Showing 39001 words to 42000 words out of 95354 words
Chapter 14 - BUGUN ZUCIYA Hausa Novels Complete by Fadila Lamido.txt
gobe babu tsoho babu Yaro shara ne kawai"
Hannu tasa ta rufe mai baki sannan tace, bazaka iyaba deeni, kasan dawa za'amin aure ?
Gargiza kai yayi tare da kura mata ido"
Jamal, tafada tana share hawaye"
Wata irin muguwar dariya yayi sannan yace, jamal"?
Eh Jamal, ka kwatar da hankalin ka, bazan taba zama da jamal ba, na yake shawara adaren da aka kaini aranan zan kasheshi, karkace zaka dauki wani bataki, ka bari harsai nakasa"
A'a asma'u bazaki iya ba, insha Allahu bazakije kidan saba, ke macece bawani karfi gareki ba, ni kuma *na dad'e ina dama furata bazan so wani ya shanye min ba,* abin da yafi kawai kije gida da asuba kisan yadda zakiyi ki fito zanzo na daukeki mugudu"
Shiru tayi zuwa can tace......
Deeni wacce fura ce wannan?
Kau da idon shi yaye gafe, tare da fadin bazaki gane ba"
Cikin sauri tace nagane deeni, ummi na nan ne ?
Daker iya cewa taje anso min magani"
Shiru ta sake yi zuwa can ta kalle shi tace toh me zai hana kashanye furan taka yanzun"ππΌ
Heart Beat
*Mmn Yazeed*
[24/01, 11:04 a.m.] βͺ+234 906 689 6652β¬: ππππ
β*BUGUN ZUCIYA*β
( βHeartbeatβ)
πππ
π
πππ
βByβ
π
ββ*Fadeela Lamido*
*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATIONπ€*
β
Dedicatedππ»
*Firdausi Sodangi*π
4β£4β£to4β£6β£
πππ
Da saurin shi ya mika hannun shi kan kafadan ta, ido ya zoba mata, itama kallon shi take cikin ido"
Sun kwashi tsoyon lokaci ahaka, zuwa can ya sake shigota"
Asma'u nasha kika ce?
Kai ta gyada masa sannan tace indai hakan zaisa ka yadda dani.....
Bata gama rufe baki ba, ya rarumo bakinta, sunbatan ta yake kaman zai cinye ta"
Sun dauki tsayon lokaci haka, deeni duk ya fita ahaiyacin shi"
Acikin wannan hali ummi ta riske su, babu abin da take ban da salati"
Cikin sauri ma'u taja jikinta, deeni ko ya kasa sakinta sai kara binta yake yana rokota"
Hannu ummi tasa ta rike ma'u, tare da fadin ke asma'u meya fito dake da tsohon daren nan"
Ma'u bata iya cewa komai ba, kanta ta sunkuyar akasa"
Kanta ta maida kan deeni daya rike hannun ma'u daya da kyau"
Ta dade tana kallon cikin idon shi sannan tace, auta haka mukayi dakai"
Jan ma'u ya fara, yana kokarin shiga dakinsa da ita, batare dayace wa ummi komai ba"
Dan haka ummi tabi su, fadin take kai auta kana hauka be?, saketa mana"
Ummi ina zuwa mana, akwai sakon da zan bata"
Runtse ido tayi tana fadin bana so auta, kasake yariyan muta ne, ta wuce gida karka jawo mana abin mgn"
Daramm gaban ma'u ya fadi, muryan Abba taji yana mata Yawo aka, lokacin da yake cewa.... da kijwo mana abin mgn gara namiki aure, cikin sauri ta zame hannunta ta fara kokarin tafiya"
Binta deeni yayi ya sake jawo hannun ta, sannan ya matsa daf da ita, hannu yasa aljihu ya ciro wata yar karamar wuka acikin dan gidanta, ya mika mata, cikin rada yace ki rike wannan koda anyi nasaran kaiki gidan wannan danta shegiyan, inason ta zama filonki, ma'ana akarkashin filonki, kara cije baki yayi, ya dage shi sama, sannan yace, daya neme karban wani abu awajen ki, ki kaddamar mass"
Kuma kisan yadda zakiyi kifito daga gidan tun kafin akiran asuba"
Idan ban ganki ba zansan baki zamu daman fitowa bane, kuma washeri za'a daura miki aure, idan haka ta faru Asma'u, banason ki wuce kwana 3 banji lbrn mutuwan Jamal ba, idan kuma kin kasa kina da no zamuyi waya"
Kuskus sukai mgnr dan haka babu mejinsu"
Ummi ce tarako asma,u, tame cigaba da mata fadan ditowa da daddare"
Tana isa kofar gidan ta cire takalminta ta rike ahannu, bakinta dauke da addu,ai"
Allah ya tai make ta me gadin benan, hakane ya bata daman shiga gidan cikin sauki"
Harta shiga bayi tai wanka ta fito tai sallah babu wadda ya nemeta"
Dan haka tai zaune ta fara aikin nata wato kuka"
Hayaniyan mutane taketaji cikin raha suna wasa da dariya, azuiyarta tace dafa haka kawai ne da yanzun ina cikin su ina kasan dariya"
Zuwa can tafarajin ana cewa wai ina amaryan ne ya kamata asata alallai dare nayi"
Cikin sauri ta juya ta haye gado ta kudunne kanta"
Wata kanwar mama ce ta shigo ta yaye bargon ta fesheta da turare, sannan ta rangada guda"
Ba ma'u kadai cikinta ya karta ba harda na jamal, jin wannan gud'a ya tabbatar mai auren nan babu fashi"
Dare ya tsala kowa yayi shirin bacci amman banda ma'u, zau ne tayi ta rafka uban dagumi"
Da misalin karfe 4:30am ta fara jin wani dan siririn fito, haka ya tabbatar mata deeni ne, dan haka tafara kokari meman yadda zatayi ta fice"
Waigawa tayi ta kalli Anty fa'iza dake kwance akan gadonta, tare da yariyar kanwar mama Khadija, bacci su suke kashir ban, dan haka ta mike, daman hijjabin ta, na jikinta ahankali ta bude kofofin tayi waje, a harabaan gidan taji gabanta na faduwa dalilin tunawa datayi, ai get din kwado ake samishi yanzun yaya kenan?, dan dakatawa tayi, zuwa can Wata zuciyar tace mata maza kisan duk yadda zakiyi kibar gidan nan, idan ba haka ba gobe Aure za,amiki da jamal"
Guiwanta taji ya kara kwari dan tana ganin duk duniya babu wadda yakaita tsanan jamal"
Karasawa tayi bakin get din, abin da yayi matukar bata mamaki, abude gidan yake, ahankali ta bude karamar kofan ta fita"
Cikin Sauri deeni ya karasu ya riketa da duk hannun wanshi guda biyu ido ya zuba mata zuwa can yace muje ko?
Jikinta taji yayi sanyi ko wani hali Abba da mama zasu shiga idan suka wayi gari basu ganta ba, amman kuma bazata iya tsayawa ba, haka kurum ahadata da Jamal, dan haka ta gyada masa kai, tafiya suka fara amman ma'u saitaji kaman anfito daga cikin gidan"
Waigawa tayi ta kalli get din, bataga komai ba, saboda duhu, dan haka ta juya sukaci haba da tafiya"
Sunyi kaman taku 5 sukaga andallare su da filan mota mai tsananin haske"
Gaba dayan su suka juya, ganin Abba tsaye abun yayi matukar razanata ahankali ta zame kasa tare da daura hannuwan ta aka, tana fadi na shiga uku na"
Deeni ko fadi yake tashi muje asma,u karki yadda suyi nasara akan mu bazan iya rayuwa babu ke ba, kinsa ni ina tsananin sonki"
Karasuwa Abba yayi cikin tsananin tashin hankali yace"
Asma'u tashi Ki bishi, ai bansan cewa ni ban isa dake ba sai yau, dan haka bazan hanaki Ki bishi ba, amman kisani idan kika Saka kafa kika wuce nan wajen Allah ya isa takanina dake, sai yanzun nake dana sanin saka miki sunan mahaifiyata danayi, baki cancanci sunan nan ba"
Deeni ne ya karkace baki shi sama sanan yace toh saika goge sunan, maza sa ruwa ka goge sunan sunan tsuhuwar taka"
Zare ido ma'u tayi abba ko kokarin karasawa gaban deeni yake, saida yaje dafda shi sannan ya bigi karjin deeni tare da fadin zakamin rashin kunya ne ai daman na sani kai d'in fitsararre ne"
Murmushi deeni yayi sannan ya kalli ma'u yace tashi muje"
Kuje Abba ya fada yana nunawa ma'u hanya tare da fadin tarihi ne zai maimaita kan shi, kallon deeni yayi cikin ido, sannan ya cigaba da cewa haka ubanka yayi Wa uwarka"
Dan zaro ido deeni yayi tare da zuba su akan abba"
Dan haka Abba yace, eh kaje ka tambayi uwarka saratu, ta gaya maka yadda tayi ta zame ka"
Runtse ido deeni yayi tare da dunkule hannuwa"
Abba ko juyawa yayi ya nufi gida, yana kaiwa saitin motan yace"
Jamal sakko ka rufemin gidana"
Ganin haka yasa ma'u ta mike tabi bayan abba aguje yana Saka kafa acikin gidan tana saka tata, kafafuwan shi ta rike tana kuka take fadin Abba ka yafe min"
Hannu Yasa ya begeta tare da fadin na tsane Ki asma'u kin siremi, kwata2 Allah yacire min ke azuciya ta, tashi ki bani guri bana son ganin ki"
Yana mgnr ne hannun shi dafe da kirjin shi"
Muryan Jamal taji yana cewa, yi hakuri abba, ka yafe mata"
Jamal baka ganin inda take neman tozarta ni bataga darajata ba bare da tausaya min, duk irin adalcin dana mata arayuwa, wlh 'ya'ya mata fitina ne, sun azaftar dani"
Cikin sanyin jiki Jamal yace abba hakuri zaka yi jarabawa ce"
Juyawa Abba yayi ya shige gida batare da yace komai ba"
Dan haka Jamal ya juya ya kalli ma'u yace"
Ke kuma tashi kiban guri tunkafin na hadaki da bango"
Bata bari ya rufe baki ba, tamiki da sauri ta shige gida".
*****
Deeni tsayawa yayi kaman gunki, mgnr abba ce ke mishi yawo akai, *kaje ka tambayi uwarka saratu, ta gaya maka yadda tayi ta same ka*"
Jijiyon kan shi ne suka fito rudu rudu, idon shi yayi jawur kaman gar washi, acikin wannan halin ya isa gida, lokacin anfara kiran assalatu"
A kitchen yaji motsin ummi dan haka ya manne ajikin bango"
Besan abun da zaiyi ba damuwan ta mishi yawa, zuwa can ummi ta fito dauke da butu ahannun ta"
Ganin deeni tsaye jikin kofa yasa ta fadin Auta menene haka? Karka yadda son asma'u yasa ka zama rago, dan naga yana shirin zauta ka"
Ummi inason nasan yadda kikayi kika same ni"
Dafa kirji ummi tayi tare da fadin kaman ya?, ban gane ba?
Ummi inason nasani wanene ubana, kuma yaya akayi aka same ni?
Ajiye butan ummi tayi, cikin faduwan gaba ta matsa daf dashi tace"
Auta wani yace maka baka da baba ne?, ai kai kasan uban ka, ahannun shi ka taso"
Kara kankance wa idon deeni yayi, tare da fadin ummi ki fadamin kawai, kar kice zaki boye min wani abu, nafara mugun tunani akan ki, mahaifin asma'u yace nazo na tambaye ki yadda kikayi kika same in"
Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, zamewa tayi ta zauna akasa duk da cewa garin akwai sanyi amman ummi zafi takeji"
Idon ummi gulu2 tace auta tashi muyi sallan saina kaya maka"
Bazanyi ba yaseeen, idan kikaga nabar nan nasan matsaya ta"
Binshi da kallo ummi tayi, tare dajin nadaama irin wacce bata taba ji ba"
Tana matsanancin kuka tace"
Auta akwai kuskuren babban Dana ai kata abaya"
Nakasan ce ni daya iyayrna suka haifa, dan Haka na tashi cikin gata, duk da cewa iyayena bawani karfi garesu ba"
Mahaifina yana kokarin bani tarbiya daidai gwargwado harnakai munzalin Aure"
Dan haka yamin baiko da yakubu Dan kanin sa, ana saura wata 2 aurena da ya kubu, wani bakon matashin saurayi ya sauka agidan mu"
Ina daki naji baba na ya shigo dashi yana cewa ummata ga boko nan munyi, matafiye ne, yana neman masauki daga garin baguma can wani kyauye kafin akai Niger"
Da hannu 2 mahaifiyata ta karbe shi"
Baya Wata 1 shakuwa me karfi ta shiga tsakani na dashi, har takai idan yakubu yazu banason zuwa wajen shi"
Dan haka yakubu ya farajin haushin bashir"
Dahaka soyya me karfi ta kama mu nida bashir wato mahaifin ka"
Shirye shiryen baki naga anatayi agidan mu, dan kaha naje nasamu baba, nace mishi nifah yanzun bashir nake so"
Nuna min yayi baxai yuyo ba, dan yariga yaba yakubu ni, tun ina karama, sannan yakara da cewa ban da abinki saratu, shi bashir ina mukasan asalin shi, bako ne fah?
Haka na dage nifa bashir nake so, har ana saura kwana 3 ban daina cewa inason bashir ba"
Bashirma kullum kara huremin kunne yake tare damin wasu abubuwa wadda basu dace ba, ana jibi bikina mahaifina yazo ya samemu cikin irin wannan hali, ranshi ya baci sosai dan haka ya kori bashir"
Nikuma yayi fushi dani"
Da misalin karfe 8:00 na daren ranan maman yakubu ta shigo da gudu tace ga yakubu can duk an yanke shi"
Dan haka duk suka bita aka barni ni kaidai agidan"
Bayan fitan su babu dadewa bashir ya shigo arude hado kayan ki muje"
Bayiwa bashir musuba na hada kayana nabi bashi"
Wanan tafiya tawa ita ta haddasar da halin da mike ciki ayanzun"
Natafi batare da sanin halin da iyena zasu shiga ba"
Bayan mun isa garin baguma tun kafin mu isa gidan su bashir, nafara ganin al'dar su tasha babban da tamu, kusan kowa ka gani da makami ahannun shi, muna isa kofar gidan bashir yaja ya tsaya tare da kallo na, sannan yace"
Idan muka shiga gida zance ke matata ce, dan haka duk irin tanbayan da za'a miki kar bari musaba baki"
Bayan mun shiga gidan sun karbeni hannu biyu, koda suka tanbaye shi ni, cewa yayi matar sa ce ni"
Daki aka bamu ni da bashir, cikin kankanin lokaci Akasamu cikin ka"π
Sai alokacin nafara tunanin halin da iyaye na suke ciki, amman bashir akulum lallashi na yake, tare da bani duk wani abu da nake so"
Dan haka na acire Kowa azuciyata naci gaba da zama harna haife ka"
Sosai Bashir da mahaifin sa suke nuna maka kyauna basu barin kowa ya dake ka, koda nikai nace"
Tun kana dan shekara goma kakanka ke tafiya farauta dakai, bashir ko akulum cikin koya maka fada yake, dan haka na matsa asaka amakaranta, bayan ka fara zuwa makaranta saina kula bakason karatu ko kaje makarantar ma, daga ace kayi fada da wannan, sai ace kayi da wancan"
Idan ankawo karanka gida kuwa, bashir dariya yake tare da cewa, shi yasan danshi jarumi ne, idan kuna iyawa kuje kurama ma dan Ku"
Komai girman Mutun baya kada ka afada, idai da wuka ne saidai ayanke juna, akarshe kuma kaine me nasara"
Duk abinda kayi daidai ne awajan bashir, nikaina bani da bakin mgn"
Har zuwa lokacin da kacika shekara 25, lokacin ne duk ka addabi mutanen garin"
Nasan yana nan a idon ka, baka manta ba, kuma alukacin ne aka nemin baban ka aka rasa, wanda hakan yayi sanadiyan dawowan mu nan"
Kuka deeni Yake sosai, take yaji ya tsani ummi, yana kukan yake fadin gsky kuncuce ni Ashe duk abinda ya faru dani kune sila, ku kuka jefani cikin halin da nake ciki, Ashe shiyasa danaje daukan Asma'u mu gudu abbanta yace tarihi zai maimaita kanshi?
Tuni idon ummi suka kankance saboda tsabar kuka, auta karka sake ka raba asma'u da gidan iyayenta, dan shine abun daya zama min babban kuskure arayuwa ta, naiwa iyayena laifi babba, lokacin dana dawo na neme gafaran su, akace min shekaran su 2 da rasuwa, sai filin gidan gashi kana gani, da hannuta take nunamai tsakar gidan da suke zaune aciki, tare da kara rushewa da kuka"
Shima deeni kai ya hade da guiwa yayi kuka me isar Sa"
Rawan sanyi ummi ta fara deeni na kallo amman saboda tsabar jin zafita daya ke, yaki kulata"
Zuwacan ya miki tsaye ya daga kanshi kasama tare da karkace baki, dan ya riga ya zaman mai jiki, guri daya ya kurawa ido sannan yace"
Na rantse da sarkin dake busan numfashi saina auri Asma'u, babu uban da zambarwa, inanan inakan bakata, ko ana muxuru ana shaho saita dawo gareni"
****
Ma'u ko sanda ta shiga gida samu tayi kowa yana tsaye duk suntashi, kallonta kowa keyi dan haka ta gane sunji abin da yake faruwa"
Koda ta shiga daki babu wadda ya biyuta, har misalin 12 na rana tana kwance"
Haniyan mutanen da taji ya kara yawa haka ya tabbatar mata zancen auren nanan babu fashi"
Zuwa can ta farajin karan motoci, mikewa tayi ta kama labulen window ta leka"
Manyan mutane taga suna futowa mahaifin Jamal kawai ta shaida"
Komawa tayi ta zauna ta daura tagumi, zuwacan ta sakejin wasu motocin nashigowa tare da hayaniya"
Agogo ta kallah 2:30pm arikice ta miki afili tace yanzun dan Allah har