Showing 6001 words to 9000 words out of 95354 words

Chapter 3 - BUGUN ZUCIYA Hausa Novels Complete by Fadila Lamido.txt

29 Oct 2025

480

shi ake mata, saidai abu daya abban su baya barin yawo indai ba gidan dada tace zataba ba a barinta zuwa ko ina, dan haka lokacin da ta kare secondary ta samu daman tafiya jami'a ta balle bishashanta acan, ahankali fiddausi ta zama bata da abokai sai maza, haka zaka ganta tsakiyar maza ita kadai mace"

Babu wadda keda lbrn halin da fiddausi take ciki amakaranta, dan da antashi gida take yowa dan tasan ko minti 10 takara sai ance inata tsaya"

Ana haka maza suka fara canzawa fiddausi tunani domin ko duk abokanta kusan su 7 babu wadda baya lalubeta da sunan wasa, dan haka ta farajin babu abin da take so illah taga ta kadai ce da namiji"

Duk abinda suke sauran dalubai na kula dasu, yayin da wasu daga cikin matan suke tur da halin fiddausi, ita kenan yau ka ganta manne jikin wancen gobe jikin waccen"

Yauma kamar kullum tana cikin motar wani abokinta KB suna manne da juna ita da kanta ta lalubo bakin shi ta cusa nata ta, saida suka gama shagala, sanna ta gabatar mai da kudurinta"

Murmushi KB yayi dan yasan za'ai haka, yayi mamaki ma da har aka kawo yanzun bata bada kai ba, sabo da salon da suke mata"


Kwantar dakai KB yayi tare da fadin babu damuwa, amman fa saidai kizo muje Ki tayani kwana"

Zaro ido tayi dan tasan zancen shi bamai yuwuwa bane, tace KB ? Kana son Abbana ya kasheni ne?

Tsaki yaja sannan yace haba meyasa kike abu kamar wadda bata waye ba, ai dibara zaki masa"

Bayan kwana 2 fiddausi ta kasa hakuri dan haka ta shirya tayi sallama akan zata gidan dada ta kwana"

Gidansu KB ta wuce wadda har ya kaita da kwana adakin kb kuma har komai ya kasan ce, karfe 7:09am ta isa gidan dada da kayanta ajaka kamar yadda ta shiryu, ganin inda take tattale kafa yasa dada fadin ke lfy meya sameki kike wani tafiya saikace agwagwa"

Akafa fah na taho dada wlh gajiya nayi"

Ruwan wankan dada ta juye tayi wanka tare da gasa jikinta, ko karyawa bata tsaya yi ba, ta haye gado sai bacci domin KB be bari ta runtsa ba"

Damisalin karfe 8 alhaji sani ya iso gidan ganin fiddausi agado hankalin shi ya kwanta"

Tun daga ranan wannan dabi'a ta zaman mata jiki har saida ya kasance gaba dayan su 7 sun gama sanin wacece fiddausi"

Ankwashi tsayon watanni ana haka kullum fiddausi tana hanya wata rana takan kwana gidan dada amman sauda yawa dakin samarinta take wucewa idan ko har ta kwana gidan dada toh safiya nayi zata wuce gurin samarinta, babu wadda ya lura da halin da fiddausi take ciki har saida fiddausi ta fara rashin lfy, ana zuwa asibiti gwajin farko aka shaida musu tana dauke da ciki Wata 2"

Mummunan tashin hankali suka shiga ba kadan ba, wadda da takai har abba ya kwanta asibiti saka mukon hawan jini daya kamashi,

Duk abinda ake usman bashi da lbr dan lokacin yana mkrnt yana kokarin karasa karatun shi na soja"

Bayan abba ya samu sauki ne suka zauna da yayan shi alhaji musa tare da sanya fiddausi agaba ta fada musu wadda ya mata ciki"

Tashin hankali ba'a sa maka rana nan idon fiddausi ya raina fata damin kuwa acikin abokanta guda 7 babu wadda baya kusanta ta dan haka batasan sunan Wa zata kira ba








Heartbeat
Mmn YazeedπŸβ€‹
[24/01, 11:03 a.m.] β€ͺ+234 906 689 6652‬: πŸ’—πŸ’πŸ’πŸ’—
​*BUGUN ZUCIYA*​
( ​Heartbeat​)

πŸ’“πŸ’πŸ’—
πŸ’—

πŸ’“πŸ’πŸ’—
​By​
πŸ’—
​​*Fadeela Lamido*



πŸ”Ÿ to 1⃣1⃣




πŸ““ Nadama ce me tsanani ta shigeta cikin kuka ta furta KB, koda alhaji musa yasa aka binciko masa KB nunawa yayi ai bashi kadai ke nemanta ba dan ko satin daya wuce a dakin abokin sa ballo ta kwana, dan haka babu wadda ya isa yace ciki nasa ne"

*Bugawa* zuciyar abba tayi jin yarshi tana kwana dakin maza, duk irin tsaron da yake bata, hawaye masu dumi suka fara zubo masa"


Ganin inda abba ke zubar da hawaye hankalin fiddausi yayi mummunan tashi, acin kuka tace abba dan Allah kayi hakuri ka yafemin"

Mikewa KB yayi yana fadin ni kar a kara kirana akan wannan xancen danni tun farko ita ta nemeni gatanan ku tambayeta cewa tayi intaima keta"

Fashewa abba yayi da kuka kaman karamin yaro, alhaji musa ne yace bazaibar xancen ba, yan sanda yasa suka kama KB, cikin bin ciken su suka kama mutun 7 da fiddausi take kwana dakin su"

Lokacin da abba yaga tika2 maxan da fiddausi ke kwana agurin su abin ya bashi tsoro kuma gashi kamar hadin baki dan kowanne cikin su cewa yake ita tace ya taimaketa"

Nan take abba ya fara aman jini, asibiti aka nufa dashi kai tsaye, satin shi 2 asibiti ya fara samun sauki"

Aban garen fidausi kuwa tunda tasamu lbr rashi lfyn abba kulum cikin kuka take, figewa tayi ta lalace gawani uban baki da tayi"

Kwata2 mama bata mata mgn , ko gaidata ma da takeyi cewa tayi idan ta Kara mata mgn Allah ya isa"

Rayuwa tayiwa fiddausi zafi haka zataita kwara amai mama naji amman ko kallota batayi adaki take zama tace kukunta takoshi, hakika fiddausi tasan ita ta basu KB dama amman ai su sukasa hartakai wannan matakin saboda irin wassannin da suke mata, kuka taci sosai tundaga ranan ta kama rashin lfy"

Satin ta daya adaki bata ko iya tashi, goggo tani ce tashiga dakin dan taji shirun fiddausi yayi yawa, samunta tayi duk ta rame ta tsutse gashinta baje akan gado bakinta ya bushi yayi wani bawo2"

Furgita sosai goggo tayi tana xare ido tace ke kina cin abinci kuwa?

Ruwa ruwa kawai fiddausi take fadi"

Tashin hankali sosai abba ya shiga lokacin da dada takai mai lbr"
Hakika yana matukar son firdausi saidai wannan Abu data aikata yana sosa masa zuciya"


Firdausi naganin abba ta fara rokonshi da girman Allah ya yafe mata tari ne ya kwace mata, babu kyaukyautawa dan haka hankalin kowa ya koma kanta"

Zuwa can jini ne ya fara fita ta baki ta hanci, cikin rudu abba ya wuce ya tallabeta tare da fadin firdausi na yafe miki, kuma zanci gaba da addu'a duk wadda ya lalata miki rayuwa uban giji Allah ya saka mike"

Murmushi tayi kadan sannan ta jawo hannun mama ta rike acikin nata, ta karyan da kai alaman roko"

Mama ta fahimce ta, itama karya kai tayi hawaye na sauka afuskanta tace na yafe miki duniya da lahira"

Murmushi tayi sannan ta daga hannu tanawa su dada bye byeβœ‹πŸ»"

Abba ne yace ya kamata mutafi asibiti dan naga jikin ya matsa mata"

Murmushi firdausi tayi tare da girgiza kai tana mutsa baki"

Ahaka abba da alhaji musa suka dauketa suka nufi asibiti, banda murmushi babu abin da take"


Emergency aka shiga da ita, yayin dasu abba sukai cirko2, zuwa can likintan ya fito yana share zufa tare da fadin alhaji saidai kui hakuri dan *zuciyar* yariyar yariga ya *buga*"

Mekake nufi? abba ya tambaya yana me kallon cikin idon likitan"

Cikin sanyin jiki yace ta rasu"

Innalillahi wa inna ilaihir raju,un shine abin da kuwa yake cewa agurin"

Lokacin da abba ya tsaya akan gawan Fardausi, Hawaye ne sosai yake fita a idon shi kanta ya dafa yace Allah yajikan ki Allah yasa mutuwa ta xame muki hutu, kukane yaci karfin sa dan haka alhaji Musa ya kamashi yayi waje dashi"


Bayan ankwai Firdausi gidanta nagaskiya ne alhaji musa ya tura adauko usman"

Bayan isowan usman ya shiga munmunan tashin hankali, kuma yaci alwashin daukan fansa agun su KB"

Abba cewa yayi babu wani fansa daza,a dauka duniya ce wadda bezoba ma jiransa take dan haka abar ma Allah"

usman ya koma makaranta bayan sadakar 7 mama da Abba kuwa sunfi shekara 1 suna cikin jimamin Abba yau ciwo gobe lfy"

Wannan dalilin yasa abba ke matukar sawa ma,u ido tare dayin kaffa2 da ita"

Ayanxun usman ya gama karatun shi ya zama cikken soja kuma yayi aure shekara 1 data wuce

itako ma'u awannan watan ta kare secondary dan haka yanzun islamiya kawai take zuwa"



*CIGABAN LABARI*


Dakin baccin mama ta nufa aguje tana fadin mama dan Allah karki bari yaya usman ya dakeni wlh dada ce ta aikeni.....

Fita kiban guri cewa mama dake nunawa ma'u hanya"

Kuka ta fara tana rokon mama tsayowar mota taji dan haka ta ruga dakinta"

Usman ne ya shigo falon tare da matarsa Fa'iza, bayan ta gaida abba ta fita ta basu guri"

Abba ne ya kwashe duk abin da ya sani ya fada ma usman, shiru yayi zuwa can ya mike yace abba bari naganta"

Kofar dakin ya tura ya shiga, ma'u na tsugune agefen gado idon nan zuro2"

Zama yayi agefen gado sannan yace ke zonan"

Bata iya mikewa ba da rarrafe ta matso, jikinta sai kerma yake"

Ina kikaje?


Toshe bakinta tayi da hannunta hawaye na zobowa afuskanta tace"

Yaya narantse dada ce ta aikeni, kuma ka tambayeta ka......

Wani uban tsawa usaman ya buga mata wadda yai matukar razanata, sannan yace"

Wasa nake dake?, zaki gayamin inda kikaje kosaina karya ki tukuna?

Mikewa tayi arude tana fadin yaya dan Allah karka karyani wlh dada ce ta aikeni "

Mikewa taga usman yayi yana nan nade hannun rigar sa, uhu ta bara lokacin da taga yana kokarin kwance ma dauri wandon sa"

Batai aune ba ta farajin saukan duka, yana dukanta ne yana gara tambayanta inda taje amman har yamzun mgn daya take maimai tawa dada ce ta aiketa, dan haka usman be dena dukanta ba har saida yaga ta kasa tashi, ihunta ma ya daina fita sannan ya tsagaita"

Bakin gadon ya koma ya zauna sannan yace kince dada ce ta aike ki dan haka inason ki gayamin inda ta aike ki"

Tsintan kanta tayi tana fadin carbin ta ne ya tsinke tace nakai mata gyara"

Carbi? Jitayi yasake hada mata mari akumatunta duka guda biyu, bata kara sanin inda take ba"

Zuwa can ta bude ido taga matar yaya usman zaune agefenta tana mata fifita"

Muryanta adashe tace anty Fa'iza kina gidan nan kikabar yaya yana neman kashe ni?

Rufe mata baki tayi idonta cike da kwallah tare da fadin Asmau naso na shigo mama ce ta hanani"

Kuka ma,u taitayi Anty Fa'iza na lallashinta"

Washegari da safe ma,u ta tashi jikinta ya mata tsami ga fuskanta duk ya kunbura, jin muryan dada afalo yasata farin ciki , tashi tayi tana takawa ahankali ta fito falo"

Salati dada tasa lokacin da idonta ya sauka afuskan asmau sannan ta juya ta kalli abba tace"

Au yanzun nan saida ka duki yariyar nan?, aida kasani ka hada haddani tunda nice babban me laifi, amma ba komai Allah ya baka hakuri, juyawa tayi zata fita ranta bace"

Hakuri abba yaita bawa dada, daker ta yadda ta dawo, rike asmau tayi suka shige daki, bayan sun zauna ne dada ta kalli asmau cikin tohuma tace"

Toh asmau mgn nazo muyi me mahimmanci, kuma inason kisa aranki wannan mgn tsakanin ni dake ne babu mejinta"

Gyada kai ma,u tayi tana share ragowan hawayen dake fuskanta"

Asmau menene tsakanin ki da wannan ibbilishin yaro?

Shiru tayi tana kallon kafar ta, tare da zubo da wasu sabbin hawaye"

Takwara badake nake mgn ba?

Cikin kuka tace dada ni wlh babu komai tsakanina dashi ahankali takwashe duk yadda akayi ta gaya mata"

Shiru dada tayi tana mamakin hali irin na asmau, ace yariya ba'abin da tasa agaba sai tsokana, zuwacan ta kalli ma,u sannan tace"

Karki kara irin wannan rashin hankalin, ban da kuruciya me ya dameki dashi? Mutumin da manya ma gudunshi suke, shine ke zakina shige mishi?, kinatsu sosai kisan me kike keba karamar yariya bace, koko so kike kisa ubanki atashin hankali?

Girgiza kai tayi sannan tace aina bari bazan sake kulashi ba kuma dan Allah idan yaya usman ya tambaye kice kika aikeni"

Hmmm takwara kenan, naji kuma zan fada amman saikin min alkawarin baxaki sake kula wannan shaidanin yaron ba"

Har cikin zuciyarta batajin dadin sunan da Dada take kiran deeni, dan haka saida ta runtse ido sannan tace, nayi alkawari"

Bayan kwana biyu jikin ma,u yayi sauki saidai har yanzun akwai shaidan duka ajikinta kuma fuskanta be gama sabewa ba"

Shiryawa tayi cikin kayan mkrnt sannan tayiwa mama sallama ta wuce"

Wata zuciyar ce tace kibi ta gurin mana ko hangoshi ne kyayi daga nesa, a'a nayiwa dada alkawari ta fada afili, koda takai daidai lungun fasa bi tayi dan jitake idan bata gansa ba kaman wani abu zai faru"

Tunkafin ta isa gurin ta hangoshi sai waige2 yake kamar dai yana neman wani, zuwa can ya juyo da kallon sa, gurinta, wani munafukin murmushi ya sake sannan ya fara tahowa"

Kaucewa ma,u take, tare da kara sauri, amman duna sai dad'a binta yake"

Ganin haka ma,u tasa kuka, tare da tsayawa cak"

Wani irin kallo yake mata, tare dason kallon kwayar idonta, zuwa can ya mika hannun sa ya shafi kuma tunta shedan yatsu ya gani kwance"

Nan danan idonshi ya rikice ya kuma jawur, sannan ya karkata kai yace"

Shedan hannun waye afuskan ki?? uban waye ya dake ki??

Jikin asma'u banda kerma ba abin da yake, agigice ta kauce tana kokarin guduwa"

Damkanta yayi tare da fadin ina wasa dake ne? Ashe yau unguwar nan babu zaman lfy indai baki fadamin wadda ya bata miki fuska ba ton wlh duk wadda nagani sara ne"

Rudewa asma'u tayi cikin kuka tace a'a wlh yaya nane"

Yayan ki?, toh wlh sainaci uwassa, zai shaida cewa bakin rijiya bawajen wasan makaho bane, yasin saina canza mai halitta



Hannu ya zura aljihu ya dauko wata karamar waya ya danna sannan ya kara akunnen shi, zuwa can taji yana fadin *Shazali* ka hadu min karnukan nan ka kawo su yanzun nan, kacewa *Caka* ya tahomin da *Duna* yau akwai aiki idan ba ayi wasa ba saina mai yankan rago



Heart Bear
*Mmn Yaxeed*πŸβ€‹
[24/01, 11:03 a.m.] β€ͺ+234 906 689 6652‬: πŸ’—πŸ’πŸ’πŸ’—
​*BUGUN ZUCIYA*​
( ​Heartbeat​)

πŸ’“πŸ’πŸ’—
πŸ’—

πŸ’“πŸ’πŸ’—
​By​
πŸ’—
​​*Fadeela Lamido*



*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATION🀝*



1⃣2⃣ to 1⃣4⃣





πŸ“– Hannu asmau ta daura akai πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ domin kalaman deeni sun tsuratata tsugunawa tayi sannan tace dan Allah kayi hakuri karka masa komai yaya na ne, kuma abba nane yasa shi ya dake....

Bata kaiga karasawa ba taji andauketa cak ana tafiya da ita"

Wuntsula kafa take tare da kara me tsanani"

Tana kallo ya shiga da ita wani gida wadda kusan shine gida na marusu karfi agunwar"

Wata dattijuwar mata ce ta fito aguje tare da fadin auta yau lfyr ka kuwa?

Bece komai ba kokarin shegewa dakinsa da ma'u kawai yake, ganin haka mahaifiyar tashi ta sake shan gaban shi tare da cikuikuye hijjabin ma'u tace haba auta bansan ka da wannan dabi'a ba, ka dubeta dakyau mana islamiyya zata, idan ma wani abu ta maka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login