ? Ko tafiyar ce baka so?

A'a momy nima bansan me yake damuna ba, haka nan dai nakejin babu dadi"

Shiru momy tayi zuwa can ta sake cewa, Jamal naga dai ba yau ka fara tafiya ba, ban taba ganin ka daga hankalin ka kaman wannan ba"

Shiru yayi tare da sunkuyar da kanshi kasa"

Kallon shi Momy tayi sannan ta sake cewa"

Jamal kodai kana son katafi da matarka ne?

Kanshi akasa yace a'a bahaka bane"

Kollonshi kawai Momy tayi ta tabe baki"

Da daddare bayan yayi shirin kwanciya ya nufi dakin ma'u"

Tana kwance, ta kurawa sama ido, har ya zauna kusa da ita bata sani ba"

Tsintan kan shi yayi da hura mata ido"

Cikin sauri ta lumshe idonta sannan ta bude su akan Jamal"

Husna tunanin me kike?

Bakomai ta fada atakaice"

Shiru yayi zuwa can ya sake cewa momy ta gaya miki Zanyi tafiya jibi"

Eh ta fada atakai ce"

Shiru yayi tare da lunshe ido zuwa can ya sake cewa idan na tafi zanyi wata 7 ko sama da haka, ban yadda kije ko kofar gida ba, ki natsu ki tsare mutuncin kanki, karkimin wasa da aurena, ki sani duk abin da zakiyi idan ni bana ganin ki Allah na gani"

'Dauke kai tayi tare da turo baki"

Kyau yaga tamasa dan haka ya zuba mata idanuwa, zuwa can yasake cewa"

Idan akwai abinda kike so ki fada ko kirubuta kobe ki bani, hannu yasa a aljihu ya ciro wata waya ya mika mata tare da fadin gashi nasa miki no duk wadda ya gamata aciki, bayan su ban yadda kiyi waya da kowa ba idan kikayi Allah na kallon ki kuma ban yafe ba"

Kara turo baki tayi tare da dan murgudawa"

Murmushi yayi kadan sannan yace gashi har zan tafi baki sake min kunshi ba, ko baki son na gani ne"

Saida ta murguda baki sannan tace ninace banaso dan Momy tace zata kirata nace a'a

Abun mamaki Jamal beji haushi ba, murmushi ya sakeyi sannan yace toh dan Allah gobe Ki daure kiyi, kinga jibi zan tafi"

Kara bata rai tayi sannan ta jawo bargo ta rufe kanta' ganin haka yasa ya mike ya fita"

Washegari Jamal ya samu daddy da momy afalo"

Zama yayi nesa dasu, cikin nishadin daddy ya juya ya kalli momy sannan yace"

Kinko gaya masa anga shamsudeen?

Ziro ido Momy tayi tare da fadin na manta ko"

Shiko Jamal fadi yake waye haka?

Dan wajen kanina alhaji bashir dana baka lbr, tun muna yara mukayi alkawari idan muka haifi 'ya'ya maza zamusa musu shamsudeen da jamaludeen, kuma gashi Allah ya cika mana burin mu" gobe zan dauko shi ya zaauna tare damu, kai kuma gashi gobe zaka tafi"

Eh daddy ma gaisa ta waya daya iso akirani awaya











Heart Beat
*Mmn Yazeed*
[24/01, 11:04 a.m.] β€ͺ+234 906 689 6652‬: πŸ’—πŸ’πŸ’πŸ’—
​*BUGUN ZUCIYA*​
( ​Heartbeat​)

πŸ’“πŸ’πŸ’—
πŸ’—

πŸ’“πŸ’πŸ’—
​By​
πŸ’—
​​*Fadeela Lamido*




*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATION🀝*
​


*Sadaukarwa*

*Faty Afreen Firdausi Sodangi Miss xoxo Zeenaseer, Deeja Wazari, Aisha Ali Garkuwa, Safiya Galadanchi Cwtjiddah Hamagee*



6⃣4⃣to6⃣6⃣





Naso ace kana nan dan zaifi jin dadin zama agidan"

Yake Jamal yayi kandan"

Daddy ma gyara zama yayi sannan yace"

Daman akwai mgnr da zan maka" kaga iyalin ka ya kamata ta koma makaranta sabo da yamzun zamani ya canza idan babu ilmi kana ji kana gani za,a barka abaya, dan haka kafin kadawo zaka samu ta koma makaranta"

Jamal ji yayi gaban shi yayi mummunan faduwa, tare da tashin hankali me tsanani"

Daddy ya kula da haka dan haka ya tsare shi da ido, tare da fadin Jamal ko baka son taci gaba da karatun ne?

Cikin sanyi jiki
yace gsky daddy abari saina dawo"

Me zakayi idan kana nan din, ai duk daya ne, kaga nafisa takusa karasa nata gara ta fara tun nafisa nacen ko?

Gyada kai kawai yayi badan ransa yaso ba, amman hankalin shi tashe yake"

Tashi yayi yabar falon, part din su ya nufa, nan falon ya kwanta, rufe ido yayi kaman me bacci, zuwa can ya bude, wayar shi ya jawo ya danna sannan ya karata akunne"

Zuwa can yace Usman ya gida"

Daga can cikin wayar usman yace lfy lau manga ya iyali"

Tsaki Jamal yaja kadan sannan yace lfy, gobe ne fa tafiyan mu"

Eh ai ina lissafe Allah yasa kuje lfy kudawo lfy"

Ameen yace ahankali sannan yaja wani gwaron ajiyan zuciya"

Ya dai ? Naga kamar bakajin dadi ne?

Wlh usman banaji dadi narasa meke damu na, kwata2 bana son tafiyan nan"

Dan murmushi usman yayi sannan yace haba Jamal kayi tunani dole zaka san abin da yake damun ka"

Shiru yayi zuwa can yaja tsaki yace"

Nasan dai banason barin Husna gida"

Kecewa da dariya usman yayi, saida yayi me isarsa sannan ya sarara, tare da fadi"

Me zai hana kasata ajaka"

Tsaki Jamal yaja sannan yace usman bafa wasa nake ba, dagaske nakeyi da akwai yadda zanyi afasa tafiyan dana yi"

Sabo da Asma'u ?

Kin amsawa Jamal yayi, shiru sukayi nadan wani lokaci, zuwa can, Jamal yace"

Usman duk da baka nan garin nabaka amanar husna, akwai waya ahannunta yazun zan turo maka no ta ka kirata ka mata nasiha ta kulamin da aure na"

Shiru usman yayi yana sauraron shi, lallai Jamal soyayya ta mika harda sambatu, dahaka sukayi sallama"

Jamal tashi yayi ya zauna hannun shi duk biyun yasa ya dafe kanshi, ya dade ahaka zuwa can ya mike ya nufi gurin Momy"

Tana zaune kan kujera yaje ya zauna kusa da ita sannan ya kwantar da kanshi akan cinyanta"

Hannunta ta dauka ta daura akanshi tare da fadin Jamal wai meyasa kanada damuwa amman ka kasa fadamin, Jamal jikina yayi sanyi akan yadda kake yi"

Kamar bazai yi mgn ba, zuwa can yace, momy idan zai yuyo abar mgn maranta husna harsai na dawo"

Shiru momy tayi zuwa can tace Jamal wai me zai hana ka tarkata husnan ka tafi da ita tunda naga hankalin ka yaki natsuwa"

Momy muna da yawa zamuyi tafiyan nan, bamusan taka memen gurin da zamu zauna ba, kinga bazai yiyu intafi da ita ba"

Toh jamal ka kwatar da hankalin ka kuma ai ba ita kadai bace agidan"

Ajiyan zuciya yayi sannan ya mike ya sake komawa part din su"

Afolo ya samu ma'u tana zaune kanta babu dan Kwali"

Saida ya tsaya ya gama kare mata kallo, sannan ya karasa daf da ita ya zauna"

Cikin sauri ma'u ta matsa dan saitaga abin ya mata ban barakwai"

Kallo yabita dashi sannan ya kara matsawa tare da sa hannun sa yajawota jikin shi"

Kokarin kwacewa take Amman ta kasa duk da cewa hannu daya yasa amman saida yayi nasaran kwatar da ita akan cinyan shi, tare da zuba Mata jajayen idon shi"

Cin wata irin murya yace husna gobe zan tafi, inajin wani iri ajikina"

Cikin tsiwa tace toh ni ina ruwana dan Allah ka sake ni"

Idon shi ya kara zuba mata tare da fadin husna kallah"

Idonta ta bude akan nashi, gani tayi idonshi yayi jawur kaman garwashi gefen kanshi ko wasu jijiyoyi ne rudu2, jikin shi ko banda rawa babu abin da yake, taso ta danji tausayin shi Amman saita kawar da idonta daga kallon shi Cikin san yin jiki tace yaya Jamal sake ni"

Bazan sake kiba husna inason kafin na tafi na neme gafaran ki dan nasan ni me laifi ne awajen ki, duk da cewa duk abinda na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login