Showing 24001 words to 27000 words out of 134057 words

Chapter 9 - FARRAH BOOK COMPLETE DOCUMENT BY MY SHAKUR .txt

24 Jan 2025

7513

gawani babban dutse (rock) awurin tsakiyan dajin hawa dutsen tayi sanan tashiga cikin wani lungu daga waje bazakace lungun nada fadi aciki, daga waje barama kagane lungu baneba dan yay kama da dan fashewan dutse, sai kashiga daga ciki, fadi ne dashi dayay girman daki gawani kalan sanyi ni’ima aciki, wani kofi ne mai kyau awanke awajen, tsugunnawa tayi tadauka tana murmushi sanan ta ijiye sandarta tajuya tafice, cikin tumakan ta shiga sanan ta tsugunna gaban wata saniya ta tara kofin tana tatsan nono tana murmushi, saida tagama tatsan iya nonon datakeso sannan ta mike tsaye rikeda cup din a hannu yana kallon fresh nonon dake cikin kofin, wani kalan murmushi tasaki daya bala’in karama fuskanta kyau sanan tawuce wajen dutsen tahau batare daya shiga kogon ba tazauna awaje, ijiye kofin tayi agefenta sanan taja hulan kanta ta saukarda shi abayan wuyanta sanan tasa hannu tadauki kofin takai bakinta tafara shan nonon, tanasha tana kallon yanda shanaye da tumakan ke shanawa abinsu sunacin abincin su suma, kaman daga sama taji wani kalan ihu daya bala’in firgitata saida cup din hannunta ya kibude yafadi tundaga nan sama inda take har zuwa chan kasa nonon ciki yabare akasa kofin ya fashe, bin ko’ina tashigayi da kallo bataga kowaba, duka rugarsu ita kadaine kezuwa kiwo wajen nan dan nan bangaren dajin babu kowa anrigada anfita daga karkaransu daman gudunma su Modibbo kada yasan inda take zuwa kiwo yasa batayi a rugarsu saita kawo tumakan sun fita daga gari, cikin ikon Allah kuma Allah yabata har daki awajen Wanan dan kogon nata idan tazo dazaran tagama shan nono shiga take ta narki bacci abinta bayan ta tashi takara debo nono tasha sanan da yamma sutafi gida. Babu wani kwana ko lungu da sako dabata sani ba cikin wanan dajin gabaki dayanshi, bata sabajin mutane adajin ba hakan ta firgita sosai to waye adajin nan dahar yake ihu? Kodai koma waye ke ihun maciji ne ya sareshi kokuma wani abune yafaru? Taje taduba ne? Wani kalan ajiyan zuciya tasauke tasan ba Modibbo bane dan baisan wajen nan ba, hannunta tasaka ahankali tabaya tajawo hulanta tamaida kanta tasake kulle igiyan da kyau yakama fuskanta chas, sanan ta tashi tashiga kogon sandarta tadauko tafito wanan karan bata tsaya sauka normal sauka ba wani kalan tsalle tayi tadiro tundaga kan dutsen har kasa chak, murmushi tadanyi dan ta tuna Shafa ne, Shafa tahanata tsalle tsalle da dirke dirke tacemata babu kyau mace nayi.


Ahankali tafara tafiya zuwa direction din dataji ihun wanda taji yataho daga yankin gabas din dajin, gently take tafiya babu ko alamun tsoro akan fuskanta sosai tai tafiya mai nisa bataga wanda yay ihun ba hakan yasa tace to Kodai kunneta ne kokuma kukan tsuntsune, dan tabe baki tayi ganin tayi nisa sosai da inda take tajuya tafara tafiya kaman daga sama taji magana. “Nifa nagaji Lamba tun jiya banci abinci mai kyau ba, munje rugar fulanin chan ko shaguna basu dashi, gashi Oga yahanamu mu shiga cikin city mu kashe yaron nan muhuta” jin sahun tafiya yasa dawani irin sauri Farrah takalli bishiyan dake kusada ita na mangwaro dayakeda ganye acike, hawa bishiyan tayi da bala’in sauri kada aganta abunku da yar karama bacewa tayi asaman bishiyan tai lamo tana rungume da sandarta kirjinta na bugawa dum! Dum! Dum!


Dazaran taji ana maganan kashe mutum ko kisan kai gabanta ke fara faduwa dan tanada trauma da kisankai, daidai gaban bishiyan Lamido da Lamba suka tsaya duk suna sanye da bakaken kaya hannun Lamba da bindiga yana gogewa da handkerchief yace “nima Lamido nagaji, jibi yanda bindigata tai kura ace tun shekaran jiya batasha jini ba saikace ba Lamba ba, ni wlh dama tsiyayemai duka idanun biyu kayi ba dayaba kachal, bantaba kidnapping mara dadi ba kaman wanan” dariya dukansu sukayi Lamido yace “dadin zaizo saiyafi na duka kidnapping din daka tabayi dadi aduniya” sukai wani irin dariya, Lamido yace “ni kawai so nake na nakasa yaron gabaki daya hakanan kawai na tsaneshi” dariya Lamba yayi yace “kodan kaganshi yaron kyakkywa dashi, nasan tunda kake baka taba ganin yaro namiji mai kyau kaman shi ba” hararanshi Lamido yayi yace “tsiyayemai idanu da karyashin danayi basu isheni ba, farkamai ciki nakeso nayi wlh da ask zomuje kaga” yawani ja hannun Lamba suka wuce bin hanyar dasukayi Farrah tayi da kallo gabanta nafaduwa din dim din, yanzu mutanen nan wani sukai kidnapping zasu kasheshi, yanzu yaya zatayi? Taje tafada ma kai gari? Jikinta har bari yake tana tunani taje gidan mai gari kafin ma abarta taganshi saita bata awanni akama bari ta ganshi Tayaya zatai musu bayani, yanda suke da bindigan nan kuma tasan yan garinsu da tsoro bazasu taba zuwa ba, to taje takira Shafa? Takara tambayan kanta, yanzu taje Shafa batanan ta tafi yawon ta, ihun azaban Zayn taji dayasa tawani kalan dirko daga kan bishiyan ko’ina na jikinta na rawa, takalli gabanta takalli baya tagudu ne koko taje tagani, kasa daurewa tayi tai hanyar dasu Lamba sukabi da rarrafe daga nesa ta hangosu su hudu tagani yan fashin sai wani saurayi da kallo daya tamai taji kirjinta yabuga sabida yanda fuskanshi ya kumbura suntum idanunshi daya duk jini yabata idanun arufe sai dayan yake iya budewa kadan, an daddaureshi, kallo daya tama hannunshi tagane akarye sabida yanda yake lilo.




Ahankali Zayn yana kallon pure water shi natun jiya yace “ru……ru…wa” dariya dukansu hudun sukayi Lamido yace “Oga yaji wuya wai zaisha ruwan” dariya duk sukayi Oga yace “bashi ruwan” daukan ruwan Lamido yayi sanan yataho gaban Zayn din yakai ruwan bakinshi yabude yadauko kan Zayn daya bude baki yana zazzago da harshe baida burin daya wuce yaji ruwan nan abakinshi, pure water Lamido yakai kaman zai samai abaki Zayn yataho da sauri Lamido yawani buga ledan pure water ruwan tafashe kan Zayn yace “kamutu da kishi” hawaye Farrah taji yazo mata a idanu sosai dawani irin sauri tajuya tana rarrafe saida tai nisa da wajen sanan ta mike tsaye ta kwasa da gudu cikin one minute takai wajen tumakan ta, wani kalan bari jikinta yashigayi tana shaking tana tafiya tana zagaye tarasa mema zatayi kaman daga sama takai hannunta gefen zaninta goran turaren yajin da Shafa tamata taji, cirowa tayi tai wani kalan murmushi dudda gabanta na faduwa, rikewa tayi a hannunta gam sanan tashiga hada shanayen da tumakan zuwa direction din gaban, sanan cikin wani kalan sauri da karfi tashiga dukansu hakan yasa suka wani haukace suka kwasa da gudu ji kake dim dim din kaman saukan aradu yanda suke gudu haka itama yake gudu gasu da yawa saida sukakai ta saitin hanyar dasu Lamba suke ita tai kwana danta bullo ta baya sukuma su bullo ta gaba.




Kaman daga sama duk suna tsaye suka shigajin alamun gudu kasa na amsawa, dasauri Oga yace “kunji abinda nakeji miye ke sauti kaman gudun mutane, haka? Jeku dub……” kafin yakarasa maganan wasu bijiman sanaye da raguwa da bazasu iya gane iya adaddinsu ba sun shigo wajen da gudu uwa ana korasu, wata saniya taci karo da Lamido ta watsar dashi, gabaki daya sakasu a tsakiya shanayen sukayi sun cika wajen tas sukuma duk sun firgita abunku da criminals kowa na ciro bindigarshi yana setawa.


Ganin haka yasa Farrah tafito daga inda take leke dan ita tazagayo tabaya ne tazo gaban Zayn da shanu ya kare da gudunta, baima lurada ita ba ko kadan sabida wahalan dayake ciki hannun mutum kawai yaji an daura akan kafadarshi daga tabayanshi dayaji wani kalan sanyi ya shigeshi saikace hannun kankara dasauri yadago kanshi da idonshi kwara daya dayake iya kallon mutane dashi daya kankance Ya daurashi kan Farrah, cute little farin index finger dinta Farrah tadaura kan pink lips dinta alamun yay shiru, bama ta tsaya kallonshi ba tasa hannunta da bala’in sauri tashiga warware mai kullin da akayi a hannunshi Zayn nawani irin kallonta da ido daya tazare igiyan hannun ta yar, sanan tashiga kwance na kafan nashi da bala’in sauri kafin kidnappers din su juyo suganta, tundaga kan hulan kiwon dake kanta yake kallo irin na kauyen nan da akeyi da itace daya daure igiyan akasan gemunta yake kallo, zuwa gefen fuskanta da gashi ke kwance akai kaman na yar jaririya har zuwa kumatunta zuwa red dogon bead Earings dinta dake lilo a kunnenta zuwa fararen hannuwanta datake kwancemai igiyan dasu, kodan yana tsakiyan azaba ne and she appeared from nowhere but ahankali cikin muryan dashi kadai zai iya jinta yace “is she an angel?” Wani kalan fincikota akayi. “Ke Yar Fulani? Dama Kece kika cika mana wajen nan da tumakai”? Oga daya damki Farrah yafadi hankali tashe ranshi abace.






To jama’a is FARRAH going to be okay???


💫 FARRAH 💫




✍🏻M SHAKUR




EPISODE 🔟
Damke wuyan Farrah yayi ganin sotake ta taimaki wannan yaron da sukeda burin samin duniya ta sanadin sa, wani kalan jijjigata yayi yace “kinsan wanene kike shirin kwancewa ke agwai? Kinsan biliyan nawa zamu samu akan yaron chan”? Ihu Farrah tayi da kyar danji tayi kaman zata shide sabida yanda ya damke wuyanta, kokawa tashigayi tana kokarin kwace kanta amman takasa kwace kanta daga hannunshi sabida karfin dayake dashi, Zayn ta kalla da kidnappers biyu suke tsaye kanshi dayan nakokarin daukan igiyan yasake daureshi, bin dan jinin dagefen idanunshi ke fitarwa tayi dakuma karyayyen hannunshi taji wani kalan karfi da kwazo yazomata bazata bari su kashe yaron nan ba, maybe yanada iyaye yanada kannai dazasuyi tunaninshi kaman yanda kusan kullum take tunanin Yar uwanta da aka kashe agabanta, wani kalan ihu Farrah ta yanka. “Eeeeeeeeeeeeeee!” Shi kanshi Oga baisan lokacin daya saketa ba yay baya yana kokarin taushe kunnenshi dan muryanta yay wani kalan piercing dodon kunnenshi, dawani kalan sauri cikin bala’in kwazo da jarumta da ita kanta batasan tanada shi ba tajuya batai wata wata tai kan Oga dake karkade kunnenshi sabida yanda yakejin ihunta har yanzu, gabanshi tasha hakan yadago kanshi zai kalleta tai targeting kwayar idanunshi goran yajin ta danna ta fesama a fuskanshi da bala’in yawa, Ya shiga idanunshi da kyau ya shiga hancinshi atake yashaka da baki, ihun dababu shiri Oga yayi yajuya ahaukace gabaki daya yama zare danjin yajin yayi har kwakwalwa yana tattaba fuskanshi azare yace “ku kamata Lamba takasheni da yaji, wayyo idanuna” juyowa tayi da sauri jin yakira mata sauran, Lamba da dayan sukayo kanta, daganan inda take ta fesa musu dudda suna kokarin kaucewa amman saida ya shiga kwayar idanunsu da jikinsu dan har fatan wuyansu ta watsamawa sukahau ihu suma kowa yay gefe azare wato yaji bala’i ne barinma awajen maza, ganin haka yasa ta arto aguje inda Zayn yake yana kallonta kaman wanda har yanzu bai yarda cewa mutum bace, da duka karfinta takai hannuwanta takama hannunshi mai lafiyan tana ihun kokarin magana with so much force. “Ahhhhh jeh….jeh..…” tana kokarin gayamai suje da baki da hannu, da kyar Zayn ya iya tashi yana kallon yanda hannunshi ke lilo kaman ba hannunshi ba, sakin hannunshi mai lafiyan Farrah tayi tazo ta bangaren hannunshi mara lafiyan ahankali takama hannun saida Zayn ya lumshe idanu hawaye suka zubo sharrrr, daura hannun tayi akan kafadarta sanan takai hannunta daya kan waist dinshi dan yafita tsayi sosai tafara tafiya dasauri dasauri tana waigen bayan su, Oga dasu Lamba na kasa suna fama da yaji kaman wayanda jinnu yabuge, Lamido dasai yanzu ya iya tashi daga wurgan dashi da saniya tayine yashiga gyara bindigarshi da settings din ya birkice sabida barar dasu da akayi, ganin zai harbesu yasa Farrah tawani ja Zayn dawani kalan gudu shima Zayn dayaga bindiga wani kalan karfin gudu ne yaji yazo mai sukahau gudu kaman ba gobe, harbi Lamido yafara yana binsu dagudu shima cikin ikon Allah ko bullet daya bai samesu ba sabida yanda suke famfala gudu, sosai Zayn ke gudu yana kallon gefen fuskan Farrah da kusan itace jagoran gudun nasu tana zufa sosai, dan nauyin hannunshi na kanta, baitaba ganin brave yarinya karama kaman itaba tunda yake in his life, shi baimasan mata can be this brave ba sai dai a tv!




Juyawa baya Farrah tayi dan hakanan jikinta yabata wani abu, wani katon dutse Lamido ya dauka yawani jefo musu yayo saitin Zayn, cikin zafin nama tasaki hannun Zayn karyayye sanan tawani fada kirjinshi ta kankame shi tareda juyarda shi ita tadawo saitin dutsen, dutsen ya sauka akan bayanta wani kalan mugun kara tayi dan har kirjinta taji dutsen ta kankame Zayn sosai dashi kanshi saida yaji yanda dutsen ya daketa akirjinshi sanan ahankali tadago fuskanta ta kalleshi hada idanu sukayi shima kallonta yayi da idanunshi daya dayake iya amfani dashi, ahankali tasakeshi sanan yafita daga kirjinshi sanan tawani juya takalli Lamido dake tahowa yana dariya yace “Au kin tsaya kin ci saa bullets dina sun kare da wlh nai wasting rayuwanki, Shegiya akwai, sai shegen wayau uwa yar dula” dan murmushi tayi da kyar sanan ta tsugunna kasa ahankali dutsen daya jefomata ta dauka sanan ta kalleshi yana dunfaro su yana tafiya yana dan dingishi saitashi tayi tadage da duka karfinta jefamai dutsen tayi dudda yaso ya kauce amman saida dutsen ya sauka akan goshinshi haba sai jini, wani kalan tsalle Farrah tayi tareda mai gwalo dayasa Zayn yadan ware idanunshi cikeda mamaki, dan juyowa tayi takalli Zayn dake tsaye yana kallonta kaman yasami tv baki tabude kaman zatamai magana jin sahun gudu yasa duk suka kalli wajen, su Oga kezuwa but still sunada nisa hannun Zayn mara lafiyan takama suka shiga gudu daga ita har shi wanan karan yamafi na dazu, sunyi gudu nakusan 10min sanan suka kai wajen wani rami da bishiyoyi suka kare bazaka taba sani da rami a wajen ba, tsayawa gaban ramin tayi tana haki sosai sanan tasaki Zayn tanunamai ramin da hannu alamun ya shiga, ramin ya kalla sanan yakalleta dan bola nema cikin ramin, sake nunamai tayi tana kallon bayansu dan yanzun nan su Oga zasu cimmusu ganin inda take kallo shima baison akamasu yasa yashiga ya tsugunna yana taushe hanci amai na tasomai, juyawa tayi da sauri ganin ya shiga ciki zuwa gaban wani bishiyan mangwaro duk Zayn na kallonta wani kalan tsalle tayi tahau bishiyan sanan ta karyo babban reshe dakeda ganyayyaki da mangwaro nunannu ajikinsu, da wasu different itace sanan ta dirko kasa ta taho da gudu fadawa cikin ramin tayi daidai su Oga sun karaso wajajen ahankali tasa reshen tarufe saman ramin dasuke ciki, ganyayyakin suka rufesu sanan ahankali tajuyo takalli fuskan Zayn dake kallonta, hannunta ahankali takai tadaura kan lips dinta alamun yay shiru, samin kanshi yayi da gyadamata kai ahankali kaman wani obedient child, sanan takalli hannunshi dataga yadaura hannunshi mai lafiya akai yarike kana gani kasan hannun azaba yakemai, ijiye itacen data karyo daga bishiyan tayi akan jikinta sanan takai hannayenta ta kwance igiyan hulanta tacire hulan shima ta ijiye akasa, ahankali tasaka hannunta tazame dan kwalin atamapan dake kanta wani kalan zubewa tulin churdadden gashinta yayi daba gyara abaya da Zayn yagani yana taba har kasan wajen dasuke zaune, ko kadan bata damuwa, yaga dan kwalin yaga tayi tararaba shi, sanan tadago kanta takalleshi hada idanu sukayi ahankali takalli monkey jacket din dake saman white shirt din dake jikinshi, da hannu ta nunamai monkey jacket din sanan tamai alamu yacire kallonta yayi dan baigane metake cewaba, hakan yasa ta daura hannunta kan jacket din tadan ja alamun yacire, dan yunkurowa yayi sanan yacire da kyar yabata, karba tayi sanan ta dukunkune rigan takai saman bakinshi duk yana binta da idanu, sanan takama hannunshi mai lafiya tadaura akan rigan asaman bakinshi sanan tanunamai saman ramin dakuma nunamai alamu yay shiru ma’ana kada yay ihu ya taushe bakinshi kada mutanen nan suzo sujisu, sanan ahankali yaga tasaka duka hannayenta kan hannunshi karyayye takama runtse idanunshi gam yayi koyaya aka taba hannun shi kadai yasan yanda yakeji, ahankali take taba hannun ta lumshe idanunta, ta iya gyara karaya awajen maman ta takoya, Mamanta na gyara karaya sosai kusan shine ma aikin datakeyi a birni ana biyanta tana dauri agida, ita kawai gani tayi ta iya a kauyen nan tama mutane biyu dauri kuma sun warke, gano karayan tayi hakan yasa ta bude idanunta tadauki itacen data ijiye akasa ta daura kan jikinta sanan tawani kalan murde hannunshi tahade kashin dayasa yay wani ihu bakinshi taushe gumi na ketomai tako’ina, sanan ta jera itacen tass kafin tasaka igiyoyin dan kwalinta ta daure hannun layi layi tam tam, sanan tasaki hannun nashi ahankali bude idanunshi yayi yakalleta harta dauki hulanta tana daurawa akanta tana kulle igiyan a gemunta, dayan igiyan daya rage ta dauka shi yanada fadi sanan ta kalleshi bayan tagama gyara zaman hulanta, tasowa tayi tazo da gabanshi takalleshi sanan tadaura hannunta daya kan idanumta, kafin ahankali takai igiyan tadaura ma idon mara lafiya tadaurea kullin abayan kanshi sanan takoma tazauna, wani kalan dadi yaji da idon namai kaman zai fadi yanzu saiyaji kaman abu yatare idon daga fadi, ahankali yakalli hannunshi dudda yanamai zugi sosai but he’s feeling much better kan dazu……… ”bazasu taba wuce nan wajen ba kuduba dajin nan tass, duk inda za’agan su agansu, inba hakaba saina kashe kowa na kauyen su dan nasan daga rugar fulanin chan take, itane kaje kagani jiya da daddare Lamido” dasauri Lamido yace “a’a Oga, ni wata bazawara nasamu Oga”.






This book is 500 VIP is 2k
3107021073 aisha Muhammad first bank pay and chat me up by clicking on this link;
wa.me/+2347012181461




💫 FARRAH💫






✍🏻M SHAKUR




EPISODE 1️⃣1️⃣
Cikin tsananin fushi dakuma tashin hankali Oga yace “Duk inda zaku shiga ku shiga kufito min da yaron nan, that boy life is our golden ticket to paradise” baisan ya akayi ba but jiyayi yasa hannu yakama hannun Farrah gam gam atsorace jin maganan da Oga keyi kirjinshi na bugawa dum dum dum! Ahankali Farrah takalli hannunta dataji ya kama yarike kafin gently tadago manyan idanunta takalli fuskanshi, ko kadan hankalinshi baya kanta fuskanshi na kallon sama dan asaman kansu yakejin maganansu gani yake kaman zasuyi missing step kawai su taka reshen mangwaron su fado cikin ramin dasuke su gansu su kasheshi, zufan dakebin gefen fuskanshi ta kalla dan murmushi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login