Showing 3001 words to 6000 words out of 95354 words
Chapter 2 - BUGUN ZUCIYA Hausa Novels Complete by Fadila Lamido.txt
kuma ma bandan rashin hankali irin naki ya zaki hado harda bra dinki kice wai akwaiwa bala, yanzun ke bazaki iya wankewa ba acikin toilet"
Mama nifa wlh abani duk wani aiki amman banda wanki" ni ban ma iya ba wlh"
Toh aiko zaki koya maza ki kwashe kayan ki kije ki wanke babu me wanke miki agidan nan"
Buga kafa ta fara akasa tare da kara kallon agogo cikin kuka tace"
Mama nifah inason ne naje mkrntn yamma Kuma gashi yanzun lokaci ya kure, kuma idan banje yau ba duka na za'yi gobe"
Karfe nawa kika shigo gidan nan?, ai suma malaman sunsan yau bazaku samu zuwa ba, tun da su suka saku aiki"
Juyawa kawai tayi ta koma daki, dan bata da bakin mgn, kan gadonta ta fada, murmushi ta sake lokacin da ta tuna baccin duna, tare da wassafa fuskanshi a idon ta, mutun ne kyakyawa sai dai yaya akayi ya saka kanshi adaba, gashi duk anji mishi ciwo ajiki, da alama ma bashi da karfi tunda yake bari na jimai ciwo, tsaki taja tare da fadin katon banza kana Yawo da wukake amman kana bacci atiti badole ayanyanke ka ba"
Washegari tun karfe 7:30 ta nufi mkrnt bata biyawa zainab ba dan tasan bazata barta tai abinda tayi niyya yadda ya kamata ba"
Tafe take cikin kayan mkrnt idan ka ganta gwanin ban sha'awa, ita ba dugowa ba ita ba gajera ba, fara ce tas, ga wani siririn hanci da bakin ta madaidai ci shekarunta basu wuce 16 zuwa 17 ba amman kirjinta cike yake kai kace wata cikkakiya budurwa ce"
Lokacin da ta isa kofar gidan da taga duna dubawa tayi ko ina babushi babu alamar sa, azuciyar ta taji babu dadi dan taso ace ta ganshi"
Kad'a kai tayi ta wuce mkrt har aka tashi bata cikin natsuwar ta, Allah2 take atashi tabi hanya"
Tana ganin akusan tashi ta tsiri rubutu, dan haka su rahama basu tsaya jiranta ba sukayi
tafiyan su"
Saida ta dainajin hayaniyan yan mkrntr sannan ta dauki littafinta ta fito"
Dakalin ta da ta ganshi akai jiya yauma yauma kwace yake agurin ya daura kafarsa daya kan daya, ya daura hula kan fuskar"
Babu kowa alayin dan unguwa ce ta masu hali kowa yana cikin gidan sa babu ruwan wani da wani, hakan ne yaba ma'u daman isa gaban duna cikin sanda"
Cikin siririyar muryanta ta rangada sallama taji shiru babu amsa dan haka ta gara matsawa daf dashi tare da tabbacin yauma baccin shi yayi nisa kaman jiya, ahankali ta daga hannuta ta dafa hular dake kanshi, jitayi be motsaba dan haka ta daga hular fuskan ta bai yana"
Idon shi rufe dan haka ma'u ta bude baki da hanci tana karemai kallo"
Deeni wankan tarwada ne dan baza akirashi baki ba yana da duguwar fuska tare da dogon hanci daidai gwargwado, sakko da idonta tayi kan kirjishi da tat bai su kai kaca kaca dashi, yatsa ta cija sannan tace afili, meyasa kake bacci atiti bayan kuma ka sani sarai nauyin baccin gare ka, koni danake mace zan iya kashe ka ma ba jimaka ciwo ba, kallo ta kara masa sannan ta saka hannu ajakar makaranta ta dau waya ta daukeshi hoto har guda biyar sannan ta kwashe da dariya tare da fadin kai gskiya ni jaruma ce, agogo cikin wayar ta duba sannan ta nufi gida cikin sauri"
Washegari ko ta nuna ma kawayen ta hotunan duna kaman yadda tayi niyya, mamaki ne ya kamasu tun daga ranan zee bata kara yadda ta jera da ma'u ba, dasu rahama take jerawa su jirata daga can gefe ta gama tsokanan duna tazo su tafi suna kyalkyalketa dariya"
Ahankali wannan dabi'a tazama jiki agun ma'u kullum idan aka tashi mkrnt saita sameshi agurin yana bacci, haka zata gama surutun ta akan duna ta wuce gida"
Haka har aka samu tsawon wata biyu ,wannan lokacin ma'u intaje gaban deeni bata sanda ko mgn ahankali dan tasan idan har yayi bacci idan kaso zaka iya daukan shi ka gudu"
Abu ya zaman ma ma'u jiki harta kai alhamis da juma'a da babu makaran ta tana shiga damuwa dan haka yau juma'a da wuri ta isa dakin abban ta"
Bayan ta gaida shi ta zauna daf dashi"
Kallonta yayi da murmushi akan fuskanshi yace mamana ya akayi? duk yadda akayi akwai abin da kike so"
Cikin shagwa ba tace abba na tuna Dada ne"
Dada tana nan lfy mamana kulum tana cewa nagaishe mata da takwararta, ba inagaya miki ba?
Eh abba amman ni inason ne naje naganta"
Shiru yayi zuwa can ya dago yana share zufa yace, to naji amman kibari nasamu lokaci zan kaiki da kaina"
Shiru tayi badan ranta yaso ba, tana fitowa ta fara matso hawaye, karo sukaci da mama zata shiga dakin, ganin ma'u cikin hawaye yasa tabita da kallo"
Alhaji yau kuma fada kukayi kaida maman taka?, naga ta fita tana share hawaye"
Au kuka takeyi? Allah sarki, wlh ina matukar jin dadin yadda Asmau take nuna soyayyarta ga dada, amman kash bazan iya barinta ta zauna acan ba, sabo da gudun kar abinda ya faru shekarun baya yasa ke faruwa, shi yasa bana son na nuna mata gida biyu, kuma nacewa dada ta dawo ta zauna tare damu tace a,a bazan iya bari Asmau ta dinga zirga zirga atiti ba yau tana gida gobe tana gidan dada, dan gudun haduwa da gurba tattun samari"
Mamace ta dago da kanta bayan ta gama sauraren shi ahankali tace alhaji Allah ne fah yake tsarewa, kuma ai be kamata ace anhanata zuwa gidan dada ba itama dadan ai bazataji dadi ba"
Mikewa yayi fuskan shi babu annuri yana kokarin fita yace kice mata idan shirye take ta fito na sauke ta"
Dagudu ma'u ta fito fuskanta cike da fara'a ta shiga motar ta zauna har suka isa bece mata komai ba"
Akofar gidan ya sauketa sannan yace ki jirani idan nata so zanzo na dauke ki, ranta be soba, amsawa tayi ta shige gidan"
Bakaramin dadi dada tajiba dataga ma'u, aikace2 gidan sukayi tare sannan suka zauna suna hira, suna cikin haka dada ta fara gyangyadi, ma'u naganin haka ta kalli agogo 11:15 tagani, zama tayi har taga 11:20 dan haka ta mike ta dauki bakin gyalenta agefen gadon dada sadaf2 ta fice"
Da sauri take ta fiya dan taje ta dawo kafin dada ta tashi, tun daga nesa ta gane baya nan, dan gurin da yake kwanciya babu komai awajen, ja tayi ta tsaya domin taso ace ta ganshi"
Gajiya tayi da tsayowa dan haka ta juya ta fara tafiya da nufin komawa gida, kaman ance ta juya ta hango shi kwace, kai yaya akayi haka? Ma'u ta tambayi zuciyarta, juyawa tayi cikin sauri ta isa gurin tare da sallama, jin babu amsa ya tabbatar mata da bacci ya wuce dashi daf dashi taje ta cire hular dake fuskanshi, idonshi rufe yake kamar kulum, fuskanta takai saitin tashi sannan ta huramai iska ahankali"
Wani gwaron ajiyan zuciya ya Saki, da sauri ma,u taja baya"
Ganin yaci gaba da baccin yasa ta sake matsawa ta bude baki ta sake hura mai fuska akaro na biyu, karaf taji anrike ahannunta"
Subuhanallah yau nashiga uku na lalace, wayyo abba na waiyo dadata kuzo ku ceceni, dan Allah kayi hakuri
wlh takalmi nane ya tsinke na tsuguna zan dauka bansan akwai mutum agurin ba
Heartbeat
Mmn Yazeedπβ
[24/01, 11:03 a.m.] βͺ+234 906 689 6652β¬: ππππ
β*BUGUN ZUCIYA*β
( βHeartbeatβ)
πππ
π
πππ
βByβ
π
ββ*Fadeela Lamido*
7β£ to 9β£
π Murmushi yayi kadan batare da yace komai ba, binta da wani mayan kallo kawai yake"
Ma'u ko duk ta firgice tana rokon shi ya sakar mata hannu"
Mikewa yayi tsaye batare da ya saki hannun ba, kuma har yanzun idonshi na kanta wani maya tatcen kallo yake mata"
Cikin wata irin murya da bazata iya tattance yanayin sa ba yace"
Ke baby natsu, bason gaddama, kishiga hankalin ki, kinji ko?
Hannunta tasa duk 2 ta rufe bakinta tana daga kai alamar eh, acikin zuciyarta ko fadi take tawa ta kare"
Menene sunan ki?
Cikin rawar baki tace Asmau"
Lumshe ido yayi sannan yasa ke cewa menene ya fito dake yau bayan babu mkrnt?
Dan Allah dan darajan annabi kayi hakuri wlh daga gidan kakata nake, nasan yanzu tanacen tana nema na"
Cikin wata irin murya yace baruwa na da wata kakarki ni ke kadai nasan.....
Kukane ya kwace mata, cikin kukan tace to aini ban sanka ba wlh tsautsayi ne kawai ya kawoni nan, wlh da nasan haka ne da banzo ba"
Murmushi ya sakeyi ahankali ya kara runtse hannuta cikin nashi, tare da lumshi ido"
Zuwa can ya bude yace inace kinzo gadi nane?, dan kada abokan gaba su kawamin farmaki, dan kinsan nifa nauyin bacci gare ni, ke fah?
π« Nima inada shi wlh, narantse inada shi"
Wannan karan saida yadan dara sannan ya dan jawota jikin shi tare da fadin baby ki kwantar da hankalin ki, bazan miki komai ba, jarumtar ki ta birgeni, ni jarumi ne dan haka inason naga mace jaruma, kin yi kokari sosai dakika tunkare ni, amman meya hana kika kasa hakuri zuwa gobe asabar kika fito yau?
Ainace maka gidan kakata naje yanzun ma tsautsayi ne ya fito dani"
Hmmm kawai yace sannan yaja hannuta zuwa gurin kwanciyar shi ya zaunar da ida"
**
Aban garen dada kuwa da misalin 12:09 sallama alhaji ne ya tasheta daga bacci"
Afirgece ta tashi tana fadin takwara shine baki tasheni baccin ba bayan kinsa ina tafiya masallacin juma,a da wuri"
Gaba dayan su wurga ido suke suga ta ina ma'u zata bullo daga abba har dada"
Jin shiru yasa dada ta shiga kwala mata kira taji shiru, mikewa tayi azabure tana fadin zoka zauna inaga ta shiga gidan tabawa bari nakirata"
Zama yayi kamar yadda dada tace sannan ya cire hular kansa ya aje agefe, tare da fadin Hmmm Allah ya kyauta"
Lokacin da dada ta shiga gidan ta bawa cemata tayi ko kallita bata gani ba, dan haka tayo waje hartana tuntube"
Azauren suka hadu da dan tabawa yana kokarin shiga gidan, kallon shi dada tayi tace kai iro baka gamin Asmau ba?
Aiko dazun naganta nan wajen hanyar mkrtnr su......
Bata bari ya rufe baki ba tabi hanya tana gudu2 sauri2"
Kalu innalillahi wa Inna ilaihir raju'un ta fada lokacin da ta hango ma'u rike hannun Duna"
Jikintane ya fara rawa bata San sanda ta kwasa aguje ta nufi gida ba"
Ganin dada agoje abin yabawa iro daya biyo bayan mamaki, shan gabanta yayi dan gudun karta tuntsura, riketa yayi tare da fadin dada lfy menene ya faru?
Ajiyan zuciya ta fara bata iya cewa komai ba saijan hannun iro take"
Daga nesa tamai nuni dasu, lokacin suna zaune ita da Duna"
Salati yayi sannan yace dada, ki tsaya inwuce saiki kwala mata kira tunda ke tsohowa ce kila bazai miki komai ba, amman ni idan ya ganni akwai matsala dada, tunda shi fadan shi baya wucewa inda kikasan shedan haka yake, cikin sauri iro yabar wajan yana me Kara karfafawa dada guiwa da hannun shi"
Tashin hankali ne sosai azuciyar Dada, kafafuwanta banda rawa babu abinda suke, kallo ma'u tayi tana mamakin yaya akayi ma'u tasan deeni harta bari suka zauna guri daya , kuma da alama ba tursasata yayi ba, kawar da tunanin tayi sannan ta daga murya ta kwalawa ma'u Kira"
Tana hango dada ta mike azabure, ta nufota aguje, ganin haka duna ya mike ya biyo bayanta"
Takaici ne ya kama dada dan haka ma'u na isowa ta daga hannu ta sharara mata mari, hannu ta sake dagawa zata kara mata, taji andaka mata tsawa cikin wata irin murya ta kyauraye"
Ke ! Ke!! Yasin yasin kika sake hannunki ya kara kaiwa jikinta sena sassara ki, Allah wlh *gunduwa gunduwa* zanyi dake, yasin hannunki ya kara kaiwa jikin ta kigani"
Suman tsaye dada tayi, fita tayi daga hayyacin ta, lokacin da network dinta ya dawo gani tayi suna tafe ita da ma,u sai janta take, tana kara fadin dada taho mana"
Bata iyace mata komai ba illah binta da take da kallo, sai dai akwai tashin hankali karara a idon ma,u"
Sauri ta kara dan sai yanzun ta tuna abban Asma'u yana gida yanajiran su, jitayi kaman lema ajikinta dan haka takai idonta kan zaninta jike yake sharkaf nan ta tabbatar fitsari ne"
Suna karya kwanan layin, ma'u ta hango abbanta sai zagaye yake akofar gidan dada, gefen shi iro ne azaune ya rafka uban tagumi"
Hunnun dada ta matse tare da fadin wayyo Allah na, nashiga uku"
Kallota kawai dada tayi ta tabe baki tare da fadin Hmmm"
Jikin ma'u ban da rawa ba abinda yake, cikin mtsanan cin tashin hankali ta taja ta tsaya tana me tsiyayar da hawaye dan ta tabbatar yau kashinta ya gama bushewa"
Ganin abba na tahowa yasa ta faraja da baya ahankali, tana kokarin rike Dada"
Yana isowa yasa hannun shi ya rabata da jikin dada ya zaf ga mata mari har saida ta fadi kasa, cikin karaji yace daga gidan uban wa kike?, jin da yayi babu amsa yasa ya daga kafa ya nufi cikinta yana kokarin tokarin ta aciki, tare da fadin badake nake mgn ba?
Cikin matsanan cin firgici dada ta rike Abba da wani irin karfi da batasan tana dashi ba, tana fadin kasheta zakayi ne?, toh bismillah nunamin yarka ce, nace kanuna min ka haifa kuma ni mahaifiyar ka ban isa na aiki yar ka ba"
Sanyi jikin Abba yayi, cikin natsuwa ya shiga bata hakuri, badan ya yarda cewa dadan ce ta aiketa ba"
Haka dada taita fada abba nabata, hakuri da karshe da kanta tasa ma,u amota abban ta, tana cigaba da fada"
Dada na tsaye akofar gida har motan abba ta bace, ajiyan zuciya ta sauke sannan ta juya ta shiga gida tana mamakin inda ma,u tasan deeni"
Kulle gidan tayi da sakata domin ita har yanzun gani take kamar duna zai shigo mata gida dan ba karamin tsorata tayi ba, wanka tayi ta gyara jikinta sannan ta wanke kayan da ta cire ta shanya, aranan dada bata runtsaba data rufe ido duna take gane"
Asmau kuwa suna isa gida ta sauka aguje tayi cikin gida"
Binta da kallo Abba yayi tsananta me tsanani yaji acikin ransa dan haka bayan ya shiga falon ya zauna, ma'u daga daki taji yana waya yana fadi"
*Usman* na gari ne?, toro mun shi yanzu yanzun nan, akwai matsala"
Faduwa ma'u tayi daga kan gadon dan ta tabbatar yau sai dai buzun ta indai ta bari har ya usman ya riketa"
*WAIWAYE*
Alhaji sani haifaffen jahar Kano ne, su 2 iyayen su suka haifa, daga shi sai yayan shi Alhaji musa, alhaji sani shine mahaifin Asmau, su uku suka haifa, tare da matar sa Fatima, usman shine babban, sannan fiddausi sai yar auta asmau wacce taci sunan kakanta"
Shiko alhaji musa Saida ya shikara 15 be samu haihuwa ba, dan haka kaninsa alhaji sani ya bashi danshi usman alokacin yana da shekara 5"
Usman ya taso cikin gata gidan alhaji musa tamkar dan da suka haifa da cikin su, yayin da alhaji sani yaci gaba da kula da fiddausi wadda take yar shekara 2"
Alharji sani da yayan sa ma,aikatan gwamnati ne, kuma suna samu daidai gwargwado dan a unguwar su idan xa ai lissafin masu hali baxa a kirga 5 babu su aciki ba"
Fiddausi nada shekara 10 aka haifin Asmau, tun daga kan asmau basu sake samun haihuwa ba"
Bayan shekara 8 fiddausi ta zama cikakkiyar budurwa meji da kanta duk abin da take so