Showing 30001 words to 33000 words out of 134057 words

Chapter 11 - FARRAH BOOK COMPLETE DOCUMENT BY MY SHAKUR .txt

24 Jan 2025

7515

wani kalan mugun kwarjini yana kujeran dake bayansu, kaganshi zaka dauka wani almajiri ne, ringing da wayan Alhaji yayi yasa ya farka daga zurfin tunanin dayakeyi dasauri yadauki wayan ganin Gwamnar Adamawa ne ke kiranshi, amsa wayan yayi sanan yay murmushi yace “Alhamdulillah, thank you excellency, to to to shikenan” zare wayan yayi daga kunnenshi ya katse sanan ya kalli Uncle dake kallonshi yace “ankama daya daga cikin kidnappers din” dasauri Uncle yace “Alhamdulillahi naji dadi sosai Yaya” shiru Alhaji yayi yanadan karkada kafa yana tunani sanan yace “zan iya yafema mutum duk wani laifi dazai iyamin aduniyan nan dakake tunani amman banda laifi daya shine cutar mini da Zayn” yasakeyin shiru saikuma ya bude malummalum dinshi yadauko wani clean handkerchief yakai kan idanunshi yana share hawayen dasuke fitowa yace “inda sun kashemin Zayn da yaya zanyi da rayuwata eh” kama kafanshi Uncle yayi yace “Yaya dan Allah kadaina kuka nace kuma kadaina maganganu haka bagashi yanzu an ganshi ba” cikeda damuwa da rauni yace “inda yarinyar chan bata taimakeshi ba, da yanzu shine yake kwance a operation room rai a hannun Allah, you know something I am going to reward that girl handsomely wallahi kuwa” sanan yajuyo yakalli Malam dake dunkule waje daya sanyin AC ya isheshi yace “Malam kome kakeso kafadamini zan maka shi dan diyarku ta chanchanci sama da haka awajena mekake so kanason gida a birni”? Wani kalan washe baki malam yayi yana murmushi azuciyan shi yace “inama tamutu su biyani diyya nafi kowa kudi a kauyen mu” anatse yace “a’a Alhaji Baran iya rayuwan binni ba, kawai dai kudi nafiso na gyara gonata da sauran ayyuka” murmushi Alhaji yayi yace “tom shikenan zan saya maka gona dai dai gonaki dari a kauyen ku” wani kalan zaro idanu Malam yayi yakasa gasgasata maganan dayaji gonaki dari yajiance sanan Alhaji yace “zan kara maka da naira miliyan goma kaje kaja jari” wani kalan fadowa yayi daga kujera yay rarrafe yazo gaban su Alhaji, kwanciya yayi flat akasa yana kuka yana musu addu’a, murmushi Alhaji yayi yace “tashi kaje ka zauna” sanan yakalli Uncle yace “jeka kawo cash na 10M kabashi” dasauri Uncle yace “nadauka sai an sallami yarsu za’a bashi”, girgixamai kai Alhaji yayi yace “kawomai miliyan gomanshi a leda kabashi yazauna yana kallo shima yanajin farin cikin da sanadin diyarshi nima inajin kalan farin cikin nan yanzu ahaka. “Kaico! Wayyoo Alhaji, aradun Allah zuciyata zata buga, yau ni Malam nine mai da miliyan goma, Wayyoo Allah na” dan dariya Alhaji yayi sanan yatashi yawuce dakin da Zayn yake ciki shikuma Uncle yatashi fuuu yafice ko kallon Malam baiyiba Malam kuma sai sumbatun kudaden daya samu yake.






Yana zaune awajen Mami tafito tana sanye da kayan operation, tashi Malam yayi dasauri ganinta yace “ta mutu ne”? Turus Mami tayi tana kallonshi tambayan yamata bambaran akunne amman takakalo murmushi tace “bata mutu ba, kuma Alhamdulilah mun samu mucire kwayar bindigan nan da yan awanni zata farka zomuje kaganta” gyadama Mami kai yayi sanan tai gaba yana biye da ita abaya zuwa dakin da Farrah keciki, tana kwance kan gado da kayan operation ajikinta, kanta sanye da hulan operation, an rufamata bargo zuwa cikinta, daga wuyanta kana iya hango katon plasta da aka manna a kirjinta inda akai aikin, ga oxygen a hancinta tana fitar da numfashi tana saukewa, wani kalan bakin ciki Malam yaji daya ganta shi da yanzu zata mutu dayaji dadi daya huta daman ta zamemai nauyi aka, yanzu tamutu zai sami kudin diyyanta sanan yahuta da fitinan Inna, dan kallonshi Mami tayi itadai batasan ko kawai she’s seeing it out of paranoia bane but the man doesn’t look happy to see yarinyar tai surviving surgery, to anya ma uncle dinta ne as he claim kuwa, anatse Mami tace “kace ba kaine mahaifinta ba”? Janye idanunshi yayi daga kan Farrah cikeda kauyanci yace “eh hasalima haryau ba’asan mahaifinta ba duka kauyen mu” ahankali Mami tace “Maman ta fa kace tarasu”? Gyadama Mami kai yayi yanadan tabe baki yace “mahaifiyarta dani kadai iyayen mu suka haifa, tunda tafara fita binni tana saida nono ta lalace, hartazo tagudu muka nemeta muka rasa, rana daya kawai tazomana da durmeme ciki kauye, wai ita tai aure amman mijin ya gudu yabarta todai a kauye ta haifesu yan biyu, yan kauyen mu suka tasata agaba tai cikin shege tazo tana karya cikin sunna ne da aurenta akanta, shine ta tattara ta gudu da yaran tasake barin kauyen, bata kara dawo da yaran ba saida sukai shekaru shadaya aduniya ta dawo dasu gida tana ciwo sosai da kauye yadauka ciwon kanjamau ta kwaso ayawon Duniya shine tadawo, babu kalan kunyan duniya da uwarta bata sakani ba, Toh dai ahaka ta mutu ciwon shine ajalinta, yaran suka dawo hannuna, bata wani dade da mutuwa ba yayan wanan ma ta mutu” yanuna Farrah, ahankali Mami tace “Allah ya jikan su da rahama” hakanan taji Farrah tabata tausayi taga tabon duka daban daban ajikinta yafi akirga wanda kana gani kasan clearly is the case of child abuse amman dai tai shiru, ahankali tace “bari nadan je chan wajen su Zayn naduba shi zaka iya zama da ita, dazaran ta farka bayan kwana biyu idan taji sauki za’a maidaku” “to Hajiya angode Allah saka da Alkhairi, Allah yakara girma” fita Mami tayi security dake gaban dakin tama whispering. “I don’t trust him, keep an eye on him please” yes Ma ya amsa mata sanan tawuce.






Kujera Malam yaja ya zauna yana kallon Farrah, kaman yadauki filon nan yadanne mata fuska tamutu yahuta yakeji, yana zaune ahaka ya saka ya warware shi kadai aka bude kofan dakin, Uncle ne rikeda Leda baka wani irin tashi Malam yayi yace “wayyo Allah kudade na sunzo” kafin ma Uncle yabashi kudin ya karba yana leka ledan saikuma ya rungume kudin yana hawaye wani kallon wulakanci da raini Uncle yamai sanan yawuce yafita daga dakin yawuce dakin Zayn.




Kallon kudin Malam yayi sanan yakalli Farrah yace “tunda yanzu ga miliyan goma na a hannuna chass ni nama yafe gonaki darin na gudu abina ko, Allah yabani miliyan goma daga sama babu abinda nayi tasha kawai zani nakoma kauyen mu, Wanan kuma idan sunga dama su yardata kosu dawo da ita kauyen mu su suka sani koba hakaba” yana gama tunanin yawani mike tsaye ledan ya ijiye kan kujera yadauko bandir daya na kudi yakirga dubu goma yasa a aljihu sanan ya daure bakin ledan ya makaleta a hammata gam gam sanan yabude kofa yafice, fita yayi daga asibitin batare daya hadu dasu AlhaJji ba yana fita motan daya gani yatare yace akaishi tasha.






Imagine yourself kina kwance a comfort na bed dinki kina duba pictures and videos na hadaddun atampopi kina gamawa kawai ki zaba, place an order, make payment akawo miki har gida batare dakin fita kinje kasuwa ba.




Imagine yourself in the middle of stress da kata kata na biki but you don’t have to worry akan atampopin anko dan akwai wacce zata miki supplying nasu har gida?


Imagine yourself kina tunanin that perfect and best gift dazaki bama kawarki be it birthday gift, wedding gift, suna gift or just casual gift, and M Shakur told you Atampa ne!


Just picture it lokacin da za’a kawo miki atampan acikin wata lafiyayyen fine jaka za’a saka miki atampan akawo miki ba abakin Leda ba kaman yanda aka sabayi a kasuwa?? Sweet right?
What if M Shakur tagaya muku yau all imaginations, dreams dinan naku can become through by introducing ATAMPA REALM to you guys💃
ATAMPA REALM is an online store dake saida atampopi variety of them, daki bari, masu kyau, masu ado, wayanda ake yayi, akan kudi kuma kalilan don’t you want that??
Atampa Realm are life savers, biki, akwati, birthdays or anything they come through and represent!! Ina gayamuku atampopin su makes statement🌹


All you have to do is give them a call 📞 +2348097573597


Ga wayanda basason kira you can chat them up a WhatsApp by clicking on this link:;
wa.me/+2348097573597




You can also follow them on Instagram by clicking on this link;
https://www.instagram.com/p/CiQcu1loZ7c/?igshid=YmMyMTA2M2Y=




You can join their WhatsApp group by clicking on this link;
https://chat.whatsapp.com/CUmRWXy4evqLtOoYp3XmNt






EPISODE 1️⃣4️⃣
Sai bayan sallan isha’i Mami da Alhaji suka taho dakin da Farrah keciki, ganin babu Malam adakin yasa Alhaji yace “why is she alone ina Uncle natan yake”? Yay tambayan yana juyawa baya, bodyguard dinshi dake biyedashi yasa kiran security itakuma Mami tai gaban gadon tana duba vitals din Farrah, shigowa security yayi Alhaji yace “ina Uncle dinta yake ko yaje masallaci ne”? Girgiza kai security yayi yace “I think he left” ko ita Mami dake shirin yima Farrah allura saida takalli security dasauri tace “left kuma”? Gyadamusu kai yayi yace “after kince I should keep an eye on him daya fita nabishi, anan gaban asibiti yatare mota yace akaishi tasha” dan murmushi Alhaji yayi yakalli Mami yace “are you sure dan uwanta ne kuwa”? Gyadamai kai Mami tayi tace “eh, I think she’s a burden to them saisa daya sami kudi ya gudu, ko dazu I told the security to keep an eye on him cus I get this feeling kaman baiso tai surviving ba” girgiza kai Alhaji yayi yace “mutane kenan basusan yara rahama bane, Allah ya kyauta, how is she yanzu?” “She is fine, I will stay with her saika tafi gida da Zayn ko” gyadamata kai yayi yace “okay, I will tighten the security here no more taking chance dan kowaye keson hurting dina yanda Allah bai bashi galaba kan Zayn ba bazai taba hutawa ba sai burinshi yacika, be careful okay, if anything come up ki kirani” gyadamai kai tayi tana murmushi shima murmushi yamata sanan yawuce yafita zuwa dakin da Zayn yake, har yay wanka ya chanza kaya zuwa wasu simple top da short masu kyau farare dasuka bala’in amsanshi, yasaka wata dark blue wool hula dayama fuskanshi kyau ka kalleshi saika kara kallonshi, farin designers socks yasaka dawani vintage slippers mara hanci kana ganinshi kasan sanyi yakeji, babu abinda yasami idanunshi amman saida aka wanke idon akai plasta gobe zasu dawo abude idanun, murmushi Alhaji yayi ganinshi yanda yay kyau dudda har yanzu bai dawo daidai ba jikinshi ya bala’in nuna yaci duka sanan ya wahala, hannunshi Alhaji ya kama yace “let’s go home, but first muje kama maman ka sallama ko” cikin Wanan muryan nashi na baison yin magana yace “is she not going home da mu”? Girgizamai kai Alhaji yayi yace “nooo, Uncle na yarinyar yagudu cus I gave him 10M, kasan ur Mom is the most generous woman dana sani aduniyan nan, she offers zata zauna da yarinyar” shiru Zayn yayi bai kara cewa komiba, hannunshi Alhaji yaja yace “muje to” binshi yayi suka fara tafiya tare ahankali har sukakai dakin.




Budemusu kofa bodyguard yayi suka shiga cikin dakin daidai lokacin Farrah ta kwaye baki tafashe da kuka cikin bacci batare data bude idanunta ba, ahankali tadaga hannunta takai inda akai mata aikin aka rufe da plasta tafashe da kuka sosai cikin wani kalan siririyan murya da dakin yake echoing yana amsawa idanunta a lumshe har lokacin tana kokarin sosa wajen da aka mata aikin.




Dawani kalan sauri Mami dake zaune kan kujera ta tashi hannunta tasa da sauri tarike hannun Farrah datakai wajen tace “Allah sarki sorry, sannu kinji yafara mata zafi wajen, alluran yafara sakinta sannu karki taba” kara karfin kukanta tayi dayasa for the first time Zayn Zayn da suna shigowa dakin yanemi waje kan coach na dakin ya zauna yana danna sabuwar wayan da Baban shi ya kawomai dan dayan tabace yadago kanshi, gently kaman wanda bayaso yadaura idonshi akanta, blue operation net cap din da aka samata yadan zame baya haka ya bayyanar da dark curkudadden black hair dinta, gashin goshinta sun kwanta tass tass sunyi wani kyau, kodan sabida kalan hasken wutan dakin ne oho but wani kalan haske tayi sosai kaman baturiya idanunshi a rufe ruf amman lafiyayyun hawaye ne ke fitowa daga cikinsu bana wasa ba, wasu nabin gefe suna hanyan kunnenta wasu na gangarowa kasa, dogon hancinta har kyalli yake sabida maiko, ta tabe baki sosai irin yanda bakin mai kuka keyi, lips dinta sun tattare sun bushe sunyi pink yirrrr, baisan mesa ba tunda yake arayuwanshi baitaba jin urge na kaman yacema mutum sorry ya lallasheshi ba sai yau, kaman tausayi tabashi ne ko she looks innocent ne oho, ganin understand what exactly yakeji is hard for him yasa yadauke kanshi da sauri kaman ance yadaina kallonta yamaida hankalinshi kan sabon wayanshi yana daddannawa.






Dayan hannunta tadaga zatakai kan ciwon jin anrike hannunta tana kuka sosai Mami tasake rikewa hakan yasa da sauri Alhaji yazo gaban gadon yace “mesa takeson ta taba wajen aikin”? Murmushi Mami tayi tamikamai hannunta daya tace “tayani rike hannun nan kaga” karban hannun Alhaji yayi yarike yana kallon Mami, Mami takai hannunta kan fuskanta tashare hawayen dake gangarowa sanan ahankali kaman mai whispering tace “dazafi”? Gyadamata kai Farrah tayi ahankali still idanunta a rufe, satan kallonsu Zayn yayi saikuma yasake dauke kai, ahankali Mami tace “kin tashi”? Gyadamata kai tasakeyi kaman Yar yarinya alamun eh, murmushi Mami tayi tace “meke miki ciwo yanzu to”? Shiru tayi batace komiba cikin lallashi kaman tana magana da Yar yarinya Mami tace “fadamin sunan ki inji” shiru tayi batace komiba still. “She can’t speak” Zayn yafadi ahankali batare daya kallesu ba yana danne danne awayanshi, daga Mami har Alhaji dasauri suka yakalleshi, Alhaji yace “kaman ya she can’t speak”? Dan yatsine fuska Zayn yayi batare daya kallesu ba har lokacin yace “she is dumb Daaaad” yay maganan irin yafara gajiya da tambayan su dinnan, “kurma”? Alhaji yafadi dasauri, gyadamai kai Zayn yayi yadan kallesu yace “the girl that was with her told me she can’t speak at all” maida hannunta Mami tayi da sauri ta ijiye akan gado, sanan tajuya da sauri tafita daga dakin batare datace musu komiba, bata wani jimaba tadawo dawani torchlight karami a hannunta, fuskan Farrah ta taba ahankali tace “Farrah” dan motsi Farrah tayi, murya chan kasa Mami na shafa gefen fuskanta tace “budemin bakin ki nagani” tai maganan tana bubbuga gefen fuskanta dan har yanzu bata gama farfadowa daga alluran ba, ahankali tabude bakinta, haska bakin Mami tayi saida takoma baya hakan yasa da sauri Alhaji dake tsaye kusada ita yace “menene”? Ajiyan zuciya tasauke sanan tama Alhaji alamu da idanu yazo yagani sanan yakoma baya yace “why is her throat that black”? Maida mata bakin Mami tayi tarufe sanan cikin harshen turenci tace “this girl has been suffering, this is clearly a child abuse case, Alhaji kaga tabobin duka ajikinta kuwa? Kaga bakin nan nata garwashi aka samata awuya is not like she can’t speak, ita kanta batasan she can speak ba sabida tsoron azaban datasha lokacin da aka samata garwashin” yanda idanun Alhaji sukaija zakasan ranshi yabaci ainun, cikin fushi sosai yace “me wanan Yar karaman yarinyar tamusu daza amata irin wanan zalincin garwashin wuta a wuyan mutun? Eh? Sunsan menene y’ay’a kuwa sunsan cewa rahama ne su, why will people be so wicked and cruel, wlh wlh saina kullesu, zasu fadamin meta musu aka mata haka, let’s go Zayn” sanan yajuyo yace “make sure taji sauki kinji wife” gyadamai kai tayi sanan suka fice yarufo kofan itakuma Mami ta zauna ahankali kan kujera tai folding hannunta akirji tana kallon Farrah, batasan kodan sabida ta taimaki Zayn bane but hakanan taji she’s growing strong affection for yarinyan, ga yarinyan is so fine, very fine beautiful girl, gata Yar karama duka duka yarinyar nan bazata wuce 17/18 ba,how can you be wicked to this small girl.




Wani kalan kuka Farrah tafashe dashi sosai cikin baccin dayasa Mami takara tashi, hannayenta takama ahankali tana kiran sunanta. “Farrah, Farrah, gani nan” wani kalan yunkurowa Farrah tayi cikin bacci tawani kalan rungume Mami kamkam cikin wata kalan little voice tace “uhnnn Maa….m” wani kalan lumshe idanu Mami tayi ahankali takai hannunwanta tadaura abayanta tana bubbugawa jin takirata da Mama almost 1min sukai ahaka sanan Mami tamaidata ta kwantar da ita, murmushi tayi taja bargo tarufa mata da kyau sanan tawuce bayin dakin alwala ta daurOo tazo tasa hijabi ta shimfida dadduma tai nafila sanan ta kwanta akan lafiyayyen massaging chair dake dakin ta Minat da kafafunta.






EPISODE 1️⃣5️⃣
Wuraren 6 nasafiya tashiga bude idanunta dasuka mata nauyi sosai sunyi tsami, da kyar take budesu kafin takarasa budesu gabaki daya tanabin saman dakin datake da kallo dakeda haske mai kyau, kodai tamutu ne ta tambayi kanta tana sake kulle idanunta sanan tabudesu ahankali kaman wacce ke kokarin tantance abu, ganin still dakin take yasa ta juyarda kanta tabi ruwan da ake kara mata da kallo zuwa hannunta da ake karama ruwan, yunkurawa tayi zata tashi zaune amman takasa sabida zafin dataji agefen kirjinta batasan lokacin data saki wani malalacin kara ba. “Asshhh” dagokai Mami dake kan dadduma tana lazimi tayi ganin Farrah ta farka yasa tai murmushi, shafe addu’an datakeyi tayi sanan ta mike tsaye ta taho gaban gadon, tunda tafara tafiya tana tahowa Farrah dake kwance akan gadon ta tsare Mami da idanunta dan ganin wata faran kyakkyawan mata tayi tanada dan jiki ba yarinya bace, tanada kyau na gaske kaman wata Yar arab, gawani lafiyayyen murmushi kwance kan fuskan matan tana kallon Farrah itama hakan yasa Farrah tace “to kodai tana aljanna ne” tsayawa Mami tayi gaban gadon daidai saitin kan Farrah sanan takai yatsunta biyu tadaura kan saman goshinta tana duba temperature dinta ahankali tace “kin tashi”? gyadamata kai Farrah tayi ahankali tana kallonta still kana ganin kallon kasan kallon na wanda bata sani bane kallon sabuwan fuska, ganin yanda Farrah ke kallonta yasa Mami tai murmushi tace “zaki zauna”? Gyadamata kai Farrah tayi dasauri hakan yasa Mami ta taba wani abu gadon yadago Farrah ta zauna tana dan yatsine fuska sabida tsami da jikinta yayi, “jikin ki na ciwo”? Mami ta tambayeta ahankali, dagokai tayi ta kalli Mami batasan mesa ba samin kanta tayi da gyadamata kai ashagwabe kaman zatai kuka, murmushi Mami tayi takai hannunta guda biyu tai cupping face nata murya chan kasa tace “duk zai daina nan bada jimawa ba, yanzu zakiyi wanka saiki salla, saikici abinci saina baki magani, kinajin fitsari”? Dasauri Farrah ta gyadamata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login