Showing 81001 words to 84000 words out of 95354 words

Chapter 28 - BUGUN ZUCIYA Hausa Novels Complete by Fadila Lamido.txt

29 Oct 2025

491

Hularshi yacire ya aje agefe, sannan ya kalli Momy"

Kauda idonta tayi tare da fadin ya me jikin?

Yaji sauki, ya farka tunda rana, sai dai har yanzun kuka yake yi, kuma ya fada ma abinda ke damun sa yaki fada"

Shiru daddy yayi momy ma mikewa tayi tafara hada kayanta"

Muryan daddy taji yace......


Zauna mana akwai mgnr da zamuyi"

Cikin sauri momy ta aje kayan ta koma ta zauna"

Gyaran murya daddy yayi sannan yace......


Inason ki saurareni da kyau kuma ki fahimceni"


Wani irin kallo momy tamai sannan tace inajin ka"

Akan mgnr shamsudeen ne, nasani kin san cewa asma'u itace yariyar da shamsudeeni ke matukar so"

Cikin ido momy takalli daddy tace....

Ina jinka"


Cigaba daddy yayi da fadin dan haka nake ganin mezai hana shi Jamal ya hakura ya saketa.......


Mikewa momy tayi da sauri tare da fadin Alhaji kasan abin da kake fada kuwa, Asma'u fah matar Jamal ce, kuma ciki gareta, tayaya za'ace ya saketa shamsu ya aura, antaba haka"

Dakewa daddy yayi tare da fadin idan ma ba'ataba za'a fara akan su, dan hakan ne kadai mafita idan ba hakaba za'a iya rasa shamsundeen"

Alhaji wannan mgnr bazai yiwuba sam, dan Jamal nason matar shi, tunda nake da Jamal banta tunanin zaiso wani abuba kamar yadda yake son matar shi"

Gutun murmushi yayi sannan yace nidai abinda nake so dake kiyi addu'a Allah yasa hakan shine mafi alheri"

Nifah alhaji sam ban amince ba, kama aje wanan zancen wlh bazai taba yiyuwa ba"

Daure fuska daddy yayi sannan yace....


Karki nemi yin jayayya dani, daga ke har Jamal akarkashina kuke, babu wadda ya isa nace ga abinda zaiyi yacemin ba haka ba, Jamal dana ne be isa yayi jayayya dani ba"

Mikewa momy tayi tare da ficewa tana fadin wannan ai zalinci ne"

Girgiza kai daddy yayi sannan ya mike ya nufi dakin Jamal"

Gaisar dashi Jamal yayi sannan ya tambaye shi jikin shi"

Shiru dakin yayi zuwa can daddy yace......

Jamal nazo ne muyi wata mgn, kasan cewa dan uwanka yana asibiti ko?

Eh Jamal ya fada ahankali"

Toh abinda nake so dakai, akoda yaushe mutum ya zama me karban kaddara yadda tazo mai, wani alfarma nakeson kamin"

Tashi jamal yayi ya zauna tare da jingina bayanshi da bango"

Daddy yaciga da cewa nasan kana son dan uwanka, dan haka inason ka tausaya masa ka duba halin da yake ciki, ka sakar masa asma'u bayan ta haihu shi ya aureta"

Wani irin firgita Jamal yayi tare da sauke ida nuwan shi akan daddy hannu Yasa ya mustsuke ido sannan yace daddy kaine ko mafarki nake"?

Ba mafarki bane Jamal zahiri ne, inason shamsu yaji daddi rayuwa bana so rayuwar shi ta kare ahaka, rayuwar shi abaibai take"

Jim, Jamal yayi sannan yace daddy ai wannan ba kaddarata bace tashi ce, shiya kamata ya karbeta bani ba"

Cikin ido daddy ya kalli Jamal sannan yace nasan haka Jamal amman ai lalurace ta kawo haka"

Shiru dakin yayi Jamal ji yake kaman anamai daka akirji, daddy ne yagaji da shirun yace.....

Jamal inasauraron ka"

Murya kasa kasa yace banzan iyaba daddy, dan Allah kayi hakuri"

Cikin fusata daddy yace nina rokeka alfarma kace min bazaka iyaba, to bari kaji wannan karon umarni zan baka, kafin nan da wayewar gari ka rubuta ma Asma'u sake"

Afusace ya Mike ya fita, wani irin zugi zuciyar jamal kemai tare da tukukin baccin rai wacce irin rayuwa ce wannan yaushe daddy ya sauya hali da zai zabi deeni akaina"

Inason asma'u banga dalilin dazan saketaba, zanyi koma menene dan nakare martaban aurena, shi wanene dabazaiyi hakuri da kandara ba

Irin tunanin da Jamal ya kwana yi kenan washegari dasafe daddy ya sake duruwa dakin"

Jamal naganin shi gabashi ya fadi, hannu ya mika mishi tare da fadin bani"

Sunkuyar dakai yayi batare dayace komai ba"

Cikin fada daddy yace karka maidani dan iska kanaji ko?

Wani irin mummunan tashin hankali Jamal yaji, tunda yake betaba jayayya da iyayenshi ba, kuma baya so ya fara, aman bazai iya aiwatar da abin da daddy yake soba"

Ahankali Jamal yace daddy dan Allah kayi hakuri wlh baxan iyaba, ba nason jayayya dakai, dan gaskiya inason asma'u bazan iya rabuwa da itaba......







Heart Beat
*Mmn Yazeed*
[24/01, 11:04 a.m.] β€ͺ+234 906 689 6652‬: πŸ’—πŸ’πŸ’πŸ’—
​*BUGUN ZUCIYA*​
( ​Heartbeat​)

πŸ’“πŸ’πŸ’—
πŸ’—

πŸ’“πŸ’πŸ’—
​By​
πŸ’—
​​*Fadeela Lamido*




*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATION🀝*
​




*Masoya BUGUN ZUCIYA kuyi hakuri plsπŸ™πŸ»πŸ™ˆ abubuwa ne sukamin yawa, naso yau nabaku mamaki amman nakasa, gobe insha Allahu page 2 ko 3 zan turo, nagama typing editing ne ya rage, wadan da sukamin mgn ban amsa ba kuyi hakuri plsπŸ™πŸ» sakon ne yamin yawa*




1⃣0⃣3⃣





Indan katafi ka barni zan shiga wani hali bansan inda Zanyi ba"

Husna kiyi hakuri, nima bansan inda zani ba, kinga bekamata na dauki da karamin ciki inkaiki inda xaki wahala ba"

Cikin kuka tace nidai wlh xan bika, duk Inda ka zauna nima zan iya zama, wlh yaya karka tafi ka barni"

OK toh shikenan daina kuka, maza Ki share hawayen ki kuma ki saki ranki"

Make kafada tayi kamar tana gaban Sa, sannan tace a'a saika min alkawarin bazaka gudu ka barni ba"

Namiki husna, ki shirya yau dinnan inanan tafe, amman karki gayawa kowa"

Dahaka sukayi sallama, jikin ma'u sanyi ya kara haka ta takure guri daya taita kuka"

Jamal ko yana gama waya da ma'u ya tashi ya dingisa, mahimman abubuwan shi ya hada guri daya sannan ya sauya kaya"

Awaya ya kira drive bayan ya shigo yace ya dauki jakar yasa amota gashi nan zuwa"

Drive ya fita babu dadewa Jamal ya fito, babu kowa afalon dan haka har ya fita babu wadda ya ganshi"

Hanya suka dauka acikin su babu me cewa kala, yamma likis suka isa Kano"

Sauka Jamal yayi ya nufi cikin gidan cike da zumudin son ganin ma'u

Salama yayi abakin falon, daga ciki mama ta amsa"

Ma'u tunda taji muryan Jamal ta mike tare da ajiyan zuciya"

Cikin ladabi ya shiga falon yana dingisawa tare da sunkuyar da kanahi kasa"

Mama naganin Jamal tace ah'ah Jamal kai da kanka ka kwaso hanya kana fama da kafar ka"

Shafo keyarsa yayi tare da satan kallon ma'u yana murmushi"

Itako ma'u tsaye tai ta kasa cewa komai, kallon Jamal kawai take tare sonjinta jikin shi"

Bayan sun gaisa mama ta shiga kitchen sannan ta kira ma'u"

Bin bayanta yayi da kallo tare da hadiye miyau"

Zuwa can ta dawo dauke da kayan marmari ta aje gaban shi"

Tana kokarin ajewa ya rike hannunta tare da kokarin dagota"

Kan cinyar shi yaso zaunar da ita ta cije tare da fadin ciyon ka fah?

Gefe ya nuna mata tare da fadin daga nan zaki zauna"

Zama tayi sannan ya hada hancin shi da tana tare da fadin kince zaki bini ko?

Kai kawai ta daga almar eh"

Cikin sauri ya wawuro bakinta, nisa yayi sannan ya fara shafa jikinta"

Ummi ce ta sawo kai bakinta dauke da sallama, cikin sauri ta juya tun batakai ga karasawa ba"

Hakan yayi daidai lokacin da suke kokarin rabuwa da juna"

Ganin mama tajuya ya tabbatar musu ta gansu dan haka takaici yasa ma'u ta fara kuka"

Jamal ma kunya ta kamashi, amman fuskan sa na dauke da murmushi yake kallon ma'u, zuwa can yace......

Ke dai kuka be miki wuya, yanzun dan Allah meye abin kuka?

Cikin kukan tace mama fa ta ganmu"

Toh menene husna?, nifa mijin Ki ne bare kice za'amiki fada, dallah ni tashi ki dauko gyalen ki, sai kice ma mama zaki rakani naganu Firdausi"

Wlh yaya bazan iya ba, ni yanzun kunyan hada ido da mama zanji"

Mikewa jamal yayi tare da fadin toh shike nan, ni bari na wuce, dan bani da lokaci'

Rikeshi tayi da sauri, tare da fadin to yaya ai kai ya kamata ka gaya mata"

Shiru yayi yana kallon ta zuwa can yace....

Ok toh yanzun abin da za'yi, kije ki Debi kayan ki kadan kisa amota"

Yana tsaye harta dawo sannan ya matsa kofar mama yace.....


Mama zantafi"

Fuskarta dauki da fara'a tace yau yau din nan ai na dauka kwana zakayi"

Cikin jin kunya yace a'a yau zantafi nazo ganin Firdausi ne"

Murmushi kawai mama tayi dan haka jamal ya sake cewa......

Zamuje da Husna ne ta raka ne"

Adawo lfy Jamal kaida matar ka"

Dan sosa keya yayi sannan yajuya ya kalli ma'u yace dauko gyale"

Basu wani zauna agidan usman ba suka fito bayan Jamal ya gama tofawa yariyar addu'oi"

Tasha Jamal yasa drive yakai su sannan suka sauka tare da kayan su"

Gargadi yawa drive sosai cewa duk wadda ya taban baye shi yace kano ya kawo shi, daganan karya kara komai"

Saida drive ya wuce sannan suka hau motan sokwato"

Drop suka dauka dan haka karfe 10 da wasu mintoci suka shiga cikin garin sokwato, lokacin har Bacci ya kwashe ma'u tana manne ajikin Jamal"

Har suka isa kofar gidan da Jamal yama drive izinin shiga, ma'u bata tashi ba, kallonta Jamal yayi, bacci take kuma dagani tanajin dadin macci"

Kallonta yake vabu kyaukyautawa muryan drive yaje yace oga nagama sauke kayan"

Azabure jamal ya kalleshi sannan yace......

Toh kashi kuma madam tana bacci ni kuma inada matsalan kafa bazan iya daukanta ba"

Cikin sauri drive yace oga tashinta zakayi ai"

A'a bazan tasheta ba, hukuri zakayi har ta tashi ko wani abu ne saina kara maka, dan babu kyau mutum yana bacci atasheshi"

Shiru drive ban yayi acikin zuciyar yace......


Lallai wannan ba karamin so yakewa matar nan tashe ba, ni ina ruwana indai za'abani kudi, Allah yasa ma karka tashi sai gobe"


Jamal babu abinda yake banda kallon ma'u, tun da yake betaba tsayawa ya kallita hankalin shi kwance kamar yau ba"

Tayaya daddy zaice saina sakeki, bayan na farajin dadin aurena, tayaya hakan zai kasan ce, Addu'a yayi azuciyar shi Allah yasa abba ya fahimci gaskiya"

Ma'u ce ta bude idonta tare da fadin nifa nagaji har yanzun bamu kawo ba"

Munkawo husna cewa nayi bazan tasheki ba sai kin gama baccin"

Wani irin kallo tamai tare da mamakin jamal, kwallah taji ya cika mata ido, Ashe Jamal zaisota haka?, lallai ta yadda kiyayya na komawa soyya"

Waigawa tayi ta kalli gidan tare da zare ido, barikine irin na sojuji, ko ina sojujin ne ke zurga zurga, suna fitowa daga cikin motar wani ya taho ya sarawa Jamal sannan ya mika masa key"

Ma'u na manne jikin shi ya bude kofar suka shiga"

Falo ne madaidaici me dauke da daki daya tak da bayi aciki, daga can gefe kuma akwai madaidaicin kitchen"

Bayan ya zaunar da ma'u yace ina zuwa bari nayi sallah ke kuma kibari ki huta"

Kallon shi kawai tayi yana fitowa toilet din ta shege, dan haka tare suka yi sallah"

Bayan sun idar yace bari naje na samo mana abinci"

Be dadeba ya dawo bayan sunci sunsha, ma'u ta fara hamma "

Kallonta Jamal yayi tare da fadin tashi kije Ki kwanta"

Hawa gadon tayi sannan ta kalli shi yana zaune akasa ya mike kafafuwan shi tace......

Yaya gidan nan fah ya mana kadan, yazun kai a inazaka kwanta?

Ban gane a ina zan kwanta ba?

Jan bargo tayi ta rufe idobta sannan tace naga gado daya ne, kai kuma mace bata hawa gadon ka"

Take sanda ya fada mgr ya dawo mai, dan haka yayi dariya sannan yace.....

Ke bakya mantuwa ne?

Bata sake cewa kalla ba ta rufe idotan tai shiru"

Tanajin shi ya mike ya sauya kaya, sannan yahau gadon tare da yaye bargon ya shiga, zuwa can ya mika hannun sa ya rungumota jikin shi"

*Abuja*



Bayan tafiyan jamal, zuwan momy dakin uku bata ganshi ba, lekawa waje tayi nanna megadin yake shaida mata Jamal ya fita tare da drive"

Momy bata tsorata ba, saida taga drive ya dawo babu Jamal"

Tambayan shi tayi ina jamal, kamar yadda Jamal ya fada mai haka ya fada"

Acikin zuciyarta tace wai meyasa Jamal bejin mgn, wannan kafar tashi so yake ta rube, idan ba hakaba me zai kaishi kano"

Da daddare daddy suka dawo tare da deeni da alhaji bashir harda ummi"

Rike daddy yake da deeni yana mai sannu"

Bayan sun zauna momy ta kawo musu abinci"

Daker deeni yaci kadan kallon shi momy tayi taga ya rame"

Shima daddy kallon Sa yayi sannan ya mike cikin sauri ya nufi dakin da Jamal yake"

Alhaji Momy ta kirashi, sannan tace......

Jamal baya nan"

Bayanan?, ina yaje?

Kwashe yadda sukayi da drive tayi ta gayamai"

Shiru daddy yayi na wani lokaci, sannan yace"

Ni Jamal zai watsawa kasa a ido?, shi kenan nasan abin da yake nufi, wayar sa ya dauka ya kira abba"

Bayan sungaisa yace Jamal yazo"

Daga can Abba yace........

Eh haka na samu lbr ance yazo amman ni bangansa ba"

Asma'u fah ?, tananan agida, koya dauketa ne?

Eh mamanta tace sun fita tare, kasan yaran zamani, ita maman tasu dai yace mata gidan usman zasu"

Wani zancen daddy ya dauko sannan sukayi sallama"

Koda ya kashe Wayar alhaji bashir ya kallah cikin tsananin bacin rai yace......

Wlh zan nunawa Jamal nina haifeshi be isa yaja dani ba"

Meyayi ne haka da zafi?, cewar alhaji bashir"

Umarni nabashi shine bazaibiba, yaje ya dauki asma'u ya tafi da ita"

Cikin rashin fahimta alhaji bashir yace.....

Ban game umarni ba?, kuma inda yake kwance beda lfy kamata yayi atausaya masa"

Cikin ido daddy ya kalli alhaji bashir sannan yace.....

Yanzun kaman Jamal bazaiji tausayin d'an uwansa ba, ni dashi nagaya mai halin da shamsu yake ciki, yau zan gaya muku abin da nake ganin shamsu be gaya mukuba, Asma'u yariyar da deeni ke tsananin so itace asma'u matar da Jamal ke aure"

Alhaji bashir da ummi mikewa sukayi ummi harda gutun hawayenta"

Daddy yaci gaba da cewa ganin inda shamsu ke tsananin sonta yasa nace ma Jamal ya saketa bayan ta haihu shamsu ya aura, bantaba ba Jamal Umar yaki biba sai akan mace?

Komawa alhaji bashir yayi ya zauna sannan yace sai kamai uzuri, kaida kanka ka fada wannan ne na farko, kuma aikai ka nemi yama tawaye, tayaya mutum na zaune lfy da matarsa acemai ya saka wani ya aura"

Shiko deeni wani irin kallo yakewa daddy mekama dana Allah ya kiyaye"

Fada daddy yaita yi tare da yin fushi me tsanani da Jamal"

Itama momy hankalinta tashi yayi, ina Jamal zaikai ma'u tana cikin yanayi irin na laulayi, shikuma yana faman dingisa kafa, yaya za'ayi wannan zaman gashi ta kula jamal yacika fitana, baya duba yanayin jikin shi"

Kuka take sosai deeni na kallonta juyawa yayi ya kalli daddy yaga shi sai fada yake, har zuciyan shi so yake d'an shi yasaki mata shi ya aura"

Tunawa yayi da lokacin da alhaji vashir yace idan ansami mutumin daya aura asma'u zai kashe konawa ne dan ya saketa"

Wannan nanufin baba bashir besan kowaba sai ni kenan, daman haka sukemin tun ina Karami abin da nake so shi suke min"

Sun kuyar dakai yayi sannan yace....

Toh shi daddy be kyaunar jamal ne? Nasha jin daddy nawa Jamal fada kota waya ne, niko basu min fada har gara ummi takanyi wani lokaci"

Ahankali deeni yaketa babbacewa tsakanin shi da jamal akwai babbaci, dakanshi ya hango ashe ma idan ka samu wadda zai tsaya ya maka fada kai dan gata ne"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login