Showing 30001 words to 33000 words out of 95354 words
Chapter 11 - BUGUN ZUCIYA Hausa Novels Complete by Fadila Lamido.txt
mu"
Juyowa yayi da sauri ya kalleta, akwai alaman tsoro a jdon shi, yace Allah yasa baki watsar da mutunciki ba ?
Karuwa kukanta yayi, cikin kuka tace... Wlh bakomai Abba"
Tsayawa yayi ya gama kare mata kallo, sannan yajuya ya fara tafiya tare da cewa daga yau karki sake fita ko haraban gidan nan bance kije ba,
Juyawa yayi ya fice abinshi"
Ma'u ko kuka taita yi, tana share hawayen"
Da daddare mama ta shigo dakin ma'u ranta abace, ganin haka yasa ta takara shiga cikin hankalinta"
Mama kasa mgn tayi illa kallo kawai data bita dashi, bayan ta gama kare mata kallo, ta juya ta fita batare da tace komai ba"
Washegari ma'u tanason ta sanar da deeni, ta rasa ya zatayi, gashi abba ya hata fita, kuma gashi bata taba karban no deeni ba, dan haka ta yanke shawaran ta rubuta taba drive ya kai mai"
Bayan ta gama rubutawa, ta miki tana tunani yama zatayi tabawa drive, bayan abba yace ko haraban gidan be amince taje ba"
Goggo tani ce ta fado mata, dan haka taje ta sameta, cikin ladabi tace mata goggo daman sani nake son nabawa sako, kuma gashi Abba ya hanani fita"
Mikewa tayi tana fadi.... to bari nayo miki kiran sa, hala laifi kikayi"
Sani drive nazuwa ta bashi takardan sannan tamai kwatan cen gidan, ya wuce"
πππ
*Wanene *Jamal* ?
*Jamal* shine d'a name farko agun alhaji inuwa manga, mahaifiyar shi hajiya Sadiya bafulata ce ta usuli, bayan haihuwan Jamal suka samu sabani wadda harta kaisu da rabuwa"
Bayan rabuwan su ne ya aure hajiya asabe wadda ta haifan yarta guda daya Aisha, ran hajiya asabe besoba, taso ace namiji ta haifa, dan haka ta dauki tsana ta daurawa Jamal, Jamal yasha matukar wahala agun hajiya asabe wadda suke kiranta da mami"
Tun daga kan Aisha bata sake samon haihuwa ba, dan haka tsanan Jamal yake kara ruruwa acikin zuciyarta, jitake tamkar ta kashe shi"
Jamal yasha wahala bakadan ba, duk da cewa mahaifin shi attajiri ne, amman mama taki bari yaji dadi, ta kanainaye komai"
Dan haka tun yana karamin ya taso dason ya zama soja, saboda yawan zaman kunci dayake, ya saba da zaman shiru, zama shi kadai be dameshi ba, kulum yana daki saboda mami bata barin shi ya sake, kullun ida ya tafi makaranta tun safe sai 6, daya dawo zai shige dakin sa, haka yasa bashi da abokin hira sai karan ce karan ce, aban garen addini ma ba,abarshi abaya ba kullum da subahi yakan karanta Qur'ani, dan haka tun yana karami yake da kaifin basira"
Har tasowan shi karatun shi kawai yasa agaba, bayan ya kammala karatu ne hankalin Alhaji inuwa ya fara dawowa kanshi,
Kuma lukacin ne ya lura dabi,un shi, sun canja, baya son yawan mgn, dan haka ya fara janshi ajikin shi, itama mami lokaci da ta fahimci yanzun ya mallaki hankalin shi saita fara sakar mai fuska, agaban idon shi"
Itako momyn jamal bayan rabuwanta da alhaji inuwa ta aure wani attajiri har suka haifi 'yarsu 1 Nafisa, sheran Nafisa 14 mahaifinta ya rasu dan haka bayan Momy ta gama takama ta dawo gidan alhaji inuwa, ayanzun haka shekaranta 2 da dawowa gurin daddy Jamal, tare da 'yarta Nafisa,
Bayan Jamal ya fara aiki ne akafara mai zancen aure, amman ko kunya bayaji yake cewa Allah ya kyauta nine Zanyi aure, 'yar karamar yariya ta rainani, ni ba auren da zanyi"
Lokacin daya fara fadin haka, daga Momy har daddy dariya suka yi, tare da ganin wauta ce ta mai yawa, hartakai duk abokan shi sunyi aure, amman shi ko abokin shine zaiyi aure daga gun daurin auren ya keyin sallama acewan shi bazaije gun taron mata ba haka kurum su raina shi, dan haka lokacin da usman ya matsawa Jamal ya kawo musu ziyara, yace zaixo amman fah bazai sauka gidan shiba sabo da kar matar shi ta raina shi"
Dariya kawai usman yayi sannan yace toh kazo saika sauka gidan abba, haka tasa dole yayi karyan matar sa tayi tafiya"
Acikin abokan Jamal babu wadda besan halinsa ba nashegen son girma"
Momy da daddy suyi mgn har sun gaji akan yayi Aure amman killum mgnr daya ce, shifa bazaiyi Aure ba dan kada yariya tace zata raina shi"
Tun daddy da momy nawa abin dariya, har yazo ya fara basu haushi"
Ranan daya dawo daga gidan su ma'u kuwa kasa zama yayi, bashi falo bashi dakin momy, hakanan yaji zancen auren ma'u ya dame shi"
Momy ce ta lura zirga zirgan shi yayi yawa dan haka ta bishi da kallo tare da fadin kai lafiyan ka ?
Kusa da Momy yaje ya zauna sannan yace Momy wata 'yar tatsiyar yariya ce wai za,a mata aure, idan kika ganta kamar 'yar tsana"
Tsaki momy taja tare da fadin kaifah baka da kan gado, na kula adawa kake da aure"
Momy wlh yariyar da kadan tafi Nafisa"
Hmmm Jamal kenan toh ai ko Nafisan ana iya mata aure, lallai ma Jamal kaman Nafisan kake kira 'yar tsana, Allah ya shirye ka"
Haka ya kwana bayajin dadin, gashi ya rasa me yake damun Sa, dan haka washegari ya tashi bayajin karfin jikin sa"
Gajiya yayi da kwanciya adaki karfe 11:30 ya tashi ya zauna abakin gadon, azuciyar shi yace waini meke damu na ne? Husna yaji wani bangare na zuciyan shi na fadi"
Tsaki yaja afili yace.... Babu wata *Husna* kawai ban da lfy ne, ji yayi kaman yanajin sanyi gashi har yanzun beji natsuwa tazo masa ba, dan haka yajawo bargon daya rufa dashi ya rufe jikinshi ruf, kanshi kawai kake hangowa ya nufi part din momy"
itako momy tana zaune afalo, Nafisa kwance ajikinta tana kuka ahankali"
Cikin tausayawa mama take cewa haba nafisa ki dinga hakuri mana, yakamata ace yanzun kin saba tunda duk Wata haka yake miki"
Daidai lokacin mama ta hango Jamal yana tahowa ya kudundune cikin bargo"
Da mamaki take kallon shi, harya karaso daf da ita ya zauna bata daina kallon shi ba"
Menene haka kuma Jamal?
Momy wlh bani da lfy"
Allah na gode maka, meke damun ka?
Yana kara lullube jikin shi yace... Inaji dai kaman zazzabi ne"
Toh Allah ya sauwake, ka tashi ka koma daki kasha magani, kaga Nafisa ma tun safe mata jin dadi"
Kallonta yayi sosai sannan yace.... Nakoma daki fah kikace, nace miki bani da lfy kuma kice na koma daki na zauna ni daya?
Hmmm Jamal kenan, toh idan ka zauna anan ni me zan maka, kaga amfanin iyali kenan"
Shiru yayi yana girgiza kai, zuwa can yace..... Momy nida Nafisa akwai banbaci kenan tunda gashi kin dauki nafisa kin daura ajikin Ki, nikuma kince nakoma daki,nayi jinyan kaina"
Tunawa momy tayi da kishi irin na jamal dan haka ta fara kokarin daga Nafisa tana fadin zo ka hau"
Mikewa yayi cikin sauri yana kokarin fita yana fadi, ai kince na koma daki idan na mutu shi kenan"
Yana wucewa momy tace Ja'iri duk yadda akayi zama shi daya ne ya soma damun shi, bari dai daddyn sa ya dawo asan abinyi"
****
KANO
Tun da sani ya tafi ma'u ta koma dakinta tana zaman jiran dawowan sani tare da addu'an Allah yasa komai ya tafi daidai ππ»"
Lokacin da sani drive ya isa gidan da asma'u ta kwatan ta mai fitowa yayi yai sallama akofar gidan"
Ummi ce ta leko bayan sun gaisa yace.... Shamsuddeeni yake yake son gani"
Kaman daman jira yake, ya fito yana mazurai, jada baya sani yayi domin tsorata da yayi da ganin deeni"
Cikin mazurai deeni yace..... Kai!! Menene lfy?
Jikin sani na rawa ya ciro takaddan ya mika mashi,tare da fadin asma'u ce tace nakawo maka"
Murmushi ne ya baiyana afuskan deeni nan take ya warware takardan ya fara karantawa, bayani tamai akan kiran da abbanta yake mai, dadi yaji ba kadan ba, idon shi ya dago ya kalli sani sannan yace shikenan kace mata ina gaisheta, Jim yadanyi sannan ya juya zai shiga yana fadin inzuwa"
Sani ya dade tsaye akofar gida yana jiran deeni, zuwa can saiga gashi ya fito, takarda ya mika masa sannan ya nuna masa hanya tare da fadin ware"
Ahanya babu abunda sani yake banda tunani, tun da yake betaba tsam manin asma'u zata saurari mutum irin deeni ba, duba fah wai ni yake nunawa hanya saikace bani na kawo kaina ba, irin su abu kadan zaka musu su rufeka da duka, addu'a ya fara yi azuciyar shi Allah yasa kar akara aiko shi"
**
Deeni yau ji yake babu ishi, wani mugun farin ciki ne yaji ya kamashi, ummi ma taji dadin lbrn saidai ta wani bangaren gabanta na faduwa, dan ayadda taga ma'u tasan cewa iyayenta bazasu so dabi'un autan ta ba, dan haka daga deeni har asma'u tana tausaya musu, dan itace sheda tafi kowa sanin inda suke son junan su"
Zama tayi ta zuba uban tagumi tana bin deeni da kallo sai murmushi yake yi, hakan nan taji yana bata tausayi"
Gyaran murya ummi tayi sannan tace.... toh auta goben kai kai kadai zaka ?
Toh ummi nidawa zani, saidai idan idan caka zan kira, kai ninafison na tafi ni 1 "
Da Sauri ummi tace eh gare katafi kai kadai, kuma dan Allah kayi shiga na mutunci karkai irin shigar nan taka, ni kaga asubanci zanyi domin inason nayi mgn da yaya larai"
Bece mata komai ba ya mike ya shige dakin Sa"
Itako ma,u tunda sani drive ya kawa mata sakon deeni karantawa take tana sake maimaitawa, dadi taji dataga no banshi aciki dan haka bata bata lokaci ba wajen kiran shi"
Da wayar mama ta kirashi dan ita har yanzun ba,a bata damar rike waya ba"
Hira sukasha sosai sannan ta gaya mishi lokacin da abba yake gida"
Goggo tani ta samu ta roketa dan Allah ta gayawa mama bakon nata zaizo gobe da misalin 11:30am"
Dan haka washegari ta tashi da tunani guda 2, ko nasara ko akasin haka"
Aban garen deeni ko, shiri yake tayi domin zuwa ganawa da sirikin shi, tun da duku2 ummi ta wuce dan haka shikadai ne agidan"
Bayan yayi wanka ya gama kintsa jikin sa, karamar riga ya dauko hannunta iya daidai kafada, sannan yasaka wandon shi ya dan wuce guiwa da kadan, turare ya dauka yana fesawa ajikin shi, sai alokacin mgnr ummi ta fado mishi, da take cewa... idan ka tashi tafiya kasa kayan mutunci, kallon kayan ya kara yi sannan ya kalli gurin dayake ajiye kaya, gani yayi duk acikin kayan wannan ne me dama dama, dan haka ya saki fito tare da dage kansa sama"
Fitowa yayi ya rufe gidan ya fara tafiya, ji yayi kaman akwai abinda ya manta agida, jayayi ya tsaya tare da shafa wuyan shi, sai lokacin ya tuna
ya bawa ma'u sarkan shi, da yanzun ita zatamai rakiya yana tafiya tana kara, tare da tashi sama, tsaki yaja afili yace.... Ina bazai yuyoba tafiya babu sarka kuma babu duna ai sai na dade banje ba"
Hannu yasa aljihun shi ya ciro waya sannan ya karata akunnesa
yana fadin...... Caka kawomin Duna da matar sa zasumin rakiya"
Cikin kankanin lokaci Caka ya kawa su kamar yadda ya bukata"
Cikin wani irin taku ya fara tafiya duna da matar sa nabin shi abaya suna mishi haushi duk inda aka kan shi kyaucewa ake abashi hanya.....
Heart Beat
*Mmn Yazeed*
[24/01, 11:04 a.m.] βͺ+234 906 689 6652β¬: ππππ
β*BUGUN ZUCIYA*β
( βHeartbeatβ)
πππ
π
πππ
βByβ
π
ββ*Fadeela Lamido*
*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATIONπ€*
β
*πππ Salam masoya BUGUN ZUCIYA, hakika kun nunawa wannan book kauna, tare da ni kaina, farin cikina bashi missaltuwa, sai dai nace muku nagode2 Irin sosai!!! din nan, kuma ina fatan kun fara fahimtan darasin dake cikiππππ*
*SADAUππ»KARWA*
*Masoya BUGUN ZUCIYA aduk inda suke*ππ
3β£6β£to3β£7β£
πππ Cikin wannan yanayi deeni ya isa kofar gidan su ma'u"
Yana kokarin taba get din sani drive na fitowa"
Wani mugun faduwan gaba yaji dan haka besan sadda ya kauce ya bashi hanya ba"
Mannewa yayi ajikin bango tare da bin karnukan da kallo, har suka shige cikin haraban gidan"
Suna shiga gidan karnukan suka daina haushi sakamakon hannu da deeni yasa yana shafa musu kai"
Zuwa can deeni ya dago ya kalli sani cikin daure fuska yace..... Gaya mata na iso"
Jikin sani na rawa ya nufi cikin gidan, mama ya samu afalo jikin shi na rawa yace wai bakon Asma'u ya iso"
Tabe baki mama tayi sannan tace toh ka bude masa falon alhaji"
Juyawa sani yayi badan ransa yaso ba"
Sani nagaba deeni nabinsa abaya, har suka isa, kofar ya bude, tare da fadin bismillah"
Shigewa deeni yayi, su duna na take mushi baya' tsaye yayi yana karewa falon kallo, tare da fadi azuciyar shi, lallai mahaifin ma'u me kudi"
Waiwaigawa yayi ya zabi kujeran dayaga tamishi ya zauna"
Yayin da karnukan shi suka kwanta agefe"
***
Ma'u tunda taji sani yana gayawa mama ta shiga damuwa tare da addu'an Allah yasa deeni manyan kaya ya saka, kuma Allah yasa ummi ta gargade shi ya gyara harcen sa"
Addu'oi da tai tayi kenan, har zuwa lokacin da taji fitowan abba da baba"
Cikinta taji ya kada dan haka ta tashi ta shiga bayi"
Alhaji musa ne agaba abba na binsa abaya dan haka alhaji musa na tura kofar yayi to zali da duna"
Tsayawa yayi cak sannan ya juya ya kalli abba tare da tambayan shi, Gamo nayi ne?
Atare suka maida idon su cikin falon, tare da karasa shiga ciki, ko wanne su bakin shi dauke da addu'oi a bakin shi"
Wani irin BUGAWA ZUCIYOYIN su yayi atare ganin matashin saurayi zaune, karnuka kewaye dashi, cikin bin bango abba ke kokarin shiga ciki hannun shi daya dafe da saitin ZUCIYAR shi"
Alhaji musa ne yayi karfin halin karasawa gaban deeni tare da fadin.... Daga ina?
Deeni cike da kwarin guiwa yace nine bakon da Asma'u ta sanar muku da zuwan shi"
Runtse Ido alhaji musa yayi tare da dafe kirjin sa yana sauke wani irin nufashi, ja yayi da baya ya nemi wata kujera ya zauna"
Abba kuwa yana rike da kirji shi acikin zuciyar shi ko fadi yake Allah Yasa yazamto mafarki ne"
Ganin inda Abba ya sandare aguri guda, yasa alhaji musa dakewa, ya fara kwalawa Asma'u kira"
Tunda asma'u ta jiyo irin kiran da baba yake kwalawa tasan akwai Marsala, dan haka jikinta narawa tafi falon abba"
Tagaban Abba ta wuce haryanzun yana nan a inda yake"
Gabantane yai wani mummunan faduwa ganin duna kwance atsakiyan falon mahaifinta"
Ganinta kawai tayi ta daura hannuwanta 2 aka, tare da zubar da hawaye"
Sauke hannun ki taji Abba yace, bashiri ta sauke su kasa sannan tabi Abba da baba da kallo"
Deeni ko ma'u yake kallo fuskan shi dauke da murmushi"
Ahankali Abba ya nemi guri ya zauna, alhaji Musa ko, kallo yake bin ma'u da deeni dashi"
Abba ne ya kalleta sosai sannan yace.... Asma'u wannan shine yaron da kikace kina so ?
Eh, tace batare dajin kunya ba, dan ita ganinta wannan itace daman ta na karshe"
Girgiza kai Abba yayi tare da fadin yayi kyau, shiru yayi zuwa can ya sake cewa.......Asma'u kikace wannan shine wadda kika amince ya zama uban 'ya'yan ki ?
Kasa mgn tayi hawaye na zuba a idon ta"
Shiko deeni, wani irin kallo yake yi Wa abba dan ya rasa inda mgnr abba ta nufa be amince bane, koko so yake ya tabbatar?
Inajin Ki abban ya sake fada"
Ahankali ta daga kai alamar eh"
Abba komawa yayi ya kwanta ajikin kujera"
Alhaji Musa ne yayi ajiyan zuciya sannan ya juya ya kalli deeni yace......... To kai Yaro bamu gaisa ba bare musan sunan ka"
Cikin murya nan da kukasan deeni da ita ya karkace baki yace..... Sannu