Showing 27001 words to 30000 words out of 95354 words

Chapter 10 - BUGUN ZUCIYA Hausa Novels Complete by Fadila Lamido.txt

29 Oct 2025

498

kike so shi zan baki bazan miki auren dole ba da iznin Allah, inason nasan meye azuciyar ki game da jafar ?

Motsa baki tai tayi daker ta iya bude baki tace Abba ni banason shi"

Saboda me ? abba ya tambaya

Abba tsoho ne fah kuma yana da mata"

Murmushi Abba yayi kadan sannan yace ashe jafar ya cinka daidai, toh bakomai amman nayi miki sha,wan shi, dan yaro ne me mutunci da sanin ya kamata, haka iyayen shi mutane ne masu karamci, kuma bawani babba bane mamana, ko zai girmin usman bazai wuce shekara daya ba, amman ba komai tunda kince haka, gabe wani zaizo ki ganshi, kinji ko?

Saida gabanta ya fadi wato abba bazai bar mgn haka ba, da wannan tunanin ta tafi mkrnt ko wa Abba zai sake turo mata oho?

***

Akofar gidan su deeni ta hango samari cike, da alama yaran duna ne kome suke agurin oho, acikin su caka kawai ta sheda yanata fada yana daga hannu saidai har motan su ta wuce bata tsinci abinda suke cewa ba"

Ko a aji batai karatun kirki ba Allah2 take atashi break taje taga me akeyi"

Kawayen ta kallonta kawai sukeyi, domin sun kula akwai abun da ke damunta"

Ana buga kararrawa ta fito ta nufi gidan su deeni saidai yazun babu kowa akofar gidan"

Cikin gidan ta nufa tana tura kofar sukayi ido 4 da deeni, zaune yake kan kujera ummi tsugune agefen shi tana tsuma tsunma aruwa zafi tana dannan me ajikin shi"

Hunnu tasa ta mumtsuke idonta sannan ta sake sauke shi akan deeni, aguje tayi kansu, jinta kawai tayi jikin deeni ya rungume ta yana sumbatan ta"

Cikin sauri ummi ta dauke bokitin ruwan zafinta ta basu guri, jefe2 tana satan kallon su"

Sun dan juma ahaka ahankali asma'u ta zame ta koma gefe sannan ta zubawa deeni ido"

Shedan bulala ne ajikin shi rudu2 wasu guraren hadda ciwo, hawaye taji ya cika mata ido, nan danan suka fara zubowa acikin kuka tace nina jawo maka nasan bakowa bane yayi maka haka sai Jamal dan Allah ka yafe min"

Hannuta ya jawo ya riketa dakyau sannan yace....

Shine Asma'u amman karki damu yanaso ne wai ya nunamin shi Soja ne amman ba jarumi ba, wanna abin daya aikata ya nunamin be kai ba"

Kara karkace baki yayi sama sannan yace.....
Ai nagaya masa dan *uwas* data haife shi, idan yana jin yakai shege, ya goyo *uwassa* abaya, ya fadi ina zamu hadu, daban daban zasu koma gida"












Heart beat
*Mmn Yazeed*

​
[24/01, 11:04 a.m.] β€ͺ+234 906 689 6652‬: πŸ’—πŸ’πŸ’πŸ’—
​*BUGUN ZUCIYA*​
( ​Heartbeat​)

πŸ’“πŸ’πŸ’—
πŸ’—

πŸ’“πŸ’πŸ’—
​By​
πŸ’—
​​*Fadeela Lamido*




*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATION🀝*




Dedicated πŸ‘‡πŸ»
*Sa'adatu LamidoπŸ‘ŒπŸ»*



3⃣1⃣ to 3⃣2⃣





πŸ™‰πŸ™‰ Hannu shi yasa yana share mata hawaye, yana cigaba da fadin.....
Ki daina zubar da hawayen Ki abanza ni be tsoratani ba kuma banyi nadamar hadashi da duna ba, kisan menene, tuhumata yakeyi akan ki"

Ido ta zare akaina kuma?

Eh dan ya nemi nabashi takardan da kika wurgu min da ita"

Tashin hankali bai yane afuskan ta tace... Kabashi ne?

A'a na nunamai bansan wannan zancen ba, amman sai naga yayi dariya, na lura kanshi na aiki sosai, murmushi deeni yayi kadan sannan yace.....
Asma'u da kika samu lbrn Sojoji sun tafi dani ya kikaji?

Wani sabo hawaye ne ya fara zobo mata cikin kuka tace....
Komawa nayi tamkar marainiya, kullum cikin kuka nake, gashi ranan na taho da matsalata, domin mune mi mafuta, wlh ranan jinayi kaman bani da lfy, kuma bansan abinda kemin ciwo ba, tun daga ranan hankali na bekara kwanciya ba, kum.....

Deeni ne ya matse hannun ta, dan haka ta kasa karasa abin da tayi niyya, sannan ta daga ido ta kalleshi"

Shima ita yake kallo sannan yace.....
Inason nasan wacce matsala ce kikazo da ita ranan?


Shiru tayi zuwa can tace abbana ne yace.....
Inayin sauka zai min aure, kuma gashi saura sati 6, yace bazan wuce wata 3 agida ba, shine hankali na ya tashi sosai"

Hannunta ya kara runtsewa sannan yace.....

Toh menene abin damuwa anan Asma'u ?, ko bakison muyi aure ne ?

Shiru tayi tana kallon kasa, zuwacan taji ya sake cewa....

Gayamin meye matsalan ?

Kanta akasa tace inajin tsoron gayawa abbana kai nake so"

Matse hannunta yayi da karfi harsai da tayi kara, cikin yanayi irin na mejin zafi tace.....
Wayyo, hannuna dan Allah kabari da
Zafi fah"

Me yasa kike tsoro? taji ya fadi fuskan shi murtuk"

Saboda ina tunanin bazai yadda ba"

Bangane bazai yadda ba, shi zai zauna miki da miji ?

A'a ba haka bane, ta fada tare da kautar da idanta gefe, haka nan taji bata ji dadin furucin ba, sai take ga kamar da raini aciki"

Shiko ido ya kura mata zuwa can yace.... Inajin ki"

Idan ta kwal2 yayi kaman zatai kuka tace....
Yaya deeni ni. nasan waye abba na, mawuyacin abu ne ya amince dakai, ko hankan zata kasan ce ko, to saida sa hannun kakata, kuma nafara mata zancen duk tabi ta firgice, saboda ta tsorata dakai, gashi abbana jiya ya turo min wani mutumi wai mu daidaita, karashe mgnr tayi tana zubar da hawaye"

Tana rufe baki deeni ya zabura ya mike tsaye, kashi ya daga sama yana kallon sararin samaniya tare da fadin..... Kikace baban ki ya turo miki wani ?

Kaita daga alamar eh"

Kuma wadda aka turo din yaxo ?

Eh tasake cewa tanabin kanshi daya dage sama da kallo"

Shiru yayi, zuwa can yace..... Kinyi mai dariya ne?

A'a"

Mgn fah ?

Ahankali ta shiga fada mishi yadda sukayi da jafar"

Ajiyan zuciya ya sauke sannan ya sakko da kan shi ya kalleta, hannushi Yasa ya dagota sannan ya saki murmushi tare da fadin, na yadda kina sona, kuma duk wadda ya sake turo miki karki yadda ki kulashi bare har kimai dariya, ke bama haka ba, ko fuskanki karki yadda wani ya gani"

Shiru yayi ya kura mata ido sannan yace kince babanki dan rayi ne ko?

Shiru tayi ta kasa bashi amsa, dan tasan darajan abban ta, tsoro take kar yazo ya fadin mata wata mummunan kalma akan abbanta"

Shiru yaji dan haka deeni ya sake cewa.... Kakar nan taki mamanki ta haifa ko babanki ?

Jimmm ma'u tayi sannan tace abbana"

A haf, a gurita ya dauko, dan kakar nan taki, lutiyar munafuka ce, amman bakomai Wata rana zamu hadu"

Mamaki furucin deeni bawa ma'u, nan take ta fara hawaye wannan ai zagi ne, yana nufin abbanta ma munafuki ne kenan, cikin matsanan cin kuka ta mike tare da kwace hannunta daga rukon daya mata"

kofar gidan ta nufa, cikin sauri ya mike yabi bayanta , tana daf da fita ya riketa, ganin inda take hawaye yasashi fadin menene ?, na miki wani abune ?

Wani sabon haushi ne ya sake kamata dan haka kukanta yaki tsayawa"

Ganin inda take kuka ya sashi ya kwalawa ummi kira"

Bayan ta iso yace ummi kinga yariyar nan munacikin mgn ta rikece min da kuka"

Hannuta ummi ta rike suka shiga daki, deeni yaso shiga Amman ummi tace yajira su awaje"

Zuwa can suka fito ummi rike da hannun ma'u tana kara rarrashinta tare da share mata hawaye"

Ummi me tace miki? Deeni ne ya tambaya tare da tsare su da ido"

Auta ina yawan gaya maka karinka gyara kalamin ka, iyaye fah ba,abin wasa bane"

Nan take ya fahimci laifin shi dan haka bejira ummi ta gama mgn ba yaja hannu ma'u yayo waje da ita"

Akofar gida yaja ya tsaya sannan ya kalleta yace..... Allah ya huci zuciyar ki, basan mgnr zata baki haushi ba, lallai kinason abban nan naki, gashi shi kuma ko kadan be damu dake ba, ganin inda ta daure fuska yasashi ya kama kunnen shi duk 2 sannan yace na tuba"

Be barta ta tafi ba harsai da yaga ta saki jikinta, tana dariya"

****


Washegari da misalin karfe 5:00pm bakon Asma,u na 2 ya iso"

Tafiya take jiki babu kwari domin isa falon da abba ya ke sauke baki, zuciyarta cike da tunanin deeni dan komai takeyi jitake kamar ana kara mata sonshi"

Tana shiga falon da kujeran data fara cin karo ta zauna sannan ta juya mai baya"

Bata ce kala ba shima bece komai ba, sun kwashi kusan minti 15 ahaka, sannan taji wata siririyar murya tace..... hajiya ba mgn ne?

Yi tayi kamar bata jishi ba, dan haka ya miki ya dawo kujeran dake kallon tata, cikin sauri ta sake juyawa ta kalli ban garen daya baro, kafarta daya ta daura akan daya tana dan girgizawa"

Jitayi yana fadin OK nine bazaki kalla ba kenan, toh idan ke bazaki kalleni ba ni kibari nagan ki"

Nan ma shiru yaji kada kafa kawai take"

Zuwa can ya sake cewa Asma'u ni akan hanya nake, ya kamata ki juyo muyi mgn yamma nayi"

Batace kala ba dan haka ya mike yana fadin OK shikenan, na fahimta, bekara cewa komai ba yayi waje"

Koda ta shiga gida bata tayar da hankalin taba harkokin ta ta shiga yi, dan idan ta tuna abba yace bazai mata auren dole ba hankalinta na kwanciya"

Washegari da safe abba ya aiko kiranta, hijabi ta dauka dogo har kasa ta saka sannan ta nufi falon abba"

Tun abakin kofar taji wata murya kaman ta *Jamal* suna gaisawa da abba"

Gabanta taji ya fadi tare da tunani yaushe yashigo gidan nan da sanyi safiyar nan yazu musu gida?

Tana shiga suka hada ido da *Jamal* yana zaune cikin kakin sa, agaban abba ya zauna ya cire hular shi, tare da tankwashe kafa, kamar wani me daukan karatu"

Yana ganinta ya dauke idon shi, tsunawa tayi ta gaida Abba sannan ta juya ta gaida Jamal"

Ciki2 ya amsa, kamar wanda be iya mgn"

Abba ko daure fuska yayi sannan ya dawo da hankali shi gareta, acikin bacin rai yace.....
Mamana kin fara bata min rai fah, ya zan turo miki bako kimai shiru?, towai tukuna ma, me kike nufi ne ?, nakula lamarin ki akwai abin dubawa aciki, toh bari nagaya miki niba mutumin banza bane, bazan dauki iskanci ba, duk yadda akayi acikin 2 za,a samu daya kodai wani ke hure miki kunne, ko kuma kinason kita zama agida har ki tsofe, amman banda iskanci ya zan turo miki bako ki banza dashi??

Asma'u kuka kawai take harda shashsheka, zuwa can taji muryan Jamal yana cewa....
Abba tunda bata so abarta mana, ai naga bawani girma tayi ba"

Au, au haka zakace, eh dole kace haka tunda kaima auren ba damun ka yayi ba, Abba ya fada sannan ya koma kan ma'u yace zan turo miki bako na karshe acikinsu, su 3 nan dole ki dauki daya, idan kuma kinada wani boyayye ne wadda kike so to kidaina wahalar dani"

Kuka ma'u tai tayi agaban Abba zuwa can taga ya juya gurin Jamal sun cigaba da hira, mikewa tayi tana kokarin fita taji Jamal nawa Abba sallama"

Da sarauri yake tafiya dan haka yacin mata, angajeta yayi kadan sannan ya juya ya kalleta yace..... toh ballagaza saboda rashin hankali kina kallo na kuma kika bege ni"

Cikin murya irinta wadda yaci kuka ya koshi tace ai kaine ka begeni bani ba"

Hannu ya mika ya murde mata kunne, batasan sannan da ta kwallah kara ba"

Mama ce tafito da sauri tana fadin menene ya faru?

Tseye ta same su ganin mama yasa shi ya saki kunnen, yana fadin mama wlh yariyar nan bata da kunya, tana ganina fa amman saita ture ni"

Juyawa mama tayi tana fadin wlh kabata kashi, batabari mama ta wuce ba tabi bayanta da gudu tana mamakin halin Jamal, wato banda mugunta kuma harda sharri?

Tundaga ranan abba be sake mata zancen aure ba, har ranan saukan su tazo, anyi sauka nagani na fada, abba yayi farin ciki sosai ganin inda ma'u take raira karatu hawaye yaji yana zubo mishi saboda tsabar farin ciki, addu'a ya fara Allah ya nuna mishi ranan aureta haka, itama ma,u farin ciki tayi sosai ganin dangi duk sun hallara kuma duk dominta"

Deeni ne kawai babu agurin tayi2 yasa manyan kaya yazo, amman yace shi bazai saka ba dan tunda yake betaba saka manyan kaya ba, dan haka tayi fushi tace karyazo"

Sun yi sauka da kwana 2 Abba ya aiko kiranta, mgnr dai daya ce gobe bakonta zaizo"

Kin tashi tayi tai zaune ta fara kuka, banza abba yayi da ita ya juya yaci gaba da rubuce2"

Suna haka alhaji musa ya shigo, ganin ta haka yasashi tambayan lfy?

Abba ne ya gayamai duk halin da ake ciki, shiru yayi zuwa can ya juya ya kallai ta yace"
Asma'u duba, ai shi aure dole ne, dan haka idan Allah yaso, nan da sati 2 kina dakin mijin ki, ko akwai wadda kike so ne?

Motsa baki ta fara amman ta kasa bude baki"

Alhaji musa ya sake cewa inajin ki, nakula bakin ki akwai mgn

Dago kata tayi ta kale abba sanna ta sake maida kanta kasa hawaye na zubowa tare da majina"

Abba ne yace ni Ki daina kallo na, ki fadi abin da ke bakin Ki"

Alhaji musa cikin tohoma yake kallon ta sannan yace....
Kina da wadda kike so ne?

Ahankali ta daga kai, saika kula sosai zaka gane"

Abba tashi yayi ya zauna sosai sannan yace waye shi?

Alhaji musa ne yayi murmushi sannan ya a,a bahaka za'ayi ba, ta turo mana shi kawai, ai daman mu bamu da burin yi miki auren dole, dan haka ki gaya masa munason ganin shi"

Ciki2 tace abba iyayen shi ne zasu zo, ko shi?

Girgiza kai Abba yayi cikin takaici, alhaji musa ne yace shi dai muke son gani kafin ajega mgnr iyayen sa, ai kisan aure yana son bincike ko ?













Heart Beat
*Mmn Yazeed*​
[24/01, 11:04 a.m.] β€ͺ+234 906 689 6652‬: πŸ’—πŸ’πŸ’πŸ’—
​*BUGUN ZUCIYA*​
( ​Heartbeat​)

πŸ’“πŸ’πŸ’—
πŸ’—

πŸ’“πŸ’πŸ’—
​By​
πŸ’—
​​*Fadeela Lamido*




*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATION🀝*
​


Dedicated πŸ‘‡πŸ»
*Firdausi Sodangi Aisha Aliyu Garkuwa & Deeje Waziri*😍😍



3⃣3⃣to3⃣5⃣



πŸ–€ Tashin hankali ma'u ta shiga tunkafi tabar falon, mikewa tayi jiki babu kwari ta koma dakin ta"


Ko acan din ma tunani ta shigayi, ta yaya zata kawo deeni gidan su, anya idan abba yaga deeni bazata fuskanci tashin hankali ba kuwa?

Hakika da ace zan iya hakura da deeni, da komai yazo min da sauke saidai bazan iya ba, yanzun ne ma nakejin son shi acikin zuciyata"

Shiru tayi tana tunanin hanyar da zatabi su hadu da deeni ayau"

Tana cikin wannan tunanin taga abba ya turo kofa, idonshi jawur har sun dan tasa"

Bakin gadon yazo ya zauna, yayi jugun yana kallan kasa"

Tsoro ne ya kama ma'u, kodai abba dokana yazo yi, wannan tunanin yasa ta fara ja da baya harta sauka agadon ta tsuna akasa"

Kallonta abba ya sake yi, sannan ya maida idon shi kasa, yayi haka kusan su uku sannan ya mike tsaye ya goya hannushi abaya, cikin wata irin murya wadda batasan Abba na da itaba taji yace.... Asma'u kin munafunce ni, tuntuni naso na miki aure amman sai kika nunamin ke ba yanzun ba, sai ayanzun naga laifina dana biye miki, shiru yayi zuwa can yace a ina kuka hadu dashi?

Cikin dasheshshiyar murya tace layin makarantar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login