Showing 123001 words to 126000 words out of 131263 words

Chapter 42 - MACE A YAU Document from Sulaim .txt

24 Nov 2024

4827

yake ciki ba, gaba daya ya lalace Lokaci guda, zuciyarshi ta gaza nutsuwa balle kwakwalwar kanshi ta samu ta huta ya koma kamar wani zarare, don tunda Gwoggon shi ta ganshi bai kuma taka kafarshi waje ba, gaba daya wayoyinshi ya kulle su ya hana kowa zuwa inda yake banda Kabir wanda ke tausar shi Yana bashi baki. A hankali kwanaki suka shude yayinda Al'amuran ke kara tabarbarewa Musbahu, Zuwa lokacin yaje gurin gwoggo yafi a irga amma babu wanda ya san inda ta tafi ko Kabir kin fada mishi yayi saboda warning din da Gwoggon tayi mishi, shikam Musbahu nemanta yake ta yanke mishi duk hukuncin da tayi niyya amma ya rasa ta hakan ya kara tabashi.


Sannu a hankali Khulthum ta Fara warewa, cikin ikon Allah da taemakon gadgets din da akayi amfani sphincter dinta ta dawo aiki Sede kowa yasan ba'a bari a kwashe daidai amma babu laifi lafiya ta samu!!!






Shatuuu ♥️
[9/13, 9:11 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU*
58


✍️Shatuuu♥️


🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION


#⃣Shatuuu095@wattpad


*This page is entirely, wholly dedicated to my ghost readers, those who read and go without voting or commenting, shatuuu ♥️ still appreciate and she loves Evey single one of you*


_Oh yeah... It was revealed in the Qur'an that every soul must surely taste the bitterness of death..... Allah baya barin wani don wani yaji dadi, this is life nothing is permanent, everyone of us is waiting for his time..... Kui hakuri nasan kunnuwana se sun gaji da jin complains, don't mind me... I love you_


A hankali ta Mike ta nufi toilet din dake cikin dakin da suke, Babu laifi jiki yayi kwari sosae sede dukda haka ba'a sallame su ba don ana mata sphincter training hade da treating wasu infections din da suka samu matsugunni a cikin jikinta. Alwala tayi ta fito inda carpet din sallah yake a shimfide, hijab ta zura tareda kai dubanta gefen da Gwoggo take takure, gabaki daya Matar ta rame tayi xuruxuru kana kallonta kasan akwai abu me girma dake hanata sukuni a zuciya, Tunda suka zo kasar Abu biyu take banda ibada da tarairayar Khulthum babu Abinda take, hakan yasa Khulthum din hankalinta ya kwanta kafin wani Lokaci ta Fara maida jikinta tana murmurewa gashi babu inda take zuwa banda ta sakko daga gado taci abinci Se sallah ko wanka kafin wani Lokaci me tsawo AC tayi aikinta, skin din Nata ya zama flawless tayi shar se daukar idanu take. Abu daya ne cikin zuciyarta damuwar past dinta Wanda suke hunting dinta babu dare babu Rana har ta kan zauna Tasha kuka kamar ranta zai fita, ko sau daya bata ga laifin Musbahu ba, bata kuma ji haushin Abinda yake mata ba saboda whatever life be ita ce ta saka kudinta ta siya, ita ta kai kanta har gidan Musbahu ta kuma dauki kafafunta ta kai dakinshi, inda hakane meye laifin Musbahu wanda Allah ya aiko shi don tayi realising mistakes dinta through him? Ita kanta a rayuwarta tasan she deserves abinda Yafi haka, tasan ta wulakanta mutane ta ketare iyakar da Allah ya gindaya mata to ta yaya zata ga daidai?


A bangaren TitαΦ kam abin ya wuce gaban magana, Tunda suka hada idanu da gwoggo ta zare nutsuwa, farin ciki da dukkan komai ta wuce dashi. Gaba daya ya koma tamkar mahaukaci ya lalace ya daina fita ko ina sede gida se kuma massallaci, hakan ya tada hankalin Kabir sosae don dama Irin su Musbahu basu iya tashin hankali ba Tunda ba magana suke ba Balle su fadi wani abun suji sanyi a zuciyarsu, Wata ranar alhamis Anty daddafe ya samu ya isa office saboda korafi da yake samu daga gurin board members dinshi akan shafe wata daya da yayi baya Zuwa office kuma bai nada kowa ba hakan yasa babu yadda ya iya ya koma, sede kallo daya zakai masa kasan Maza suna wani hali.


Ya dade rikeda Biro hannunshi ga tarin papers cikin files da suke jiran signature dinsa amma ya gagara nutsuwa ya karanta content din ciki Balle har ya saka hannu. Tamkar wanda aka tsikara haka ya Mike ya dauki key din motarshi bai ko amsa maganar da secretary dinsa ke mishi ba ya biyo lift Cikeda hanzari ya wuce zuwa motarshi ya tayar tareda buga wani uban horn take securities din dake gurin suka Mike afijajan, Allah kadai ya tsare zuwan shi gida, ko gate bai shiga ba ya yi wani mugun parking sannan ya fito ya shigo cikin compound din a hargitse wanda yasa securities din dake gurin maida dukkan Hankalinsu kanshi sede ko kallon inda suke ya durfafi part din Khulthum, da kafarshi ya hankada main kofar dake ba a rufe take ba yasa ta budi Sede wani Irin yanayi na sanyin jiki ne ya mishi rubdugu Lokaci daya saboda yadda parlon yayi kura alamar babu mutane a gurin, wannan sassanyan kamshin da se yau yake jin ina zai sake jin irinshi, jiki a sanyaye ya nufi dakinta Sede wayam ya gani babu kowa a ciki, kaya ya hango a tukunkune akan gado hakan yasa ya isa gurin tareda saka hannunshi ya bude amma wani wari ne ya dake shi hakan yasa ya ja da baya yana kallon yadda kashi ya bata mishi hannunshi, runtse idonshi yayi da karfi don yasan Khulthum ta samu wannan matsalar ta dalilinshi ne, don ana ya gobe zasu hade da gwoggo ya iske ta a dakin kwance a wannan halin hakan yasa yayi ficewrshi, yanzun ma tunawa yayi bafa Gwoggo kadai ya zalinta ba hatta Khulthum ya zalinta kuma idan bata yafe ba bazai taba samun kwanciyar hankali ba.


Wasawasa Musbahu haka ya koma kamar wanda ya zare kwatakwata nutsuwa babu ita a rayuwarshi hakan yasa Kabir yanke shawarar fada mishi inda Gwoggo take ko Za'a samu ya daidaita saboda ba karamar asara ake tafkawa a oil, flour da food company din saboda rashin shi. Wannan yasa Kabir kammala mishi komai ya rakashi airport yana tsaye har jirgin ya daga sede a wannan lokacin Musbahu yaji Anya Yana son ganin Gwoggo? Wani hukunci zata yanke mishi.


Misalin bakwai na safe a agogon dake kasar ta India, an kammala bawa Khulthum maganinta na safe hakan yasa ta shiga tayi wanka sannan ta fito jikinta daure da towel wanda ko gwiwa bai Kai ba, Gwoggo ta fita karbo wani sako hakan yasa Ita daya kawai ta rage a dakin, a hankali taji an turo kofar an shigo amma ba'ayi sallama ba amma kamshin turaren da ko a kabari taji shi zata gane maishi, kafin wani Lokaci jikinta ya fara rawa tamkar mazari ko wadda ake kada mata wani abu haka ta jiyo amma se me shi dinne! Musbahu ne tsaye helplessly, idanunshi sunyi jawur ga wata uwar kasumbar da ya Tara ta cika Fuskarshi tamkar wani Tsoho haka ya koma, a hankali ta dinga ja da baya tana girgiza mishi kanta yayinda shima yake takowa cikin nutsuwar da ya rasa Yaushe ta dawo jikinshi, wani kuka ta saki jin ta kai karshen bango, runtse idonta tayi jin ya riko hannunta cikin nashi tamkar Marar lapiya ya bude bakinshi karo na farka ya kira sunanta wanda yasa ta bude idonta da sauri suka sauka cikin nashi kwayar idanun, Khulthum ta sha hada idanu eye ball into eyeball amma se ta tsinci kanta cikin wani yanayi me wuyar fassarawa ta manta rabon taji Irin wannan tun akan Ashir, a hankali ta lumshe idonta saboda kallon is so intense ga effect dinsa sosae yake ratsa jikinta. Shi dinma hakan ce ta kasance bai taba tsayawa da mace so close haka ba, bai taba kallon mace cikin idanu ba, Ashe haka abin yake, is this how it feels se yaji tamkar zuciyarshi na budewa ne yaji wani bakon yanayi me nauyin gaske yana shigarshi and that's *LOVE*


Hannunta na cikin nashi yace


"Ban canci second glance daga gareki ba, I know I was bad I was never good amma dukda haka ina Baki hakuri ki yafe min, kilan Allah ya sassauta min laifukan da nayi mishi"


Kuka sosae Khulthum take lokacin ta zura wata bakar abaya wanda tun zuwanta ire iren su take sawa kawai a jikinta, hannunta tasa ta kara rufe fuskarta zuciyarta wani Irin sanyi take ji, tasan ko babu komai Allah ya yafe mata Tunda har ya kaddaro shiryuwar Musbahu to ta yaya zatace bata yafe mishi ba, Bayan itama wasu sunyi overlooking kurakuranta sun yafe mata kuma jikinta yana Bata Allah ya gafarta mata sannan Hajiya Shatuuu ta yafe mata hakan yasa ta sauke hannunta tareda kallon inda yake Zaune ya tsira mata idanu tace


"Allah ya gafarta mana duka,.... "


Bai barta ta kammalla statement dinta ba ya iso inda take ya rungume ta so close, so tight and so romantic. For the first time Musbahu yaji sanyi a zuciyarshi yaji wani abu ya darsu cikin zuciyar shi. A wannan halin Gwoggon shi ta shigo bakinta dauke da sallama sede bata iya karasawa ba ganin Musbahu shima a rikice ya Mike se kuma ya sunkuyar da kanshi saboda wata kunya da ta lullubeshi, Khulthum kwatakwata Bata san Abinda Ke faruwa ba, amma kallonsu da tayi tasan they need privacy hakan yasa ta dauki siririn mayafi ta yane kanta dashi ta fice tareda janyo musu kofar ta samu wani guri ta zauna Tana jin tamkar tayi completing wani mission ne.


A cikin daki kuwa dukkansu shiru sukai kowanne Ya kasa magana se Musbahu ne ya isa inda Gwoggon Ke zaune ya Dukar da kanshi tareda dira gwiwarshi a kasa yace


"Gwoggo ki dake ni, Kiyi min fada amma your silence is killing me... Nasan kwatakwata banyi daidai ba, nasan Allah ya hana amma nakeyi, na cutar musu yarsu banida wani uzuri gwoggo Dan Allah ki yanke min hukunci"


Gwoggo ita ta haifi Musbahu amma ta manta lokacin da taga yana kuka hakan yasa ta janyo kanshi ta Dora a cinyarta Hakan ya tsananta kukan da yake itama ta Nayi a haka suka shafe lokuta kafin Gwoggo tace


"Na yafe maka, kayi Istighfar ka nemi yafiyar Khulthum, ka rike sallah Tana Hana alfasha sannna kayi Tuba sahihan kada ka komawa laifinka ka gyara tsakaninka da matarka, ka dage da ibada Allah zai lamuranmu sannan ka manta na ganka ka dauka hakan bai faru ba, let's move on"


Wata nannauyar ajiyar zuciya Musbahu ya sauke hawaye na Kara mishi sintiri, is the thing he never expect, dukkan tunaninshi ya tafi a wahalar da zaisha kafin Gwoggon ta saurareshi Amma Allahu Akbar gashi ta karbeshi ta yafe mishi.


Kwanaki biyu suka Kara aka sallami Khulthum suka wuce saudiyya Don yin umara, Khulthum da Musbahu dukkansu masu laifi ne hakan yasa suka dage da addu'a ibada don har gwoggo na musu fada akan rashin hutawa da suke sede akwai wata shakuwa a hankali da ta Fara samun matsugunni cikin zuciyar kowannensu, a hankali suka Fara damuwa da Al'amuran juna wanda gwoggo ke Lura dasu a haka sukayiwa Nigeria tsinke.


Hannunshi dake jike da ruwan da yayi Alwala yasa ya shafa fuskar subay'a wadda Ke baccinta hani'an, a hankali ta gyara kwanciyarta hakan yasa ya dan bubbuga pilon da take kwance se ta bude idonta Wanda bacci ne fal cikinsu ta kalleshi, shima kallonta yayi yace


"Babe time for prayers! "


Kwabe fuskarta tayi kamar zatayi kuka saboda yadda bacci yake dadi kuma tasan nacin Junaid dole Se ta tashi haka ta mike ganin ta tashi yasa ya fice abinshi, yana zuwa yayi raka'atanul fajr sannan aka shiga sallah Yana idarwa kamar yadda ya saba idan Subay'a keda girki to ana Idar da sallah zai wuce gidan Sulaim, haka idan Sulaim dince Keda girki haka zaije gidan Subay'a hakan ba karamin kwantar musu da hankali yake ba don sosae yake kwatanta adalci don idan Yana tareda Sulaim tana jin tamkar ita kadai ce a duniyarshi haka idan Subay'a ce Wannan yasa kowaccensu take Zaune lafiya.


Sulaim na cikin daki ta Idar da sallah gabanta bowl ne Cikeda custard wanda Seda ta dama tukun ta tada sallah tsabar yadda yawunta Ke tsinkewa ko addu'a batayi ba ta janyo bowl din ta Fara sha babu kakautawa, turarenshi ne ya fara isar mata da sakon zuwanshi dake idan yazo key dinshi yake sawa kawai ya bude ya shigo. Kallonta ya tsaya yi baki bude ganin yadda ta zage tsakaninta da Allah, shigowa yayi ya karba spoon din hannunta yace


"Wai Dove meye sirrin custard ne? Ke yanzun da asuba ma sha kike"


Bakinta ta turo mishi tace


"Shiyasa nake sauri Karka shigo ka sameni, Barka da Asuba Heartthrob"


Zama yayi a gabanta tareda debo custard din ya kai mata bakinta sannan yace


"I'm fine baby sede missing din wannan shagwabar"


Rufe fuskarta tayi tana murmushi tace


"Kai Yaya na"


Bai bata amsa ba sakamaakon ringing din da wayarshi dake cikin Aljihun jallabiyar jikinshi ta Fara ringing ya ciro, haka kurum yaji gabanshi yayi mugun faduwa Amma haka yayi picking


"Mami barka da asuba"


Jin an ambaci sunan Mami yasa ta dago da sauri ta Kalli Junaid lokaci guda taga yanayinshi gaba daya ya canja damuwa kwance saman fuskarsa, ga kuma saurin mikewa da yayi Sannan ya fara ambaton


"Innalillahi wa Inna ilahil rajiun!!! Ya hayyu ya kayyum"


Cire wayar yayi Daga kunnenshi Cikeda tashin hankali yake kallon Sulaim wadda itama take kallonshi gabanta se faduwa yake, hannunta ya Kama Yana jin yadda harshenshi yayi nauyin abinda zai fada mata, haka kurum taji gabanta yayi mugun faduwa cikinta yayi wani Irin hautsinawa, a hankali kamar me rada tace


"Yaya waye.....? "


Se hawaye Sharrrrrrr ya fara zubar mata daga idanunta tsabar tsoron me zai fada, matsota yayi Zuwa jikinshi ya rungume hakan yasa ta kara fashewa da kuka, shima jiki a sanyaye yace


"Kiyi hakuri Allah yayiwa Imratun Ja'afar rasuwa! "


Kallonshi ta tsaya yi kamar wata doluwa saboda son comprehending abinda ya fada take, rungumeta yayi Tsam a jikinshi saboda yasan she's in shock ko ba'a fada ba, hakanan dai tayi shiru har ya kira Subay'a yace ta shirya yanzun zaizo su wuce kaduna don acan ta rasu Amma ga mamakinshi se cewa tayi


"Allah ya jikanta amma kui gaba na taho inda uzurirrika"


Baice mata komai ba ya kashe wayar tare da rike Sulaim ya zaunar da ita akan gado shi kuma ya nufi wardrobe dinta ya janyo trolley ya zuba musu kaya zuciyarshi a cunkushe tareda tunanin halin da Jabir yake ciki. Tunda Khulthum ta zauna Bata kuma magana ba har driver din da zai kaisu yazo, haka ya janyo hannunta suka shiga mota inda ta kwantar da kanta kan kafadarshi tareda runtse idonta, babu Abinda take iya ji se wani azababben Ciwon Mara dake damunta a Wannan lokacin idanunta ta runtse tareda matse hannun Junaid. Ita batayi kuka ba ba kuma tayi magana ba ta kuma kasa tantance Abinda take ji banda Ciwon mara.


A haka suka isa Kaduna babu Wanda yake magana har suka isa gidan inda tuni Imratu ta dade a makwancinta, saboda yadda gidan yake a cike haka babu yadda Junaid zaiyi ya bar Sulaim ta shiga ita daya, idanunta sunyi ja saboda azaba da kuma tashin hnkli, a parlor kasa ta tarar da mutane dankam inda ta hango Mami wadda kallo daya zai fada maka tashin hankalin da take ciki ga idanunta sunyi luhuluhu tsabar kukan da Tasha, cikin nitsuwa ta taka har gaban Mami sede kafin tayi magana wata mata dake kusa da Mamin tace


"Meye wannan yake bin jikinki? "


Da sauri Mami ta dubi Sulaim din, jini ne ya bata mata zaninta hakan yasa Mami janyota jikinta amma kafin wani Lokaci jini ya Balle mata ga azababben Ciwon mara kamar zata mutu, tuni hankalin kowa ya kara tashi, Mami ta rasa yadda zatai se kuka se Maman su Yaya Hanan ce ta kira Junaid a waya aikuwa se gashi shida Ja'afar hankali a tashe akai Asibiti da ita amma cikin dake jikinta na watanni uku ya fice Wanda babu Wanda ya san da zamanshi. Gashi ta zubar da jini sosae wanda dole Se an kara mata!


Shatuuu ♥️


[9/12, 10:38 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU*
59


✍️Shatuuu♥️


🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION


#⃣Shatuuu095@wattpad






*Halo people of Wattpad Wallahi page din naku ne, you guys are Muah.... I can't stop loving you exactly like the way I can't stop thanking you for always supporting me and gingering me Up!*








Mami na Zaune gefen gadon da Sulaim ke zaune ta hada kanta da gwiwarta tana kuka kamar ranta zai fita, yau Kwananta hudu a asibitin an samu anyi mata wankin ciki sannan Tasha jini Leda uku, yanxun ta dawo hayyacinta sosae don haka ita yanzun take kukan mutuwar Imratu, kuka sosae take Tun Mami na lallashinta har ta share ta itama tana matsar kwallar saboda yadda take tuna wacece Imratu a rayuwarta, tasan bata haifi mace ba amma Sulaim da Imratu sun mantar da ita wannan rashin da tayi.


Babyn dake kwance cikin peach Cot ta Fara kuka alamar ta farka, da sauri Mami ta cirota Daga Cot din ta Fara jijjigata har yarinyar tayi shiru, tsaida kukan Sulaim tayi ta miko hannunta babu musu Mami ta mika mata babyn, karbar ta tayi ta rungume a jikinta wani Irin son babyn na ratsa zuciyarta rayuwa kenan duk yadda ake dokin cikin Imratu ashe ajali ne don ita kanta batasan abinda ta Haifa ba tasan ta haihu Daga nan jikinta ya rikice duk wani taemakon da ya dace an bata amma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login