Showing 1 words to 3000 words out of 95354 words

Chapter 1 - BUGUN ZUCIYA Hausa Novels Complete by Fadila Lamido.txt

29 Oct 2025

479

[24/01, 11:03 a.m.] β€ͺ+234 906 689 6652‬: πŸ’—πŸ’πŸ’πŸ’—
*BUGUN ZUCIYA*
( _Heartbeat_)

πŸ’“πŸ’πŸ’—
πŸ’—

πŸ’“πŸ’πŸ’—
*By*
πŸ’—
_*Fadeela Lamido*_


1⃣ to 3⃣


*Dasunan Allah Mai Rahama maijin kyai*




πŸ“™ Dada! Dada!! Wata matashiyar yariya ce ke rangadawa tsohuwar kakanta kira"

Fitowa tsohowar tayi tana kokarin gyara daurin zaninta take fadin, nashige su nikam wannan irin kira haka?"

Turbune fuska yariyar tayi lokacin da sukayi ido biyu da kakar tata tana fadin ayya dada danma kinsamu ina murnan ganinki shine zakice wani kin shigesu?, juyawa tayi da nufin komawa, cikin sauri dada ta jawota cikin fara'a tace dawo2 ai ban dauki murya ba, maraba lale lale takwara, karashewa tayi tare da jawota jikinta ta rungume"

Daidai lokacin wani farin dattiju ya shigo tare da sallama, yana ganin su haka yasaki murmushi"

Cikin sauri yariyar ta kwace daga rukon dada ta nufi cikin dakin, tabarma ta dauko ta shinfida wa mahaifinta ya zauna tana jin sun shiga gaisawa da dada ta koma dakin dada"

Gyarawa tashigayi duk da cewa dakin agyare yake dan dada macece me matukar tsafta, gadon ta lokuikuye yayi tsaf kaman baza ahauba sannan ta dau tsintsiya tahau shara"

Bayan ta gama ne ta dauko dan kaskon turaren wuta ta nufin dan karamin kitchen din dada dake tsakar gida"

Tagabansu dada tazo zata wuce dan haka duk suka juyo suna kallonta harta kusa isa kitchen din dada tace"

Aiko takwara bazaki samu rushi a kitchen dinnan ba, dan yanzun baban ninki sun hanani amfani da murhu"

Juyowa tayi ahankali tace to yanzun baki kunne turaran rushi kenan?

Gurin tabawa nake samowa"

Cikin rawar jiki ta nufi kofar gida tana fadin bari naje na samo"

Lokacin da dada ta komar da kallonta ga dannata gani tayi yayi shiru kanshi akasa, gyaran murya tayi sannan tace girman dan mutum babu wuya yanzun dan Allah kalli yadda takwara ta girma ko yanzun aka mata aure saita xauna"

Da sauri ya dago kai, yace dada kin sosamin inda ke min kyaikayi, hankalina ya fara tashi ayau tum muna hanya zuciyata ta fara tsinkewa"

Cikin kulawa tace kakwatar da hankalin ka insha Allahu Allah zai tsare babu abin da zai faru, kuma ma ai takwarar tawa Allahamdulillahi natse take tsaf ga kunya ga tsafta"


Hmmm dada akwai wani hali dana kula tanashi wadda har yanzun banji kowa ya furta ba, ban saniba koni kadai nake gani?

Kaga, banason jajibe2 karkace komai tunda ta gama secondary data same miji amata aure, idan ma kana da burin tayi karatu ne idan tayi aure tayishi can dakin mijinta"

Nisawa yayi daidai lokacin ta shigo da sauri tashige dakin dada cikin kankanin lokaci kamshi ya cikka gidan"

Dada ko hira sukaci gaba da danta zuwa can ya dauki mukullin motar sa dake kan tabarma yayiwa dada sallama ya fice"

Mikewa dada tayi ta nufi daki tana fadin takwara maza ki fito kutafi kisan abbanki besan jira"

Aguje ta fito ranta bace ta kalli kakar tata tace kai dada memakon kice mishi yabarni anan, ninafi son zamagurin ki kuma, shiru tayi kawai ta nufu kofa cikin zubura baki"

Binta da kallo dada tayi harta kule, sannan ta sauke idananunta tare da fadin duk sanki da gidan nan *Asma'u* dole ki hakura dan babanninki ba yadda zasuyi ba"

Ko da suka kama hanya babu abinda take banda zunbura baki, abbanta na kula da ita saidai ya dauke idon daga kallon ta dan ya fahimce manufarta"

Suna isa gida ta nufin dakin mahaifiyarta ranta bace, tare da matso hawaye"

*Ma'u* ya, kin fita da farinciki kuma kin dawo min da kuka, menene ya faru?

Turo baki ta karayi cikin kuka tace mama nifah banason gidan nan nafison gidan dada, kuma aidama keda abba kuncemin idan na kare secondary zan koma can"

Shiru mama tayi tana nazari kafin ta dago kai abba yayi sallama ya shigo ganin su haka yasashi hade fuska tare da fadin yaya ne?

Mikewa mama tayi tare da fadin alhaji ai kafi kowa sanin halinta gatanan wai ita gidan hajiya takeson zama"

Bazaiyuwu ba mamana, idan kikayi wasa konan da kofar gida zan hanaki fita, kinga yau kika dawo daga makaranta karki yadda wani abu ya hadani dake ban ce bazaki koma gurin dada ba, amman sai naga yanayin natsuwar ki, yana gama fadin haka ya fice abinsa ko waiwaye babu"

Washegari


*Asma'u* ce tsaye gaban mama cikin shirinta na tafiya islamiyya jan wando farar riga tare da jan hijjabi kudin break mama ta miko mata sannan ta mata sallam ta fice"

Gidan kawarta Zainab ta nufa cikin sauri dan karta wuce ta barta"

Tana kokarin shiga gidan zainab na fitowa cikin farin ciki suka rungumi juna cikin dauki zaina ke tambayan ta yaushe kika dawo?

Jiya abba ya dauko ni, jawo hannunta tayi tana fadin zo mutafi idan mundawo mayi hirar danni tsoron bulalan baba idi nake"

Mike layin sukayi har sun kusa isa makarantar zainab tajawo hannun *Ma'u* tanufi wani dan lungu"

Cijewa *ma'u* tayi tare da fadin me zamuyi alungu kuma?

Cikin rawar jiki tace *ma'u* taho dan Allah kinga waccen, na zaune din cen, dan daba ne idan yana zaune agurin ko maza basa wucewa, kizo mu wuce tunkan ya hangu mu"

Hannu *ma'u* ta daga ta nunashi tare da ya tsuna baki tana fadin waccen din?

Bege hannunta xainab tayi tace ke *ma'u* wlh idan yaga kina nunashi munshiga uku, gudun tsiya ne dashi kuma jikin shi duk wukake ne, ranan fa muna aji muna karatu saiga baba idi aguje, sai haki yake wai duna ne ya biyoshi"

Tintsirewa *ma'u* tayi da dariya hartana rike ciki, ganin haka yasa Zainab ta sake ta arude takoma jikin wani gida ta labe"

Tsagaitawa tayi da dariyar sannan tabi bayan zainab kallonta tayi tace gaskiya ke muguwar matsoraciya ce nikam bebani tsoro ba, dan haka wlh ta gabanshi zan wuce, ai layin bana ubanshi bane dazai hana mutane wucewa dallah fito mutafi"

Fitowa zainab tayi daga mabuyarta tana share zufah, dariya *ma'u* ta kara tutsirewa dashi sannan ta kama hannun zainab tana fadin to meyasa akecemishi *Duna* kuma gashi ba baki bane?

Oho nima haka naji anacemai *Shamsu duna* tafiya suka fara dan haka kowaccen su ta tsuke bakinta"

Lokacin dasuka isa dafdashi zainab ta sunkuyar da kanta kasa tare da sauri, itako *ma'u* kur tamai da ido tana karemai kallo,
dan haka zainab ta
Wuce tabarta agurin"

Zaune yake idon shi akasa yana wasa wuka, dogo ne kakkaura bashi da haske kuma baza akirashi baki ba, gabobinshi abon tsoro ne duk sunbi sun murmurde xaikai kimanin shekara 33 zuwa da 35, tabone ajikin shi kaca2 gani tayi yana kokarin dagowa dan haka ta fara kokarin dauke kanta dai batakai ga dauke kan nataba suyi ido 4"

Tsoro ne ya kamata sosai cikin sauri ta kalli kofar makarantar gani tayi har ankulle wani sabon tsoron ne ya sake kamata, batai aune ba saiganin *Duna* tayi agabanta"

Kerma ta fara dare da kara kallon wukar dake hannunta sai kyalli take, ahankali taxame tasa gwuiwanta akasa cikin rawan baki tace * yaya shamsuddeen inakwana?

Hadiye wulakancin daya tanazo yayi tare da tsareta da ido"

Cikin daure fuska yace mike"

Da saurinta ta mike tana kokarin wucewa"

Zonan taji ya fada dawowa tayi ta tsaya tare da runtse ido dan tunda ya matso kusa da ita tagane jikinshi abun tsoro ne gashi babu rigar kirki ajikin shi"

Ta dade ahaka ganin da tayi baya da niyan mgn yasata bude idonta, mamaki ne ya kamata dumin hangoshi tayi ya koma gurin zaman shi idon shi lumshe kaman me bacci

Aguje ta karasa makaranta jikinta sai rawa yake, abakin gert din ta tsaya ta saita kanta sannan ta karasa cikin mkrntr, office din baba idi ta kalla tare da addu'a Allah yasa baya ciki dan tana masifan tsoron dorinar shi, tsuguna wa tayi ta cire takalmanta ta fara takawa ahankali sadaf2 harta wuce office din tashege ajinsu"

Saidai duk abinda take baba idi nadaga can gefe yana kallon ta hannun shi rike da buta dan yagama alwala kenan ya mike ya hangota tana sanda"

Kai ya girgiza sannan ya shiga tunani yariyar nan batajin mgn duk da cewa mahaifinta namatukar kokari wajen bata tarbiya, dukanta yaso yi sai dai yasan halin *Asma'u* da tsoron duka dan ta makalkaleshi bawani abu bane awajenta, dan haka gara kawai ya barta"

Karfe 11:30am aka tashesu sai dai ana buga kararrawan baba idin ya aiko akira masa *ma'u*

Hankalinta be tashiba kawayenta taja su uku suka isa gurin baba idi"

Hango fuskanshi kawai sukayi su kasan lallai babu wasa dan haka duk suka doje"

Haushi sosai *ma'u* taji ahankali ta fara takawa harta isa gabanshi"

Cikin girmamawa ta gaidashi sannan ta sunkuyar da kanta kasa"

Ke *Asma'u* karfe nawa kikazo makaranta?

yau?

Kinci gidan Ku, ai Ina kallon ki sanda kikazo, meya yahana ki zowa makaranta akan lokaci?

Um um baba wlh daman yaune abban mu ya daukoni daga makaranta yanzun fah ko gida banje ba......

Sakin baki baba idi yayi yana kallota yarasa ma me zaice mata shiru yayi yana kallon kasa zuwa can ya dago yace"

*Asma'u* yau yaushe?


Alhamis"

Cikin ido baba idi ya kalleta

Ganin haka *ma'u* ta fara girgiza jiki alman tsoro, runtse ido baba idi yayi domin gani yayi kirjinta na tsalle, addi'oi neman tsari yayi sannan ya bude ido yace"

*Asma'u* ? Ki kace yau alhamis?

Shiru tayi dan haka ya girgizakai sannan yace Allah ya shirye ki"

Harta fara tafiya taji muryan shi yana cewa, ai zanga baban naki"

Tsurrr cikinta ya kada, cikin sauri ta juyo ta tsuguna tare da fadin me kace?

Jeki kawai ba dake nake ba"

Marai2 cewa tayi idonta cike da hawaye tace baba dan Allah karka gayawa abba wlh daga yau nabari"

Shiru kawai yayi yana kallonta dan becika son yin dogowar magana da itaba duk da yariya ce karama tana matukar birge shi saboda saurin kadaukan karatu da anbiya data dauke shi, kiriniyarta kawai ke hada shi da da ita domin duk fadin makaranta bawanda besan da zaman *ma'u* ba sabo da tsokanar tsiya"

Kara daure fuska yayi sannan yace naji tafi"

Jikinta asanyaye ta isa gurin kawayen ta dasukayi tsaye bakin mkrntr suna jiran ta, dan duk daliban sun wuce suka dai suka rage"

Tana shiga cikin su ta manta da zancen wani baba idi, lbrn haduwanta da *Duna* ta fara basu"

Rahama da faty ne sukaita kwasan dariya dasukaji *ma'u* ta tsugu ta gaida *Duna* itako zainab kara rudewa tayi cikin sauri ta nufa lungun da taso bi dazon tana fadin nidai saikun taho"

Basu hanataba tafiya suka fara suna cigaba da zancen *Duna*"

Rahama wai meyasa ake cemishi *Duna*?, ni naga beyi bakin da za'ace mishi haka ba, ni fuskar shi wlh kyau tamin jikinshi ne kawai yabani tsoro"

Au ke har kallon faskan tashi kikayi ni bantaba mai kallon kurullah ba dan baya son a kalleshi, amman naji mutane na cewa wai *karan* shi ne bakinkirin shiyasa ake kiransa *Shamsu duna*"

Hannun Rahama ta rike sannan tace toh wai meyasa baya son akalleshi?

Oho nima bansani ba"

Faty ce takalli *ma'u* tace kefa kin cika tambayan tsiya idan kin matso kije ki tambaye shi"

Murmushi kawai *ma'u* tayi, shiru sukayi harsuka isa gurin da ta ganshi daxun sai dai yanxun babu kowa agurin, raba ido *ma'u* tafara duk ta waiga babu alamansa, cizon yatsa tayi sannan tacigaba da tafiya

sun wuce gurin da kadan suka hango shi jingine jikin wani gida ya rufe fuskan shi da hula, da alama bacci yake"

Cikin sandan suka wuce shi, ja *ma'u* tayi da baya tare da fadin kash😬 na manta xobe na aji kuxo ku rakani na dauko"

Faty ce ta bata fuska sannan tace gsky kibari da yamma kyaduba"

Sakin hannun Rahama *ma'u* tayi sannan tace kuje sai nazo dan bazan iya zuwa gida babushi ba, abba na ne fah ya sayomin shi a Dubai"

Da haka tamusu wayo ta koma baya sai da ta bari su Rahama suka bace da ganin ta sannan ta tsuna ta debi dutsinan ta madaidaita guda 3 a hankali take takawa jikin gidan dake kallon shi ta nufa ta shige dan wani lungu dake tsakanin gidajen guda 2 ta labe, dutsen ta daya ta dauka sannan tayi saitin *Duna*






_Heartbeat_
*Mmn Yazeed*
[24/01, 11:03 a.m.] β€ͺ+234 906 689 6652‬: πŸ’—πŸ’πŸ’πŸ’—
​*BUGUN ZUCIYA*​
( ​Heartbeat​)

πŸ’“πŸ’πŸ’—
πŸ’—

πŸ’“πŸ’πŸ’—
​By​
πŸ’—
​​*Fadeela Lamido*



4⃣ to 6⃣




πŸ““ Bakaramin firgita ma'u tayi ba lokacin da taga duna ya bude hannun shi ya cabe dutsen, cikin sauri ta sunkuyar da kanta dan gudun kar ya hangota"

Shiru taji dan haka ta sake lekawa, baccinshi taga yaci gaba kamar ma bashi aka jefa ba, tintserewa ma'u tayi da dariya tare da fadin ashema magagi yake, katon banza baccin rana harda magagi, dariya ta kara sannan ta sake daukan wani ta jefa mishi"

Wannan karon ahancin shi ya sauka amman ko motsawa beyi ba"

Bakaramin dariya ma'u ke kwasa ba saida tayi me isarta sannan tace kash😬 ina ma na taho da waya dana mai photo nakaiwa su zee suga mutumin da sukejin tsoron sa ashema nauyin bacci gare sa harda su magagi"

Wani dutsen ta sake dagawa, jin kiran sallah yasata zabura ta yarda dutse ta fito cikin takun kasaita ta wuce deeni tana kwambare kafada"

Sai karfe 1:15 ma'u ta shiga gida, da fada mamata taryeta tana fadin"

Asma'u wanne irin kunne gareki dazun2 nan abban Ki yace kidaina biyawa gidan dada amman dayake kunnen ki na kashi ne saida kikaje ko?


Muryanta dauke da shagwaba tace, mama nifa bacan naje ba, tun dazun fah muna makaranta baba idi ne yasamu sharan masallaci"

Fuskan mama dauke da rashin yadda tace sharan masallaci? Tsohowa bansan karya inace maza keyi?

Tun yaushe aka daina basu, ai basu iyaba duk ranan da maxa sukayi baya sharuwa muko namu yayi kyau sosai malamai nata samana albarkan Allah ya bamu miji nagari"


'Da da mahaifi sai Allah, nan danan mama ta saki murmushi tana ameen tsohowa Allah ya mike albarka"

Cikin kunya tace amin sannan ta nufi dakinta"

Kai tsaye toilet ta shige, wanka tayi sannan ta fito rike da kayan da ta cire tana kwalah kira goggo tani2

Da saurinta ta shigo dakin tare da fadin Asmau lfy kuwa?

Kayan ta mika mata tana fadin lfy lau goggo kayan mkrnt na zaki wanke min"

Toh kuma gashi yanzun bani nake wanki ba, bala ne keyi amman bari nakai masa"

Yar karamar riga ta saka tare da siket daidai guiwar ta, fitowa tayi tana tafe tana raira karatun al Qur'ani, afalo ta samu mama, cak ta tsaya lokacin da ta hango kayan makarantar ta agefen mama"

Agogo ta daga kai ta kalla 2:10pm cikin fushi tace mama kinga goggo tani nabata kayan.....

Dakatar da ita mama tayi da fadin nina hanata takaiwa bala kayan, goggon sa'arki ce ita dazaki dinga kwala mata kira kina danga daki, saikace sabowar mejego?

Shiru tayi tana cigaba da zonburo baki"

Mama taci gaba da cewa toh maza ki dauki kayanki kije ki wanke dan goggo tunda tayi ciwon hannu abban ki ya hanata wanki, bala ne keyi,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login