Showing 63001 words to 66000 words out of 95354 words
Chapter 22 - BUGUN ZUCIYA Hausa Novels Complete by Fadila Lamido.txt
haka ya fara neman dayan layin"
Saida ta kusan katsewa sannan ya dauka, cikin dariya taji suna gaisawa sannan ya gayamai gashi agidan su"
Gani kawai tayi usman ya miko mata waya, dan haka adaburce ta karba tasa akunnenta"
Gaidashi tayi saida ya dade kafin ya amsa sannan yace ya bakin, kiji sauki?
Eh kawai tace idonta akasa"
Shiru sukayi dukkan su zuwa can Jamal yace *Husna* ?
Saida Asma'u ta lumshe idon saboda muryar da Jamal yayi amfani da ita wajen kiran sunan ta"
Daker ta iya amsawa sabo da yadda muryansa ya kashe mata jiki"
Ahakali yace sanyin nan fa har yanzun inajin shi, wanne shawara zaki sake bani?
Kasa mgn tayi dan haka ta kashe wayar, Cikin sauri ta mikawa usman, saidai kafin wayar taje hannunsa Jamal ya sake kira"
Janye hanunsa yayi dan haka ta maida wayar kunnenta"
Husna meyasa zaki kashemin waya?, ko kina kunyar usman ne? Idan kunyarsa kikeji tashi ki koma daki"
Kallon inda usman yake tayi ganin tayi hamkalin shi nakan wayar da take hannusa, dan haka tacewa Jamal a'a
Toh kina jina nacemiki sanyi na damuna, da daddare bana iya bacci sosai sai naji gadon yamin fadi, wani lokacin saina rungumi filo nakejin dadi"
Sai yanzun ta fqra dago inda yasa gaba, shiru tamai dan batasan mezatace ba"
Husna ya kikayi shiru?, wlh na kosa na dawo, Husna anya kuwa bazan ajiye aikin nan ba"
Shiru yaji dan haka yasashi fadin Husna kinajina kuwa"
Ummm ta fada tare da kallon yaya usman"
Jamal ne yace meye ummm?, to shikenan tunda bazaki min mgn ba sai an jima, amman ki shirya idan na dawo akirjin Ki zan rinka kwana"
Cikin sauri ta kashe wayar domi mgnr Jamal ta girmi kunnuwanta, wai meyasa maza basu da kunya?
Da misalin karfe 4:34pm usman yayi sallama fitowa yayi nafisa da asmau nabinshi abaya rike da kayan da momy ta hada akaiwa mama"
Daidai lokacin Deeni ya fito ya wuce su ma'u ya angaje Usman"
Saura kadan usman yakai kasa cikin zafin nama ya jawo wuyan rigar deeni tare da shake shi da ita"
Kallon shi yayi sai ya ga kamar ya taba ganin wanna fuskan amman ya rasa ina ya santa"
Cikin fada usman yace waye kai?
Wata irin dariya deeni yayi , nafisa ce ta ruga cikin gida ta kira momy, itako ma'u tuni cikinta ya burga"
Cikin wata irin murya deeni yace sakarni"
Daidai lokaci Momy ta fito aguje deeni tarike tare da fadin haba shamsundeen menene haka?, sirikin ka ne fah yayan matar jamal y kawo mana ziyara"
Tsaki yaja sannan ya fincike rigarshi ya fita"
Hakuri momy ta bawa usman cikin bacin rai yabar gidan"
Har yayi nisa atafiya ya tsaya ya fara neman no Jamal domin yaji wanne dan rainin hakali ne agidan su"
Ya dade yana gwada duk layikan shi amman duk akulle suke, haka ya hakura"
Tundaga ranan deeni ya daina ko kallon inda ma'u take, amman kullum fuskan shi murtuk"
Wani lokacin d'aki yake shiga yaci kukan shi ya kushi domin zuciyar shi na gayamai Asma'u amanar shi zataci"
Akwai wani abu da ya kudura aranshi dan haka yabarta ta gama haukanta"
Dama kawai yake nema domin ya nunawa asma'u ba'a hada soyayyan shi data kowa"
Ganin yadda deeni keyi ya fara tsorata ma'u ayanzun babu wadda take son gani banda yaya jamal, dan haka ta yanke shawaran kiranshi ta gayamai, ko zata samu saukin halin da take ciki"
Tun safe take neman no Jamal har dare bata shiga ba"
Tsayon sati biyu kenan kulum saita neme no Jamal Amman bata samun shi kullum dakin Momy take kwana bata iya sakewa acikin gidan gada daya atakure take"
Ranan da Jamal yacika wata biyu da tafiya , abun ya fara damun ma'u tun daga ranan da yaya usman yazo bata kara samun no Jamal ba, dan haka yau ta yanke shawaran samun momy da zancen"
Afalo ta same momy ta rafka uban ta gumi gefen idonta hawaye ne kwance"
Zama ma'u tayi jikinta asanyaye tare da fadin momy lfy kuwa?
Zabura momy tayi domin ita batasan da shigowar ma'u ba nan danan ta kakaro murmushi tare da fadin lfy lau asma'u"
Shiru tayi zuwa can, tace momy kulum na kira wayar yaya Jamal bana samun sa"
Adaburce momy tace wata kila network ne amman ni kullum muna waya, akwai abinda kike sone?
Girgiza kai tayi tare da fadin nagadai kwana biyu be kira bane"
Gefe ta koma ta takure gsky tanaso jin muryan Jamal sannan ta gayamai deeni nacikin gidan su" tasan kome yake har yaji deeni na gidan nan zai bari ya dawo"
Tanacikin wannan tunanin wayarta tayi kara, no usman ta gani cikin sauri ta dauka"
Tana dauka taji usman na fadin Asma'u Jamal ya canja no ne?, wadda nake dashi yafi wata akashe"
Take taji gabanta ya yaken ya fadi kafafuwanta rawa kawai su, muryanta na rawa tace"
Yaya nima rabon da muyi waya tun randa kazo"
Me ?, Taji ya fada atsorace, tare da kashe wayarsa"
Hakanan taji hawaya na zubo mata, anya kuwa lfy amman momy tace yana kiranta, shiru tayi zuwa can tace"
To meyasa naga momy na share hawaye kai Jamal babu lfy"
Mikewa tayi ta shiga cikin dakin momy, agado ta sameta tana zaune sai share hawaye take idonta jawor"
Ji tayi kafafuwanta sun kasa daukanta zamewa tayi tai zaman dirshan akasa daidai lokacin nafisa ta shigo itama idonta jawur, dan haka ma'u ta fashe da kuka"
Daga momy har nafisa kan ma'u sukayo tare da kokarin boye hawayen su"
Cikin kuka tace momy ku gayamin abin da yake faruwa ku cireni aduhu, ina yaya Jamal yake ? Idan wani abu ne ya sameshi agayamin "
Jawota momy tayi ta rungume sannan tace, Jamal na nan lfy lau....
Umm umm momy ba lfyrsa lau ba wayar sa tafi wata bata aiki"
Waye ya gaya miki, ki kwantar da hankalin ki, yanzun inda suke ne babu daman waya, kuma ai wata 7 yace zaiyi dukka fa wata 2 kenan da tafiyar sa memene abin damuwa?
Daidai lokacin daddy ta alhaji bashir suka shigo ko wanne hankalin shi atashe"
Ganin momy rungume da ma'u daddy yace yaya aka yi?
Yake momy tayi sannan tace tafara damuwa darashin kiran mijinta ne"
Shima yake yayi sannan yace ai yanan lfy, Meye abun damuwa, juyawa sukayi suka fita cikin sauri momy ta zame ma'u tabi bayan su"
Ma'u naganin fitan momy ta bude jajayen idonta ta kalli nafisa sannan ta riketa katam tace"
Hardake ake boyemin ko?, dan Allah ki gayamin gsky menene ya same shi?
Bakomai nafisa ta fada tana kallon cikin wayarta"
Cikin kuka ma'u tace shikenan amman nasan ba gaskiya kuka fada ba, bayan naga momy tana kuka kema kina kuka.....
Wayarta ce tayi kara tana kallah taga yaya usman cikin sauri ta dauka"
Ba momy wayar abinda yaya usman yace kenan, cikin sanyin jiki ta nufi hayar falon kamar me koyon tafiya
Heart Beat
*Mmn Yazeed*
[24/01, 11:04 a.m.] βͺ+234 906 689 6652β¬: ππππ
β*BUGUN ZUCIYA*β
( βHeartbeatβ)
πππ
π
πππ
βByβ
π
ββ*Fadeela Lamido*
*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATIONπ€*
β
7β£8β£to8β£0β£
πππ Tun kafin ta karasa takejin muryoyin su daddy, amman suna ganinta sukai shiru"
Cikinta babu kwari ta mikawa momy tare da cewa yaya usman zaiyi mgn dake"
Bayan momy ta amsa wayar ma'u gefe ta tsaya kirjinta na dakan uku uku"
Da ido taga daddy ya kalli momy cikin sauri ta mike ta shiga part din daddy"
Bayan momy tabi da kallo sannan sannan ta juya ta kalli daddy idonta kwalkwal kamar zatai kuka"
Daddy yi yayi kamar be ganta ba, ta dadde tsaye momy bata fito ba dan haka ta juya ta koma daki"
Nafisa na zaune ta tallabe kumatunta da duk hannuwanta biyu, ga wayarta agefe tanata tsuwa"
Karasa tayi ta dauki wayar ta mika mata tare da fadin idan kin gama tunanin ana kiranki awaya"
Azabure nafisa ta dauki wayar, harara ma'u ta bita dashi sannan ta koma gefe tayi tagumi"
Tundaga ranar gidan ya zama kowa babu walwala, bama kamar momy da take wuni dakin daddy, tsakanin nafisa da ma'u ko zaman jigun suke"
Usman be sake kiran ma'u ba amman tana yawan jin suna waya da momy"
Ahaka har aka kwashe wata hudu da tafiyan Jamal"
Zuwa wannan lokacin hakali Momy yafi na barawo tashi, harta fara tunani danme za'a boyewa ma'u daddy ne me karfin halin cewa kar agaya mata bari insha Allahu zai dawo"
Deeni ko besan biken da ake ba duk da cewa yanzun yana yawan ganin babanshi na zuwa gidan amma besan meke kawoshi ba"
Burin shi be wuce yaga samu damar da yake jira ba, yasan daga ranan da yasamu damar shikenan ma'u ta zama mallakin sa, Dan haka ya barta ta gama guje gujenta, ko Jamal dawowa yayi baxai hanashi abin da yayi niyya ba"
Duk da dabi'un shi sun fara canzawa amman sonta na nan makale azuciyan shi, kuma yasa ma'u ma tana kyaunar sa so take kawai ta tursasa kanta wajen yiwa mahaifinta biyayya, amma bawai son Jamal take ba"
Itako ma'u abin duniya ya isheta, tarasa dalilin damuwan ta
Hakanan takejin ta kosa tasan wani hali Jamal ke ciki, tare da tsananin son ganin sa, meyasa nakejin haka ?ma'u ta tambayi kanta, meyasa na damu da rashin jinsa?, haka na nufin inason Jamal kenan?
Girgiza kai tayi tare da fadin ba sonshi nakeba, jimamin sa kawai nake amatsayin sa na dan uwa musulmi kuma aminin yaya usman"
Amman meyasa yanzun nabar tunanin deeni, ko haduwa dashi bana fata, ayanzun Jamal kawai idona keson gani"
Tana cikin wannan halin taji hayaniyan mutane afalon cikin sauri ta fito"
Wata dattijuwar mata ce tare da wata yariya budurwa zatakai sa'ar nafisa, daidai lokacin data shigo falon taji matar na fadin Allah ya bayyana shi"
Runtse idonta tayi tare da fadin nashiga uku"
Ganin inda ma'u ta runtse ido yasa momy ta washe fuska tare da fadin"
Wannan itace Asma'u matar Jamal tunda akayi biki baku haduba shikuma be kawo miki itaba"
Wani irin kallo matar tawa ma'u, muryan momy taji tana fadin asma'u wannan itace abokiyar zamana, sannan ta sake nuna budurwan dake kusa da ita tace wannan kuma kanwar Jamal ce"
Hakanan ma'u taji kwata kwata basu mata ba, tunda tazo gidan bata taba ganin suba saiyau"
Gefe ta nufi zama cikin sauri momy ta mike ta jata daki, dan batason ta fahimci halin da ake ciki"
Kallon momy kawai take amman tasan dole akwai abin da ya faru, ta kula ita kadai ne abason ta sani, hawaye ne suka zubo mata tasa hannunta ta share sannan ta kalli hawayenta dake hannunta tace"
Sai yaushe zan daina kuka? Sai yashe hankali na zai kwanta?
Wata zuciyar ce tace sai ranan da Jamal ya dawo, idan kuma mutuwa yayi fah?
Cikin sauri ta girgirza kai tare da fashewa da kuka, tana kukan take fadin Allah karka nufeni da ganin wannan ranan, inason nasake ganin Jamal a idona, inason nasakejin muryan sa tare da kamshin turaren sa"
Daidai momy tayi ma hajiya asabe rakiya tana shigowa taji sautin kukan Asma'u"
Aguje ta karasa ta kalli asma'u tare da fadin meye kuma?
Cikin kuka tace momy idan wani abu ya sameshi ne ki gayamin dan Allah"
Shiru momy tayi na wani lokaci zuwa can tace"
Kinga ki kwantar da hankalin ki idan Allah ya yarda lfy kyalau zai dawo"
Kallon Momy kawai tayi acikin zuciyarta tunani kala2"
Cikin dare kwata kwata ta kasa bacci burinta kawai tasan wani hali yake ciki, tashi tayi ta zauna, sai lokacin ta kula momy ma bata dakin, mikewa tayi ta nufi falo, wannan lokacin babu tsoro ko fargaba azuciyanta"
Momy tagani ita da nafisa sai sallah suke, cikin sauri ta juya daki agogo takallah karfe 2:08am, jitayi bazata iya hakuri ba dole ta kira yaya usman adaren nan wata kila bazai boye mata ba"
Tana dannan no aka dauka kamar daman jira ake Asma'u? Taji yaya usman ya fada"
Cikin dakushshayar muyar ta amsa"
Shiru yayi kaman ruwa yacishi, zuwa can yace Asma'u me kikeyi har yanzun bakiyi bacci ba?
Kuka ne ya kubuce mata cikin kukan tace bakomai"
Shiru ya sakeyi sarai ya gane kuka take dan haka ya rasa mezaice mata"
Itama rasa ta ina zata fara tayi, zuwa can yaya usman yace"
Duba asma'u ki kwanta kiyi bacci da safe zan kiraki"
Haka ta hakura badan ranta yasoba, alwala taje tayi sannan tazo ta tada sallah, tanayi kwalla nasauka idonta"
Har aka kira sallahn asuba tana azaune bayan ta ida sallah tasake kiran no yaya usman, tare da alwashin zata cire kunya ta tambaye shi Jamal"
Yana dauka yace Asma'u kinyi bacci kuwa?
Rasa abincewa tayi tare da rikecewa"
Shiru na wani lokaci sannan yaya usman yace"
Menene ke damunki ?
Tsintan kanta tayi da fadin babu komai inason ne nayi mgn da anty fa'iza"
Toh ina zuwa, ya fada sannan ya kashe wayar"
Ba adaukin lokaci ba kiran yaya ya shigo cikin sauri ta dauka"
Gaisawa sukayi a gajarce sannan ma'u ta fara kuka"
Shiru fa,iza tayi tana sauraranta domin kota bude baki batasan me zatace ba"
Zuwa can ma'u ta tsagaita da kukan sanan tace"
Anty fa'iza meye nufin ku na boyemin halin da ake ciki, sabo dame za'a boye min, idan wani abu ne ya sameshi ku gayamin, kara tsananta kukanta yayi amman a haka tace anty ko ya mutu ne?
Muryan usman taji yana fadin"
Ke, be mutuba yanan da ransa, menene kikeyi haka? tun dare kike faman koke koke, Ku daman mata haka Kuke duk kubi ku dama mutum lissafi, yanzun ki bari yau zanshigo Abuja"
Babu laifi ta dan samu natsuwa, saidai yau ta lura gidan yafi kullum rikecewa dan yau ko abun kare ba'adaura ba domin babu masuci"
Da misalin karfe 2 Usman ya iso"
Asma'u na zaune idonta duk sun kode sunyi suntum nafisa ta shigo tace tazo daddy na kira"
Afalon ta same yaya usman da alhaji bashir, momy ma na zaune agefe"
Karasawa tayi ta zauna akasa, acikin dashshiyar muryanta ta gaida su"
Fuskan daddy atunkushe ya kira sunanta, sannan yaci gaba dacewa"
Akwai abun da banso ki sani ba, Amman ba yadda zanyi, ya zama dole kisani, domin abun ya wuce tunanina, tunda jamal ya tafi yau wata uku kenan babu lbr, tun bayan ta fiyanshi da wata daya be sake kiran kowaba kuma ko ankira ba'a samunshi"
Wannan dalili yasa muka fara tsorata kuma tundaga lokaci muke zuwa ofishin su, saidai suma Kansu basu da wani lbr akansu, kullum hakuri suke bamu, tare da nuna mana sunakan meman inda suke ne, amman yanzun mun yanke shawara Usman da shamsudeen zasubi bayan sa"
Tukafin daddy ya karasa ma'u ta fashe da kuka, sai yanzo ne takeji son Jamal me tsanani azuciyarta, fuskan shi ta hango a idonta tare da dogon hancin sa, baya murmushi amman duk sanda yayi abin sha'wa ne, cikin kuka tare da jan majina tace daddy zan bisu"
Kafin daddy yayi mgn deeni ya shigo cikin shirin tafiya tare da wata jaka rataye abayan sa....
Heart Beat
*Mmn Yazeed*
[24/01, 11:04 a.m.] βͺ+234 906 689 6652β¬: ππππ
β*BUGUN ZUCIYA*β
( βHeartbeatβ)
πππ