Showing 93001 words to 95354 words out of 95354 words

Chapter 32 - BUGUN ZUCIYA Hausa Novels Complete by Fadila Lamido.txt

29 Oct 2025

494

ya hauyi gadan2 komai da ake zubawa yar gata daddy yasa anzuba agidan da yabawa deeni"

Shiko deeni bawani shiri yake ba, domin kokari yake yaga rayuwar sa ta gyaro, bema san wacece amaryar ba, kuma be damu ya sani ba, burinshi kawai yaga ya aje iyali"

Abangaren momy kuwa, kullun fuskarta daure take tam, taki gayawa kowa zancen auren nafisa, dan haka daddy da kanshi ya sanarwa dangita"

Koda yayyata sukazo lallashinta suka yi, akan tayi hakuri insha Allahu auren zai bata mamaki"

Haka shirye shiye ya dada kankama nafisa sai rawar kai take, tare da kawayenta, sosai takebawa momy haushi, saidai batace mata kala, har biki ya rage sati, kuma aranan ne Jamal yacika sati uku da barin gida"


****


Jamal da ma'u nagani agaban doctor, sai ya mutsa fuska take Jamal na tarota"

Bayan Dr ya gama rubuce rubucen sa ya dago ya kalli jamal yace"

Ranka ya dade inaganin abin da yafi kawai, ku raba makwanci har cikin yayi kwari, domin idan har zaku dinga haduwa za'a samu matsala gaskiya"

Shiru Jamal yayi zuwa can ya daure fuska tare da fadin.....

Bakomai insha allahu zan kiyaye, sai mgnr kafata?

A kafar ka Alhamdulillah ta cike saidai ansamu matsala inaganin daga Dr dake wanke maka ciwon ne tun da farko, dan gashi bata warke yadda ya kamata ba, amman bawata matsala"

Godiya Jamal yawa dr sannan ya daga ma'u suka fito"

Biyosu Dr yayi tare da fadin Oga akiyaye fah"

Bayan sun koma gida tarairayan ma'u Jamal keyi sosai baya yadda ta dauki ko kofi abinci ma abaki yake bata, cak yake daukanta ya kaita toilet yai mata wanka, cikin dare ko haka yake rungumeta tsam ajikin shi, kamar dai wani zai kwace masa ita"

Har mamakin Jamal ma'u take wai ayanzun ita Jamal yakewa bauta, duk girman kannan ya ajeshi agefe"


Bayan sati 1


Yau jamal ya tashi da tunanin gida sosai axuciyar shi dan haka yadau waya yasa no momy"

Bugu biyu ta dauka, hayaniyan mutane yaji tare da dallaman Momy"

Ahankali ya amsa"

Arikece momy tace......

Jamal?

Na'am momy kuna lfy?

Kaniyarka Jamal, kai kana da hankali kuwa?, kana inane yanzun?

Momy nakirane naji lfyr ku kuma kusan muna lfy"

Jamal ina Asma'u?

Tana toilet"

Kafarka fah?

Karamar dariya Jamal yayi tare da fadin ta warke mom......

Karya kake Jamal be isa ta warke ba"

Wlh Momy ta warke bari zan turo miki pic dinta kikani"

A'a karka turomin kadawo gida kawai Jamal, hankalina bazai taba kwanciya ba, sainaga ka dawo idan ma kai bazaka dawoba toh katuro Asma'u gida"

Kawar da zancen Jamal yayi tare da fadin momy wai baki gida ne naji hayaniyan mutane ne"

Ina gida Jamal, bikin Nafisa ake yanzun aka daura mata Aure"

Aure kuma Momy?

Fashewa momy tayi da kuka tare da fadin eh Jamal daddy ka ya matsa saiya aurar da ita"

Da sauri Jamal yace dawa?

Da shamsudeeni"

Deeni ?, momy ta yaya zaki bari adaura wa Nafisa aure da deeni?

Jamal kasan halin daddyn ka da kafiya da naso hanawa ma cewa yayi dan naga bashine ya haifeta ba, dan haka nabarshi yayi abin da yaga dama da ita"

Hakuri Jamal ya karabawa momy sannan ya mata alkawarin sunanan dawowa"

Bayan ya aje wayar ya tashi ya shiga dakin baccin su, ma'u na kwance akan gado, hawa yayi ya kwanta, sannan ya jawota jikinshi ya rungume tare da sun batanta ta, acikin kunnenta ya rada mata yau kawarki na Aure"

Zainab ? Ma'u ta tambaya"

A'a Nafisa"

Tashi tayi ta zauna tare da fadin nafisa?, naga yau satin mu 4 anan kuma banji ana mgr aurenta ba"

Eh daga baya ne"

Tabe baki tayi tare da fadin aiko banji dadiba naso ina gida za'ayi, to wa ta aura?

Kauda kai yayi sannan yace deeni"

Deeni? Yaya da gaske???

Zan miki karya ne?, yanzu nakira momy awaya take fadamin"

Guri daya ma'u ta kurawa ido, tare da kokarin danne abinda ke shirin bijuro mata"

Kallonta kawai jamal yayi sannan ya mike ya fita adakin"

Hawaye taji yana zubo mata ahankali ta fara tuno irin rayuwar da sukayi da deeni abaya"

Acikkn xuciyanta take cewa...

Haka Allah ya nufa deeni ba mijina bane bazamu zauna tare ba, duk irin soyayya da mukayi tazama abanxa abubiwan da sukaitayi ne yaita fado mata, zama tayi kamar mahaukaciya wani tai murmushi wani tai hawaye, acan karkashin zuciyanta ko bataso nafisa ta aure deeni ba taso yasamu watacan ya aura"

Tun daga ranan yanayin ma'u ya dan canza haka ma Jamal dayake lora da ita"


***

Deeni ko Sai a Wajen daurin auren yasan nafisa ce amaryan, fuskan shi babu yabo babu fallasa, abokan shi na kano duk sunzo cikin manyan kaya kamar basuba, bayan andaura aure duka suka wace caka ne kawai ya tsaya"


Lokacin da caka zai raka deeni gidan shi saida suka fara biyawa gidan alhaji bashir sosai sukamai fada harsaida abin ya bashi mamaki, bayan sun mike ummi ta kalli caka tace wlh bakuga inda kukayi kyauba, kamar baku ba, wai ya sunanka ne?

Cikin murmushi caka yace ummi sunana *Faisal*

Hannu ummi ta tafa tare da fadin sunanka me dadi ake cemaka wani wai caka, dan ALLAH auta daga yau ka rinka kiranshi da sunan shi"

Addi'oi tayimai sosai sannan suka wuce gidan deeni"

Gidane nagani nafada daddy ya mallakawa deeni tare da mota me zafi, har cikin falon suka shiga har sun nufi cikin dakin deeni ya tuna da karatun malam acikin zuciyan shi yace bazan shiga dawani har cikin dakin mamata ba"

Waigawa yayi ya kalli caka yace faisal zauna anan ina zuwa"

Bakin gado ya samu Nafisa yafe da gyalenta me tsananin shiki, hannu yasa ya yaye gyalen, cikin sauri ta sukuyar da kanta kasa, yana daga tsaye yasa hannu ya dago habarta suna hada ido ta maza ta rufe ido"


Murmushi yayi kadan sannan ya ninke gyalen ya aje agefe sannan yace kisa hijjabi ki sameni falo akwai abokina dazaku gaisa"

Kamar yadda yace haka tayi bayan sungaisa ta koma daki"

Aranan deeni be runtsaba adaren ya dama furanshi kuma yashanye ta tas"

Nafisa ta jigata sosai tayi kuka tayi magiya dan haka dasafe idonta yayi jawur bata san haka haka aure yake ba da bazata taba yadda ba"

Shima deeni tausayinta ya kamashi tsam yasata akirjinshi dare da lalabo duk Wata kallama ta lallashi yana gaya mata"

Ahankali yafarajin sonta na shigarshi, farin cikin yaji ya kamashi sosai tare da godewa Allah daya amsa addu'anshi daman ya shanye furan ne ayau Dan ya yakice burbushin son ma'u azuciyan shi"

Haka suka kwashe tsayon sati uku suna cin soyayyar su, zuwa wannan lokacin sun saki jiki da juna kuma ahankali suna kara shakuwa"

Zuwan su gidan momy 3 amman da daddare suke zuwa itama momy ta fara sakkowa domin ayanxun duk lokacin dazakaga deeni cikin farar jallabiya yake tare da carbi ahannun shi"

Har kasa yake tsugunawa ya gaisheta betaba yadda su hada ido, Nafisa ko cikin manyan hijabai take"


Tayi wani irin kiba naban mamaki"


****


Jamal ko jinyan ma'u yake, tare da kokarin cire mata kowanne irin tunani sosai takejin dadin zama da jamal, dan yi yake tamkar ya maidata ciki"

Dakanshi yake girka mata abincin da zataci, baya barinta tayi ko cangal, anacikin haka ne ya koma aiki dan haka dole yasa ya nemo me aiki"

Bayan sati 2 ma'u tana kwace afalo cikin duguwar riga, sosai cikinta ya turo kaikace cakin wata 7 ne, kyau cikin ya mata tare da Kara fari da sheki"

Daya daga cikin. yaran Jamal taga ya shigo da wusu manyan ledoji guda biyu, cikin sauri ta miki tare da mamakin meyakawo Jamal da rana"

Muryan yaya usman taji yana sallama tare da anty fa'iza"

Batasan sanda ta mike taje gaban fa'iza tana fara'a ba, amsan yariyar tayi sannan ta jawo hannun fa'iza suka zauna yaya usman ta fara gaidawa amman ke madagas yaki amsawa, ganin haka jikinta yayi sanyi gaisawa suka da anty Sannan sukaciga da hira sama sama"

Hannun anty fa'iza ma'u ta dada dagowa tare da fadin zo muje daki"

Bazataba, usman ya fada fukan shi cike da haushinta, cigaba yayi da cewa mara kunya kawai ke me miji ko ?

Kara sukuyar da kanta tayi tare da matso hawaye"

Basu dadde da zama ba taji tsayowar motar jamal tasan gayamai akayi yayi baki"

Yana shigowa ma'u ya fara kallo sannan ya koma gurin da usman ke zaune karasawa Jamal yayi tare da fadin babban yaya daman nasan kaikadai ne matsala ta tunda ka bincikoni akurgumin daji babu a inda bazaka binciko ni ba"

Wani irin kallo usman yamai sannan hace....



Yazun saboda Allah abinda kayi kan kyauta kenan?, kabar momy cikin tashin hankali"

Katseshi yayi tare da fadin haba usman ko kaine bazaka zauna ba hukuncin daddy yayi tsauri da yawa gaskiya inason matata yaya za'ayi ba acemin wani nasaketa "

Juyawa Jamal yayi yaga idon ma'u alamar tai kuka, cikin sauri ya tashi tsam, ya nufi gurinta, ganin tahowanshi yasata mikewa ciki sauri dan tasan riketa zaiyi gaban yaya"

Bayanta yabi tare da fadin.....

tsaya mana, ina daki ta shige Jamal nabin bayanta hannu sa yasa ya tarota sannan yasata ajikin shi tare da fadin usman ne ya bata miki raiko?

Guntun hawaye ta share sannan tace yaya yaushe zamu koma gida?, kaga yaya usman na fushi dani nagaida shi yaki amsawa, ina tsoron kar ace abba ma yayi fushi dani"

A'a Husna Abba bazaiyi fushi dake ba, ni mijin ki ne kuma sun san muna tare, dole ce tasa nai haka bayin kaina bane, dan haka ki daina damun kanki da tunani banza, nasan halin usman ciki dabai, zuwa dare zan kira miki abba Ku gaisa, wata kila hankalin ki zaifi kwanciya"

Sakin ranta tayi kadan, nan Jamal ya barota ya dawo falo yana zama anty fa'iza ta miki dakin ta shiga sosai ma'u taji dadi, nan hira ta barke tsakanin su, lbr yadda abba ya shiga damuwa da daddy ya gaya mushi Jamal yabar gida tabata

Cikin ido ma'u ta kalleta tace kila shima yanzun haushina yakeji?

Bawani haushi, ko jiya da mukaje ya fada mishi ya samu inda kuke cewa yayi agaida ku, kuma usman ya roki Jamal idan cikin ki ya tsufa ya dawo dake gida"

Ajiyan zuciya tayi sannan sukahau hira"

Jamal ma da usman hira sukayi sosai acikin hiran ne usman ya isar da sakon abba"

Difff Jamal yayi xuwa can yace kasan abin da yasa na kasa dawowa wlh banson ganin deeni kullum tsanarshi kaaruwa take axuciyata"

Ai kaji irin ta mutumin da yayi auren shi ina ruwanka dashi, kaifah daman kacika kishin jaraba, shiyanxun ma bata Asma'u yake ba bakaga gadda. Nafisa tai kyauba naji kanmar ma ance ciki gareta, shikanshi deeni idan ba Sanin shi sosai kayiba baka iya shaida shi"

Ker Jamal ya yadda idan cikinta ya tsufa zasu taho, anayin la'asar suka kamo hanya"

Jamal yaciga ba da lallashin ma'u harta saki ranta so daya ya taba kira mata Abba, bayan sungama waya ya kira mata momy, tundaga ranan ya kashe waryarsa"

Bayan 4

Cikin ma'u ya tsufa tafiya daker tashi daker, idan ka ganta saika tausaya mata"

Kuma lokacin ne hankalinta ya tashi sosai, cikin dare bata iya bacci tashi take ta tasa jamal agaba da kuka"

Cikin tsananin damuwa yake tashi ya zauna, tare da fadi husna kiyi hakuri mana kidaina dagawa kanki hankali"

Nina gaji yaya, ciki kusan shekara daya ajikina ni gaskiya daga wannan bazan kara ba"

Kauda fuska Jamal yayi yai dariya sannan ya juyo ya kalleta tare da fadin gobe zamu wuce gida, dan naga nema kike hawan jini ya kamaki, haba ace mutum be gajiya da kuka"

Murna ce ta kama ma'u sauka tayi wai xata hada kaya, jamal ne yahanata shida kanshi ya hada musu kaya"

Dasafe ya kira no Momy, tana dauka tace Jamal wai yaushe raini ya shiga tsakanin mu haka?, bazaka dawo da yar mutane ta haihu agida ba?, cikin watan haihuwanta fa take"

Cikin mamaki Jamal yace momy waya gaya miki?

Uwarka ce, akace maka bansani bane?, ai ina lissafi, ko ta haihu ne ma?

Sosa keya yayi tare da fadin a'a munan isowa yau"

Yauwa Jamal Allah ya maku albarka dan Allah kutaho da wuri"

Toh momy amman kafin mu tahu inason zan shiga kasuwa"

Me zaka saya indai kayan haihuwa ne nariga dana hada komai"







Heart Beat
*Mmn Yazeed*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login