Showing 9001 words to 12000 words out of 95354 words

Chapter 4 - BUGUN ZUCIYA Hausa Novels Complete by Fadila Lamido.txt

29 Oct 2025

501

toh kayi hakuri kaji?

Idonshi ya dago ya daura akan na mahaifiyar shi sannan yace ummi ba abinda tamin, kawai naga tsohunta bashi sonta ne"

Hmmm auta kataba ganin Mutun ya haifi da yace baya so?, yanzun dai sauketa sai muyi mgn"

Ummi da inason ne nasata akatifa tayi bacci"

Sai wannan lokacin ma'u ta samu bakin mgn cikin kuka tace wlh ni banajin bacci mkrnt zani"

Sai kinyi bacci wannan dole ne"

Daker da sidin goshi deeni ya sauke ma'u amman duk da haka hannunta na cikin nashi"

Kujera ummi ta aje guda 2, kan daya ya zaunar da ma,u sannan yaja dayan ya zauna, cikin Wata irin murya yace ummi kawo mata kokona tasha dan da ganinta bata karya ba"

Zare ido ma'u tayi domin ita bata iya shan kokoba baya ga hakama ai makaranta zata, gashi lokaci na kurewa, hawaye kawai taji yana zobo bata acikin zuciyarta tace meyasa ban kyauce ma hanyar da zamu hadu da deeni ba? Waini me yake shirin faruwa dani?, Allah ina rokonka karkasa nazama sanadin BUGAWAR ZUCIYAN Abbana"

Daidai lokacin ummi ta ajiye babban kofi cike da koko, sannan ta mikawa ma'u ludayi"

Girgiza kai tayi tare da fadin ummi wlh ni akoshi nake nakarya kafin na fito, mikewa ta fara sannan ta sake cewa inason zan wuce mkrnt dan abbana bayanson ina tsayawa ko ina"

Fincikota deeni yayi ya maidata kan kujera sannan ya dauki kofin kokon Yasa ludayi ya deba ya nufi bakinta, yace bude"

Girgiza kai tayi sannan tayi raurau da ido tace nifa wlh akoshe nake"

kibude nace ko dan ni babu ruwana da koshin ki"

Babu yadda ta iya dole ta bude baki deeni yaita dura mata koko tasha kusan rabi amai ya kece mata, daga deeni har ummi suna tsaye akanta hartayi ta gama"

Deeni na rike da hannun asmau yana mata sannu, kan kujerar ya maidata sannan ya dauki ragowan kokon nan yacigaba da bata"

Tanashan kokon tana kuka samuda tsabar bakin ciki"

Duk abinda suke ummin deeni dake wanke2 agefe tana satan kallon su, ganin inda ma,u take hawaye yasata fadin haba auta ka kyale yariyar nan haka indai baso kake ta amaye yanhajinta ba"

Ummi nifa so nake nakoya mata sha saboda gaba"

Hmmm auta Allah ya shiryamin kai"

Saida tashanye kokon tas sannan ya juya yace ummi sammana goro"

Kallon shi tayi sannan tayi murmushi, mikewa tayi ta nufi daki tana kara binshi da kallo"

Zuwacan ta dawo dauke da roban da take jika goro ta ajiye agaban su"

Hannu deeni ya saka ya zabe fararen ciki ya mikawa asmau haka taita karba tanaci badan ranta naso ba"

Ummice ta gama wanke2 tamike ta dauki kayan zatakai kitchen kallonta ne yakai kan deeni daketa dirkawa ma'u goro tace"

Kai jama'a auta waikai meyasa baka da kan gado ne, ya zaka dauki goro kaita dirkawa yar mutane, kai komai bakayin shi ahankali saidai da karfin tsiya, kitchen ta shige tana cigaba da korafi"

Mayar da goron dake hannun shi yayi cikin ruwan sannan ya juya ya kalleta yace toh yanzun inna zan rakaki makaranta ko gida?

Ahankali tace karfe nawa ne yanzun?

11:15am ya fada yana kallon cikin idonta"

😳 Nashiga uku ni gida zani"

Daidai lokacin ummi tayi kiran deeni, dan haka ya mike yana fadin barin dawo"

Asmau bayan shi tabi da kallo tana ganin shiganshi ta ta mike ta kwashe takalminta ahannu ta fara ta fiya cikin sanda"

Ahankali ta bude kofar gidan ta fallah aguje"

Karan kofar gidan ne ya fito da ummi da deeni daga cikin kitchen din"

Ahanzar ce ya nufi kofar gida, hango ma,u yayi tana falla uban gudu dan haka abin yai matukar bashi dariya"

Dariya yake sosai besan cewa yayi nisa adariyar ba saida yaji muryuyin yan mkrntr su ma,u , cikin sauri ya murtuke fuska sannan ya nufi gida"

Kujerar da ma,u ta tashi yaje ya zauna sannan ya dauke alaiyahun da ummi take tsinkewa ya fara tayata"

Dagowa tayi fuskarta dauke da murmushi tace"

Auta wannan yariyar a ina ka samota?

murmushi yayi kadan sannan yace nan nake ganinta idan zata mkrnt"

Itama murmushi tayi tana kallo cikin idon deeni sannan tace auta da alama dai ka fada soyayya"

Murmushi yayi kadan sannan ya dan basar yace a'a ummi"

Fuskanta kara fadada tayi da murmushi tare da kara kallon cikin idonshi tace toh idan warin ya bunkasa ai zamuji, amman dai akwai shawaran da zan baka"

Kai ya daga ya kalleta sannan yace inajin ki ummi"

Auta ba atura soyayya da karfin tsiya, ita mace yar lallashi ce, idan har kana son tasoka toh ka daina ta kura mata in banda karfin hali irin naka da baka son azauna lfy ya zaka takura yariya dole saita sha koko"

Ummi jinayi kawai inason tasha"

Toh daga yau idan ka bata wani abu tace bataci karka matsa mata"

Zan bari ummi amman ni basonta nake ba, kawai jarumtar ta ke burge ni"

Hmmm kawai ummi tace sannan taci gaba da kallon sa"


Itako ma,u saida ta ganta aharaban gidan su ta tsaya tsayawa tayi numfashin ta ya dawo daidai sannan ta shiga gida"

Ranan wuni ma,u tayi tana tunanin duna, ita dai batasan abinda ke damunta ba hakanan takeson ganin sa, duk da cewa yau ya firgita ta besa taji tana kinsa ba"

Shima deeni adaren ranan be runtsaba tunu ma,u kawai yake yana kyalkyata dariya hakika dabi'unta na matukar birgeshi, kosawa yayi gari ya waye haka ya kwaanaa babu bacci"

Washegari ma,u ta shirya zuwa makaranta kamar yadda ta saba, dakin mama ta nufa ta duba bata ciki dan haka ta nufi dakin abba"

Atsorace take dan tunda abin ya faru abba baya amsa gaisuwanta"

Tsugunawa tayi sannan ta gaida su babu laifi yau abba ya amsa gaisuwanta cikin sakin fuska, sallama ta musu tana kokarin mikewa abba ya dakatar da ita"

Hannu ya mika mata dan haka ta matsa ta mika nata"

Ahankali yace mamana idan na tambaye ki zaki gayamin gskiya?

Eh ta fada jikinta asanyaye"

Asmau ni mahaifin kine karkice zaki boye min wani abu, kinason namiki aure yauzun?

Zaro ido tayi😳 tare da fadin aure abba ai nayi kankanta kuma ma ai duk acikin kawaye na babu wacce akama aure"

Bakiyi kankanta ba mamana, dan da ace kin jawomin abin mgn gara namiki aure, nasan kina da lbrn abin da ya faru da yar uwar ki, banason makamancin hakan ya faru akanki"

Wasa ma,u ta farayi da zuben dake hannunta, hawaye na zuba aidonta tace"

Abba dan Allah karkamin aure wlh ni bana kula kowa, Abba nifa ko saurayi bani dashi kum.....

Abba ne ya dakatar da ita da fadin ya isa mamana, nikaina inason ace kinyi sauka sannan namiki aure, Amman al' amarinki ya fara bani tsoro"

Rushewa ta karayi da kuka tana fadin nashiga uku abba ka yadda dani wlh wlh bana sauraran Kowa....


Dakatar da ita abban ya sakeyi akaro na biyu sannan yace naji na amince dake amman inason kimin alkawarin rike mutuncin ki amatsayin ki na 'ya mace, karki yadda wani ya keta miki hijjabin ki, idan kikamin haka kin gama min komai duniya da lahira"

Nayi alkarin abba"

Murmushi abba yayi sanna ya sake cewa mamana duk lokacin da kikaji kinason aure ki sana da mahaifiyar ki ko Dada, nikuma in Allah ya yarda acikin satin zanmiki aure"

Dahaka ma,u tayi sallama da iyenta ta nufi makaranta, ko ahanya hawaye be daina zubo mata ba ba komai ke firgitataba sai furucin abba wai zai mata aure, tunda take bata taba kawo tunanin wani aure, kallo jikinta tayi sanna tace ko kallon namiji bazan kara ba, balle ace za,amin aure"

Yau ma'u canza hanya tayi ta lungun nan taabi dan ma karta hadu da deeni"

Koda ta isa makarata batada walwala kaman da , baayan antashi ma ta lungun ta saake bi, dan haaka yau basu ahadu da duna ba"

Tundaaga ranan ma'u takebin logu har satin ya kare"


Abangaren deeni kuwa. Kullum yana zamaan jiiran wucewa asmau amman har satin ya wuce babu itaa dan haka ya fara tsinta kanshi ciki damuwa"

Yau ta kama asabar tun safe ummi kejiran fitowa deeni amman shiru dan haka ta nufi dakin"

Tura kofar take tana fadin auta wai kwana 2 meke damunka ne? Nifa kwana 2 naga ko mgn bakaso"

Hangoshi tayi nannade abargo dan haka ta tsaya sororo zuwa can tace auta ban saba ganin ka cikin wannan halin ba, tunda kazo duniya nasan jarumi na Haifa, dafashi tayi sannan ta sake cewa auta nasan kaiba rago bane gayamin meke damun ka?

Tashi yayi ya zauna ya jingina bayanshi da jikin bango, sannan ya rufe ido"

Girgizashi ummi tayi tare da fadin auta yazun ni har kana da wani sirri daza boyemin?

Bude idon shi yayi dasuka rune suka zama jawur yace ummi yariyar nan ce yau sati 1 kenan ban ganta ba"

Kwashewa ummi tayi da dariya daman tuni ta dagoshi cikin dariya tace au daman saboda asmau kayi yajin cin abinci? lallai auta kana da aiki, toh meya hana ka kabita gidan su?

Cikin kosawa yace toni nasan gidan su ne??


Kallon shi ummi tayi sannan ta kauda kai, damuwa tagani karara a idon shi , tunani ta shiga yi wacce hanya zatabi ta gano ainihin abinda ke damun sa"

Bakin katifan ta zauna sannan ta jawoshi jikinta ta kwatar"

Hannu ta tura cikin gashin kansa tana shafawa take fadin auta ka daina boye min, nariga na fahimci son Asmau kakeyi, mu aje wannan agefe yanzun Meye yake damun ka har ka kasa dannewa?

Ajiyan zuciya ya sauke sannan yace ummi tunani nake ko wanne hali yariyar take ciki, dan naga alaman ba'asonta agidan su, ranan gabana wata munafukar kakata ta mareta, kuma ranan da nashigo da ita gidan nan wani yayanta ya daketa duk ya lalata mata fiska, ranan naso nasa *Caka* ya kawomin *Duna* ya bashi misali, amman sainaga yariyar ta tsorata tana zubar da hawayenta"

Nisawa yayi sannan ya kalli ummi data dukar da kanta kasa yace ummi kinajina narantse da sarkin dake busan numfashi duk wadda ya kara daura hannun shi akan yariyar nan da sunan duka ko mace ko namiji ko yaro ko babba ko tsoho ko tsohuwa kai gemunshi najan kasa ne saidai uwassa ta haifi wani, kai inbansa *Duna* yamin dambu da namansa ba shege nake"

Mikewa ummi tayi ciki matsanancin tashin hankali tabbas duk abinda ya fada zai iya aikatawa, amman wani hali zasu shiga idan ya aikata irin wanna aiki acikin wannan uguwar da mutanan cikinsa ke kemar dabi,un autan ta"

Kulum mutanen cikin unguwan kuka suke da halinshi wasuma cewa suke karya bata musu tarbiyan yara"

Wannan tunani yasata fadin haba auta ai idan kayi haka ita Asmaun taka bazata soba, banda abinka kuma kana son yariya kuma ka daki yayanta? Ko kana son su hanaka aurenta ne?

Hmmm Ummi kina nufin ko yariyar nasona yan uwata zasu iya hani aurenta?

Kwarai kuwa auta kasan mutanen garin nan sunsha babban da mutanen garin *Jaguma*"

Murmushi yayi Me kama da yake sannan yace ummi ashe za,a zubda *Jini*, be jira me zata ce ba ya mike ya fice"

Itama ummi jiki babu kwari ta fito ta kama aikace aikacenta"


Yauma kamar kullum 11:30am aka tashi su ma,u amakaranta, ita da zainab suka jera, ta lungu sukabi jefijefi suna taba hira har suka iso gida"

Aharabar gidan taga motan yaya usman saida gabanta ya fadi dan dama can bashiri sukeyi ba"

Tanashiga ta wuce dakinta saidai ko adakinta tanajin sautin muryan shi dan shi baya mgn ahankali muryan nan kamar ana buka ganga"

Kosawa tayi ya gama abinda yake ya wuce dan hankalinta ya kasa kwanciya"

Kwanciya tayi gefen gadonta ko kayan makarantan ta kasa cirewa saboda tsabar tsoron yaya usman datake, bacci ne ya fara dibanta acikin baccin taji muryan yaya usman yana kwala mata kira"

Asittin tamike ta nufi dakin mama tana matsa ido"

Atsaye ta samu yaya usman cikin kakin sojuji da alma tafiya yake shirinyi"

Ke dan ubanki kin dawo makarata bazakizo kice kin dawoba zaki wuce daki ki kwanta?

Kwalkwal tayi da ido kaman zatayi kuka"

Jin shiru yasa yasake cewa shegiya makaryaciya dallah zoki kwashe ledojin nan ki kaisu kitchen"

Jikinta har rawa yake wajan daukan ledan, bata san cewa ledan da nauyiba saida ta aje a kitchen taji hannuta ya rike"

Guri ta samu ta zauna saida taji tashin motar shi ta miki tana kokarin fita sukaci karo da mama"

Murmushi mama ta mata sannan tace Asmau je kicire kayan makarantar kizo kitayani aiki"

Mama aiki kuma, bayan naga goggo tani ta gama girkin"

Eh wannan na yayanki ne ya kawo amai zaiyi baki"

Baki? toh mama matarsa fah?

Akaikaice mama ta kalleta sannan tace idan bazakiyi ba ki bari"

Daki ta wuce ta canza kaya sannan ta koma kitchen ta samu mama da goggo tani sun kacame da aiki, itama wani aikin ta kama nan danan sukaci rabin aikin"

Mama na tsaye tana karasa soyan kaji asmau ta matso tace mama kawo na karasa, cikin sauri ta mikamata ta matsa gurin tani, zuwa can asmau tace caf mama bakin na yaya harsu nawa ne dazai basu wannan uban naman?

Oh asmau, ni dai mutun daya yace min, yanata min kwatancen shima bangane shi ba, sunan da naji yana kiran shi *MANGA* yasa na gane mahaifinshi *Alhaji Buba Manga* mutumin babaku ne sosai kafin ya koma Abuja"

Shima Soja ne?

Eh mama ta bata amsa cikin kosawa

Toh wai meyasa bekaima momy shi ta dafamai ba?

Dariya mama tayi sannan tace aikinsan hajiya amina bazata shiga kitchen ba, masu aiki zataba, shikuma kisanshi da iyayi"

Dakuma shegen fadinrai ta fada azuciyarta, take zacen deeni ya fado mata wai saiyaci uwar yaya usman, tunawa tayi da yadda yake ciccijewa yana karkata hanci da baki sainaci uwassa!! kyalkyalewa tayi da dariya dan tayi nisa atunani tama manta ba ita kadai bace agurin"

Dariya take babu kaukautawa ta kurawa guri daya ido"

Daga mama har tani mikewa sukayi suna binta da kallo, afirgece mamata tace ke asmau menene haka?

Batasan sunayiba kuma har yanzun dariyar take, takawa mama tayi da sauri ta girgizata cikin sauri ma,u ta hadiye dariyarta"

Asmau kinyi gamo ne? Cewar mama tana zare ido"

a,a mama wani abu na tuna jaye hannuta tayi tare da fadin barin nayi sallah na tafi makaranta"

Tundaga lokacin jikin mama ya mutu murus har lokacin da mau taxo mata sallama xata wuce"

Ahanyama babu abinda take sai tunanin deeni dan haka yau tanajin bata iya hakuri idan bata ganshi ba"

Bata biyawa zainab ba dan yau bazatabi ta lungu ba"

Sai dai har takai kofar gidansu deeni bata ganshii ba dan haka wata zuciyar tace kii shiga gidan mana"

Takawa tayi ahankali harta isa kofar gidan idonta tasa asakon kofar ta leka babu kowa sai ummi datai zaune kan kujera ta rafka tagumi"

Gabantane
yayi mugun faduwa sakamakon jin kokan katan kare abayanta, afirgice ta juyo sukai ido 4 da karan, baki ne mummuna bashi da kyan fasali ko kadan"

Tsugawa taga karan yayi zuwa can ya dago da karfii kaman zai yago mata fuska ganin haka ma,u ta saka uhu tare da neman hanyan guduwa"

Duk inda tabi shima be yake tare da kokarin yago hajjabinta ganin haka mau ta cire hijjabin tayi titi aguje"

Jitayi anjawota atsorace ta waigo deeni ne tsaye, gawani mutun mummuna agefen shi bayanta ta waiga ta hango karan aguje dauke da hijjabinta a bakin shi"

Ai batasan lokacin da ta kadandane deeni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login