Showing 24001 words to 27000 words out of 131263 words

Chapter 9 - MACE A YAU Document from Sulaim .txt

24 Nov 2024

4858

kanta da tayi. Amsar wayar daga hannun ta tayi tace


Kije kiyi shirin bacci I know you must be tired ko?


A sanyaye ta Mike batace komai ba ta fita a dakin yayinda Mami ta shiga call log dinta Eldest ta gani wanda ya tabbatar mata Junaid Sulaim ta kira. Call duration ta duba wajen 7 minutes hakan yasa taji abu ya darsu a zuciyarta amma koma dai Menene she will keep eyes on both of them.




Shatuuu ♥️
[6/27, 3:29 PM] Shatuuu😍: *MACE A YAU*
8


✍️Shatuuu♥️


🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION


#⃣Shatuuu095@wattpad


Daidai bugawar agogon dake Makale jikin bangon dakin daidai fitowar Subay'a daga parlonta, tana sanye da Abaya beige color tayi rolling da milk din mayafin da sukaxo tareda abayar. Junaid na zaune kan two seater gabanshi system dinshi ce akan center table se kafafunsa da ya daura akai. Aiki yake sosae Don Tun Azahar yake Abu daya sallah ce kawai ke tashinshi. Tun kafin ya san da zuwanta turaren da take using me dadin kamshi ya bayyana kanshi, lumshe idonsa yayi a hankali kafin ya bude su ya zube a kanta, ko bata fada ba yasan fita zatai saboda kayan dake jikinta,


Papa aikin ne har yanxu?


Ta tambaya Bayan tayiwa kanta masauki a gefenshi, kanshi ya gyada tareda dagowa ya furzar da iska me huci yace


Wallahi kua Mimi dake haka yaran Ke ce mata.


Shagwabe fuska tayi wadda tasan baya taba resisting ta saka hannunta a kan sumar shi wadda babu gashin ma saboda yadda ake saisaye ta akai akai. Tace


Sulma ta haihu an hour ago.


Dagowa yayi Sulma sister Subay'a ce tare akayi musu aure shekara takwas kenan amma bata taba haihuwa ba se yau shi baisan tana da ciki ba ma. Murmushi ya saki yace


Mashaa Allah Alhamdulillah! Me ta samu?


Baby girl!


Addu'a yayi sannan ya cigiba da aikinsa duk da yasan abinda ta ke nufi amma se ya share ta. Ta kusan 5 minutes ganin idan ta zauna haka Itace a cuce hakan yasa tace


Papa ina son Zuwa ne.


Bai kalleta ba yace


Se da safe is already late yanxun.


Baki ta turo tace


Haba mana Honim har na fadawa Yaya Suhaila tazo mu wuce tare.


Pen din hannunshi ya aje tare da rufe system din ya dago ya zube idonshi cikin nata, kasa jurar kallon tayi hakan yasa tayi kasa da kanta, babu alamar wasa yace


Subay'a kullum kin fison ki nuna min abinda kike so shi zaayi? Abinda zuciyarki ta Raya miki se kin yishi. Banda kin raina ni ma se da kika shirya kika hada connections dinki sannan zaki zo ki fada min? Nace ba zaki je ba idan kuma ban isa ba ga hanya nan.


Yana Kai aya ya Mike ya fara tattara kayanshi ranshi a bace saboda ganinshi raini ne kawai dan ta samu yana tolerating dinta shi ne zata dinga duk Abinda ta ga Dama, shi ba irin sauran mazajen yan uwanta bane da zasu dinga biye wa matansu.


Tashi tayi ganin ya nufi daki ta bishi, ranta a bace amma Tunda ita take neman abu dole ta yi kasa da kanta. A bedroom ta sameshi Yana jona system dinshi, a hankali ta bude Baki zatayi magana yayi saurin daga mata hannu yace


I've said enough kiyi yadda kike so, idan Kinje ya rage naki..


Bata jira komae ba ta fice daidai shigowar Suhaila parlon, dama ita daya ce shi mijin na waje dan haka tana shigowa ta Fara fadin


Subay'a fito mu tafi ko ma dawo da wuri.


Yadda taga Subayan yasa tace


Kada kice ya hanaki Zuwa?


Kanta ta langwabar Cikeda bacin rai tace


Wai se gobe.


Baki Suhaila ta tabe tace


Ke kuma se goben kenan? Kowa ya tafi se ke daya zaki zauna se Kace tsoronshi kike ji, ni Wallahi na rasa me ke damun Junaid dinnan.


Ba Abinda yake damuna, magana ce na gama amma idan Ke kike auranta you can go with her.


Haka suka tsinkayi muryarshi Yana fada Ashe Tun shigowar Suhailan ya fito dan daukar Flash dinshi. Itama Suhaila Bata da mutunci tace


Oh haka kace to Wallahi se taje, Sede kayi duk abinda zakai.


Kunsan hali ya banbanta hakan yasa bai ko daga kai ya kalleta ba ya wuce bedroom dinsa, Suhaila ta dubi Subay'a wadda jikinta yayi sanyi tace


Zo mu tafi?


Ina? Na fasa kinga ranshi ya baci kawai nazo da safen


Ta fada Tana me jin takaicin Junaid, su takwas suke gurin hajiyar su amma baki daya Junaid shi ne me matsala bai taba yadda an juyashi ba kamar yadda ake juya sauran sirikan kuma lokacinda ta aureshi tunani suke sun auri wawa Ashe ba anan abun yake ba. Cikeda bacin rai Suhaila tace


Karki cemin threat din Wannan hopeless element din zai sa ki fasa zumunci? Idan akwai me Zuwa gurin Sulma ai a bayanki ne.


Itama tana jin hakan amma Tunda take da Junaid Bata taba ganin ya Daga murya haka ba, it's unlike him Wannan yasa taji tsoron fitar take.


Nidai kawai kije Yaya Suhaila kinga kar na bullowa kaina wani aikin.


Wata harara ta watsa mata Tace


Kinsan Allah kafata kafarki wawuya kawai.


Haka Suhaila taja Subay'a suka tafi, Junaid dake jin komai ya saki murmushi ya fito lokacin har sun bar gidan. A cikin mota kasa sakewa tayi, suna gaisawa da Ishaq ta bame bakinta, tana jin yadda suke hira amma ita kam babu Wannan damar a haka suka iso Standard hospital dake tarauni lokacin goma Harda yan Mintina amma dakin da take kamar rana, Tun a parking space suka hadu da mijin Safina, Surayya da ita Sulma din. A waje ya tsaya suka shiga ciki a cikin su takwas Samina ce kawai bata nan itama sun je Mexico ne itada yaranta, Tun dazu da taji labari take jin tamkar tayi tsuntsuwa ta taho amman babu Hali. Suna shiga suka samu hajiya tana zaune kan wata kujera dake dakin su kuma sauran suna kasa an shimfida carpet se hira suke yayinda Sulmar idanunta ke a runtse tun dazu take son ta runtsa Tunda an sha artabu amma by mere kallo abin bazai samu ba. Suna zama aka Fara sabuwar gaisuwa se hira ta kuma ballewa, Sulma ma haka ta shiga anayi da ita. Mukhtar mijin Suhaila ya shigo Yaga baby sannan yayi musu barka ya koma waje hakan yasa hajiya tace


Subay'a ke ina naki dan ka gadama ko bai gadamar ba.


Kafin ta bada ansa Suhaila tayi caraf tace


Kinsan hajiya me yayi mana...... Nan ta kwashe komai ta fada musu, wani mugun zagi Salima ta saki tace


Shiyasa kika shigo jiki a sanyaye, Ke wacce Irin Shashasha Allah ya hada mu da ita? Ke me miji ko to Samina ma da bata kasar jibi zata iso.


Ba haka bane.....


Rufe min baki


Hajiya ta fada


Sau nawa ina ja miki kunne akan mijinki, yaro daya kusan shekara takwas kin zauna Yana juya ki Kece koma baya cikin yan uwanki, to ki sani har ayi suna babu Wanda na daukewa zuwa yaga Sulma don gobe gidana zan tafi da ita.


Da sauri Sulma tace


Gidanki hajiya? A'a munyi dashi gida zan zauna.


Suhaila ce ta maka mata harara se Safina cewa tayi


Ikon Allah, wannan fa rule ne is not yadda kukai dashi haka ne policy yake kuma haka zakiyi biyayya.


Kanta ta kada tace


A'a gaskiya....


Dallah rufewa mutane baki


Surayya ta fada waaddda kusan shi ne lokacinda tayi magana, hajiya kuwa kawai kallonsu take a ranta tana tunanin yadda zata daidaita su.


Basu suka fito ba se 11pm har da Rabi, dukkansu suka fito Sunata hira da dariya, masu drivers suka shiga masu miji suka bisu shikam mukhtar ranshi a tsananin bace yake Amma babu damar magana a haka suka isa gidan Junaid, mukhtar ya fita ya buga amma shiru Wasawasa sunfi Mintina goma suna bugawa babu Wanda ya bude musu gashi akwai echo kasancewar dare yayi sosae, gaba daya suka fito Subay'a ta rasa inda zata saka ranta taji sanyi, gaba daya ta rasa a duniya abinda Ke mata dadi kuma ta kira wayarshi a kashe haka tasu Atika da gateman hakan yasa tana kuka tace


Kinga abinda nake fada miki ko Yaya Suhaila dama nasan Wallahi Junaid se ya bata min rai.


Tsaki Suhaila tayi hakika Bata taba katari da dan iska Irin Junaid ba, ita tunanin hakan bai zo mata ba shikam mukhtar dadi yakeji a ranshi Yana inama yanada courage din Junaid. Haka Suhaila ta kira hajiya ita kuma Tace subay'a tabi su ta Kwana a can.


To fa people kunji wannan!


Tunda ta fita Junaid ya sanar dasu su rufe gida sannan kowa ya kashe wayarsa yana ganin is high time ya kamata ya fito ma Subay'a a yanayin da take so dama bahaushe yace idan kida ya canja to salon rawar ma canjawa yake.


Haka Subay'a Tana gani suka nufi gidan Suhaila dake gaba dasu, Tun tana kuka Suhaila Na bata Baki har ta share ta. Haka wannan Daren ta rabashi tana tuntuni da da nasani Marar amfani. It's too late to cry when the head is cut off.


Shikam Junaid baccinsa yayi dukda yana missing Sulaim komanta maganarta, shagwabar ta, murmushinta da ita kanta don tun ranar da sukai waya taje kaduna basu sake magana ba dukda dimbin urge din dayake jin akan son jin muryarta amma a haka ya hakura shi lallai Lokaci baiyi ba.


Da Asuba ya hada musu kaya shida yaran ya sallami duka cooks din sannan ya zubawa Matar gidan kayanta yawanci na office ne sannan ya rubuta wani abu cikin takarda ya bawa driver dinsa da key din motarta akan yakai mata gidan Suhaila, shikuma ya tasar mawa Kaduna shida yaran.


Turkashi!


Seda ya gama parking sannan ta bude kofar ta fito, idanunta suna cikin wani glasses square shape fari me fadi Wanda ya rufe kusan har kusa da cheeks dinta yayi mata kyau kuma ya bawa hancinta dayake dogo damar fito da aihnahin pointedness din nasa, fuskarta babu ko fara'a akasin yadda asalin Sulaimi take, cikin nitsuwa take takowa har tazo daidai kofar parlour taga an bude Ja'afar ne, Fuskarshi shima babu walwala amma yana ganinta tamkar dama ita yake jira ko kuma nemanta yake oho musu, hannunta ya jawo wanda yasa tayi saurin kallonshi tareda kicinayar kwacewa amma ya damke da kyau seda ya kaita har bakin motar shi kafin ya sake mata hannun aikuwa kamar jira take ta sakar mishi duka a kirjinshi tareda fadin


Don't ever touch me kaji na gaya maka.


Murmushi yayi yace


Ba wannan ne damuwata ba, the fact that kawai dan kin ganni da wata se kiyi ta fushi? Kwananki uku Amma you shun my calls ina miki magana kina basarwa Duk saboda wannan to shikenan Sulaim am sorry she's just a friend and nothing more I'm really sorry bazaki kara kamani da irin laifin ba. I'm sorry please Luff.


Tunda ta Fara magana take kallonshi wani side na zuciyarta na fada mata karya yake wani kuma want to believe him Sede na farkon Yafi rinjaye amma se ta bashi another chance Tace


Yaya Ja'afar I will never take shit from you ever again, never! Da nayi amma yanxu the world is vast I can't, Nasan halinka kuma duk wanda kake tare dasu na sani amma I never taught it can go to the point where kacewa budurwarka I'm your baby Sis. I won't take that. Idan yan matanka kake so Dan Allah kaje ni bazaka Bata min Lokaci ba.


Wani madaukakin mamaki ya addabe shi da gaske Sulaim ce ke blabbing words dinnan? Eh gaskiya university ba karya bace, wannan ba karo bane na farko da ta ganshi da wata ba amma she never fuss on it se yau tabbas akwai aiki gaban Maza.


Naji it's OK zan kiyaye yanzu smile mana.


Harara ta maka masa ta juya Don komawa ciki sede kamar ance daga kanki taga Junaid a tsaye jikin railers da suka kawata balcony saman, ya zuba hannayensa cikin pockets din wandonsa yana kallonta, wani Irin kallo yake mata me Cikeda dimbin tambayoyi, tuhuma da kamar you failed me haka ta gani cikin idanun shi, sauke kanta tayi ta kasa motasawa Daga gurin Ja'afar dake tsaye bai lura ba Yana mata dariya yace


Sweetm idan ba zaki shiga ciki ba zo muje kisha ice cream.


Kawai zuciyarta ta Raya mata kibi Ja'afar haka kuwa tasa kafarta a nutse a kuma sanyaye ta fada motarshi, Junaid da yaji kamar ya Kurma ihu haka yaja dogon huci tareda lumshe idonsa.






To fa one word for the page, for Junaid, for Ja'afar, for Sulaim and for Subay'a da danginta.




Shatuuu ♥️
[6/28, 7:40 PM] Shatuuu😍: *MACE A YAU*
9


✍️Shatuuu♥️


🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION


#⃣shatuuu095@wattpad


Yana bude idanunsa wanda suka kusan Mintina biyar a lumshe, se ganin shigowarta yayi hakan ya bashi mamaki Don a iya saninshi tabi Bayan Ja'afar ne su fita. Itama Sulaim din bata kuma dubar inda Junaid yake ba ta shige cikin parlour, Mami ce kadai a zaune se Muhammad da Ahmad, suna jin muryar ta suka taho a guje suka rungume ta, itama rungumarsu tayi tana ta murmushi, kwanaki biyar kawai da zuwana kaduna take jin tayi missing dinsu sosae. Hannunsu taja suka samu guri kan carpet suka zube suna tayi mata surutu wanda Seka rasa inda suka gadoshi kasancewar iyayensu kaf babu me surutun sede ko idan Jawad da Ja'afar sukai wa Kara.


Auta kin dawo?


Dagowa tayi ta dubi Mamin tace


Na dawo Mami, Tace Tana gaisheki sannan da zarar kayan sun iso zakiji sakonta.


Kai Mami ta gyada tace


Yayi kyau, Allah ya miki albarka, Junaid Yana tambayarki kun hadu?


Take yanayinta ya canza dama dalilin da yasa Mami yin maganar kenan tana zargin akwae Abinda Ke aukuwa between the two.


Bamu hadu ba, tare yazo dasu Ahmad?


Eh


Kawai Mami tace ta cigaba da Abinda take itakuma tana wasa da yaran.




Wani ihu Subay'a ta saka lokacinda mukhtar ya mika mata key din motarta hade da farar takarda cikin farar envelope,


Yaya Suhaila na shiga uku ya sake ni, Abban Fannah kaje ka bashi hakuri , na shiga uku!


Baki daya babu wanda ya samu courage din tunkarar ta, hatta shi mukhtar wanda Tunda Sabi'u driver ya bashi takaddar yake murna cikin ransa Don Yana son su koyi hankali baki dayansu. Amma yadda Subay'a ke yin abu se yaji baki daya tausayinta ya kamashi, itakam Suhaila ba karamin rudani ta shiga ba saboda tasan duk inda aka je tanada kamasho cikin wannan abin. Subay'a kam bazata ma iya fadar yadda take ji ba se kawai ta rabe su ta shiga dakin da ta Kwana ita bata bude takardar ba saboda tsoron content din ciki haka kuma Bata daina kukan da takeyi ba har Seda ya tashi Fannah yarinyar Suhaila, ganin halin da uwarsu Ke ciki yasa ta Mike ta fito parlour Don jin Karin bayani, a parlor babanta kawai ta tarar da Suhaila ta koma dakinta saka kaya gwara su tafi Asibiti ko gidan hajiya. Abayar da tasaka jiya ta sake mayarwa ko brush ba tayi ba ta fito hawaye Yana mata zarya, ita bata taba tunanin Junaid zai iya makamancin haka ba, ko sau daya bata taba kawowa dan abinda ya faru jiya can lead to such commotion. Tare suka fito da Suhaila wadda lokacin tace


Abban Fannah Bari muje gidan hajiya, Fannah do the right thing.


Bata jira amsar daya daga cikinsu ba tayi hanyar waje, ita ta karbi motar tana driving bayan Sulma ta tabbatar musu kowa na asibitin, don haka can suka nufa.


Kiyi hakuri Subay'a ban kawo abin zai zama haka ba, amma kema tunda Kinsan halin mijinki ai you shouldn't have followed me.


Kunji fa bayan seda tace bazata je ba ta tursasa mata amma yanzu take dora mata blame din itadai jinta kawai take amma gaba daya hankalinta ya tafi Irin rayuwar da zatayi idan Junaid ya saketa, kenan ta kaishi bango? Kenan ta kure hakurinshi? Dama idan bakaji bari ba kaji Hoho.


A asibiti kamar jiya haka suke zaune kowacce tayi shiga ta alfarma, kayan wannan yana cewa na wannan bani waje Don a su takwas babu wadda Ke Auren talaka dukkansu masu kudi ne tamkar policy haka abin yake. Tundaga sallamar Suhaila Salina tace


Lapiyarku?


Hajiya da sauran suna binsu da kallo har Subayaa ta fada jikinta tare da fadin


Hajiya Junaid ya sake ni na shiga uku.


Gaba daya salati suka saka saboda yadda abin yaxo musu a bazata.


Me ya faru?


Hajiya ta tambayeta Tana dagota Daga jikinta. Ba karya ta zayyane mata komai tareda mika mata envelope din. Karba tayi itama jikinta yayi balain sanyi ta buda sede content differs from Abinda kowa Ke tunani.... It says


Ki zauna a gida ki Bari har se ranar da babyn yayi Kwana arbain se ki dawo.




Wani sigh of relief ta saki tareda bawa Surayya wadda ta karanto a fili nan take jikin kowa yayi dadi se kuma suka Fara zaginshi shi uban waye da zai musu gatse Wallahi ba zata koma ba se ranar da ya yanka mata kuma se Sun gwada mishi tana da gata. Itakam Subay'a batace uffan ba se godewa Allah da take, anan tayi wanka dake seminar bank dinsu ya turata Hakan yasa Bata fita Tunda online ne seminar kuma se wajen laasar ake Farawa. Baki daya suka tafi suna kara lallashinta akwai solidarity sosae a tsakaninsu. Daga ita se Sulma suka rage a dakin Bayan kowa ya fita tace


Sister dama Papa bai yarda ba jiya kika fito?


Dago kanta tayi fuskarta Cikeda alhini tace


Seda naki zuwa tunda yaki bari amma tace Wallahi se naje.


Haba Sister kina me ita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login