Showing 75001 words to 78000 words out of 134057 words

Chapter 26 - FARRAH BOOK COMPLETE DOCUMENT BY MY SHAKUR .txt

24 Jan 2025

7540

office din da kallo kafin yakalli ogogon bangon office din yaga 1:30 na rana, dan ijiyan zuciya ya sauke sanan yafara tafiya yay hanyar kofa gently yasa hannu yabude kofan sanan yafita, Layla yagani zaune kusada secretary dinsu kallo daya yamata yadauke kai shi baison mace tafiya naci da maita offing nashi abin yake, maida kofan yayi yawuce dasauri Layla tabiyoshi daidai ya shiga lift kafin kofan yarufe ta shige tana kallonshi tace “wai mekake nufi ne batare akace muyi aikin nan ba kullum Saika dinga koroni kana hanani shiga office din” wani matsiyacin kallo yamata sanan ya yatsine fuska kaman badashi takeba wani kalan kulewa tayi hakan yasa tace “wai maisa kacika rainama mutane wayau Zayn eh inamaka magana kamaidani mahaukaciya” wani kalan juyoda idanunshi yayi ya kalleta sannan yadauke idanun abin bakaramin zafi yamata ba hakan yasa tace “wai sabida kazamiyan yarinyar nan Farrah kakemin haka?” Kaman ta tabo wani abu ajikinshi dasauri ya kalleta fuskanshi babu alamun wasa ganin haka yasa tace “yes Zayn, tell me meke faruwa dan bangane maka ba, kai mutum ne dabaka damu da kowa aduniyan nan ba sai kalla, why are you so caring towards that girl, kana fifitani akanta meta fini dashi? Nafita wayewa nafita ilimi nafita kyau nafita karatu, look at me kalli jikina babu abinda zaka nema da bazan iya baka ba, kana marina kanta tell me sonta kakeyi ne are you in love with Farrah Zayn!” Wani kalan bugawa kirjinshi yayi jin kalman so datafadi daidai lokacin sukakai ground floor hakan yasa yabi ta gefenta zai fita hannunshi takama dasauri tafashe da kukan datake rikewa sosai ahankali tace “Zayn please wlh kome kakeso zan baka, I want to be your girlfriend mudinga komi tare har shaye shaye please Zayn” wani kalan juyowa yayi yakalleta sannan yakai hannunshi kan hannunta data daura kan nashi yacire tareda murde hannun idanunshi suna kadawa yace “listen and listen attentively! Karki sake bari wannan bakin naki ya ambato sunan Farrah, and as for this place you can find anybody to work with but forget working with me and lastly” yay maganan yana huci yana matso da fuskanshi dab da nata yana kallon kwayan idanunta yace “I don’t f*ck beggars masu rokon maza su cisu naaaa! Zayn yafi karfinki” yakarashe maganan yana jefarda hannunta sanan yajuya fuuuu yawuce mosque abinshi.






Tsugunnawa awurin Layla tayi tana kuka, inhar bazata sami abinda takeso ba to wlh kome Momy keson mishi zata tayata, tanason Zayn yana bala’in burgeta saisa daman taso suyi soyayya suci juna dan Allah ya kera yaron da kyau wlh bata tabayin saurayi kwatankwacin Zayn ba balle nai kama da Zayn.






Salla yayi dan anriga anyi jam’i tun dazu yana idar da sallan ya jingina da bango yay shiru maganan Layla namai yawo azuciya are you in love with Farrah, son Farrah yake? Ya tambayi kanshi he’s trying to compare the thing yanzun nan Layla take kuka wiwi sosai agabanshi babu abinda yaji azuciyanshi saima dada murdamata hannu dayayi yamata warning kan karta sake kiran sunan Farrah, da Farrah ne ke kuka haka daba karamin damuwa zaiyiba, he can’t stand seeing her angry, nor sad, wani zubin idan yaganta he just want to tease her dan kawai tamai tsiwa tana zaromai manyan white eyes dinnan nata kaman idan ance ta dakeshi zata iya, he loves seeing her happy and smiling tunda yake baitabajin hakan game da any mace ba koda yay sex dake yaji dadi ba sai Farrah da babu abinda ya tabayi da ita beside ma she’s too small, is that what love is? Is he falling in love with Farrah yaya ake gane soyayya? Wayanshi yaciro dasauri yashiga browsing how to know you are in love with someone yadage yana karatun sosai.




“Assalam Zayn!” Yaji anmai magana ana shafa kafadanshi dasauri yadago kanshi wani Indian imam dinsu ne na masallacin nan, yanama Dad aiki ustaz ne sosai, dan murmushi Zayn yamai batare daya amsashi ba, zama Imam din yayi agabanshi tareda lankwashe kafa yasha ganin Zayn company nan ma waye baisan labarin Zayn only yaron Ganuwa ba saidai idan baka company nan, anatse yace “what’s the matter Zayn”? Shiru Zayn yayi yana kallon mutumin he’s elderly dan akalla yayi sa’an Uncle kuma malami ne nagidi, at least baitabama kowa magana ba outside parents nashi baida aboki yamai magana ne, yay shiru dan murmushi Imam din yayi yace “you can always talk to Me Zayn dudda nasan I am nobody zan iya taimaka maka da shawarwari” yay maganan anatse hakan yasa Zayn yaji kawai ya yarda dashi ahankali yadan cije lips sanan yasaki lips din murya kasa kasa ta yanda kowani yashigo masallacin bazai jisuba yace “Imam I am a bad boy I know you know that cus you work here” yadanyi shiru sanan yace “my parents are not happy with me, I am trying to change but kasan menene matsala na I don’t think I can leave without women” yadan yatsine fuska dan iyakan gaskiyanshi yake fadi yace “ni baran iya 2-3days without a woman ba before banama iya one day saida nadawo Nigeria ne nazo nafara koya da kyar murya chan kasa yace what do I do”? Anatse Imam yace “kodai ka dunga azumi kokuma kai aure sabida kadinga samin natsuwa daga wajen iyalinka” dan shiru Zayn yayi yana kallonshi batare dayace wani abuba hakan yasa Imam yace “kanada wacce kakeso”? Shiru Zayn yayi saikuma ahankali yadan fuzarda iska Farrah na fadomai arai yace “I don’t know, ni banmasan ko inada wanda nakeso ba all I know is kamin tambayan nan is one person yafado raina Farrah and she hates me cus ta taba ganina da wata” yasake maganan yana yatsine fuska, dan murmushi Imam yayi yasaka hannayenshi biyu yakamo hannayen Zayn anatse yace “yaune rana na farko dana taba zama na magana dakai and all I see was myself lokacin danake da shekarun ka, I was once in your position Zayn duk wani rashinji daka sani nayishi aduniyan nan but rana daya shiriya tazomini sabida question din is menene amfanin been a bad boy can you answer this question Zayn”? Ahankali Zayn ya girgizamai kai, murmushi Imam yayi yace “is not easy kabar komi da komi tashi daya but idan kai niyya kazo kafara bautama Allah da kyau he will help you, and yama baka the greatest reward by giving you the best woman” yasake murmushi yace “ingaya maka ta yanda zaka gane you are in love with someone Zayn”? Dasauri Zayn ya gyadamai kai, dan murmushi Imam yayi yace “when you care for them genuinely, baka iya jure tsana daga wajensu, u can’t stand hurting them kokuma kaga ana hurting nasu, you love seeing them happy, kuma kawai kaji kanamusu wani kulawa na musamman is love, and if this things are abubuwan dakakeji game da yarinyar daka fadimini tom you are in love with her Zayn” sosai Zayn yake kallonshi yama kasa magana, gyadamai kai Imam yayi yace “tashi ka koma aiki” gyadamai kai Zayn yayi yamike tsaye ahankali har lokacin jikinshi yay sanyi yawuce yakoma office koda yashiga kwanciya yayi kujera yay shiru tunanin Farrah kawai yake yana koran tunanin amman yakasa daina ahaka baiyi komiba yaji ankira la’asar hada tarkacenshi yayi yafito saida yafara ijiye jakan laptop din a motanshi sannan yawuce yatafi masallaci &ana idarwa yafito yashiga mota yawuce.


4️⃣8️⃣








Dagudu yake tuki as usual wani boutique yagani agefen titi da mannequin ansa musu kayan mata masu kyau sosai yaga sunmai kyau hakanan Farrah ne tafadomai arai, he’s trying to stop kanshi but gani kawai yayi yay kwana yay parking gaban shagon yashiga ciki, lafiyayyen english wears yashiga kwasan ma Farrah shirts da wanduna da gowns, yabiya kudi almost 300k masu shagon sai godiya sukemai yashiga motanshi yajawo motan zuwa gida.








Yauma kaman kullum exam din yau yamata dadi, zaune take a falo rikeda iPad din Mami wanda yanzu kusan koda yaushe yana tareda ita tana karatu dashi, Mami na kitchen dudda Farrah taso ta tayata girki kadota tayi tajetai karatun exam, hakan yasa tadawo falo tana zaune ta sanya wata Yar rigan kanti mai dogon hannu baka tanada zanen flowers farare ya tsayamata kasan gwuwanta kanta babu dan kwali sai kalaban data tufke da ribbon baki mai kyau, kaganta zaka dauka wata balarabiya ce zaune akatafaren falon, tana zaune ita kadai akan kujera da iPad din Mami a hannunta tana zane tana kallon zanen Amoeba 🦠 a iPad din tana zanawa da pencil a book din tana koyan lebelling dan gobe biology garesu gabaki daya hankalinta yay nisa a zanen, ahankali aka bude kofan falo aka shigo, Zayn ne yana rikeda katuwan ledan a hannunshi idanunshi akanta saikace tsafi ganinta kawai dayayi dudda ma bata ganshi ba jiyayi zuciyanshi tamai wani kalan sanyi tamai wani wasai now all he needs is tadan kalleshi and get all those her expression akan fuskanta.




Kamshin dataji yadaki hancinta wanda tasan kanshin Zayn kadaine yasa kaman wata Yar bera tadaina zanen datakeyi, duwawun pencil din hannunta takai bakinta sanan ahankali tadago kanta tareda juyowa hada idanu tayida Zayn daya tsaya yana kallonta kaman baitaba ganintaba ga katon jaka a hannunshi ga jakan laptop a dayan hannunshi yana kallonta, hakanan jitayi gabanta yadan fadi hakan yasa tadauke kanta daga kallonshi dasauri tana zare pencil din daga bakinta cikin kunkuni tace “mutum ko sallama bai iyabama” karasowa gabanta yayi ya tsaya dab da ita dan yanda ya tsaya akanta kafafunta nataba Yadin wandon jikinshi wani iri taji tanaji gabanta nafaduwa hakan yasa taki kallonshi drawing datake yabida kallo yace “look at abinda take zanawa kaman fuskanta” dawani sauri takalleshi zatai magana ya watsa mata mugun kallo yace “kawomin abinci I am hungry” hararanshi tayi ahankali tace “bara’a kawob…….” Daidai Mami nafitowa daga kitchen hakan yasa dasauri tabi ta gefenshi tai hanyar kitchen din tana kara budema Mami kofa da kyau tace “Mami sannu da aiki kawo nakai miki” kafin Mami tahanata ta karbe kulan takai dinning Mami takalli Zayn dayake shirin zama inda Farrah ta tashi tabari tace “kadawo” zama yayi ahankali yana daukan iPad din yace “yes Mami” “kaci abinci” dan yatsine fuska yayi yace “no” tasan dama baicika cin abinci ba hakan yasa takalli Farrah tace “kawomin serving spoon da tray a kitchen” dasauri Farrah tai kitchen ta dauko, seafood pasta da Mami tadafa lafiyayye tazubamai tahada a tray tasama Farrah a hannu tace “gashi kaimai kizo kidauki juice kikaimai ” karba Farrah tayi tawuce tazo ganin yawani kwanta kan kujeran data bari daga iPad dinta harda book dinta yajefar akasa yasa taji ranta yabaci ko kadan Zayn baida manners.
Ijiye tray abincin tayi akasa saida tray yay kara hakan yasa Zayn yadan bude idanu kadan yakalleta yanda tai da manyan idanunta kaman zata cije shi yasa yanuna mata small coffee stool nasu da yatsa in a very lazy voice yace “put the tray on that stool” hararanshi tayi tamike tsaye tana kwashe iPad din da book dinta daya Yar akasa sanan takalleshi cikedajin haushi tace “ina pencil dina”? Lumshe idanunshi yayi ahankali muryanta namai wani sanyi azuciya yana neman sakashi jin bacci, zatai magana daga kitchen Mami tace “idan kin bashi juice din kizo nan Farrah” dawani kalan sauri ta tashi ta ijiye iPad da littafin akan kujera tai dinning fresh juice din da Mami tahada ta dauko da cup suma a tray takawomai har lokacin yana kwance kan kujeran idanunshi a lumshe shima ijiyewa tayi akasa saida tray yay kara tamike tsaye jin baimata magana ba yasa tadan saci kallonshi idanunshi a lumshe kaman ma yay bacci wani irin bacci ne cikin 1min haka. “Did u put the food on the stool ko u are still looking at a fine boy” wani kalan ballamai harara tayi tana nadaman tsayawa ma kallonshi datayi sabida kawai Mami na kitchen yasa tajawo stool din tadauki tray tadaura mai abincin akai sanan tawuce batare data kalleshi ba zuwa kitchen.




Wasu kuloli Mami tanuna mata hakan yasa tadinga daukowa tana kawosu dinning itakuma Mami tafito falon, zama tayi kan one sitter tana kallon yanda Zayn kecin abincin agajiye hakan yasa tace “kagama aikin”? Gyadamata kai yayi ahankali yana kai abinci baki, ahankali Mami tace “babanka yace idan kadawo kada kaje ko’ina kajirashi” Gyadamata kai yayi ahankali yana ture abincin dako 4 spoons baiciba zai tashi Mami tace “koma ka zauna” komawa yayi ya zauna tashi tayi ahankali kaman bataso tazo kusadashi yazauna, plate na abincin ta dauka tace “tun safe ace mutum baici abincin kirki ba kuma yanzu kadan tsakuri abinci kaci zaka tashi bude bakinka” tai maganan tanakai abinci bakinshi dan murmushi kadan yayi ganin tasoma hucewa da fushin datake wato tsakanin uwa da da sai Allah, ahankali yabude bakin takai abincin yakarba ahankali daidai Farrah nafitowa daga kitchen dauke da kula baki tabude kaman wawiya tana kallon yanda ake bama katon namiji abinci, ahankali takarasa gaban dining ta ijiye kulan sanan tadago tareda juyowa ta rungume hannayenta aciki tana kallon yanda Zayn ke karban abincin da Mami kebashi awani kalan shagwabe, bata taba ganin bad boy irin Zayn ba malalaci sangartaccen banza kawai. Tai tsaki azuciyanta takaraso cikin falon ko kallon inda take batayiba tasa hannunta tadauki littafi ta da IPad din zata juya Zayn yace “pack the clothes naki ne Ke” kallon kayan Mami tayi sanan takalli Zayn din daya dauki glass cup na juice zaisha tace “kaika siyamata kaya” gyadama Mami kai yayi yana kai juice din bakinshi, itama Farrah dan satan kallon babban ledan tayi saikuma takalli Mami, Mami dake kallonta tace “yayanki yasiya miki kaya dauka kiyi godiya” ahankali kaman bataso takaraso tasa hannu tadauka murya chan kasa tace “nagode Ya Zayn” ko jiran reply dinshi batayiba tajuya tai stairs Mami tabita da kallo sannan tajuyo takalli Zayn dakeshan juice abinshi, saida ya kwalwale tass sanan ya ijiye yamike tsaye yana shafa cikinshi ahankali yace “Mami zakisa nafara tara fat ajiki, I am okay” abincin Mami takalla rabi yaci dududu ta tabe baki tace “nidai wuce kaje kai wanka kashirya masallaci” dan juya idanunshi yayi yace “yes Mom” sanan yadauki laptop dinshi yawuce yafita daga dakin Mami tabishi da kallo, she is happy Allah ma yasani dan fushin dasukayi dashi &na kwana biyu yasa yadan natsu Allah yasa natsuwan ya dore haka.




4️⃣9️⃣










Around 7 Dad yashigo gidan shida Uncle, Uncle na shigowa motanshi yawuce yace “Yaya nawuce gida saida safe” binshi da kallo Dad yayi yace “don’t forget to come early gobe duk kayi wani iri jeka kahuta” Dad na maganan yay hanyar flat din Mami burinshi duk inda zaije yadawo kawai ya sauka dakin Mami dan yasan zai sami lafiyayyen abinci da ita tagirka daki mai kamshi dayaji kamshin turaren wuta ko kwayan datti bazai taka ba, sannan ita kadai ke komi nata sai yanzu da Farrah ke komi dudda haka bata barinma Farrah girkin dazaici saidai suyi tare, da sallama yashiga falon wani lafiyayen kamshi yadaki hancinshi babu kowa a falon hakan yasa yawuce sama dakin Mami yabude tana kan dadduma hakan yasa yay murmushi yawuce dakin Farrah dashima yabude da sallama itama tana zaune kan dadduma murmushi yayi yawuce dakinshi wanka yayi yafito ya shirya cikin jallabiya fara kal sanan yadauki charbi yabude kofa yafito daidai Mami na shirin shigowa dakin ganin yasa tace “zaka masallaci” Gyadamata kai yayi yace “eh kaimin abincina sama nadawo asama zanci abinci nai sauri kada jam’i yawuceni” yay maganan yana wucewa hakan yasa Mami itama tawuce saida tafara bude kofan dakin Farrah ganinta tana salla yasa tasauka kasa abincin Dad takaimai dakinshi sanan tawuce dakinta.








Ana idar da salla yadanyi azkar kadan sanan yatashi gamamakin shi Zayn yagani a sahun farko inda yake yana zaune yay shiru wani tattausan murmushi yasaki sanan yajuya batare dayamai magana koyama bari yaganshi ba yafito yawuce gida, a falo yaga Farrah zaune da littafi a hannunta tana ganinshi ta ijiye littafin tana murmushi tace “Dad sannu da zuwa, Dady ina kaje banganka yau” dan dariya yayi yana karasowa inda take kanta yashafa cikeda wasa yace “garinku naje yau” zaro idanu tayi tana murmushi zata karamai tambaya yace “yi karatu kije ki kwanta you have exam tommorow yarinya na” murmushi tayi tace “Dad daman sabida kai na sauko kasa naganka idan kadawo nagama yanzu zanje na kwanta, Dad nagaji yau banyi baccin rana ba saida na koyi all the drawings da labelling nasu” baki Dad yatabe yace “Allah yasoni banyi science ba” Mami data fito daga kitchen rikeda jug tace “saisa kai missing ai” Farrah tahau dariya itama Mami na dariya Dad yace “Au taron dangi zakumini keda diyarki Allah yasoni nima inada Zayn dina shima dan art ne kaman babanshi” tashi Farrah tayi tace “Mami bacci saida safe” Mami tace “mu kwana lafiya sarkin baccin wuri, muje Alhaji kaci abinci” tashi Dad yayi yabi Mami zuwa daki, saida yaci abinci yay nak sannan takwaso komi tafito dashi zuwa kitchen sannan tadawo dakin zaune taga Dad bakin gado gefenshi yanuna mata hakan yasa tamaida kofan ahankali tarufe takaraso ciki anatse ganin kaman akwai abinda yakeso yafadi mata ta sauka kusa dashi.




Dan ijiyan zuciya yasauke ahankali sanan yakalleta kafinma yay magana Mami tace “menene Alhaji? Talk to me please” dan shiru Dad yayi yana kallonta, ahankali yace “I don’t really know yanda zaki dauki abinda I’m about to tell you right now Dan kinsha fadi cewa I am the only one nake taking decision in Zayn’s life tun yana yaro gashinan kuma yanzu ma still nine ke taking decision din dan nayi wani abu yau wanda bansan yanda zakiyi accepting nashi ba” Dad yay maganan ahankali yana kallonta ganin yanda ta natsu tana kallonshi kanaganin fuskanta babu komi cikinshi sai tambayoyi dasonjin mekuma yayi yau, dan lumshe idanu yayi sannan yabudesu murya chan kasa yace “nama Zayn aure yau din nan!” Wani kalan sauka maganan yayi a kunnen Mami kaman saukan aradu hakan yasa dasauri ta kalleshi trying ta gasgata shine yafadi maganan ko kunnuwanta ne sukaji akasin hakan, gyadamata kai yayi yace “yes wife na aurar da Zayn yau dazu misalin 1:30 na rana” wani kalan kallon mamaki Mami kema Dad dayasa bakinta ma yakasa motsi sai kallonshi da kawai takeyi, murya chan kasa kasa kaman Dad baiso yafadi yace “na auramai Farrah!”

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login