Showing 42001 words to 45000 words out of 95354 words
Chapter 15 - BUGUN ZUCIYA Hausa Novels Complete by Fadila Lamido.txt
2 tayi, nashiga uku na"
Gaban window ta tafi ta leka, Sojoji ne gungu2 hannun su rike da manyan bindigogi, wurin yacika makil da jama'a daga can ta hango Jamal sanye cikin shadda fara karrr, atsakiyan abukan shi yake, kowanne fuskan shi dauke da murmushi amman tashi kamar amai mutuwa"
Bakin gadon ta koma ta zauna, zuwa can taji maruki na fadin Alhamdulillahi andaura auren *Jamaludeeni* da *Asma'u*
Jitayi kaman ansoka mata kibiya akirji, hawaye taso matsowa Amman sunki zobuwa, gefen gadon ta koma ta makure"
Zuwa can taji anbude kofar ahankali ta dago kanta, momyn yaya usman ce, hannuta rike da kaya, abakin gadon ta ajiye kayan, sannan ta shiga toilet, zuwa can ta fito tace to taso maza yamma nayi"
Kaman za'a kamata haka take tafiya' bayan tayi wanka ta fito momy ta mika mata kayan ta sanya zuruf suka shige, saboda tsabar raman da tayi"
Komawa tayi ta zauna, tana haki, gyale momy ta yafa mata sannan tace tashi muje ke kadai ake jira"
Wayyo momyππΌ wlh nagaji, waida zan dan huta ne"
Me kika yi? Maza taso muje"
Haka taitabin bayan Momy kaman me koyon tafiya, har suka isa falon Abba"
Zaunar da ita tayi sanna itama ta zauna tace toh Alhaji ga Asma'u nakawota tayi sallama, tare da neman gafarar ka zamu rakata dakin mijinta"
Dauke kai abba yayi can gefe sannan yace kuje kawai Amina"
Mutumin dake gefesa ne yace a,a bazayi haka ba, ya kamata kace wani abu"
Kwantawa Abba yayi ajikin kujera ya rufe ido, dan haka mutumin yajuya ya kalli Asma'u
Yace barin ara bakinsa naci masa albasa, Allah yasa kije asa'a kinji ko?, Allah ya miki Albarka"
Kuma Dan Allah kiyiwa mijinki biyayya, yi nayi bari na bari"
Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yace"
Da zan umarci wani da ya yi wa wani sujada, da na umarci mace tayima mujinta sujada"
Manzon Allah ya kara cewa"
Baya halatta ga matar aure tayi azumi kuma mujinta bayayi, face sai da izininsa, ba tada ikon zartar da wani Abu sai da izinin sa"
Haka yaita mata nasiha amman agurin ma'u shiga yake yana fita domin ku fadi take azuciyata, Allah ya kyauta nawa Jamal biyayya"
Har akasata amota kuka take, tare da kankame karamar jakanta ahannu"
Ahaka suka nufi Abuja, gabanta na dukan uku uku, tare da addu,a insha Allahu jibi iwar haka zata sake biyo wannan hanyan"
*Abuja*
Sun shigo karfe tara da rabi na dare kai tsaye gidan Jamal suka nufa"
Agaban wani tankasheshen gida sukaga drive ya tsaya, gida ne me dan karan kyau get din aka bude musu dan haka drive yasaka hancin motan cikin gidan, tun acikin mayafi ma'u ta hango haske kaman rana, ahankali ta dan daga gyalen ta tana kallon Gidan, amma me? Wasu sojoji tahango sunfi 10 suna shawagi haraban agidan tare da manyan bindigogi, kuma da alma agidan suke, cikinta taji ya karta, cikin sauri ta rike momy tare da fadi Momy wadannan agidan suke?
Kallo momy tabi gurin da ma'u take kallo dashi sannan tace"
Eh masu gadi ne?
Innalillahi wa inna laihir raju,un nashiga uku na"
Momy na kokarin lallashin ma'u wayarta tai kara, dauka tayi tasa akunneta batace komai ba ta cire wayar akunneta ta mikawa ma'u tanacewa ansa Jamal zaiyi mgn dake"
Heart Beat
*Mmn Yazeed*
[24/01, 11:04 a.m.] βͺ+234 906 689 6652β¬: ππππ
β*BUGUN ZUCIYA*β
( βHeartbeatβ)
πππ
π
πππ
βByβ
π
ββ*Fadeela Lamido*
*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATIONπ€*
β
4β£7β£ to 5β£0β£
πππ
Amsa wayar tayi badan ranta yaso ba, daga cikin wayar taji muryan Jamal yana cewa"
Kafin ki shiga gidana ki ajiye Duk wani iskanci naki, akofar gida, karki shigan min dashi gida, dan bazan dauki rashin kunyar ki ba,"
Bejara mezata ce ba ya kashe wayar"
Guntun tsaki ma'u taja sannan ta mikawa momy wayarta, sake gyara mata gyale Momy tayi, sannan taja hannunta suka shi cikin Gidan, tare da ayarin mutanen da sukazo dasu"
Suna shiga falon tasa hannunta ta bude idonta, dan ita bataga dalilin daza'a rufe mata ido ba"
Idonta kiri kiri take kallon gidan, eh Gidan ya had'u kuma anzuba kayan daya dace aciki, amman ita basu bane agabanta, Allah ya sani tana masifar son deeni"
Haka nan taji damuwan ta ya ragu sosai, dan haka ta shiga cikin su Anty fa'iza da Khadija da suke hira adakin daya ke matsayin dakin baccin ma,u"
Su uku ne kadai adakin, manya suna falo suna kallo, dan haka anty fa'iza tayi amfani da daman tana bata shawara"
Asma'u kinga jamal yana da kirki sosai, dan Allah ki bishi sauda kafa, ku zauna lfy, kuma ki guje duk abinda baya so"
Toh kawai asma'u take cewa, Ganin haka Anty fa'iza ta ciro wani littafi ajakarta ta mika mata"
Ranan kusan kwanan zaune sukayi, sunsha fira ammam hirar tafi karkata tsakanin Anty da khadija"
Washegari suka tashi da shirin komawa gida dan haka hankalin ma'u ya tashi "
Damisalin karfe 2 na rana suka fito domin kai asma'u gida momyn Jamal, su kuma su wuce gida"
Motoci aka kawo wadatattu"
Bayan sun isa a gaban momy suka ajeta"
.
Momy da yau ne ganin ma'u nafarko, ta taso da sauri ta kamata, kan cinyan ta, tasata tare da leka fuskan ma'u"
Masha Allah, ta fada afili, sannan taci gaba da cewa Allah ya zaunar daku lfy"
Daga nan su Momy suka yi sallama suka fice da nufin daddare Jamal zai mayar da ma'u
Tun da suka fita ma'u najikin momy tana kuka, Nafisa ko na zaune agefe fuskan ta dauke da dariya"
Bakomai ke bata dariyan ba kuwa illa, tunawa da tayi yaya Jamal baya son ahau gadon sa, kuma yau gashi da mata"
Har gurin karfe Goma, ma'u na gidan Momy, tana jaran Jamal har bacci ya fara deeban ta"
Ganin ma'u na bacci Momy ta shiga kiran jamal awaya yana dauka tace"
Jamal kana ina ?
Ina gida mana momy"
Gida ? toh ina Asma'un ?
Cike da kwarin guiwa yace gata akusa dani"
Mamaki ne, ya kama momy, juyawa tayi ta kalli inda ma'u ke kwance sannan ta maida hankalin ta cikin wayar tare da fadin, kaniyar ka Jamal, abinda zakayi kenan?
Me kuma nayi momy?
Takaici ne ya kama momy harta rasa abin cewa, zuwa can tace kazo yanzun nan inason ganin ka"
Cikin kankanin lokaci ya iso kai tsaye dakin momy ya shiga"
Yan mata guda 2 ya gani suna bacci dan haka ya bisu sa Ido, ya shaida nafisa amman dayar ya kasa tantaceta"
Damamaki yace momy wacce wacece ?
Uwarka ce, waikai sai yaushe zakai hankali, kirikiri ince maka ina Asma'u kace min wai gata, bayan tun da 'yan uwata zasu tafi suka kawo ta, toh inason insan abin da kake nufi?
Jikin shi asanyaye yace toh momy Allah ya huci zuciyar ki"
Mikewa momy tayi tana kokarin fita adakin take fadin, gatanan ta riga tayi bacci, sai kasan yadda zakayi, ficewa tayi abinta"
Bin bayan momy yayi da kallo sannan ya juya ya kalli inda ma'u ke kwance ahankali ya matsa gurin cikin siririyar muryan shi yace ke, *Husna*, Husna, ganin ya kirata su biyu bata tashi ba, yasa ya tsaya yana tunanin yadda zaiyi"
Zuwa can ya matsa kusa da nafisa, hannu yasa yadan dake kafanta nan danan ta mike, sannan yace zoki tasa min Husna"
Da saurinta ta taso, tana tashin asma'u, tashi tayi ta zauna tana mutsutsu ke ido"
Lallan hannunta yabi da kallo, har ya kasa dauke idon sa ahankali yace tashi muje"
Kuka ma'u ta fara tare da fadin nidai aban ni anan dan Allah"
Harga Allah tabashi tausayi amman saiya mika hannu yana fadin zo muje dare yayi fah"
Ganin bata da niyar tashi, yasa ya fita, afalo ya samu Momy dan haka yace,
Momy taki zowa fah"
Harara momy tamai sannan ta nufi dakin zuwa cen ta fito rike da ma'u, kuka take sosai momy na lallashin ta, kiyi hakuri kinji idan ankwana biyu zanzo, in duba ki, idan naga bakijin dadi zaman sai kudawo nan, bayan momy ta zaunar da asma'u amota ta juya ta kalli Jamal tace kaikuma kaji tsoron Allah"
Suna isa gida ta bude motan da sauka, shima saukowa yayi, Amman sai taga ya nufi wani bangare daban, ido kawai ta zuba mai acikin zuciyanta tace yana nufin ni kadai zan kwana awancen part din"
Ahakali ta fara takawa harta shiga ciki, agogo ta kalla taga karfe goma sha biyu"
Tagume tayi, tare da tausayin kanta, karamar jakanta ta dauka ta Bude' ahakali ta jawo sarkan deeni, kura mata ido tayi, hawaye taji yana sakko mata na takaice, rungume sarkan tayi tare da tunani yau wane hali deeeni zai shi?
Ahaka ma'u ta kwana rungume da sarkan deeeni lolaci2 tana sunbatar ta"
Washegari kuwa ko kyalin Jamal bata ganin ba, haka ta kwashe sati biyu bataga Jamal ba" dan haka tunanin ta ya fara canjawa, gashi babu waya ahannuta bare ta kira deeni taji wani wani hali yake ciki"
Kara ramewa tayi tai baki, tai zuro2 da ita, domin babu me matsa mata data ci abinci, sai dai intaji cikinta na kugi ta shiga kitchen ta girka"
*****
Yauma kamar kullum tana zaune afalo taji ana kokarin bode kofar"
Kofar tabi da kallo Jamal ta gani ya kara wani haske tare da murjewan fata"
Zama yayi akujeran dake kallon tata, ya kura mata ido"
Zuwa can yace *Husna* babu ko gaisuwa?
Shiru tayi tana kallon gefe, domin idan taganshi jitake kama ta kashe shi"
Husna ina mgn kin min shiru"
Shirun dai ta sakeyi ganin haka ya mike tare da fadin haryanzun dai baki gama yin taushi ba"
Ganin yana shirin ficewa yasa ta mike tana binshi abaya"
Ja yayi ya tsaya tare da fadin ina zaki?
Cikin kuka tace ni wlh nagaji nagaji da zama anan"
Idon ya zuba mata tare da jin tausayin ta axuciyan shi"
Idon shi akan karjin ta yace, toh yanzun yaya za'ayi kenan"
Sunkuyar da kai tayi tare da wasa da hannuta"
Inajinki menene matsalan"
Ni gaskiya bana son gidan nan"
Shiru yayi ya zuba mata ido, zuwa can yace, zanso kiso gidan nan Husna, garama Ki cire kinsa azuciyar ki, dan ko zaki fita gidan nan toh bayanzun ba"
Kara matso wasu hawayen tayi, dan haka Jamal ya tsinta kanshi da kasa tafiya"
Tsayawa yayi ya tsare ta da ido, harta tsargu da kallon da yake mata"
Zuwa can yace Husna kukan me kike yi?
Uffam batace ba, hawaye ne kawai ke zuba kaman anbude famfu"
Ahankali ya sake kiran sunanta, dago jajayen idonta tayi ta kalle shi tare dajan majina"
Inason ki gaya min abin da yake damun ki, banason yawan koke koke, ke kuma naga dabi'arki kenan, ki gayamin meke damun Ki,
kidauka da usman kike mgn, dan nida usman bamu da banbanci, na amince da aureki ne dan na gyara miki zama, bawai dan zan iya rayuwar Aure dake ba, danni kinmin kankanta, kina fara hankali zan sallame ki, dan haka ki natsu zaman ki agidan nan na wani dan lokaci ne"
Har ga Allah taji dadin mgnr shi, dan haka tasa hannu ta fara share hawaye"
Dariya taso ba Jamal amman sai ya dake tare da juyawa ya fice"
Kan kujara ma'u ta koma ta zauna, tare da tunanin hanyar da zata billowa Jamal bataso ace har yanzun tana garin nan ba, kuma yanzu dataji kalaman Jamal tafara canza shawara, ayanzun deeni ne kawai zai iya nemo masu mafuta, dan haka ta fara neman inda zata samu waya"
Acikin zuciyanta tace wannan wata irin rayuwa ce, duk abi antsane ni, kowa baya sona, idan ba deeni ba babu me nunamin kulawa"
Haka ta wuni tana tunani tare da zubar da hawaye"
Tunda Jamal ya fita be sake shigowa ba har washegari"
Damisalin karfe tara, tana kwance adakinta taji ana sallama afalo"
Mikewa tayi, jiki babu kwari ta fito, Momy tagani ita da nafisa, dan haka ta fara murmushi batare datasa sanda ya fitoba"
Cikin sauri momy ta taho ta rike Asma'u, tajata kan kujera tare da mannata ajikinta"
Duku da kanta tayi saitin na ma'u, gani tayi hawaye na zobowa a idon ta, hannu tasa ta fara share mata, sannan ta dagota tace"
Asma'u me yake faruwa?, wani abu na damunki ne?
Kukane ya kwace ma asma'u harda shashsheka, dan haka jikin momy yayi sanyi, waya ta daga ta kira Jamal, cikin kankanin lokaci ya iso"
Har lokacin asma'u kuka take, dan haka ya tsaya ya tsareta da ido"
Momy ma kallo ta bishi dashi, sannan tace, Jamal me yasa kake haka, dan Allah ka duba yariyar nan sati 2 kawai ji inda ta dawo?
Momy to ai itace taki kwantar da hankalinta, kulum bata da aiki sai kuka, ni nagaji da koke2 haushi ma take ban"
Jamal da kaga tana kukan ka tambayeta abinda yake damunta?
Ai ni bata min mgn"
Shiru momy tayi zuwa can tace, Jamal haka ake aure?, dahar zaka kalli tsabar idona kacemin wai batamaka mgn"
Jamal bece komai ba, shiru falon yayi nadan wani lokaci, zuwa can momy ta sake cewa"
Toh shikenan tunda abi haka ne, zantafi da ita gida, ku zauna abangaran ka"
Dago kai Jamal yayi tare da fadin, a'a momy, daddy ma yace haka, amman nacemai ni nafison na zauna anan"
Aiko daddyn naka idan yaga yadda yariyar nan ta fige bazai yadda da zaman ku anan ba, domin alamu sun nuna baka kula da ita, dan wannan kukan da take yi inda kana kula da ita bazata yishi ba"
Juyawa momy tayi, kalli nafisa sannan tace Nafisa hadu mata kayanta"
Shiru Jamal yayi yana karabin ma'u da kallo, aranshi beson su koma gida dan kwai abubuwa da dama daya shirya"
Ma'u na jikin momy har suka bar gidan"
Bayan sun isa gida haka momy taitajan ma'u ajikinta harta fara sakin jikinta"
Damisalin karfe 7:30 na dare ma'u ta samu daman karban wayan nafisa, tashi tayi ta shige toilet"
Shigar da no deeni tayi, cikin kankanin kokaci ya dauka tare da fadin Asma'u ? meyasa zakimin haka?
Ajiyan zuciya tayi sannan tace deeni ? Yaya akayi kasan nice?
Ajikina naji, asma'u nashiga cikin wani hali, ina tsananin bukatan ki akusa dani, Asma'u bani da gata, bani da kowa saike, me kikeyi har yanzun baki dawo ba?
Cikin kuka tace na kasa, deeni bansan yadda zanyi ba"
Shima hawaye ya share sannan yace Allah yasa baki bari ya shanyemin Furata ba"
Kukan ma'u karuwa yayi, cikin muryanta da ta kasa fita sabo da kuka tace"
A'a naka ne kai kadai, Yaya Jamal be isa yashata ba, dan yafi karfin sa"
Ajiyan zuciya ya sauke, sannan yace kin tabbata?
Eh ta fada cike da karfin guiwa"
Shiru sukayi na wani lokaci, zuwa can, yace awacce uguwa kuke?
Bansan sunan unguwan ba deeni, tunda nazo ko kofar gida ban fitaba, nan ta kwashe duk yadda sukayi da Jamal ta fadawa deeni"
Shuru yayi, zuwa can yace, Asma'u karki yadda da duk abinda Jamal zaice miki, karya yake, yana sonki, wlh muna fuki ne, nafahimci sonki yake, tun lokacin dayazo har gida shi da mutanen sa suka tafi dani, yace ki natsu ne dan ya samu hanyar da zai cusa miki soyayyar shi, bawani rabuwa da zaiyi dake karya yake yi"
Hawaye ma'u ta share sannan tace toh yanzun yaya za,ayi?
Karki sake kimai biyayya, duk abin da kika lura baya so shi zakiyi, karkiji tsoron sa ko kadan, na kula dan zafin kai ne, inaga yin hakan zai tunzura shi ya sake ki, sannan kiyi kokari ki binciko min sunan unguwan, tare da no wayar Jamal"
Amsawa tayi cike da kwarin guiwa, dahaka ta kashe wayar badan tagaji dajin muryan deeni ba"
Wanke fuskanta tayi sannan ta fito, babuwa adakin dan haka ta nufi falo"
Fuskan momy dauke da murmushi take kallon ma'u, cike da kulawa tace, daman yanzun zan sa Nafisa ta kiraki, dan mijiki ya shigo tun d'azun"
Daramm taji gaban ta ya fadi, sabo da yadda momy takira Jamal da sunan mijinta"