Showing 45001 words to 48000 words out of 134057 words
Chapter 16 - FARRAH BOOK COMPLETE DOCUMENT BY MY SHAKUR .txt
tadingayi abaki har suka cinye, kwashe kwanukan Farrah tayi tafita dasu waje inda taga makwarara, kwanukan data gani na datti ta hada tass tashiga wankewa daga daki Mama tace “mekikeyi Farrah” “wanke wanke Mama” murmushi Mama tayi takalli Mami tace “Allah yabaku ladan abinda kukayi, sanan Allah yatayaku riko” murmushi tayi tace “Ameen” Mama tace “yanda kika taimaketa ubangiji Allah Ya taimakawa Zayn dinki haka Ya shirya dashi yakuma natsar dashi” murmushi Mami tayi tace “Ameen Mama, kin shanye magungunan ki” tabe baki tayi tace “nifa nagaji da shan magani fa Mami ki kyaleni” tashi Mami tayi dasauri tashiga uwar dakinsu gaban drawer tana dudduba magungunan Mama tace “Mama wai mesa bakishan magani, sune fa zasu dinga controlling da regulating BP dinki eh Mama dan Allah kidinga sha” naji.
Sai gab da magrib sukabar gidan Mama, har atampa Mama tama Farrah kyauta dan Farrah ta gyara gidan tsaf ta gyara dakin Mama ta share harda cire duka yanan gidan dana zaure sai dariya suke itada Mama suna tambayanta ya akayi tacire yanan Xauren nan abokanen Zayn ne wai tsoronsu yake da gizogizo, babu kalan labarin tsorace tsorace Zayn dabata jiba, suna kaiwa gida sukai Magrib anayin isha’i Mama tasata tai bacci dan goGbe monday zaa kaita school.
💫 FARRAH 💫
✍🏻M SHAKUR
EPISODE 2️⃣4️⃣
Da asuba Mami tashigo ta tada ita, salla tayi sanan tafito tasami Mami a falon sama suka fara karatun Alqur’ani, saida suka gama Mami takara duba wajen dinkinta yay healing sosai, ganin 6:30 yasa Mami tace “jekiyi wanka zan fito miki da kayan da zaki saka Zayn zai kaiki school yau” dan murmushi tayi sanan ahankali tace “Mami” kallonta Mami tayi tace “naam” murya chan kasa tace “Mami tsoro nakeji kada amin dariya a school kinga daga kauye nazo kuma ban iya turenci ba” tunda take maganan Mami ke kallonta muryanta dadi tafara magana kaman kada ta daina, dan murmushi Mami tayi tace “Zayn zai kaiki Best school dayake nan Abuja, and one of the characteristics of schools haka shine basama mutum dariya, basa bullying and zasu dauki lokacin su su koyarda ke da kyau, ban sanki da tsoro ba, sanan b’ajin kunya wajen neman ilimi kizama mai kwazo kibama wayanda zasu miki dariya kunya kinji, and I am here, ga Yayanki Zayn, ga Abban ki komenene baki iyaba duk zamuyi guiding naki, we are your parents, muje naciro miki kayan dazaki saka” Mami tai maganan tana kama kafadabta sukai daki, wardrobe nata Mami tabude wani pink long sleeve t-shirt Mami taciro mata na mata mai botura na glass agaba, sai wani black long skirt, da black gyale karami, ta ijiye mata akan gado, tace “jekiyi wanka kifito bari naje naduba breakfast nakuma tada Zayn, koda yake nasan Abban ku yatadashi yanda yasan zai kaiki school haka” ficewa tayi itakuma Farrah tashiga wanka, wanka tayi sanan tadaura towel tafito, manta tashafa sanan ta shirya tsaf tasaka kayan da Mami tafito mata dasu taje gaban madubi wani kalan kyau tayi bana wasaba, bude kofa da akayi yasa tajuyo Mami ne, murmushi tayi ganinta hakan yasa Mami taja kujeran gaban madubi ta zaunar da ita tace “yau zaki fara school ki kula da kanki, makarantan ku akwai both maza and mata ki zama yarinya mai natsuwa baruwanki da maza malamai ko dalibai bude idonka kiga” kwalli Mami tasaka mata, sanan tadau man baki na Vaseline tashafa mata a lips, lips nata kaman tasa mata pink jan baki, drawer ta taja, Mami tadauki wani gold ear ring na dan makale tasaka mata a kunne sanan tadauki wani simple chain na gold shima da babu pendant ajiki tasa mata awuya dan wuyanta yadinga walkiya, bracelet na LV Mami tasaka mata a hannu sanan tai murmushi tabata wani flat black slippers na saint Laurent size dinta 37 tasaka sanan Mami tace “muje” babban jakan makarantan da Mami tasaya mata jiya tadauka daga kan gado da bakin gyalen Mami tai gaba ita kuma biyeda Mami tana kallon kanta dan kayan sun mata kyau, tunda suka fara sauka daga stairs ta hango Zayn zaune afalon shima ya shirya yana sanye da riga da wando na jean da t-shirt all blue yana shan coffee a cup yana kallon kwallo a tV Dad dake sanye da jallabiya na zaune kusada shi, murmushi Dad yayi ganin Farrah yace “masha Allah yan makaranta an fito” murmushi Farrah tayi takaraso gaban Dad ahankali tace “ina kwana Dad” hannunshi yasa ahankali yashafa kanta cikeda so dakuma kauna shifa duk maison Zayn to yana sonshi barinma Farrah yace “lpy lau, ohh dama Wanan ne kitson da akaje akayi jiya kuka barmu agida” yay maganan yana kallon Mami datadan yi dariya, dan juyawa Farrah tayi tadan saci kallon Zayn daganan inda take gaban Dad ahankali tace “ina kwana Ya Zayn” wani kalan sweet smile Dad yasaki jin yanda Farrah takira Zayn dinshi Ya Zayn, Zayn din yakalla yana jiran amsanshi, sanin su Dad na kallonshi yasa batare daya kalleta ba bayabo ba fallasa yace “how you”? Ahankali tace “fine” kallonta Dad yayi yace “imaza je Mamanki tabaki breakfast kici kutafi kada ki latti” gyadama Dad kai tayi saman at tashi dasauri tai wajen Mami a dinning ita gani take kaman ba itaba da saitayi satan abinci wani zubin take samu taci.
Tea tasha sosai kusan kofi biyu as usual da chips da kwai saida takoshi dam sanan ta tashi zata kwashw tai kitchen Mami tace “barshi is 8 already zomuje na yafa miki gyale kutafi” shigowa sukayi cikin falon inda Mami ta ijiye school bag dinta da gyalen, ta dauki gyalen rollung nashi Mami tamata takama mata da pin sanan tadauki jakanta Mami tazo tabayanta tana goyamata tace “saka jakan to” ahankali Alhaji ke kallon Mami, duk ta gefen ido shima Zayn ke kallonsu, tashi yayi yawuce yafita daga dakin fuuu, Farrah takalli Alhaji dayabi Zayn da kallo tace “Abba natafi” “Allah bada sa’a my Farrah” hannunta Mami takama suka fita waje har wajen motan Zayn din sukaje Mami tace “to shiga” juyowa tayi takalli Mami batasan mesaba ita kawai bataso ta tafi rungume Mami tayi sai kuka, dasauri Mami tace “da girman ki kina kuka zaki school hahahaha” Mami tadanyi dariya saikuma tadago kanta, hannu tasa tashare mata hawayen sanan ahankali tamata peck agoshi sanan tadago tace “stop crying babu abinda zai sameki I promise, je makaranta ki nuna musu ke diyar Mami kine, nasa miki ruwa da snacks ajakan ki bye bye” hannu tadaga ma Mami tace “bye Mami” bayan motan Mami tabude mata inda Zayn ke zaune yana daddanna waya abinshi tace “Zayn take care” dan juyowa yayi ya kalli Mami daidai Farrah na shiga motan yace “yes Mami” maida kofan Mami tayi tarufe sanan bodyguards biyu dake gaba daya mai tuki daya na zaune kujeran gaba sukaja motan.
Tunda tashiga motan tai shiru, komi na zaman mata kaman mafarki haryau takasa manta rayuwanta just like a week ago, tun tana Yar yarinyar ta takeshan wahala agabanta aka kashe yar uwanta, dakin datake kwana na wajen tumakan gidansu, abinci saita sata idan su Inna basa nan, Shafa ita kadai ke sonta aduka garinsu, Shafa na yawan gayamata watarana sai labari wataranan ne yazo yanzu, wanan da rana daya kawai tafita taga za’a kashe mutum ta ceceshi gashi yanzu iyayen mutumin sun zamarda ita yarsu gashi yau zataje makaranta, girgiza kai tayi tareda murmushin kuka hawaye yazubo mata sharr dasauri tasa hannu tashare hawayen, hanya ta kalla tanason gidan nan babu kaman Mami dake koyamata karatu, ta shiryata ko da maman su na raye tana sonsu amman kullum fita take saida nono dakuma idan anyi karaya akirata Mamanta kullum wahala take danta kawomusu abinci basu taba ganin Baban su ba koma waye mahaifinta bazata taba yafemai ba dan mahaifiyar ta rasu da wahala hakama yar uwarta, koba komi zata dage tai karatu tanaso tazama likita kaman Mami sabida ta taimaki mutane da mata dayawa bataso mata sudinga mutuwa sabida rashin samin likita dazai lurada su. Kankame jakan makarantan ta tayi akirji tareda lumshe idanu ita tana tunanin zuci, parking dataji anyi yasa dasauri tabude idanunta tana kallon wajen, gaban wani hadadden school sukai parking, ganin motoci tayi kala kala ana parking ana sauke student maza na sanye da dogon wando, da shirt da jacket da necktie, mata kuma na sanye da skirt daya tsayamusu a guiwa da shirt da jacket da nectie sai hula na beret, da fararen safuna akafafunsu da farin safa kowa na shiga cikin school din, kana ganin school din kaga school na yan gayu, tana zaune ahaka lost in thought tana kalle kalle bodyguard yabude mata kofan motan, adan firgice ta kalli bodyguard din sanan tafito ahankali tana kankame da jakanta a hannu kaman irin mutanen nan da aka dauko daga kauye ana shirin kwace musu jakansu, zagayowa ta inda take Zayn yayi yana tafiya ahankali yana gyara zaman farin glasses na idanunshi dan satan kallonshi tayi da sauri tadauke kai wuceta yayi hakan yasa tabishi da sauri suka shiga cikin school din student na kallon Farrah duk inda sukayi sabida yanda ta kankame jakan makarantan ta a kirji tan tafiya kaman wacce ke shirin sata, ganin yanda ake kallon Farrah some student na pointing nata ana dariya yasa Zayn ya tsaya chak batare daya juyoba yanda take kalle kalle tana biyedashi yasa bamata lura ya tsaya ba kawai karo taji taci dashi students sai dariya, juyowa Zayn yayi yakalleta itama kallonshi tayi jikinta har bari yake baki ta tabe zatai kuka idanunta sun cika da kwalla sosai girgiza mata kai yayi tareda kai hannunshi ahankali ya karbe jakan data kankame akirjinta, zagayowa yayi ta bayanta ya tsaya yakama hannunshi da kanta yasaka mata jikinta na rawa sanan yazo ta gefenta yakama hannunta sukai wajen lift ya shiga da ita sanan yasa 5th floor yarufe kofan, jin abu na sama yasa kuka data rike da kyar tasakeshi hannunshi takama da sauri takalli fuskanshi cikin muryan kuka tace “Ya Zayn dan Allah kamaidani kauyen mu ni banson makarantan nafasa” baitaba jin abu yabashi dariya ba sai yGau.
💫 FARRAH 💫
✍🏻M SHAKUR
EPISODE 2️⃣5️⃣
Gimtse dariyan yayi yadan daure fuska baisan ya akayi ba kawai ji yayi yace “dama kinada tsoro”? Gyadamai kai tayi kaman wata Yar little baby tace “za’a dingamin dariya idan ban iya abu ba” yatsine fuska yayi kaman baiso yay maganan sai kuma ahankali yace “I will teach you” dan kwalalo mai manyan idanunta dake jikeda hawaye tayi alamun bata ganeba ahankali yace “zan koyamiki anything dabaki iya ba, babu wanda zai miki dariya” gyadamai kai tayi tasauke kanta kasa har lokacin jikinta na bari tana wasa da yatsunta, yatsun ya kalla saikuma yadauke kai yace “kidaina jin tsoro babu abinda zai faru” gyadamai kai tayi daidai kofa yabude yafice tana biyedashi tana kalle kalle har office din headmistress din school din, suna shiga office din Babban matan dake ciki wanda kana ganinta kasan itane headmistress din tace “ohh Zayn welcome, sannunku da zuwa have a sit” zama sukayi tana kallon Farrah tace “hello pretty lady” Farrah tasan hello hakan yasa ta kakalo murmushi ahankali tace “ina kwana” murmushi matan tayi tace “lafiya kalau” sanan takalli Zayn cikin harahen turenci tace “your Mom told me everything about her, zamu mata papers na primary school, yanzu abinda zai faru I will test her inga daga wani class zata iya farawa” wani textbook na English na SS1 matan tabata tabude mata wani passage ta tura mata gabanta tace “read this Farrah” tanuna mata wajen dan kallon matan Farrah tayi dudda bataji turencin ba tagane cewa karanta duka rubutun wajen akace tayi, ahankali ta gyadama matan kai, Zayn takalla ahankali shima kallonta yake raurau tayi da idanu baisan mesaba ji yayi kaman shima yace yafasa sakata a school din yatafi da ita sabida yanda tayi dauke kanshi yayi da sauri yaciro wayanshi yafara dandannawa headmistress din tace “uhum ina jinki Farrah fara” Gyadamata kai Farrah tayi dasauri kafin ahankali tace “kam…..fri…hen…..shon(comprehension), da…..man…..sta…..tree(the monster tree)” dan murmushi headmistress din tayi ganin daga asalin farkon page na textbook din tafara bama passage din take karantawa ba, dudda haka tayi kokari, dama the main challenge da ita da Mami suke tsoro shine yazo bata iya hada baki ba amman tunda yanzu ta iya hada baki kawai ahausance take karatun turencin she will pick up fast, wani takarda da maths question ke ciki aka bata wanda mainly addition subtraction da multiplication ne aciki, sai kuma numbers raise to power 2, pen tabata tace “yimin lissafin nan nagani” karban pen din tayi tayi talla hakan yasa ta iya lissafi kuma tun a primary school datayi tasan addition subtraction multiplication sign da square and power sign nan da nan tayi taba headmistress din dubawa headmistress din tayi with so much excitement tace “good job Farrah” dudda Farrah batasan metace ba but yanda tai maganan tasan ance tai daidai ne tai kokari washe cute white teeth nata tayi ta screen na wayanshi yake kallon face dinta, murmushi yadanyi ganin this is her first smile tunda tazo school dinan, tashi headmistress tayi tace “muje nakaiki class naki SS1, Zayn wait for me here u will fill out the forms” tashi Farrah tayi ahankali tana kallon Zayn ganin yanda ta tsaya yasa headmistress tace “Zayn baraka bimu ba” dan dago kanshi yayi yakalleta tashi yayi ahankali yafice tabishi dasauri har class nasu anan sama shiga class din headmistress tayi da ita shikuma ya tsaya abakin kofa teacher na ciki duka ajin tashi akayi aka gaidata murmushi tayi tace “settle down student, this is your new class mate, everyone welcome Farrah Muhammad Ganuwa with Atama clap, ATAMA 👏 ATAMA👏 LABAKO👏 LABAKO👏 LAMARINAAAAAAAA👏👏👏👏” yanda suke tafi headmistress namusu wakan Atama saida yasa Farrah taidan murmushi tana kallon yan ajin, dan tabe baki Zayn dake kallonta yayi yace “silly girl” headmistress tace “can I hear you all say welcome Farrah” atare duka yan ajin sukai ihu “welcome Farrahhhh” washe baki Farrah tayi sanan Headmistress tabata wani sit dake gaba gaba tace “once yayanki yagama cike komi zansa akawo miki all books and textbooks naki” Gyadamata kai Farrah tayi sanan headmistress tajuya tafice Farrah na binta da kallo, leka wajen tayi ganin bataga Zayn abakin kofan class din nasu dayake da ba, kalle kalle tashigayi ta window chan saigashi yazo zai wuce yana maida waya aljihu kaman waya yayi kallo ajin yayi dasauri tadagamai hannu alamun bye dauke kai yayi kaman bai Santa ba hakan yasa ta harareshi. “Focus Farrah” malaman dake ajin tai magana da sauri Farrah takalli gaban allo gabanta nafaduwa.
Komawa office sukayi kudin komi Zayn yabiya tundaga kan takalmin makarantan su, socks, sport wears, uniform, books, textbooks, babu single abu na school din dabai biyamata ba sanan ya ciremata all the forms tass kusan 1hr yayi a school din sanan yagama komi, headmistress tayi tace “ko waye direba nata dazai dibga zuwa daukanta idan an tashi needs to go to our security office yay register sabida asan dashi, we don’t release our students to just anybody for safety purpose” kallonta Zayn yayi kaman bazaice komiba sai chan yace “for now I will be the one coming” murmushi headmistress tayi tace “indai kaine ba matsala” tashi yayi yace “lemme get going” gyadamai kai headmistress tayi tace “regards to your Mom” ficewa daga office din Zayn yayi headmistress na binshi da kallo saida yafice ta girgiza kai ahankali tace “yaran yanzu, Allah dai ya gyara mana jibi yanda ya maida gemunshi jama’a, wai Wanan ne gayu awajen su” secretary nata ta kwalama kira tana shigowa note and textbooks na Farrah da Zayn yabiya tanuna mata tace “kaima Farrah GSS1 Science” kwasa tayi tafice.
💫 FARRAH 💫
✍🏻M SHAKUR
EPISODE 2️⃣6️⃣
Sosai take concentrating a karatun da ake koyamusu her only problem shine rashin iya turenci, ranan gabaki daya maths da further math kadai tasan tagane shima sabida lissafi ne amman sauran abubuwan dasukayi bata ganeba sabida rashin iya turenci.
Break aka kada, kowa na ajin tashi yayi yafice banda ita dake zaune kaman an dasata awajen bude jakanta tayi sanan tadauko water bottle da Mami tasaka mata aciki dawani kula tabude, fries ne aciki da pepper chicken da sausage, sai fork murmushi tayi ahankali tasa fork tafaraci shigowa ajin akayi wata yarinya data dan dare Farrah tsayi da kadan tashigo ciki tana rike da cups biyu na parfait ta taho inda Farrah take kujeran dake facing Farrah ta zauna akai tana kallon Farrah da itama ke kallonta, dan murmushi tayi tamikama Farrah parfait daya tace “my name is Maryam, kowa call me Miemie agidan mu, I am a baker, na iya bakin cakes and so many many other thing kefa” abinda take bata Farrah takalla sanan ahankali tasa hannu ta karba dan kartaga kaman tamata wulakanci but bamata iyacin abinba, ahankali Farrah tace “sunana Farrah, ni ban iya yin cake ba but Mami tace zata koyamin” murmushi yarinyar tayi tace “ohh that’s nice, tun ina yarinya Mom tafara koyamin baking, yanzu is officially my business you can search me on Instagram @alfasimcakes, I really like you Farrah tunda kika shigo nake kallonki, you are so pretty” murmushi Farrah tayi batace komiba, ganin kaman batagane abinda take fadi yasa Maryam tamika mata hannu tace “friends? Muzama kawaye?” Shiru Farrah tayi tana kallonta batare daya mikamata hannunta ba, murmushi Maryam tayi tace “don’t be scared nima just last week aka sani a school dinan, a Saudi muke zama, sabida Yayan mu Ya Habeeb anturoshi yayi wani project anan Nigeria more like a course for 3yrs shine fa dukanmu muka dawo nan, Mom da Dad wai bazasu iya barin yaronsu yazo Nigeria yana wahala shi kadaiba babu mai girka mishi abinci ba, Dad dina is a Doctor, shima anan Nigeria aka haifeshi but he works at Saudi, the whole thing is so annoying nafison Saudi kan nan garin, tunda nazo banda any friends tundazu da aka shigo dake nake kallonki, kinga tsayinmu daya, though nafiki kadan, kuma kaman we are age mate, sanan bakida hayaniya, and you are very very very pretty, ni banma taba ganin someone as pretty