Showing 54001 words to 57000 words out of 131263 words

Chapter 19 - MACE A YAU Document from Sulaim .txt

24 Nov 2024

4849

ba me Cikeda tsantsani ba se ranar yace


Nayi da na sanin furta kalmar so gareki, naji kunyar tunanin Baki matsayin uwar 'ya'yana, Nayi asarar Bata Lokaci na gurinki......


Dakata Ashiru ko whatever your name is! Kayi kadan ka cimin mutunci saboda wata useless 20,000 dinka da kake tunanin ta siya maka ni! Allah ya kiyaye. Nima na fika bakin cikin tarayya da kai abun kunya na tsaya da bai not knowing dubannin mazan dake waje suna jirana.... Hopeless element kawai!!


Tana gama fadar haka ta balle Jakarta............




Shatuuu ♥️
[7/29, 6:16 PM] Ayshatuuuu: *MACE A YAU*
24


✍️Shatuuu♥️


🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION


#⃣Shatuuu095@wattpad


.....Ta Balle Jakarta wadda a ciki kudi ne da ya tasarwa 50k, cikin fushi ta irgo 20k ta zura mishi cikin aljihun gaban shaddar dake jikinshi sannan tace


Ga tsiyar ka nan, ga kudinka da Kake tunanin ka siye ni dashi, aje can me tsautsayi ta dauka amma banda ni Ummu_Khulthum na wuce ajinka Wallahi.


Tana gama fadar haka ta buga mishi kallon wulakanci sannan ta wuce ciki abinta, kallonta yake tayi bakinshi a bude tamkar statue haka ya zama a tsayen yana tunanin da gaske Khulthum ce? Da gaske? Shi ne abinda ya samu bayan shekarun da ya dauka zaman jiranta, Yana dakon sayayyarta. Tabbas kowa ka kalleshi ka barshi kawae.


Zan iya ce muku Wannan shi ne mafarin lalacewar rayuwar Khulthum, that's what makes Khulthum what she was a halin yanzu amma ko yaya kuma kome Khulthum ta zama ita ce sanadi.


Cikin gida ta shiga tana jin tamkar ta taka Arfa tana jin ta yakice kwallon mangwaro, Tana jin Duk duniya she's free. Kowa harkarshi yake hakan yasa ta shige daki ta Adana kudaden sannan ta cire kayanta ta zauna itada zani se vest Tana kallon film cikin system.... Ni dai nasan Khulthum batada system amma bansan inda ta samu ba. Tana nan kwance ta jiyo muryar Baba yana kwallawa Mama kira. Tsaki tayi a ranta tana fadin na tsani gidannan kayi aurenka babu ruwanka da hayaniyar nan. Bata Kara jin duriyar Baba ba se bayan 10 minutes sannan taji salatin Mama tana fadin


Amma yarinyar nan anyi 'yar banza. Khulthum! Khulthum!! Khulthum!!!


A hankali ta Mike Tana mitar kiran da ake mata kamar wadda tayi sata kuma Bama haka ba ita batai tunanin cewar abinda ya faru tsakaninta da Ashir zai iya shigowa gidan da wuri har hakaba. Fitowa tayi ta yafa dan karamin mayafin abaya Tunda taji muryar Baba, suna tsaye tamkar zakaru itama taje ta tsaya tana binsu da kallo


Dan ubanki me kika yiwa yaron can Ashiru?


Kallon Mama tayi ta kalli Baba Wanda fuskar ta kasa boye damuwar da yake ciki tace


Shi ne ake ta kwalla min kira kamar nayi wani laifin.


Mama wadda zuciyarta na wuya tasa hannunta ta bige bakin Khulthum tace


Mu sa'anunki ne kike mayar mana da magana? Uban me kika yiwa bawan Allah nan.


Tsaki tayi a ranta tace ni kuma bawan shedan kenan? Dauke kanta tayi hakan yasa Mama tayo kanta zata buge ta Baba yace


Karki taba ta, khaltume zauna.


Babu musu ta zauna kamar yadda yasa Mama ta zauna shima hakan yayi kafin ya gyara muryarshi yace


Ina saurareki


Baba bana son shi, nace mishi ya rabu dani yaki saboda kamar zargina yake kuma yayi tayimin gori......


Shi ne kika maida masa Dubu ashirin dinshi?


Mama ta katse ta, Baba ne yace


Maman Aisha Kada ki Kara magana se na baki izinin yin hakan, ke khaltume kikace bakya son shi?


Kanta ta gyada batareda ta furta komai ba, kai Baba ya jinjina yace


Lokacinda kika kawo Ashiru a matsayin me nemanki, ke Kika karbi kudinshi ko ni?


Kai ne


Yayi kyau, me yasa yanzun kika bashi Bayan Baki sanar dani ba, karamin mutum kike son maidani?


Bakinta ta turo a ranta tace wai karamin mutum? Shi babba ne Dama? Talaka futuk se shegen policy na banza da na wofi!


Ganin haka yasa Baba ya gyada Kai tareda ciro sababbin 1000 naira notes guda ashirin ya mikawa Khulthum yace


Ga kudinki nan na mayar mishi da nashi, Amma ki sani kin nuna min ni ba ubanki bane kuma duk Abinda zai faru dake hannuna bazan kuma sawa a ciki ba. Ke kuma Maman Aisha


Ya juya kan Mama Ya cigaba da fadin


'yar ki ce na tsame hannuna daga kanta, Duk wani abinta kukai wa dangin mahaifinta.


Haba Malam! Haba


Kanshi ya girgixa yace


Ki bar maganar kawai. Aisha!


Dama tana kusa se gata ta fito ta tsugunna gefen Khulthum wadda Tana ta Harare Harare a ranta tana ayyana taji dadi da me yake mata zai zo Yana kumfar baki kamar ubanta, ita Wallahi tun tuni take son komawa dangin ubanta me take tsinta anan? Banda wahalarsu da aka daura mata. Zancen da Baba yake Yi ne ya saka ta dawo hayyacinta


.......Daga yau inhar kin daukeni mahaifi inason duk lokacinda Ashiru ya shirya ki aureshi, don na Karba kudin 'yar uwarki na maida kanki.


Mama ce tayi saurin fadin


Haba Malam, ya zaayi haka? Idan Khulthum a bacin rai ne fa tana son abinta fa?


Mamaki kwance saman fuskar Baba yace


Dama na dade da sanin haka, khaltume a gurinki ita kadai ce 'Ya , na miki uzuri saboda haka dan fari yake amma son kan naki yayi yawa. Ki sani na Bata dama don haka A'isha ki sawa ranki bakida miji se Ashir sede idan wani cikinku ne ya mutu ko kaddarar rayuwa!


Mikewa yayi Don ficewa Khulthum tayi saurin mikewa tace


Basai an nuna min cewar banida uba ba, basai an nuna ni agola bace Aisha ita ce yar masu gida, idan da kara kwarton uwa ai uba ne, naki abu sannan abawa Aisha shi ba? Da idan kunsan yar ku kuke son ya aura meye abin labe......


Ke amma 'yar iska ce, Baban kike fadawa haka saboda bakida mutunci?


Amir ya fada wanda Shigowarshi kenan yaji diban albarkan da Khulthum take musu. Juyowa tayi ta kalleshi tace


Nayi din kuyi abinda zakui, Dan rashin mutunci.....


Bata karasa ba saboda yadda Amir yayo kanta tamkar zaki sede bai Kai ga yin abinda yayi niyya ba Baba ya dakatar dashi tareda fadin


Kyaleta, batada laifi. Uwarku ce me laifi don haka ko na fita kada wanda ya kulata. Allah yayi muku albarka.


Yana fadar haka ya sa kanshi ya fito, Mama daki ta wuce tunda ba Abinda zatace kuma a ganinta Baba yaso kanshi ne da yawa.




Cikin makeken office dinshi na Managing Director of TitαΦ Flours Yana zaune kan kujerar yana rocking kanshi, Kwana biu nan bashida nutsuwa sosae ya rasa inda zai saka ranshi yaji dadi. Knocking yaji yasan bazai wuce secretary dinshi ba hakan yasa ya bada izinin shigowa,


Sir, Kabir is here


Let him in


Ya fada batareda ya dago ba, ba'a fi 3 minutes ba Sega Kabir ya turo kofar ya shigo, Yana ganinshi ya Mike suka dawo kan cushion din office Bayan sun gaisa aka kawo musu coffee, Seda suka shanye tas kafin Kabir yace


Akwai wani move ne? Naga Kwana biu kamar kana da damuwa.


Tsaki Musbahu yayi yace


Ba kamar bane ina da ita, kana ji ko Amra zan aura ne?


Cikin rashin fahimta Kabir yace


Amra? Kada Kace min 'yar Baba Balarabe


Ita dai!


Cikeda mamaki da kuma takaicin maganar Musbahu Kabir yace


Amma me TitαΦ ka samu matsala, ina tunanin ka yaje har zakai tunanin Auren Amra? Then Jeka fadawa gwoggo me kakeyi mana.


To ya zanyi Kabir? Gwoggo is insisting!


Ya fada Yana dafe kanshi, shi ya rasa Wannan masifar na se yayi aure? Shi yace baya so to me ye ne matsalar mutane.


Maslaha mu nemi Yarinya Marar gata wadda ko tayi kuka babu me damuwa ka aura, amma Amra Tana da gata bazata taba jurar zama da kai ba.


To fa! Kunji wata sabuwar. Wanene Musbahu? Meye yake boyewa? Me yasa bayason aure?


Lokaci daya Junaid da Subay'a suka dawo gida, kowannensu basai yayi maka bayanin gajiyar da yayi ba a kwance take a saman fuskarsu. Suna shigowa kowa ya shige part dinshi se takwas sannan suka hadu duka parlor, Junaid na koyawa Ahmad homework ita kuma Subay'a Tana surfing internet a system dinta. Sulaim dama bata fito ba Tunda ta dawo Tana dakinta dukda taji hayaniyar sun amma tana ganin Lokaci yayi da zata nisanta kanta daga Junaid Tunda har zuciyarta tayi gangancin sonshi. Ganganci ne mana Tunda tana son abinda bazata samu ba, Abinda is beyond level dinta. Da hanzari Junaid ya Mike jin sallamar Jabir da Imratu, Jabir a gaba Imratu na bayanshi suka shigo har cikin parlon sede fuskar Junaid kamar zata yage saboda murmushi Yana son a kawo mishi ziyara sosae yake jin dadi amma yasan halin Subay'a ke sawa yan uwanshi Suki Zuwa.


Kan 2 seater suka zauna Ahmad tuni ya bar homework din yayiwa kansa mazauni cinyar Daddy (kamar yadda suke cema Jabir) shi kuma Muhammad ya sauka Daga cinyar Subay'a ya koma kan Imratu wadda se caressing dinshi take a ranta tana addu'ar samun nata na kanta. Imratu ce ta Fara fadin


Yaya ina yini.


Da murmushi ya amsa sannan suka gaisa da Subay'a suna tambayar juna aiki kafin kuma Jabir suka Fara hira dukansu, Subay'a ta kwalla kiran


Atika


Bata karasa fada ba ta fito dauke da plate da bowls, seda ta aje Kan dining sannan ta iso ta gaisheda su Jabir kafin tace


Gani


Bakiji anyi baki ba, kiyi setting table mana.


Dan Dukar da kanta tayi Cikeda ladabi tace


Ina shirin fito da abincin kuma naji shigowarsu shi ne muke kara wani dish din amma yanzu zan kawo.


Tsaki tayi ta cigaba da Abinda take itakuma Atika ta koma kitchen ranta a bace kwatakwata Subay'a batada dadin zama sudai adduar su daya Abinda suke tunani tsakanin Sulaim Da Junaid ya kasance. Imratu ta dubi Subay'a Tace


Maman Ahmad ina Sulaim ko bata dawo ba.


Dagowa tayi tace


Bansani ba ko ta dawo, ban dai ganta ba.


Kanshi ya girgixa Jabir sannan Junaid yace


Ahmad kirawo Anty a daki.


A guje ya nufi dakinta lokacin ta gama sallar ishai amma bata tashi akan carpet din ba Ahmad ya shigo yace


Papa yace....


Kafin ya karasa tace


Kace ina zuwa.


Seda ta bata Mintina kafin ta Mike ta nade Sallayar ta cire Hijabin da abayar sallar sannan ta yafo mayafi Kan baggy skirt din jikinta da faffadar top, kanta cikin hula ta saka kalar skirt din ta fito bakinta dauke da sallama wadda take a ciki ciki. Kamshin turaren ta na Zahrat Banafsat ya fara mishi sallama, aikuwan shi ya fara juyawa ya bita da ido har ta shigo parlour fuskarta babu annuri ko digo, sede idanunta sun kasa jurar rashin kallonshi, zuciya Tana tuhumarta why zata yi shakalatun Bangaro ma abinda zuciyar ke so


_I love you... Please say you love me too... This three words they could change our lives forever and I promise you that we'll always be together. Till the end of time!_


Dagowa tayi ta dubi inda ya kafe ta da idanu ya manta da kowa a gurin, kawai se taji kamar ana zare mata damuwar dake cikin zuciyarta, har batasan ta sakar mishi murmushi ba seda ya mayar mata martani, se Jabir yayi gyaran murya wanda ya dawo dasu hayyacinsu. Jabir ya kwashe da dariya tareda kallon Subay'a wadda take deep a abinda take.




Shatuuu ♥️
[7/29, 6:16 PM] Ayshatuuuu: *MACE A YAU*
25


✍️Shatuuu♥️


🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION


#⃣Shatuuu095@wattpad


Dariyar da Jabir yayi yasa Junaid ya kalleshi da sauri, Subay'a ta dago, Imratu ta dubi mijinta tana mishi kallon kaima ka gani? don kuwa Tunda Sulaim ta fito take Lura dasu har wannan flashy smile din da sukayiwa juna. Sulaim kam tuni ta isa jikin Imratu ta rungume ta tana fadin


Fushi nakeyi daku har Yayan ma.


Dagota Imratu tayi tace


Kya yi mu bamuyi fushi ba se ke?


Bakinta ta turo Irin nayi fushi ta dubi Junaid


Yaya kace su bani hakuri.


Baki sake Subay'a take kallon shagwabar da yarinyar ke yiwa mijinta. Gyara zamanshi yayi yace


Ku bata hakuri yanzunnan.


Me Jabir zaiyi idan ba dariya ba, tabbas ana abu cikin gidannan. Subay'a mikewa tayi kamar zata tashi sama ta wuce kitchen nan da nan suka hada baki wajen fadin


Afuwan!


Are you OK?


Ya fada Yana mata kallo me Cikeda kulawa, kanta ta gyada Imratu ta bugi bayanta mamaki fal fuskarta.


A table kowa maida hankali yayi kan cin abinci dukda ana exchanging glance Lokaci Lokaci tsakanin Junaid da Sulaim. Tabbas kafin ka samu careless wife irin Subay'a zaka dade Duk Wannan Abinda ake hankalinta baya kansu tana can tana tunanin maganar da hajiya tayi mata dazun dasuka hadu da safe. Ta rasa ta ina zata bullowa ala'lamarin gashi bata san dago maganar Tunda har yayi mata maganar zuwa Estonia tana ganin zata Bari su dawo se ta tunkareshi taji!


Parlon Junaid Jabir dashi suka kebe don zantawa kasancewar sun jima basu hadu ba, yayinda Subay'a ta koma dakinta, Imratu da Sulaim suka wuce dakin Sulaim din. Hira sosae suke tsakanin su kasancewar ba karamin sabo bane tsakanin biyun. Suna hira Sulaim na harhada kayan da zatayi amfani dashi a Birnin kudu Don Junaid ya sanar mata tareda su Yaya Jabir zata wuce suma can din zasuje , wata katon gift ta dakko anyi wrapping da farin sheet se kyalli yake, Imratu tace


Wannan fa?


Jujjuya shi tayi tace


Sakon Yaya Ja'afar ne, Yaya Hanan ta bayar a bashi.


Kai ta gyada ta bi Sulaim din da kallo a ranta tana tunanin Sulaim batasan tsakanin Hanan da Ja'afar ba kenan? Kasancewar ita ba mai shiga abinda babu ruwanta bane yasa ta kauda tunanin da take dole wata Rana komai Zai bayyana amma bata taba yiwa Sulaim shaawar auren Ja'afar ba, kwatakwata he's not a Man, idanunshi baya zama Kan mace daya. Idan banda zalama da kuma iskancin Ja'afar Tunda har hankalinta yana kanshi Bata tunanin ta cancanci hakan. Sede bata sani ba yau Abinda idanunta suka hango yana faruwa tsakanin Junaid da Sulaim ko idanunta ne ko kuma gaske ne? Abu daya ta sani time will tell!


Da murmushi saman fuskar Jabir ya dubi Junaid wanda hankalinshi na kan Jabir din yace




Bros Kana son Sulaim ne?


Baiyi mamaki ba saboda yanzun son Sulaim nema yake ya maida shi rago, nema yake yasashi ya zama desperate and Babban abin Yana ganin idan ya cigaba da kauran baki to zai iya furtawa gaban Subay'a ba kuma zai taba son hakan ya faru ba at least Subay'a matarshi ce, first love dinshi bazai taba wulakanta ta ba Sede idan ita ta wulakanta kanta kamar yadda suke yanzun.


Kana son sani ne ko confirming Kake son Yi?


Junaid ya tambaya Fuskarshi dauke da murmushi, shima murmushi yayi yace


Confirmation ne.


Then is true, I love her!


Babu mamaki a Fuskarshi se wani farin ciki da at once ya lullubeshi yace


Amma naji dadi, Baban Sulaim zai auri Sulaim itama Naga kamar tana ciki, a ina kuke?


Kanshi ya shafa Lokaci daya murmushin ya dauke dif se kamar fear da wani abu da shi Jabir din ya kasa karatowa Junaid yace


Ba ta sani ba, ban fada mata ba.


Why? Waiting for what?


I dunno Jabir, banda courage din.


Haba Bro, Sulaim ce fa, your Sulaim ita ce Kake tsoro? Ni zan fada mata da kaina


Da sauri ya girgixa kanshi yace


No please! I promise ina dawowa daga Estonia I'll let the word out Inshaaa Allah.


Yasan Junaid baya magana biyu su kuma bazasu taba barin such a golden opportunity ya wucesu ba, dama bai kamata ace bare ya auri Sulaimi ba Tunda basu san wani hannun zasu mika ta ba. Hira cikin nishadi sukai dukda Jabir se zolayar Junaid yake akaan Sulaim. Abin gwanin shaawa don bazakai tunanin cewar brothers bane sunfi Kama da abokai. Wajen goma Jabir ya dubi Junaid yace


Bari mu wuce ko room bamui booking ba.


Cikin rashin fahimta Junaid yace


Kana nufin hotel zakuje, already an gyara wancan dakunan, idan baiyi maka ba se ku zauna anan.


Babu yadda Jabir ya iya haka suka koma part din dake gefe don dama don haka aka tanadi gurin.




Wallahi yau ba se gobe ba Seka fada min Abinda Ke tsakaninka da waccen yarinyar.


Subay'a ta fada idanunta taf da hawaye, Haba ta gaji bazata iya ba, kowa daukarta yake shashasha a gidanta mijinta na son wata. Kallonta yayi yaga yadda take tada jijiyoyin wuya amma tausayinta yakeji kuma for Sulaims safety yasa bai kulata ba ya cigaba da Abinda yake cikin system. Gefenshi ta matso tareda kawar da system din daga gabanshi ta Maye gurbin tace


Wallahi se ka fada min Junaid kaji na rantse.


Idanunta na digar da hawaye da Lokaci daya sukai nasarar wanke mata fuska, abin ya fara kaishi Anty bango amma baisan bacin rai yasa yayi Abinda zai yi Dana sani daga baya yasa ya Mike don zuwa cikin bedroom dinshi, Sede kamar wata zakanya ta rigashi isa gurin tareda blocking hanyar tace


Ai kaji abinda nace, babu inda xakaje se ka fadamin.


Dagowa yayi ya dubeta, se kuka take kamar wadda akaiwa mutuwa Amma yadda take abin ransa ya baci hakan yasa yace


You want to know right? OK! Son ta nake kamar yadda kike zargi kuma aurenta zanyi. Is that all?


Lokaci daya numfashinta ya fara fita cikin sauri sauri tamkar wadda tayi gudun marathon. A gigice Subay'a ta farka daga wannan mummunan mafarkin, hannunta ta kai ta kunna bedside lamp din Lokaci daya haske ya gauraye dakin, idanunta suka sauka kan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login