Showing 3001 words to 6000 words out of 134057 words
Chapter 2 - FARRAH BOOK COMPLETE DOCUMENT BY MY SHAKUR .txt
Shafa suka juyo suna kallonshi, hannun Farrah Shafa takama ta iza kan tulun dake cikin rafin tace “rike tulun nan Kurma” sanan tamike tsaye takalli Modibbo tace “Hamma Modibbo kaga bamasan bala’i kuma bama neman fitina karabu da Farrah dan Allah, nasan sabida ita ka kafa majalisa agaban rafin nan dan kasan tana zuwa debo ruwa, inhar kanason Kurma dagaske bazaka dinga jazamata bala’i ba bayan kasan Rakiya sonka take, kumama Hamma Modibbo waye zai barka ka auri Kurma iyye, dan Allah kafita harkan yarinyar nan ka tausaya mata, ka tausayama maraicinta haka mutanen kwarai suke” tunda take maganan yake binta da kallo saida tagama yanuna kanshi cikeda isgilanci yace “wai dani kike Shafa’atu?” Kwashewa da dariya abokanen sukayi ganin rainin wayon da Modibbo yama Shafa, daya daga cikin su yace “Modibbo bakin ciki take ba ita kakeso ba kawarta kakeso” wani mugun kallo Shafa tamai shikuma Modibbo yabi ta gefen Shafan yay inda Farrah take datake kokarin daukan tulun ta daya cika da ruwa zata iza bisa ka ganinshi yasa atsorace tasaki tulun zatai baya dasauri Modibbo yasa hannu yadauki tulun yarike yana kallonta yace “zona iza miki” girgizamai kai tayi ahankali kanta akasa taki zuwa, ahankali yataka zuwa gabanta yana kallon yanda jikinta kerawa sanan yadaura mata tulun aka dawani bala’in sauri kaman mazari tajuya zata wuce yace “bansallameki ba ai” chak ta tsaya batare data juyoba, hannunshi yatura a aljihu sanan yaciro ledan biscuit na Oreo dazun nan aka kawoma Mai gari biscut din daga binni nashine amman yakici dan yabata wani murmushi yakarayi yasan zata fara sonshi dan babu wanda yataba ganin irin biscuit din akauyen nan zuwa yayi tagabanta yamika mata ledan ta kalla sanan ta girgixamai kai ahankali yace “biscuit ne daga binni ki karba kona kama hannunki nasamiki” Shafa tadan kalla kaman zata fashe da kuka ganin haka yasa cikin fushi yace “idan Shafa kesaki tai abu kotahanaki kiyi abu zansa akoresu daga garin nan” akufule Shafa na tattauna baki tace “mafashi” dasauri Farrah tamikamai hannunta jin zaisa akori su Shafa, gently yasamata biscuit din yana murmushi sosai dasauri tawuce Shafa ma ta watsama dukansu harara tawuce shikuma yabita da kallo saida suka bace sanan yakoma inda suke ya zauna yana murmushi abokanenshi sukace “wai kai mezakayi da kurman nan ga hadaddun matan kauyen nan dake mutum maka kanace ma kurman nan mara galihu” wani kalan murmushi yayi yana karban shayin da aka zubamai a kopi kaman mai tunani yace “kap matan kauyen nan babu mai baiwar da kurman nan kedashi” Muji yace “wanan gajeran gata kurma wani baiwa tafi matan garin nan dashi Haba Modibbo Kodai magani tamaka ne” murmushi yayi sosai yadan kurbi shayin sanan Ya hadiye yace “aradun Allah duka kauyen nan babu wanda yakai kurman nan kayan alatu ajiki, ahaka da wahalan da komi kaga kidirmon datake dashi kuwa balle ma nacigaba da bata dadi ina bata su kaza da biscuit’ din binni” yay dan dariya yana sake kurban shayi, tabe baki Muji yayi yace “kaima kasan kozaka mutu kanadai magajin gari baza’ataba barinka ka auri Kurman nan ba, babu wanda yasan ubanta, ance kanjamau yakashe uwarta ma, dataga tana shirin mutuwa ta tattaro da ita da yaran nata suka dawo nan kauye tazo tamutu anan” tabe baki Modibbo yayi yasake kurban shayin yajaye kofin daga bakinshi sanan yadagakai yakalli abokanan nashi daduk suke kallonshi suna jiran amsan shi dan dariya yayi yace “yo uban me kukeso nafadi muku? Kuda kunku kunsan ba aurenta zanba ai hakan yabaku amsan manufata akan kurman” wani kalan kwashewa dukansu sukayi da dariya suna tafi, Tanko yanunashi da yatsa yana kadakai yace “Modibbo, Modibbo anyi dan iska awajen nan wlh” suka kara kecewa da dariya, murmushi Modibbo yayi yace “gobe zaku kawomin ita dakina na gangare idan duhu yayi” tafi sukahau yi, Muji yace “kace kai Modibbo gobe Kwanan ango lahiya lau ne kaida Yar kurman ka” dariya Modibbo yayi yace “dasafe gobe zan kawo mata kwai da cinyan kaza da shayi, nabata dadi tabani kindirmo”.
Tofah jama’a ana wata gawata!
~Sai mun hadu mako nagaba dan jin yanda zata kaya tsakanin Modibbo da Farrah, shin Allah zai kubutar da ita daga hannun Magajin Maigari koko tana ruwa?? Kubiyoni danjin cigaban wanan kayataccen labarin na FARRAH wanda ni M Shakur ke kawo muku dahaka nace Bissalam😘~
💫FARRAH💫
✍🏻M Shakur
EPISODE 2️⃣
Wani magidancin mutum ne da akalla zaikai 59 zuwa 60 haka aduniya yana sanye da suit dark blue yana sintiri cikin wani arnen hadaden falo yana kaikawo kana ganinshi kasan akwai abinda kedamunshi, daga gefen dakin kuma wajajen kofan shigowa falon wayansu bodyguards ne suna sanye da bakaken suit da bakaken glasses a idanunsu duk suna tsaye kikam kaman sojoji kagansu zaka dauka samudawane sabida girmansu dakuma karfinsu, wayan dake hannun daya daga cikin bodyguards dinne yahau ruri hakan yasa yadaga wayan yakalla sanan yadago kanshi yakalli mutumin dake sintiri a falo daidai shima mutumin dake sintirin afalo yakallo bodyguard din yace “Alhaji ne ko”? Cikeda girmamawa yace “yes sir” hannu yamikamai yana dan sauke ijiyan zuciya yace “give me the phone”? Dasauri yataho zuwa inda yake tsaye yabashi wayan karban wayan yayi yakai kunenshi yay shiru da alamu yana sauraron abinda ake fadamai a dayan bangaren ne ajiyan zuciya yasauke yace “Yaya duk inda kace muje nan ne wajen shakatawan shi munje all of them bayanan, yanzu gamunan mun kara dawowa gidan shi, dukdai inda yaje dole agida zai kwana” shiru yasakeyi sai chan yace “eh achan bayan layin ma mukai parking, bazaima gane akwai mutane agidan ba Yaya, karka damu zamu dawo maka da Zayn Yaya, I promise I will not disappoint you” dan murmushi yayi sanan yazare wayan daga kunnenshi yabama bodyguard din sanan yajuya yadaura hannayenshi kan saman kujeran dayake tsaye gefenta yasake sauke ijiyan zuciya daga gani kasan akwai abinda kedamun shi sanan ahankali yakara mikewa tsaye yana gyara zaman agogon hannunshi this is 3:27PM, tun wuraren 8 suka duro garin nan amman basugan yaron nan ba, kaman daga sama sukaji karan gate na budewa dasauri yay wajen window dakin yanasa hannu a lips nashi yana kallon bodyguards din alamun kar wanda yay magana sanan kaman barawo yadan dage gefen labulen window kadan yana kallon tsakar gidan, dayake remote gate ne budewa katafaren gate din yayi da kanshi wata arniyan Ferrari 296 GTB ce ta danno kai cikin gidan wani irin ijiyan zuciya mutumin dake leken yasauke yace “there we go, Alhamdulillah, Allah ya jefoka finally Yaya zai barni nasha ruwa da kyau” yakara gyara tsayuwa yana leken kaman barawo, kashe motan akayi amman ba’a fitoba, girgiza kai mutumin dake leke window yayi yace “malalaci nasan gajiya yayi yanzu haka hutawa yake” yana nan yana kallon motan kusan 10min sanan aka bude kofar motar, damn! What a ride! Wato Kofar motan sama yayi da aka bude, ahankali kaman ba’aso ayi wata black beauty leg dake sanye cikin wani brown Tomford Wicklow logo suede sandals yafito, kumbunan kafan nan farare sol kaman ana gyarasu da chalk and milk tsabagen kyansu, kafafun saida sukai kusan 1min awaje sanan ahankali wani dogon cikakken lafiyayyen matashi yafito daga cikin motan yana bama window baya yana maida kofan motan yana rufewa, wani off white jacquemus Le Gelati bermuda short ne ajikinshi daya tsayamai iya guiwa, yahadata dawata AMI Paris coeur hoodie brown akai, kana ganin kayan dake jikinshi from leg to head designers ne, juyowa yayi ahankali yanadan yatsine fuska sabida ranan daya hasko fuskanshi bakinshi na tauna cingam, wani kyakkywan black beauty guy ne dakeda wasu irin jajayen lips, yanada manyan idanu dakuma dogon hanci, gashin kanshi a kwance gashin sajenshi suna shinning saidan gemun dayadan tara wanda kana kallon gemun zakasan na yan iska ne dan gefe daya baki gefe daya fari yayi dying rabin gemun, yanada cikan jiki dan full guy ne baida rama ko kadan kaganshi zaka dauka all this black American rappers ne, fuskanshi yadan shafa zuwa gemunshi dayadan ja sanan yasake yatsine fuska yafara tafiya ahankali kaman baiso yayi zuwa katafaren only flat dake durmemen gidan dakenan da Glassdoor, yana kaiwa gaban Glassdoor din password dinshi yasa sanan ahankali yatura kofan yashiga ciki chak ya tsaya yanabin mutanen dake dakin da kallo one after the other kafin idanunshi yasauka kan mutumin dake tsaye wajen window daya juyo yana kallonshi murmushi kan fuskanshi, daure fuska yayi tamau kaman baisan menene murmushi aduniya ba sanan yawuce ciki yana tafiyan nan agajiyance yacigaba da taunan cingam dinshi yay hanyar dinning, dasauri magidancin mutumin yabishi yace “Zayn yanzu Uncle dinka baida darajan gaisuwa ma a wajenka”? Kaman badashi ake magana ba kojuyowa baiyiba yakai gaban lafiyayen fridge din dake dinning mai kama da madubi, hannunshi yasa yabude fridge din yasa hannunshi zai ciro bottle water cikin wata kalan lazy voice yace “what do you want Uncle”? Yay maganan yana bude marfin goran ruwan ya tofar da cingum din bakinshi anan kasa yakafa ruwan abaki yana sha, kallonshi mutumin daya kira da Uncle yakeyi kaman yaga abin kallo saida yaga ya shanye ruwan tass ya jefar da goran da marfin duka akasa kaman wajen bola ne, goran dasu cingum din daduk yazubar akasa ne Uncle din yabi da kallo sanan yakalleshi yace “Zayn Baban ka yace nazo nataho dakai Nigeria” Dawani irin sauri yakalli Uncle din nashi fuskanshi karara yanuna bacin rai, dauke kai yayi yajuya azuciye yafice daga dinning din yace “I am not going anywhere Uncle ka kwashe yaran nan daka kawo kubarmin gida” yayi hanyar kofa zai fita da idanu Uncle yama bodyguards din alamu su tare kofa hakan yasa sukai wajen suka tare kofan dukansu su 6 din, chak ya tsaya yana kallonsu ranshi a bala’in bace hakan yasa cikeda bacin rai yawani irin juyo yakalli Uncle din nashi yanamai kallon what is all this, anatse Uncle din yace “it’s an order Zayn daga mahaifinka, bazamu taba barin garin nan ba saida kai, so get parking mu wuce” runtse idanunshi yayi da karfi sabida takaici, yanda ranshi ke tafarfasa azuciye yayi wani irin ball da flower verse din dake kan center table na falon wanda akalla kudinshi zaiyi 5Million, jikake rukukuuuu karan fashewa sanan awani irin wuce zuciye yafada kan lumtsatsen kujeran falon ya zauna jikinshi na bari sabida fushin dayake hannunshi na rawa yatura cikin aljihun hoodie dinshi wani hadaden kwali yaciro na Doubletree cigarette kaga kwalin bazaka taba sanin taba bane zaka dauka wani chocolate ne ashe taba ma akwai na yan gayu, kara daya ya zaro sanan yadauki wani very cute lighter dagakan centre table dinshi ya kunna taban yazuka yana fuzar da hayakin sanan yadauki wayanshi wani custom made iPhone 13 ne da akayishi da gold yay dialing number dayay saving da Papa, ringing daya aka daga kaman jira yake yamike tsaye cikin fushi sosai still karan taban na hannunshi yace “what is the meaning of all this Papa? Are u baby sitting me now ne or what exactly? Am I a kid nizaka aika a dauko maka tundaga Nigeria harnan Indianapolis, am I some toy to you ko ina crèche dazaka wani aika a daukoni huuun Papa”? yay maganan yana jefar da karan taban hannunshi dan bayama barinshi yay masifa da kyau, da sauri Uncle yakaraso yatake taban yana murjeta da takalmin shi kafin yaja gobara agidan, sanan yakoma inda yake tsaye yana kallon Zayn din da wayan ke kunnenshi ko kaffara bazaiyiba idan ya rantse yasan lallashinshi Yaya keyi, kaga yanda yakema mahaifinshi masifa zaka dauka dawani mate dinshi yake magana, sunkai kusan 20min suna wayan sanan yakalli Uncle din nashi ranshi abace yawani jefar da wayan tashi awulakance akasa Uncle din yabi wayan da kallo sanan kawai ya girgiza kai yaduka yadauki wayan yanabin wayan da kallo dahar ta tsage sabida yanda yajefarda ita sanan yakai wayan kunnenshi yana sauraron abinda Yayan shi kefadamai, cikeda girmamawa yace “to Yaya, In sha Allah Yaya, yanzu zamu taho Yaya, tom I promise” ya katse wayan kafin ahankali ya ijiye wayan kan kujeran kusa da Zayn din dake huci sanan yawuce stairs, wani daki yabude dazaka dauka dakin governor ne, komi a gyare akwati daya yadauko yashiga hadamai kaya wanda yasan kawai wahalar da kanshi yake dan kawai afaranta mai raine Yaya yasashi Wanan aikin dan basaka kayan zaiyiba, tass yahada kayan sanan yadauko wani Versace bargo mai bala’in laushi yarike a hannunshi yafito yakira wani bodyguard yazo yakarba yafice dashi tsakar gida wani yabiyoshi sukaje suka kwaso motocin dasukai parking chan zuwa gida aka jera komi a mota sanan suka dawo, Uncle yadubi Zayn din dake zaune inda yake akan kujeran ya kishingida da kujera ya lumshe ido yace “let’s go Zayn everything is set” dan bude idanunshi kadan yayi yakalli Uncle din nashi sanan yace “I need 5min nap” wani irin ijiyan zuciya Uncle Hali yasauke yana kallonshi kawai irin kallon nan na babu yanda ka iya da mutum, yana tsaye akanshi saida 5min din yacika daidai sanan yace “Zayn 5min yayi tashi muje dare nayi” ko motsi baiyiba kuma Sarai yasan yana jinshi hakan yasa yakalli bodyguards din yace “kuzo ku dauke shi” bude idanuwanshi yayi da sauri yamusu wani mugun kallo sanan azuciye yamike tsaye yace “duk wanda keson rasa aikin shi yau yazo yatabani yagani” sanan yawuce yafice daga dakin rai abace bodyguards din suka bishi abaya dasauri, Uncle kuma ya tsaya yakashe komi na gidan sanan yafito rikeda wani bagpack na yan tarkacen abubuwan Zayn din ya kulle dakin yawuce wani babban jeep da yasan nanne Zayn din yake ciki bodyguard yabudemai kofa yashiga yazauna kusada shi, dauke kai Zayn yayi yana kallon hanya ko kadan baiso Wanan tafiyan ba babu yanda zaiyi ne kawai he’s so hurt, cikin wani irin fushi da neman bala’i yace “where is my headphone Uncle” da sauri Uncle din yashiga bude bagpack din yace “gashinan na dauko maka cus nasan you will ask for it” yay maganan yana cirowa yana mikamai, wani irin fizgewa yayi daga hannunshi sanan yadauke kai cikin kunkuni yace “I hate this old man” sarai Uncle yajishi murmushi kawai yayi yana girgiza kai irin na manya yaciro wayanshi yana daddannawa, ahaka sukakai airport bangaren PJ, budemusu motan akayi, Zayn yafara sauka daidai da wayanshi bai dauka ba yabar shi kan kujeran duk Uncle na lura yasan neman abinda zai hanasu tafiyan nan yake at all cost kuma hakan bazai taba faruwa bane, dakanshi ya tattaremai wayan da komi nashi sanan yafito daga motan bodyguard din suka rufe suka wuce wajen jirgin Zayn shi harya shige, shiga Uncle yayi yaganshi zaune kan 3sitter chair jirgin ya kishingida ya lumshe idanu kaman mai bacci dake komawa gado, bargonshi Uncle yakarba daga hannun bodyguard din yazo wajen ya ijiyemai a gefenshi, sanan ya ijiyemai jakan tarkacen shi, saida suka gama komi sanan 4 daga cikin bodyguards din sukama Uncle sallama suka wuce, shikuma uncle da 2bodygurads din suka nemi waje suka zazzauna kowa yasa sitbelt nashi, wata Moroccan air hostess ce tafito cikin turencin ta na Arabs ta gaida su Uncle sanan takalli Zayn dakenan kaman yau bacci tace “Sir is sleeping, I think we ready” sanan tajuya dan kullo kofa Zayn yadan bude idanunshi kadan yanabin bombom dinta da kallo dan short skirt tasaka sanan yadan yatsine fuska ya bude idanunshi tass yakalli Uncle cikin fushi yace “where is my phone? Kuma am hungry” anatse Uncle yace “ga wayanka nan ajakan dake kusada kai, abinci we are about to take off, let’s take off saikaci ko” daure fuska yayi yakalli jakan bazaima iya budewa yadauki wayan ba, hakan yasa Uncle yacema bodyguard din “give him his phone” tashi yayi yazo yabude jakan yadauki wayan yabashi karba yayi yace “with the headphone” ciro headphone din yayi yabashi ya karba yana makalawa a kunnenshi shikuma bodyguard din ya maida jakan yarufe sanan yatashi yakoma wajen zamanshi, air hostess din ta rufo kofan jirgin sanan tadawo ta zauna akan kujeranta dake facing mutanen jirgin tana kallon Zayn dake tabe taben wayanshi tanadan murmushi takasa daina kallon handsome black Nigerian richboy din dakowa na jirgin nan uban yaron yakema aiki hatta pilot dinsu dan jirgin nan daya daga cikin jiragen Baban shi ne, she has been hearing labarai daban daban kan only don din boss dinsu kan bayaji menene menene but bata taba sani he’s this cute, sexy and handsome ba, jibi yanda yake abinda yaso kuma dole abishi wayan nan ma bayanda ya iya ne shima hala da cewa zaiyi arikemai yay ta tabawa tasake sakin murmushi.
Jidayayi ajikinshi ana kallonshi yasa ahankali yadago idanunshi karaf idanunsu sukai clocking awani irin kunyace ganin yakamata tahau murmushi tana shafa kanta, dan tabe baki yayi irin na yan iskan yaran nan sanan yawani kashe mata idanu daya yakai hannunshi yaja dan iskan gemunshi dinan idanunshi kan fararen cinyanta, jitayi kaman zuciyanta zai buga ganin yanda yake kallonta da mayun idanunshi tahau murmushi tana kokarin dauke kai takasa, Uncle dinshi yakalla ganin yafara bacci daga gani kasan yagaji tun safe halan yasan suka shigo garin nan suna nemanshi ko tausayinshi baijiba ya kwalamai kira. “Uncle Uncle” firgigit Uncle yabude idanunshi yakalleshi yace “Zayn mekakeso” “food” yafadi atakaice dasauri Uncle yakalli air hostess din dahar tafara cire sitbelt zata tashi tace “I am on it sir” sanan tawuce da sauri tai kasa zuwa kitchen Zayn yabita da kallo ta gefen idanu, lafiyayyen abinci takawomai a tray da wine tazo gabanshi tana murmushi still tashiga ijiyewa yana bin ko’ina najikinta da kallo saida tagama sanan takalleshi cikin idanu tace “enjoy your meal sir” dan lunshe idanu yayi yabude su saida kirjinta yabuga what! This guy is super hot Innalillahi zuciyanta yagama narkewa akanshi, sanan tawuce wajenta ta zauna tana saka sit belt Uncle kuma yakoma bacci dan ya bala’in gaji, sosai take kallonshi yanda yake tsatsakuran abinci yaci Wanan ya yatsine fuska yature yaci wanan karshe non alcoholic wine dinne kawai yadansha sosai in a very lazy voice yakallleta yace “take it away” gyadamai kai tayi ta taso dasauri tazo ta shiga kwashw komi tana lumshe idanu kamahin dayakeyi na neman tafiya da ita sanan tawuce takai komi ta ijiye tadawo tasake zama wajenta tana kallon shi, dan tsaki