Showing 39001 words to 42000 words out of 134057 words
Chapter 14 - FARRAH BOOK COMPLETE DOCUMENT BY MY SHAKUR .txt
ahankali shima Alhaji yace “na’am Zayn dina meke damunka haka nafara shiga damuwa wlh, menene talk to me, kome kakeso consider it done” dan ijiyan zuciya Zayn yasauke sanan yakalli hannunshi dake nan adaure yana kallon igiyoyin dan kwallin Farrah data dauremai hannunshi dashi, yatsanshi yakai kan igiyan yana tabawa murya chan kasa kaman mai tunani yace “When those goons kidnapped me Dad I went through a whole lot, I lost all hopes, was thirsty, hungry, ga karaya ga idanuna ga lot of spiders Dad at that point everything was a thing for me, I looked up to the sky nace Allah ya taimaken, then that gurl came from nowhere kaman daga sama aka jefota” yadanyi shiru yana kallon hannun nashi still in a very very low tone yace “Dad that girl protected me with all she got, at first I thought she was an angel, Dad kasan dan kwalinta tayaga ta dauremin hannun nan” yay maganan ahankali yana shafa hannunshi saikuma yadan yatsine fuska ahankali yace “Dad kasan I couldn’t thank her, whenever I looked at her sainaji she’s too small nace mata thank you and I am not use to thanking anybody” yadanyi maganan yana murmushi iya lebe kafin ahankali yace “Dad jikina is telling me I need to do morethan a thank you, she saved my life nima I should save her life and even give her a better life, education, da sauransu, Dad ina Uncle dinta kasa an daukoshi?” Dad na kallonshi right in the eye ya gyadamai kai, ahankali yace “tun around 3 chopper su yasauka, suna biyeda ni maybe ma yanzu haka sun shigo gidan nan” shiru Zayn yayi yana kallon mahaifinshi, lips dinshi ne yashiga rawa kaman yana fighting da abinda yakeso yafadi dan lumshe idanu yayi sanan yabude su yadaura su kan Dad ahankali yace “Dad can you adopt the girl please?”! Shi kanshi Alhaji saida yakara kallon Zayn maganan tazomai wani bagtatan bawai adopting yarinyar ne matsalan shiba ko kadan but this is the first time in history Zayn yacemai please kan wani abu mamaki ma hanashi magana yayi, ahankali Zayn yakai hannunshi yadaura kan na Alhaji yace “Dad lokacin da Mami tace the girl has been abused I felt so so guilty, bansan anything akanta ba but I know batada iyaye, and I know her uncle ran away they don’t like the girl, she’s like a burden, let’s call our lawyer muyi adopting nata idan ma so suke mukara musu wani kudi zamu kara, Dad I want to sponsor her education with my money not your own just to repay her kaji Dad” yakarashe maganan yana jijjiga hannun Alhaji, wani kalan sassanyar ajiyan zuciya Alhaji yasauke yana kallon fuskan Zayn din sanan yace “duk wanda cannot see beyond this your face da ake gani kaman u are rude is blind cus this your heart” Alhaji yakai hannunshi kan kirjin Zayn yace “is made from gold” dan murmushi Zayn yasaki, dan hararanshi Alhaji yayi yace “what are you waiting for, jeka saka kaya karakani nayi adopting yarinya ta Farrah” dan murmushi Zayn yayi yatashi glass cup nashi yafara dauka ya shanye milk din ciki sanan yawuce sama bai wani dade ba wani dark blue hoodie yasaka da gajeren wando iya gwuiwa milk, ya sanya eye glasses dinshi sanan ya feffesa turare yafito kafafunshi sanye cikin wasu navy blue designers crocs simple kayan zZama gida but still ka kalleshi saika kara kalloOnshi suka fito daga side din Zayn din tare.
2️⃣0️⃣
Side din Mami suka wuce, Mami na zaune a falo tana magana da Mama awaya suka shigo ganinsu tare yasa ta hararesu tacigaba da wayanta zama kusada Mami Alhaji yayi yana kallonta sabida tai kyau taci gayu sosai cikin kace kai kyau, katse wayan tayi takalleshi tace “ne kake kallona haka” cikeda tsokana yace “wai ke baki tsufa ne jibeki saikace ba kene kika haifi wannan gansamemen saurayin ba” yanuna Zayn, dan dariya Mami tayi tace “I take that as a compliment” “ina Farrah”? Alhaji ya tambayeta anatse, murmushi tayi tace “tana sama nabarta cartoon take kallo a IPad dina, you need to see yanda maganan ta ke improving Alhaji, one thing I like about her is she is fearless tanada kwazo da jajircewa” murmushi Alhaji yayi yace “kiramin ita” tashi Mami tayi tai sama bata wani jimaba suka shiga saukowa tareda Farrah, tana sanye da doguwan riga na atampa brown dinkin yamata das das ajiki sai dan kwalinshi data daura aka kanta na kasa wani kunya taji tanaji ita Mami tafiso da Mami kawai tasaki jiki saukowa kasa sukayi Mami ta zaunar da ita kan kujera kusada ita kasa zama tayi tazame jikinta ta zauna akasa da sauri kanta na kasa tashiga wasa da yatsunta Dan dariyan manya Alhaji yayi yace “Farrah yaya jikin? Wajen dinkin yadaina zafi”? Gyadama Alhaji kai tayi ahankali cikin zazzakan muryanta tace “eh…..Ab….ba” jinjina kai Alhaji yayi yana murmushi yace “Masha Allah, ga muryanki nan Tubarkallah Allah kara sauki” “Farrah” yasake kiranta anatse hakan yasa ahankali tadago kanta ta kalleshi, ajiyan zuciya Alhaji yasaki, yace “kingan ni nine mahaifin Zayn, mijin Mamin ku, da Mariya da Fatima da Maryam, Zayn kadai Allah yabani, rana daya kuma Allah yakawoki cikin rayuwan mu, akwai abinda yasa nasaka aka kiraki, inaso na tambayeki ne naji amsanki kafin nai komi” yasakeyin shiru sanan ahankali yace “Farrah kawunki ya sanar damu ke marainya ce, matata nan Maman Zayn likita ce, itace tamiki aiki a operation, taga tabo da dama ajikinki wanda yake nuna na alamun duka ne, yanzu inaso namiki wani tambaya banso kimin karya kinji” gyadama Alhaji kai tayi ahankali, anatse Alhaji yace “wanene yasamiki garwashin wuta abaki?” Shiru tayi gabanta nafaduwa dum dum, dafata Mami tayi ahankali tace “kada kiji tsoro ki yayi gaskiya kinji” gyadama Mami kai tayi sanan takalli Dad, batasan ya akayiba kasa karya tayi ahankali tace “In…na” “Matar kawunki”? Gyadama Alhaji kai tayi tace “eh””ita ke dukanki ma”? Gyadama Alhaji kai tayi takai bayan hannunta dasauri tashare hawayen daya zubomata, shiru dakin yayi Alhaji na kallonta, murya chan kasa yace “akwai abinda ake cema adoption aturence, yana nufin zaki dawo diyata ni da Mami da kotu tabamu mune custodian naki, kula dake yafita daga hannun su kawunki yadawo hannunmu dundundun ki dawo yarmu musaki amakaranta da sauran su, nakira lawyer na halama ya iso yanzu, yanzu hakama kawunki da matarshi na gidan nan chan bangaren baki, amman so naki nafara jin bakin ki kafin nasa akawo kowa nan, Farrah” Alhaji yakirata ahankali murya chan kasa tace “Na’am” ahankali yace “kin yarda ni da Mami muzama iyayenki?” Wasu kalan hawaye ne suka cika idanunta, tunda take baa taba bata daraja da mahimmaci dahar za’a zaunar da ita atamabayi yardanta Awani abu ba sai yau, tunda tahadu da mutanen nan sunada kirki sosai, batada kowa aduniyan nan banda kawu shi kadai gareta amman shima baya sonta baya kaunarta agabanshi aka kashe mata yar uwa baice komiba, dafata Mami tayi dasauri ta kalli Mami, Gyadamata kai Mami tayi alamun tace “eh” ahankali tace “eh Abba” rungumeta Mami tayi tana share mata fuska tace “daina kuka to” sai alokacin Zayn yadan saci kallonta, fuskanta na jikin Mami tana goge hawayen dasuka zubomata kaman ance ta kalleshi hada idanu sukayi da Zayn din hararanshi tayi tareda dauke kai.
Dauke kai shima Zayn yayi dasauri yana regretting kallonta ma dayayi waya Alhaji yayi sanan ya katse wayan yakalli Mami yace “tafi da ita sama”.
Wani Babban lawyer Alhaji ne yashigo falon tareda Uncle, sai Malam da idanunshi sukai zuru zuru da Inna da itama idanunta sukai zuru zuru, Malam yay mamaki dahar gida aka shigo aka daukesu suka shiga jirgi, Inna ihu tadingayi a helicopter wai zata mutu hanjin cikinta zasu zube.
Malam na ganin Alhaji da gudu yataho gabanshi ya tsugunna yahade hannayenshi biyu yace “Alhaji dan girman Allah kayakuri kada ka karbe kudaden daka bani, wlh wlh shairin shaidan yasa na gudu nakoma kauyenmu, to inbama shairin shedan ba ai nasan Kunsan kauyen kuma nakama nagudu, Alhaji dan Allah kayakuri wlh bazaka gane bane, Alhaji nima diyata daya rak, ina fama dakai na, kanwata tazo ciwon datayi shine ya tsiyatar dani tatas banda ko kwandala matata ce keda awakai suma awakan ranan da Farrah ta ceto dan gidan ka duka ta batar dasu, wlh ashirmena naso nagudu ne kawai nahuta inje na karata da matata da diyata guda amman nai kuskure kuya kuri” tunda yake maganan kowa ke kallonshi, cikin fushi Uncle yace “ina miliyan goman damuka baka bamu kayanmu ku dauki yarku amaidaku kauyenk……” tsayar da maganan datakeyi yayi ganin Alhaji yadagamai hannu, nuna kanshi Alhaji yayi yace “kai tun kana dan kankanin ka kataba ganin nai kyauta sanan nadawo na amshe kyautan danayi” sunnar da kanshi kasa Uncle yayi yace “a’a Yaya” maida hankalinshi kan Malam Alhaji yayi da Inna da itama ke zube gaban mijinta jikinta na rawa tunda take bata taba ganin aljannan duniya irin gidan nan ba, murmushi Alhaji yasakin musu yace “ku zauna da kyau dan Allah ni bakamin komi ba kuma bansa adaukoka sabida kudin danabaka ba nariga nabaka gonakin suma nariga nasa anma mai garin ku magana shi gwamnan Adamawa duk sanda ka koma zaka amsa koba komi yarinyar da bakaso yarinyar daka gudu a asibiti kabarta kaga kaci arzikinta” Alhaji yakara murmushi jikin Malam yay sanyi yakoma ahankali ya zauna hakama Inna, gyaran murya Alhaji yayi yace “abinda yasa na nasa akawomin kai nauyin dake kanka kake kokarin gudun mawa nakeso nacire maka shi daga kanka gabaki daya, diyarku Farrah nakeso nazama mahaifinta a shar’ance, cinta shanta, suturanta karatunta duka yadawo kaina, zai zamto Farrah tadawo diyata shine kawai abinda yasa na nemoka zaka bani”? Alhaji ya tambayeshi dasauri Malam jikinshi har bari yake yace “eh eh wlh nabaka Alhaji” Inna ma dan sosa keya tayi azuciyanta tanaji inama ace Rakiya ce ta taimaki yaron, kaman ta chakama kanta wukan bakin ciki takeji, kallon Lawyer Alhaji yayi yace “give him the papers” tashi yayi zuwa wajen Malam dan yabashi papers din yakuma nunamai inda zaiyi signing, dan yatsine fuska Zayn yayi yamike tsaye hanyar stairs yayi yay sama abinshi, shi kanshi baisan mesa yazo saman ba kujeran dakenan falon sama ya zauna yana kallon kofan dakin da yake tunani nan ne dakin Farrah dan shine dakin dake kusada na Mami, yadade yana kallon kofan, kaman akwai abinda ke controlling nashi tashi yayi zuwa gaban dakin yay jimmm yana kallon kofan, ahankali yadaga hannunshi yakai zaiyi knocking kofan dan cizan lips dinshi yayi yasauke hannun kasa ahankali, sake daga hannun yayi zaiyi knocking daidai nan aka bude kofan Farrah ce tabude kofan da saurinta dan ana kiran IPad din Mami dake wajenta zata kaimata saura kadan tafada jikin Zayn ta tare kanta ta hanyar kai hannunta daya ta daura kan kirjinshi daidai saitin zZuciyanshi as kariya daidai loOkacin kirjinshi ya buga dumm!
21
Yanda taji bugawan kirjinshi a hannunta da sauri ta janye hannun daga kan kirjinshi hannun nata nadan rawa, dauke kai yayi dasauri daga kallonta kaman ance dole yay magana yace “on Monday zan kaiki school ki shirya” yana maganan yajuya da sauri yawuce itama juyawa tayi takoma dakinta da wayan batasan mesa ma gabanta ke faduwa taganshi ba ya chanza mata a idanu gabaki daya kaman bashine mutumin daya bata tausayi ranan dataga za’a kasheshi ba.
Sauka kasa yayi ya barsu suna kan maganganun dasuke yafice daga falon ya sauka yana tafiya a side ahankali zuwa side dinshi. “Hi Zayn” yaji an kirashi dan tsayawa yayi sai alokacin ma yalura da Layla data kirashi tana zaune kan swinging chair dake hanyar zuwa side din Zayn ta sanya wani rigan bacci mai spaghetti hand na silk fari, yanada lace agaban wuyan ya tsayamata iya cinya sai silipas akafanta, dan tsaki Zayn yaja yawuce batare daya amsata ba da sauri ta taso tabiyoshi tana murmushi tace “common Zayn the least u can do is be my friend, am back a Nigeria banda any friend fa bansan kowa a naija ba, at least ni da kai we are related and we live in the same house, I know kaida Mommy baku wani shiri and it’s okay ni baruwana da wanan just be my friend” duk maganganun nan tana yinshi ne tana biyedashi saida yakai gaban flat dinshi ya tsaya hannu yamikama bodyguard hakan yasa bodyguard din yaciro kwalin taba daga aljihun shi da sauri yabashi, budewa Zayn yayi yaciro kara daya zai maida kwalin aljihun wandonshi Layla ma tamikamai hannu tace “at least give me one nima” dan kallonta Zayn yayi for the first time ganin tamikamai hannu, bai dauka tanashan taba ba ko ajikinshi kwalin yamika mata itama ta zare daya sanan yamaida kwalin cikin aljihun shi yasa karan taban abaki, zuwa bodyguard dinshi yayi gabanshi yasa lighter ya kunna mai sanan ya kunna ma Layla ma dake kusada shi, wucewa Zayn yayi ya shiga cikin garden dinshi dan yanada nashi seprate garden dinshi agida banda na asalin gidan kuma, zama yayi kan kujera yana shan taban da sauri itama Layla tazo tazauna kusadashi tana kallon yanda yakeshan taban hankalinshi kwance, murmushi tayi tace “who is your girlfriend Zayn”? Batare daya kalleta ba kai tsaye yace “I don’t have” dan juya idanu tayi cikeda mamaki tace “yaushe zakai aure to” dan kallonta yayi kadan yana fuzo hayaki waje sanan yadauke kai yace “I don’t know” dan dariya tayi sanan ta matso kusada shi saikuma ta sauka daga kan kujeran tazo ta gabanshi ta duko fuskanta na saitin nashi gabaki daya kirjinta awaje dan dama dan yagani tayi kallon fuskanta yayi kafin ahankali yasaukar da idanunshi kan boobs dinta da he could see them da kyau dama kuma dan yagani tayi tsaresu yayi da idanu dan shi dama baisan kunya ba, cikin wani kalan murya dakejan hankalin mutum tace “nima banda saurayi Zayn, and I badly need one” ta mike tsaye tana gyara riganta dan ijiyan zuciya Zayn ya sauke ahankali sanan yadan lumshe ido satan kallon wandonshi dataga yabalain tashi sama Layla tayi dan murmushi tayi tajuya cikeda son jan hankalin Zayn tace “gud night” dan bude idanu Zayn yayi yakalleta tawuce wani kalan juyamai bombom take he don’t think akwai pant ajikin bombom dinma sabida yanda suke rawa still tanashan taba abinta, saida yadaina ganinta sanan yaja tsaki. “F**k” yafadi ahankali, shifa he can’t lie to kanshi bayason mata mace bata gabanshi but he totally loves sex, baya iya resisting sex, mtswwww yasake jan wani kalan mugun tsaki sanan ya yarda taban daya gamasha inama zai iya fita yaje club kawai tsoro yakeji wayanda keson kasheshi suna nan, dakinshi ya shiga har yanzu he’s still very much erect, fridge dinshi yatafi a kitchen yashiga dubawa gabaki daya wines din dayake dashi non alcoholic ne, he’s just looking for something dazaisa shi to be drunk, fitowa yayi yawuce sama closet dinshi yaje inda yake boye wani shisha pot dinshi amman babu yasan Dad ne yafitar dashi komi nashi saida ya hargitsa looking for wani abu amman baidashi wani kalan ihu yayi ya barar da kayan shafanshi yace “f**k this house” fitowa yayi azuciye idanunshi sunyi ja fadawa gadonshi yayi yashiga juyi his tummy hurts kaman zai fice, jijiyoyin kanshi sun fiffito da kyar bacci ya kwasheshi wuraren 2 nadare.
Da Asubahi Alhaji yashigo side dinshi tadashi yayi da kyar da kyar yatashi dan saida yasa Alhaji yay missing first raka’a amman bai damuba haka yatasoshi agaba suka tafi masallaci, tunda yadawo Nigeria yaune yaje masallacin anguwansu yay salla, ana idarwa ya yunkura zai mike dan bacci yakeji Dad yarikemai hannu, fizge hannunshi yayi yace “leave me alone Papa” dasauri Alhaji yasakeshi kafin yan masallacin sujisu fitowa yayi shima Alhajin tashi yayi yabiyo bayanshi dasauri suka shiga gidansu tare, Alhaji yace “good morning Son” “morning Dad” yafadi ahankali yawuce side din Mami batare dayaje side nashi ba, babu kowa a falo hakan yasa yay stairs yawuce sama tun kafin yakai saman yakejin muryan Mami tana biya karatun Al Qur’ani sai chan yaji muryan Farrah na amsawa ahankali, tsayawa Zayn yayi batare daya karasa hawa saman ba yadan lumshe idanu, yanajin muryan Farrah har cikin zuciyanshi, muryanta nada wani kalan secret dadi tana karatun Al Qur’ani dinan dudda muryanta na breaking but voice nata sounds like voice na larabawa and yay mamaki dayaji tana karatun da kyau dan shi yadauka bata iya komiba she’s an illiterate, ahankali kaman baiso yadaga kafanshi yacigaba da tafiya yashigo falon saman daga Mami har Farrah dasuke zaune kan carpet na tsakiyan falon saman suna karatu duka juyowa sukayi suka kalleshi, hanyar dakin Mami yayi yace “morning Mami” mamaki Mami tayi ganin Zayn yatashi da safe hakan yasa anatse tace “katashi lpy Zayn” dan ita bata biyemai da turencin nan nashi, kallon Farrah tayi tace “baki gaida yayanki ba Farrah” dan satan kallonshi Farrah tayi daidai yabude kofan dakin Mami zai shiga tace “Ina kwana Ya Zayn!” Murmushi Mami tayi jin takira Zayn da Yaya abin saiya wani kalan karamata son Farrah azuciyanta, faduwa gaban Zayn yashigayi sosai no one has ever called him Yaya da yarinya nan takirashi da Ya Zayn he really felt something, lips dinshi yadan bude kadan shima sabida kar Mami tamai fada ne yace “fine” daga ita har Mami sunga motsin bakinshi amman babu wanda yaji abinda yace shigewa dakin Mami yayi abunshi ya maida kofan yarufe hawa gadon Mami yayi ahankali ya kwanta yay shiru yana sauraron karatun su, a suratul asr dazu yasame su yana nan kwancEe yana jinsu wani zubin yabisu wani zuObin yay shiru har sukakai suratul naba’i.
22
Lumshe idanunshi yayi kaman yana bacci yanaji Mami tacemata taje tai wanka itakuma Mami ta taho dakin, bude kofanta tayi tana kallon Zayn daya kwanta akan gadonta ya lumshe idanu kaman mai bacci, maida kofan tayi tarufe sanan ta cire hijabin jikinta ta linke ta ijiye ta taho gaban gadon tana kallon Zayn din barin gemun nan nashi, dan girgiza kai kawai tayi tajuya zatabar wajen hannunta Zayn yakamo dasauri hakan yasa tajuyo tace “ohh dama idonka biyu” tashi yayi yazauna ahankali yana kallonta saikawai ya rungumeta yadaura kanshi akan cikinta yace “Mami yanzu bakida lokaci na” dan