Showing 66001 words to 69000 words out of 95354 words

Chapter 23 - BUGUN ZUCIYA Hausa Novels Complete by Fadila Lamido.txt

29 Oct 2025

488

πŸ’—

πŸ’“πŸ’πŸ’—
​By​
πŸ’—
​​*Fadeela Lamido*




*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATION🀝*
​


8⃣1⃣to8⃣3⃣





Wani kallo deeni ya watsa mata sannan ya dauke kanshi"


Cikin tausayawa daddy ya kalli ma'u sannan yace,....

Ki kwantar da hankalin ki asma'u ke macece babu abin da zaki iya illa ki kara musu aiki"

Zaman ki agida shi yafi ki zauna kiyiwa mijin ki addu'a"

Kuka ta kara fashewa dashi, Usman ne yacire tagumin sa yace....


Ke karki kawo mana hauka, yaza tasa mutane agaba keta mana kuka, meye amfanin kukan?


Tsagaitawa tayi da kukan tare da to she bakinta"

Ciga usman yayi da fada har sai da daddy yace ya isa haka usman ka mata ahankali, kasan mata da miji sai Allah

Wani haushi ne ya sake kama deeni, cikin shi yaji yayi sanyi aranshi yace wannan kukan da asma'u keyi na meye, anya ba babu soyayyar Jamal azuciyarta, dan yaga ko kallon inda yake batayi"

Ji yayi kamar yace bazashi ba ya zauna yaga iya gudun ruwanta amman bazai iya ba soboda ayanzun yana Ganin Momy ne tamkar ummin Sa dan haka bazai zauna ba agidaba bayan yana Ganin hankalin ta atashe"

Shiko usma sosai asma'u take bashi mamaki wai ita da take ikirarin zata kashe jamal saigata wujuga wujuga tana kukan rashin sa, kara kallonta yayi yaga idonta duk sun kunbura"

Juyawa Usman yayi ya kalli daddy yace"

Daddy ni zan wuce basai natafi da wani ba, nikadai ma zan iya"

A'a usman zanfi son ku tafi ku biyu zaifi"

Ba yadda usman ya iya dole tasa zai tafi da deeni badan ransa yaso ba"

Koda suka mike suna sallama ma'u kuka kawai take"

Bayan fitan su momy taita lallashim ma'u, tare da nuna mata ta rage damuwa karya jawo mata ciyo"

Bayan tafiyan su da kwana biyu usman yayiwa daddy waya amman batasan abinda suka tattauna ba, dan haka da daddare tacewa momy abata no da yaya usman ya kira dashi"

Momy bata mata musuba dakanta tasa mata no din"

Acikin daren ma'u takira no saidai usman naji muryanta ya kashe"


Washegari duk suna zaune afalo, kowa babu bakin mgn, zuwa wannan lokacin kuka ya daina zuwa ma'u saidai kunan zuciya wani irin zafi takeji akirjinta ji take kamar tayi tsuntsu ta ganta agaban Jamal, idan ma mutuwan ne ta daukesu tare"


Mikewa tayi ta fita daga falon"

Momy da nafisa ne suka bita da kallo"

Ankwashi kusan minti 15 ma'u bata dawoba dan haka Momy ta kalli kofar tace"

Nafisa dobumin Asma'u kigani waje ta zauna?

Dasauri nafisa ta fita zuwa can ta dawo tace momy bafata waje"

Bata waje ? Amman nan naga tayi, kota dawo ne ta wuce ne bamu kulaba, duba ciki"

Dawowa nafisa tayi tace momy saidai ko toilet ta Shiga amman bata daki"

Zama sukayi suna jiran fitowanta, har aka kwashe minti 30 dan haka momy ta mike gaba daya part din saida ta duba toilet din amman babu ma'u dan haka ta fito afirgice tana fadin nafisa asma'u fa bata gidan nan"

Gaba dayan su waje suka nufu, suna isa gurin me gadin suka hada baki wajen fadi"

Asma'u ta fita ne?

Gargiza kai megadin yayi tare da aje radion shi agefe sannan yace tun fitan Alhaji nake zaune gurin nan banga fitan kowa ba"

Shiru momy tayi zuwa can tace anya baba kodai bacci ya debeka ta wuce baka gantaba"

Girgiza kai yayi tare da fadin idona biyu hajiya babu wadda ya wuce"

Cikin sauri momy ta nufi part din Jamal nafisa nabinta abaya, tun kafin ta karasa tahango alamar kofar abude take"

Da saurinta tashiga cikin falan babu kowa dan haka kai tsaye ta nufi dakin ma'u, saidai abinda ya bata mamaki ma'u bata dakin, dan haka arude momy ta fito tana fadin nagaya muku asma'u bata gidan nan, har momy ta kama kofa zata fita Wata zuciyar tace baki duba dakin Jamal ba"

Cikin sauri ta juya hartana hadawa da gudu nafisa ma ba'abarta abaya ba"

Suna shiga dakin suka hango ma'u kwance akan gadon Jamal"

Bacci take idon ta duk shedan hawaye ya bushe, hannunta daya dauke da glass din Jamal yayin da dayan yake rike da jaridan Sa"


Kara matsawa momy tayi har bakin gadon ta kurawa ma'u ido, bacci take sosai, hannuwan ma'u tasake kallo take taji kwallah tacika mata ido, domin ita kanta hango Jamal tayi zaune sanye da gilashin sa, hannun shi dauke da jarida kamar yadda ya saba"

Kuka ne ya kubuce mata cikin sauri tasa hannunta ta toshe bakinta dan karta tashi ma'u

Nafisa ma kuka take tare dabin dakin da kallo"

Ahankali momy tace Allah ina rokonka dan tsarkin mulkin ka Kadawo da jamalumdeen gurin iyalan sa, muna tsananin bukatar sa"

Haka momy taita addu'oi me kama da sambatu, daga karshe ta jawowa ma'u kofar suka fita"

Sai yamma likis ma'u ta shigo, babu wadda yace mata kalla harta nemi guri ta zauna"

Zuwa can momy ta kalleta tace kinyi sallah?

Eh kawai tace sannan tasa kanta akasa"

Abinci nafisa ta dauko ta aje agaban ma'u sannan ta zauna tace muci"

Wani haushi ne ya kama ma'u dan haka tasa hannu ta ture abinci tare da fadin banci "


Momy ce ta kalle su sannan tace wanni irin bakici ina kula dake yau kusan kwana nawa? bakicin abinci, kina nufin rayuwa zata yiwo ahaka?

Kamar me shirin kuka tace momy konaci awuya yake tsayamin wlh baya wucewa"

Haka nan zaki daure Asma'u nikaina idan inacin abinci ji nake kamar inacin magani"

Momy wlh bazan iya ba yanzun ma kirjina zafi yake min ji nake kamar nufashina zai dauke"


πŸ™†πŸΌKinga?, Asma'u ki rage tunani karki jawowa kanki ciyo"


Washegari da safe ma'u taji wayarta na kara, tana dubawa taga Abba ne, duk da tana cikin wani hali saida taji farinci, dan ta dade tanason kiran Abba da mama tsoro ne yake hanata"

Cikin siriyar muryarta tayi sallama, Abba ya amsa sannan ta gaida shi"

Ya amsa babu yabo babu fallasa, nasiha ya shiga mata tare da nuna mata komai mukkadari ne daga Allah kuma babu wadda ya isa ya canja yin Allah"

Wanna mgn ta Abba ya kara tayarwa ma'u hankali saitake ganin kamar Jamal ya mutu ne, dan haka ta kara rikicewa da kuka tare da fadin abba ya mutu ne?

A'a waye yace miki ya mutu?

Toh abba naji kana min nasiha ne"

Jim, yayi zuwa can yace yanzun asma'u sai jamal ya mutune zanmiki nasiha?, toh yanzun wannan kuka da kikeyi meye amfanin sa?, kinfi iyayensa son sa ne?


ance baki cin abinci, rashin cin abincin shine zai dawo dashi?, ki natsu kimai addu'a shi yafi bukata ayanzun, kuka da rashin cin abinci bazaiyi magani ba, irin wannan nasiha daddy yaita mata harta sarara da kukan sannan yaba momy wayar, itama nasiha taita mata daga karshe sukayi sallama"

Ma'u bata daina zuwa dakin Jamal ba, kulum can take bacci rana, domin da dare bata iya bacci adakin nasa ma, wani abunsa take dauka ta rungume, bacci ne yake daukanta batare da sanin lokacin ba"


****


*Somalia*



Tunda Usman da deeni suka taho magana bata hada suba ko kallon juna basu yi"


Yau kwanan su biyo agarin, gida daya suke kwana kowa da barayin shi"

Hakanan usman yaji be yadda da deeni ba dan haka yake kulle dakin daya yake"


Shiko deeni yarasa wacce hanya zaibi dan yaga jamal dan yana son ya ganshi kafin kowa ya ganshi"


Ranan da suka cika kwana uku agarin deeni zaune wani soja ya shigo yace Oga yace ka fiti idan kashirya idan baka shirya ba xai wuce"


Tashi yayi cikin sauri domin aganin shi yafi kowa son ganin Jamal dan haka duk wulakancin da usman zai mai zai jure"


Amota daya suka tafi, wani katon waje yaga anshiga wadda yayi ma deeni kama da gidan sojoji"

Suna tsayawa Uman ya fita ya fara tafiya cikin hanzari irin naso na sojoji"

Ko ina ka kallah sojoji ne ke shawagi"

Gadan gadan usman ya nufi shiga cikin sauri sojojin dake wajen suka dakatar dashi"

Hannun Yasa yaciro idcard dinshi ya nuna musu, cikin sauri suka saramai tare da bashi hanya"

Ko waiwaye usman beyi ba ya shige, deeni ko basu barshi wucewa ba dan haka yacika kamar zai fashe











Heat beat
*Mmn Yazeed*
[24/01, 11:04 a.m.] β€ͺ+234 906 689 6652‬: πŸ’—πŸ’πŸ’πŸ’—
​*BUGUN ZUCIYA*​
( ​Heartbeat​)

πŸ’“πŸ’πŸ’—
πŸ’—

πŸ’“πŸ’πŸ’—
​By​
πŸ’—
​​*Fadeela Lamido*




*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATION🀝*
​



*SADAUKARWA GA*
*Masoya BUGUN ZUCIYA*πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ’‹πŸ’˜πŸ’˜




8⃣4⃣to8⃣6⃣




Wani guri deeni ya nufa ya zauna, abin duniya ya dameshi, yana kallon yadda sojojin ke kaiwa suna dawowa, dan zaman shi gurin ya fahimci suna girmama manyan su, koda kuwa sun wuce su ashekaru"

Dan ko usman da suka sara masa, da yawa daga ciki sun girmeshi, wani tunani ne ya fadon masa acikin rana waishi yana ina ne lokacin da wadannan yan fici ficin yaran sukai karatu?, me nakeyi agida? Har waddan da aka haifesu abayana suka zama wani abu ni ina zaune?

Yanzun gashi ina kallo akabar waccen me kama da lagwanin ya wuce, ni aka hanami, duk su ummi ne suka jamin, gaskiyan momy ne su ummi basu daurani hanya mekyau ba"

Tunawa yayi da malamin da ummi ta turo masa shima dukka bazai wuce 22 ba, amma gashi har na kiranshi malam, karatu abakin shi kamar me, shiru yayi na dan wani lokaci zuwa can yace"

Yanzun idan nace zanyi karatu ta ina zan fara?, ko secondary ban gama ba taya zan zama kaman wadancen"

Hawaye yaji yana zubomai hakika su ummi basumai adalci ba, kusan ma su suka kashemai rayuwa, ayanzun ya fahimci ilmi shine gaba yanzun gashi yana da lfy yana da karfi amman ya zama dan kallo"

Share hawaye yake yanayi yana basarwa dan kar wani ya fahimci halin da yake ciki"

Saida usman ya kwashe kusan awa biyu sannan suka fito, su da yawa ya gani, yayin da wani ya taho da gudu ya bude musu mota suka shiga"

Itakanta motar daka ganta saika tsorata domin fentinta kallar kakin su"

Yana kallo motar ta tashi yayin da wasu motocin suka rufa musu baya"

Shiko deeni yanan zaune agurin babu wadda ya sake bin ta kansa"


Misalin karfe 9:38 sanyin gurin ya fara damun sa, zucigarshi babu dadi wani irin radadin yake ji azuciyan shi, nisawa yayi, zuwa can yaji wayarsa tayi kara daddy ne"

Bayan sun gaisa ya tambayeshi halin da ake ciki"

Beji kunyan cewa babu abinda ya sani ba, kwashe duk halin da ake ciki yayi ya gayawa daddy"

Jamm, daddy yayi sanan yace toh bari nakira usman din yasa akaika masauki, idan babu dama ma kai ka dawo gida"

Basufi Monti 5 da aje wayaba wani yazo yacewa deeni ya taso yakaisa gida"

Tunda ga ranan be sake Saka usman a idonshi ba har tsayon sati biyu, amman idan sunyi waya da daddy yana ce masa yanzon suka gama waya da usman kuma babu wani lbr"

Ranan da suka cika sati 2, da rana deeni na zaune yana tunanin ma'u aharabar gidan"


Ganinta yayi acikin idonsa ranan da ya fara sakata a idonshi"

Tsugunawa tayi har kasa tace ina wuni yaya shamsudeen, tun lokacin yaji ta shiga ransa"

Dan kaha yake mata bakam ta gama budurinta aka shi, kuma lokacin ne ta gama shiga zuciyan shi, murmushi ya sakeyi tare da fadin Asma'u yariya ce me shiga zuciya, inama farincikin da muka samu afarkon haduwan mu ya daure har yanzun" duk da naga asma'u na kokarin tura son Jamal acikin zuciyanta kamar yadda nima nekeyi ayanzu, amman azahiri banason Jamal natsane Sa, bantabajin na tsani wani ba kamar yadda na tsane sa, nasani Malam ya gayamin ciwa babu kyau gaba, amman nakasa cire kiyayyan Jamal acikin zuciyata, cire kiyayyan sa ko nanufin nabar basa Asma'u, nikuma bazan iyaba, *Na dad'e ina dama furata bazan yadda haka nan wani ya shanye min ba*


Karan motocin dayaji ne ya tsayar mai da tunanin"

Usman yagani ya dakko daga mota duk yayi furu furu ya fita hankalin sa"

Suna saukeshi suka juya suka fita daga gidan, part dinshi ya shige batare daya kalli inda deeni yake ba"

Tashi deeni yayi yabishi yana daba kofar yajita kulle, dan haka ya koma gefenshi ya zauna zuciyan shi cike da tunani barkatai"

Washegari karfe 7:00am daddy ya kira deeni"

Cikin sanyin jiki suka gaisa da daddy sannan yace"

Shamsundeen ya kamata muhakura haka, dan atunanina Jamal baya raye, duk inda ake tunanin ganin su anje babu shi amman ansame gawan wasu daga cikin su, shima Jamal din ansame jakar sa tare da wayoyin Sa, amman shi babu shi cikin kuka daddy ya karasa mgnr"

Shiko deeni yarasa abin da yakeji yayi, farin cikine ko bakin ciki be sani ba"

Daddy ne yaci gaba da cewa ka hada kayanka yau zaka dawo, usman yace akwai abun da zai yi bayanzun zai dawo ba"

Koda suka aje waya deeni cewa aidaman nasan asma'u tawace"


Deeni besake ganin usman ba sai afilin jirgin sama, gani yayi ya rame idonshi jawur kamar garwashi, jakar dake hannunshi ya mikawa deeni yace kabawa daddy jakar Jamal ce"


Har jirgin ya tashi usman natsaye ya rungume hannun akirji"


*Abuja*

Koda deeni ya isa gida samun kofargidan yayi cike anata zuwa wa daddy jaje, abban ma'u ya hango zaune kusa da daddy dan haka yayi maza yabi ta baya dan bayanson ya ganshi agidan nan"

Daddy ko yaga wucewan deeni dan haka ya tashi yabi bayansa"

Zuwa can ya fito dauke da da jakar Jamal ahannun shi sannan ya kira Abba da alhaji bashir suka shiga cikin gida"

Falon ma cike yake da yan jaje cikin harda da momyn usman, tare da anty fa'iza"

Atsakiyar falon daddy ya tsaya yace inna asma'u?

Tana dakin nafisa"

Kai tasaye suka nufi dakin momy ma bayan su tabi"

Ma'u na zaune tayi tagumi taga abbanta ya shigo dan bata san da zuwan su ba"

Afirgice ta mike tare da dafa bango dan tasan hakanan abba bazaizo ba, idan ma yazo toh bazai shigo har daki ba"

Kamata momy tayi suka koma suka zauna, suma su daddy zama sukayi sannan suka fara mata nasiha daga karshe ya fada musu halin da ake ciki tare da ajiye jakar Jamal atsakiya"

Fashewa Momy tayi da wani irin kuka, me tsuma rai sannan tace ban yadda ba, alhaji be mutuba, idan kuma ya mutu babu abin da na isa nayi amman kubani gawan sa"

Ma'u ko batace kala ba, kuma batai kuka ba, asalima gutun murmushi ne akan idonta"

Wani irin mikewa tayi, cike da karfin guiwa ta tsuguna agaban jakar"

Ahankali ta zage zip din ta zazzage kanyan ciki akasa, Abba ne yayi yinkurin hanata amman daddy yace abarta"

barbaza kayan ta farayi nan taci karo da hotona ahankali ta zaro daya, kara zaro ido tayi ganin pic dinta, akofar gidan su deeni lokacin da taje ana gobe dauri auren su, ajiyewa tayi agefe sannan ta kara dauko wani, shima natane lokaci da yayi zuwa nafarko zai tafi bata manta ba lokacin ne yake ce mata yayi ciwo harya warke batamai sannu ba"

Haka taita fitowa dashi, duk natane alokuta daban daban, mamakine ya kamata dawani lokaci yake daukata hoto batare da ta sani ba, zabura tayi ta watsar da huton sannan ta rarumo wayar sa"

Kunnawa tayi, pic din tane ya bayana akan fuskan wayar tana zaune afalo hannnuta zane da lalle, daga cen gefen pic din an rubuta My Queen"

Tundaga lokacin wuta ya daukewa ma'u, ta kame kam, kwata kwata bata motsi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login