Showing 33001 words to 36000 words out of 134057 words

Chapter 12 - FARRAH BOOK COMPLETE DOCUMENT BY MY SHAKUR .txt

24 Jan 2025

7536

kai, murmushi Mami tasakeyi tabata hannunta tace “sauko to muje” da taimakon Mami ta sauka daga gadon ahankali, slippers Mami tabata tasaka sanan suka shiga bayi, dakanta Mami ta hada mata ruwan zafi na wanka, sanan tasamata toothpaste a sabon brush dake bayin tace “ki brush saiki wanka, ina zuwa” Mami tafito daga bayin, fita tayi daga dakin tasauka kasa wani boutique dasuke dashi a asibitin tashiga, tundaga kan pant, wani pink gown, da black hula, da after dress Mami tasaya mata da cream, tabiya kudin ta taho, bra ne kawai batasaya ba shima dan bazata iya sawa yanzu bane sabida aikin da akamata, komawa dakin tayi, landline na dakin ta dauka tamusu order lafiyayyen breakfast asibitin babban gaske ne kaman hotel yanda zakai order abinci a restaurant na hotel haka asibitin ma yake, ijiye komi tayi sanan tawuce gaban bathroom din knocking tayi tace “kin gama”? Jin shiru yasa tashiga bayin tana zaune tagama wankan amman takasa daukan towel, kare kirjinta tayi a kunyace, towel Mami ta dauka sanan tazo inda take lullubeta da towel din tayi sanan ta dagata tashi tayi ahankali tarike Mami batada karfi ko kadan, fito da ita Mami tayi da taimakonta ta shiryata tsaf sai kunya takeji, pink gown din Mami tasamata daya amsheta da black hula, Mami tace “kinyi kyau” sata tayi tai salla azaune kafin ta idar an kawo musu abinci, gado ta dawo zama tayi Mami tabata tea ahankali ta karbi cup din tana kallon Mami, murmushi Mami tayi tace “baki sanni ba ko” Gyadamata kai Farrah tayi, murmushi Mami tasakeyi tace “sunana Mami” anatse tace “nine mahaifiyar Zayn, yaron dakika taimakamawa har aka harbeki tasanadin hakan, munzo dake asibiti nan Abuja tareda mahaifinki Baffan ki amman shi yatafi, yanzu kina wajena har kiji sauki karkiji tsoro kinji zan kula dake ni Maman kine kinji” Gyadamata kai tayi ahankali, murmushi Mami tayi tace “sha tea dinki to” tea takai bakinta saida ta tada kofin sanan tacire daga bakinta tabama Mami kofin, wani irin tausayinta Mami taji tace “nakara miki tea”? Gyadama Mami kai tayi dasauri, tea dinta Mami tamika mata karba tayi shima ta kwankwade, ahankali Mami tace “nasa akawo miki wani”? Girgiza ma Mami kai tayi alamun ta koshi, ajiye cup din Mami tayi sanan takalleta tace “fadamin sunan ki” kai tazo zata girgiza Mami tace “a’a bude bakin ki kifadamin da baki, naduba bakin ki jiya nasamiki magani, muryanki yadawo zaki iya kina magana yanzu, fadamin sunanki naji” ahankali tabude bakinta tana kallon Mami kaman yanda Mami ke kallonta, da duka karfinta da tsantsan kwazo da struggling da kai kanka dake kallonta zaka iya gani a kwayan idanunta ta danne idanunta tace “F…….Ffffff…………Farrrr……” bude idanunta tayi da sauri hardan zufa ya keto mata a goshi tsabagen kokari, murmushi Mami tayi sosai tace “sannu kinji, all you need is just a little therapy, amman kina magana, ke ba kurma bace, u can speak, karasa fadamin sunan naki inji” ahankali tace “Farrrrrr………..r……….rahhh” wani kalan huge smile Mami tayi tace “wowwww” itama Farrah murmushi tayi takai hannunta kan bakinta tana shafawa dudda sunan ararrabe takira but she was able tafadi sunanta yau, Shafa kadai take iya kira, itama da kyar take fadi, but yanzun nan tafadi ma Matar nan sunanta. “Kinji dadi?” Mami tamata tambayan ganin yanda take murmushi takira sunanta, kai ta daga zata gyadama Mami dasauri Mami tace “no, dabaki zaki amsani” dan runtse idanu tayi kaman yanda mai in’i’na keyi tace “e….h” murmushi sosai Mami tayi tace “good girl” wani strawberry smoothie dake cikin wani fine bottle da straw dinshi tadauka tasamata straw din tabata, ahankali tasa hannu ta karba cikeda dason gwada magana kuma tace “n……….a……g…..de” dan murmushi Mami tayi tana saka labcoat nata tace “kigodema Allah” tab dinta ta dauka ganin zata barta ita kadai yasa ta shiga YouTube wani cartoon movie tasa mata sanan tabata, ahankali Farrah tasa hannun ta daya ta amsa dan sayan tana rikeda smoothie Mami tace “kiyi kallo bari naje naduba wasu patient ko, yanzun nan zan dawo kinji” zata gyadama Mami kai Mami ta girgiza mata kai alamun no hakan yasa tace “tttttt….o” murmushi Mami tayi tajuya tafita daga dakin, saida tamaida kofan tarufe sanan tasaukar da kanta ahankali bayan Shafa wanan ce mata tabiyu dake sonta aduniya, Matan kaman Maman ta, hawaye ne suka zubo mata daga ido dasauri tasa hannunta ta share sanan takai goran smoothie baki tafara zuka dadin dataji yasa tahau sha sosai tana kallon cartoon dinta ita kaman ma abarta a asibitin taitai zama.






Bude musu bayan motan bodyguards sukayi, ahankali yasauko daga motan yana sanye da Greg Lauren horizon print crew neck t-shirt, black color ne t-shirt din dakeda zanen rana ajiki da color na sunset, yasaka wani jean na Ksubi, frescobol Carioca round toe espadrilles (takalmi) yasaka, yauma wani Rick Owens sarka yasaka daya fito dashi yasauka agaban riganshi yana kyalli kana gani kaga dimond, fuskanshi har wani sheki yakeyi idanunshi sanye da bakin glasses na police sabida plastan dayake idanunshi, duk wanda ya kalleshi saiya sake juyowa ka kalleshi zaka dauka wani musician ne yazo, agogon dake hannunshi ya kalla na Horus, ganin 11:15AM yasa yadanja gajeren tsaki, bayanda zaiyi ne yazo hospital dinan all he needs right now is to smoke and yasami mace, rabonshi dayasha taba tun ranan nan, fitowa Dad shima yayi daga motan waya a kunnenshi yana magana awaya sanan yasa hannunshi yaciro wani katon teddy babba na lion king mai remote, idan kadanna remote din zaka dauka live lion ne yana tafiya sanan yay haushi, karasowa gaban Zayn yayi sanan yace “hold on Barrister lemme talk to my Son” cire wayan daga kunenshi yayi yakalli Zayn din, teddy yasamai a hannu yace “ga teddy daka sayama patient dinmu, jeka sami Mami ka Dr ka will see u daga nan I need to rush, one of the kidnappers da aka kama yay magana I need to go” yakalli bodyguard dinshi yana daya magana yace “go with Zayn” sanan yashafa fuskan Zayn din yace “bye son” ahankali yace “bye” sanan yawuce yana tafiya ahankali har zuwa gaban dakin da Farrah keciki, bodyguard din dake biyedashi yakalla yace “get me a pack of cigarettes” batare daya jira amsan shiba yabude kofan dakin yashiga ciki, jin anbude kofa an shigo dakin yasa Farrah tadago kanta da wuri hada idanu sukayi da Zayn daya kallo gadon dudda idanunshi nacikin bakin glasses but tsaf kallo daya Farrah tamai ta ganeshi, kafeshi tayi da idanu bata ko kyaftawa tana kallonshi kaman yanzu tafara ganinshi ganin ya chanza mata kaman ba mutumin jiya ba dahar kuka yake, yawani kara zama mata babba sosai a idanu kuma yay wani kalan kyau kara kallonshi take sabida sarkan dataga yasaka kaman mace, wani zirrrrrr yaji ajikinshi sabida yanda take Farrah ke kallonshi da manyan idanuwabta dake nan kar kar kaman madara dawani kalan sauri yadauke kanshi yakarasa shiga cikin dakin sanan yawani kalan defa mata teddy lion din akan gado tawajen kafafunta dasauri takalli teddy sanan ya jefa mata remote dinma da mistakenly ya danna remote din ya kunna teddy, Farrah dake kallon teddy ita Allah yasan bama tasan akwai abu kaman haka aduniyan nan ba, gani tayi teddy dake kwance kafanta yawani tashi tsaye lion din yana kallonta in the eyes, bala’in faduwa gabanta yayi, ganin yafara nishi yana bude bakinshi yay wani kuka tareda tsalle gabaki daya yasa daga pad da drink din datake sha duka tawani watsar dasu kan gado ta kurma ihu da Zayn dake zaune kan kujera yaciro wayanshi yana dannawa baimasan abinda ke faruwa ba yadago kanshi dasauri. “Aahhhhhh” wani kalan tsalle tayi ta dirko daga gadon tama manta tanada ciwo shima lion din tsalle yayo zai fado kanta wani wawan ihu tayi tama rasa inda zata fadawa kan dogon coach din da Zayn kezaune tayi tawani kalan fada jikinshi daga ita harshi fadawa sukayi flat kan kujeran yana kwance tana kwance saman jikinshi ta kankameshi gam gam jikinta nawani kalan rawa ta kulle idanunta, sake tsalle lion din yayi tareda haushi zaiyo kansu hannunshi da baida lpy Zayn yasa chak yakama lion din yana kallon fuskanta yanda lips dinta ke bari, gabaki dayan hanuwanta ta rirrikeshi dasu, kafe fuskanta yayi da idanu yana kallonta is she scared? Ya tambayi zuciyanshi, tureta yashigayi daga jikinshi kin sauka tayi taki bude idanunta ta makalemai wuya alamun barata sauka ba, baki yadan bude cikeda kulewa yace “sauka daga jikina” kaman wacce ke tsoroOOn bude idanunta tabudesu tadaura idanunta kan fuskanshi hakanan jJi tayi gabanta yafadi dum!….




EPISODE 1️⃣6️⃣
Dudda yana sanye da black glasses bata ganin kwayar idanunshi amman wani kalan cika mata idanu yayi gashi yana wani kalan kamshi da takeji kaman kada tasakeshi tunda take aduniyan nan bata tabajin irin kamshin dayakeyi ba Subhanallahi kamshin dadi, ganin yanda yabata rai yana jiranta ta sauka daga jikinshi yasa ahankali tashiga dagashi tana satan kallon lion din dataga yarike a hannunshi, komawa gefen kujeran tayi ta nannade kanta cikeda tsoro tana kallon hannun nashi dake rikeda lion din sai yanzu ma taji inda aka mata dinki namata ciwo, tashi Zayn yayi ranshi bace, kayan jikinshi ya kalla ganin yanda suka yamutse dudda bawani yamutsewan kirki bane amman jiyayi ranshi yabaci kallon Farrah yayi da itama daidai lokacin tasaci kallonshi wani dan iskan tsaki yaji. “Mtswwww stupid girl” yafadi ahankali ware idanu Farrah tayi jin yazageta bata wani jin turenci but tasan stupid tun a kauyen su wucewa yayi fuuu yafita daga dakin da teddy a hannunshi daidai bodyguard din daya aika siyomai taba nadawowa teddy yamikamai cikeda masifa yace “donate this teddy to children ward, apparently the stupid girl na tsoronshi” yay maganan yana fizge kwalin tabanshi yawuce waje jikinshi har tsuma yake yakosa yasha taban.






Shigowa dakin Mami tayi ganin Farrah zaune kan kujera yasa tace “Iyye kin sauko”? Kai Farrah tadaga zata gyadama Mami, Mami tai mata kallon no, hakan yasa tadan runtse idanunta tace “e……h” murmushi Mami tayi sanan yawo wajenta gefen kujeran ta zauna hannunta takama tace “nasan yanda kikeji, but idan zaki magana, relax, take it easy, kiyi maganan a sannu akuma hankali batare dakinyi tunanin komi ba, once kika koyama kanki kina amsawa da maganan nan da 2days zaki fara magana lafiya lau kinji” wanan karan bata lumtse idanu ba ahankali tace “ehhh” murmushi Mami tamata tace “ina Zayn, Dr shi na jiranshi” ahankali tana kallon Mami tace “f…….iiii…ta” “okay yafita waje, bari naje nakirashi muje ganin Dr, I am coming idan nadawo zamuje gida, zakije gidana”? Mami tamata tambayan cikeda so, wani cute smile tama Mami ahankali tace “eh” wucewa Mami tayi tafita daga dakin tana murmushi she so much love Farrah bama tasan mesaba.




Tana kaiwa gaban entrance din Zayn na zuwa wajen shima daidai yana yarda karan taban hannunshi wani kalan mugun kallo Mami tamai sanan kawai tajuya cus da mutane awajen binta abaya yayi zuwa office din babban likitan idanun wanda yake bature ganin Zayn yasa yau murmushi yace “Mrs Zayn I really like this your boy he’s so cute” murmushi Mami tayi tana kallon Zayn dako gaidashi baiyiba yawuce yay zamanshi kan gadon duba patient, tashi Dr yayi yazo yacire plasta idanun yana kallon idon yace “can you see me”? Kallonshi Zayn yayi yana ganinshi da idon amman ba sosai ba, murya chan kasa yace “I can’t see clearly with it” murmushi Dr yayi yadagashi yace “I expect that to happen, I made a glass for you dagakai amfani dashi for 3month, zaisa idanun su warke” yay maganan yana kawomai fararen glasses din, yasamai sanan yace “can you see me now” gyadamai kai Zayn yayi yana kallonshi Dr yay murmushi dan glass din yanamai kyau sosai kaman wani professional Dr dinan, Dr yace “that’s all” kaman jira Zayn yake yasauka daga gadon yafice, Mami ne ta kakalo murmushi tace “thanks Dr OP” murmushi yamata yace “you are welcome” fitowa Mami tayi Zayn haryadanyi nisa tace “Zayn” juyowa yayi jin Mami takirashi, anatse tace “to my office” tajuya tawuce, dan yatsine fuska yayi sanan yabiyota abaya, shiga cikin wani hadadden office tayi ta tsaya gaban kofan tana jiranshi shigowa yayi hakan yasa tamaida office din tarufe tasa key sanan tawuceshi taje ta zauna, agaban table dinta wasu kananun photo frames guda uku ne gaban table dinta daya na Zayn ne yana jariri, daya dayay graduating daga university dayan kuma hoto ta ne da Alhaji da Zayn tareda su, kujeran dake gaban desk din nabaki ya zauna ahankali tareda dan sosakai irin na yan iskan nan dan yasan fada Mami zatamai, Mami takai kusan 1min tana kallonshi yanda yakeyi tasan cewa yasan fada zatamai, tasowa tayi ahankali ta zagayo inda yake, dayan kujeran dake gaban desk din dake facing na Zayn din taja ta zauna ahankali tana kallon fuskanshi, cikin wata kalan tattausan murya tace “Zayn” dan dago idanunshi yayi yakalli Mami ahankali yace “Yes Mami” hannu Mami tadaura kan bakinta kaman tana kokarin taushe kuka ne komenene ma takeji oho kafin ahankali ta zare hannun tace “Zayn is this how you show Allah you are grateful daya ceceka yay saving rayuwan ke eh? Two days ago Zayn you were kidnapped, this is Abuja aka tafi dakai chan wani kauye wai kuduri a Adamawa inda badadan Allah yasa that girl” tanuna kofan office dinta, tace “that girl, dake kwance akan gadon chan ta taimaka maka tasamo maka waya munyi magana dakai ba hankalinmu ko tunanin mu bazai taba kawomana kanachan wata duniya Adamawa ba” Mami tai shiru sanan ahankali tace “Zayn you almost die, you almost lost your life, look at your hand” tanunamai hannunshi dake nan akarye an daure, tace “look at your eyes” tanunamai idanunshi dake sanye da glass, tace “look at your whole body an zaneka blue black, Zayn u remembered you were crying danai waya dakai kana fadamana you were scared Zayn harka manta” Mami tai maganan ahankali tana kallonshi, dan lumshe idanunshi yayi kana ganin yanayin shi kasan maganan ta shige shi, ahankali Mami tace “Zayn tunda kataso bakasan menene wahala ba but rana tsaka within just 48hrs Allah ya nuna maka akwai rayuwan da ita sunanta wahala, ukuba da tsantsan azaba, sanan yanuna maka dukiyarka is nothing bata isa ta ceceka ba alokacin dazai kamaka, sanan yanuna maka shi kaskantaccen mutum dabaka dauka a komi ba zai iya maka abinda babu wanda zai iya maka shi aduniyan nan, Zayn badadan this incident ba someone like that girl Farrah can not even come close to you cewa zakayi she looks scary sabida Yar kauye ce bata da kudi irin na gidan Baban ka, Zayn did you know cewa second chance Allah yabaka” Mami tai maganan tana dafa knees dinshi, ahankali tace “Allah has given you second chance amman harka fara misusing nashi, kafara shaye shayen ka, mutum bai isheka da kallo ba, ba salla ba salati, babu wanda yakai matsayin kacemai kagode or thank you, did you thank that little girl that saved your life and took a bullet for you”? Mani tai maganan tana daga murya, shiru Zayn yayi kanshi akasa hakan yasa Mami ta dakamai tsawa. “Zayn did you thank her”? Ahankali ya girgizama Mami kai alamun no, wani kalan murmushi tayi tace “Baban ka nada kudi kafi karfi kama mutum godiya ko Zayn, you feel idan taji sauki u can give her money, jirgi and just send her off that’s your thank you” Mami tai shiru tana kallonshi, takai kusan 2good minute kallonshi take idanunta sunyi ja kaman kai shirin kuka, ahankali tace “all this behavior naka Zayn is my fault, lokacin dazaka fara JSS1 da zaakaika outside I had the chance nace baza akaimin yaro wajeba anan gida agabana zai karatu but nai shiru nabiyema Allah kiri kiri inaji ina gani kaki dawowa Nigeria tundaga nan kana makale da baturiyan Nany dinka dake kula dakai achan look at you now Zayn at 26yrs old you can’t differentiate between right and wrong, ba salla ba salati, ba komi, rayuwa kawai kake mara amfani magana ma sai anyi da gaske kakeyi, Zayn why why Zayn hmmm? Kataba tunanin inda munrasaka in this incident yaya zamuyi da rayukanmu dagani har Baban ka, why don’t you wanna be a better person for the sake of son damuke maka eh” Mami tai maganan hawaye na gangarowa daga idanunta sharrrr, wani iri Zayn yaji dasauri ya kauda kanshi gefe tunda yake baitaba ganin Mami na kuka ba sai yau, sanyi jikinshi yayi ahankali yace “s……sorry Mami” girgiza kai kai tayi tace “I don’t want you to tell me sorry, I want you to start doing the right thing, amend your ways ka koma ga Allah, kafara rayuwa kaman wanda yakeda hankali yay girma, someone of your age, kasakama wayanda suka maka hallaci da alkhairi Zayn, I believe in you, you are a very good boy Zayn I know that cus ni ne mahaifiyar ka kaji” kasa daurewa yayi yanda yaji Mami na kuka ahankali yatashi daga kan kujeran juyawa yayi ahankali yace “Mami I am sorry” hannunta tasa dasauri kan idanunta tashare fuska nata dan murmushi tayi tace “zonan Zayn” juyowa yayi ahankali yakalleta ganin ta share fuskanta yasa ahankali yaje gabanta, murya chan kasa tace “promise me you will change” ahankali yace “I promise Mami” murmushi tamai sanan tai pecking goshinshi tace “tashi kaje I am coming” tashi yayi yawuce yafita daga office din tabishi da kallo.


Ahankali yake bude kofan dakin da Farrah take, zaune yaganta yanda yabarta dazu akan dogon kujeran nan tana bacci ga wayanshi daya gani tarike a hannunshi, dawani kalan sauri yataba aljihun shi jin babu wayanshi yasa yadan yatsine fuska probably dazu ne ya manta dashi adakin, maida kofan dakin yayi yarufe sanan yazo gabanta ya tsaya hannunJhi ya mika mata yace “ke give me my phoOne”.




EPISODE 1️⃣7️⃣
Ganin ko motsi batayiba yasa yay dan gajeren tsaki yaduko yana kallon fuskanta, hannunshi yakai ahankali yadaura kan wayan yaja cikin bacci itama taja tarike wayan gam tanadan gyara yanayin zaman datayi cikin baccin taredayin hamma, fuskanta ya tsaya chak yana kallon yanda take hamman tareda yin dan nishi ahankali, she looks super cute baisan mesaba hakanan kawai yatashi batare daya karbi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login