Showing 66001 words to 69000 words out of 131263 words

Chapter 23 - MACE A YAU Document from Sulaim .txt

24 Nov 2024

4846

kyau ne. Shima dariyar yake yasa Dayan hannunshi ya rungumo Khulthum zuwa jikinshi suna sakkowa daga upstairs Din, haka suka wuce ta don da duka zaa Tambayesu bana tunanin sunsan da wanzuwar halitta a gurin.


Kanta a take ya fara sarawa idanunta sukai ja, zuciyarta tana bugawa da sauri da sauri kamar zata fito Daga thoracic cage dinta. Tafi 15 minutes kanta a kasa kafin abinda take ji ya sassauta saboda kiran sunan Allah da takeyi. Hannun yaran ta Kama suka fito se surutu suke mata amma ina bata hayyacinta. Daga haka ta saka kurani tana saurare har sukaje gida. Booth ta bude me gadi ya fito da kayan sannan ta kulle motar ta nufi ciki hankalinta har lokancin bai gama dawowa jikinta ba.


Atika shigo da kayan ciki, zan dan kwanta Zuwa anjima mu fara aiki.


Kanta ta gyada ta fita ita kuma ta kunna musu cartoon channel sannan ta shige dakinta ta fada gado tayi rub da ciki!


Tana kan sallaya tana addu'a Allah yasa dukkan abubuwan da suke faruwa cikin rayuwarta ya zama mabudin bude kofofin alkhairi. Knocking akai hakan yasa ta karkare adduar ta fito, Atika ce rike da Muhammad wanda yayi bacci, sulaim tace


Ya akai yayi bacci ai kuwa my baby you're going to wake up yanzunnan.


Hannu tasa ta karbeshi ta nufi parlour dashi dake ta gefen dining area dinsu akwai sink nan taje ta wanke mishi fuska, Yana bude ido ya bare baki don yin kuka tace


Yi hakuri babyn Anty muje na baka sweet kaji but don't sleep.


A kafadarta ta dora shi Ahmad na rike da hannunta har lokancin ita daya tasan Abinda takeji a zuciyarta amma haka dole ta yakice abin ta nufi kitchen dan fara aiki. Kan working space ta daurasu duka ta ciro candy ta basu suka Fara aiki itada Atika ita kuma Laraba tana gyara abubuwa da yanke yanke. Seda komai ya zama ready Washegari akan ta harhada abubuwa. Da wurwuri ta kwanta Don yaran ma tuni sunyi bacci itama tana son kadaici tana son yin tunani Bata taba tunanin Khulthum zata iya abinda tayi mata ba amma wata zuciyar tuna mata take matsayin Khulthum din a gareta. Ta dade kafin bacci me nauyi ya dauketa.


Asubar fari ta tashi da dama dama saboda murnar dawowar Junaid, wayarta ta dauka ta Kara duba arrival time dinsu daya turo mata 9am. DA sauri ta karasa kitchen ta Fara aikinta har takwas da Mintina kafin ta kammalla ta wuce daki dama tuntuni an shirya mata su Ahmad hakan yasa tana fitowa ta dakko Wannan sabon farin lace da cone pattern baki a jiki, dinkin skirt da Riga ne, har ta ware se ta jingina da jikin bango tana tuhumar kanta dalilin da yasa zatayi kwalliya har haka? Mijinta ne? Ko saurayinta ne? None of the above so meye abin zakewa kawai se ta mayar ta dakko gown na atamfa milk da red. Tana gama shiryawa wayar Aimana ta shigo, da sauri ta dauka gabanta na faduwa don batasan Abinda zai fitar da ita


Aimana how far?


Test din Family Law Nanda 30mins kiyi sauri.


Oh no! Ta furta ranta a bace amma ya zatayi haka ta dauki key da veil da Jakarta ta fito gaskiya an karya mata budget da yawa.


Atika test gareni na fita, nasan su Yaya sun kusa Dan Allah komai ya zama in place.


Kanta ta gyada tace


Se kin dawo.


Waving tayiwa yaran ta fice cikin hanzari, ranta duka a jagule kamar zatayi kuka. Tana yin parking ta fito sega wasu yan mata su biyu suna tsaye ko abu suke jira oho. Tana fitowa dayar tace mata


Dan Allah ke sister Dr Junaid ce?


Kallonta Sulaim tayi, irin Ajebos dinnan ne yar gayu kana kallonta kasan naira ta Jikata yadda take magana kadai abin kallo ne.


Me ya faru?


Ta tambaya Tana kare musu kallo har yar rakiyar.


Dama ina crushing dinsa ne so please ko zakiyi hooking dinmu up?


Batace komai ba saboda abinda zai fita a bakinta ba Mai dadi bane hakan yasa ta gewaye su zata wuce, dayar tace


Please mana help a soul, Munga Kuna Kama sannan ga motarshi Kina zuwa da ita.


Ta fada Tana nuna motar da hannunta, juyawa tayi tace


Mijina ne ba yaya na ba!


Gaba daya suka zaro ido tare da kokarin kare kansu ta wuce ta Barsu a gurin gwiwa a sake, ranta a matukar bace ta shiga cikin class din, ina irin yanayin da Kake jin tamkar kowa da komai is against you, irin you're helpless haka ta dinga ji idanunta sukai ja tamkar me shirin kuka. Idanunta akan Khulthum dake gefen Khairi ya fara sauka, Tana zaune Tana duba wayarta, yi tayi kamar zata wucesu se ta fasa ta dawo ta zauna kusa da Aimana, kafin suyi magana Dr. Halliru me family law din ya iso, babu bata Lokaci aka Fara test, test din tayi wuya duk yadda kayi karatu hakan ya karawa Sulaim tension. A haka aka kammalla ya karba sannan ya fice, mikewa tayi Don tafiya taji Aimana na fadin


Ki zauna akwai mood trial Anjima.


Kanta ta dafe tace


Tafiya zanyi kice banida lapiya.


Hannunta Aimana ta rike tace


Zauna Sulaim me yene yake damunki?


Shi ne furucin da bata so idan tana cikinhi damuwa aikuwa se hawaye da sauri ta tsugunna don Bata son wani yaga halin da take ciki, Aimana ta damke hannunta batareda tace komai ba su kuwa su Khulthum suna ta faman instagramming so basu lura da halinda ake ciki ba. Seda ta sha kukanta kafin ta Mike fuskarta a rufe ta fita don wanke fuskar at least taji dan sanyi cikin Zuciyata she have let out some emotions. Ruwan hannunta tasa ta wanke fuskarta sannan ta dawo ciki kafin ta karasa ta hangosu sun nufota itama bayansu tabi anan Khulthum ta kalleta ta tabe Baki tace


Ke kuma yau me ya sameki kike bata rai.


Aimana tayi saurin fadin


Batada lapiya ne.


Allah ya sawwaqe.


Ta fada itakuma khairi ta juyo tace


Ayya kanwar Yaya sannu.


Kanta ta gyada musu har suka isa joint din da suka saba cin abinci. Khairi ce tayi placing order yayinda Sulaim ke mamakin sauyawar Khulthum akanta, tabbas tayi mamaki ba kadan ba ta yadda Khulthum tayi watsi da ita Abinda bata taba ba kenan, kowa yasan yadda Khulthum da Sulaim suke different Womb sisters.


Seda sukaci abincin sannan Khairi ta Fara magana tace


Tohm, kowa ya bani hankalinshi nan saboda muhimmiyar magana zanyi.


Babu Wanda baiyi complying ba saboda Khairi is always not serious amma duk lokacinda tayi magana a nutse to tabbas she's serious.


Seriously, banji dadin Abinda ya faru ba, cikin class kowa se ya nuna mu saboda friendship dinmu Tun level 1 amma se kawai abu ya shigo ciki na cin amana da yaudara.


Tayi shiru Tana binsu da ido, Khulthum tace


Malama ki fadi Abinda zaki fada mana.


Kallonta tayi tace


Komai a kanki ne Khulthum, ta yaya kina kawar Sulaim ki kwace mata saurayi?


Da sauri Sulaim tace


No please Khairi.....


Da sauri Aimana tace


What the hell? Khairi da gaske?


Khulthum dake binsu da kallo tace


Eh da gaske ne! Se meye a ciki?


Khairi tayi mata kallon wulakanci tace


Se jin kunya, Wallahi kinji kunya ki rasa ......


Ke rufewa mutane Baki kija gefe, ina ruwanki Naga zan iya ne.


Sulaim ganin attention din mutane zai dawo kansu ga Khulthum ta Fara daga murya yasa tace


Dan Allah magana ya wuce indan Salim ne let her have him Sede abu daya na sani, Salim is a bad person Tunda zai iya ketare dangantakar mu yayi soyayya dake. Have him sannan ki sani Salim bashi ya hada mu ba Allah ya hadamu.


Khulthum cikin ranta taji babu dadi sosae saboda bata taba tunanin haka Sulaim zatayi reacting ba, amma bata nuna ba se ta Mike tace


Ai na fada muku Duk wadda tayi sake da nata sede wani bashi ba, Sulaim Allah ya bada karfin zuciya


Tana fada ta fice, khairi ta Mike zata bita Aimana ta hanata, Duk sukai shiru ranar haka aka tashi babu dadi kuma taki basu fuskar yin magana ma. Ana gama mood trial kowacce ta fito sukai sallama ta shiga mota ta nufi gida, farin cikin da take ciki ilahirin shi ta nemeshi ta rasa kuka kawai take son tayi ko taji sanyi Amma ya kamata ta isa gida kilan idan taga farin cikin rayuwarta ta ji sanyi.


Honk tayi Baba ya bude mata ta daga mishi hannun ta shigo inda ta samu motoci kusan hudu tasan 'yan sannu da zuwa ne. Parking tayi ta fito Tana sauke ajiyar zuciya, nan aka bude kofa Subay'a ta fito tayi kyau se kyalli take ga haske da ta kara tayi kubul jikinta, take wani kishi ya dirar musu lokaci daya, bayanta yan uwanta ne su hudu Baki daya suka saki Baki suna kallonta lokacinda take rufe motar Junaid din. Dauke kanta tayi ta nufo inda suka ja tunga tamkar masu jiranta. Dama ranta a bace yake hakan yasa ko inda suke bata kalla ba ta gebare su tayi ciki. Salima wadda karo na farko da ta Fara ganin Sulaim tace


Wacece Wannan yarinyar Subay'a?


Cikin Bacin rai tace


Sulaimi ce kanwar Junaid


Bata ganmu bane? Idan idona daidai ya nuna min kamar motar Junaid na gani a hannunta.


Surayya tayi dariya tace


Subay'a da gaske ne? Ko kuwa hallucination nake motar mijinki a hannun wata?


Samina tace


Ku muje Dan Allah, ko bakuga kallon da take mana ba .....


Na yan iska ko?


Suhaila ta fada muryarta Cikeda tsanar.


Mu fara kashe kurar dake gabanmu kafin mu dawo kanta. Ku muje.


Haka suka wuce suka bar Subay'a tsaye tamkar mutum mutumi, Tunda suke da Junaid bai taba ko da wasa bata motarshi ba amma gata hannun Sulaim Wallahi yau ko ita ko sulaim.


A ciki kuwa.........




Who wants to know wani Irin kallo zaayi tsakanin Junaid da Sulaim? Don't miss it out! Ga Junaid ya dawo will he let the word out? Meye Subay'a zatayi kuke ganin?




Shatuuu ♥️
[7/30, 10:36 PM] Ayshatuuuu: *MACE A YAU*
30


✍️Shatuuu♥️


🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION


#⃣Shatuuu095@wattpad




Hey pipu.....I'm sorry for the late update, wallah yau kam I was so busy ne.... Amma gashi na baku sleeping mate, I hope everybody will enjoy it!






Na taba fada muku yadda Sulaim take? OK let's go Sulaim is an Epitome of beauty kyakyawa ce ta gasken gaske. Fara ce fari me sanyi me kuma haske bamai dau ba, saffa saffa. Fuskarta oval shape ce wadda ta samu brows me cikakken gashi baki wuluk tamkar anyi shaping haka girar take wadda saboda yadda gashinta na kai yake har goshi yasa yake neman haduwa da girar fuskarta. Idanunta suna da haske me rikitarwa, idonta nada girma amma saboda yadda suka Saba da kuka yasa ba a ganin girman saboda bata ware su da kyau se on special basis. Hancinta Mashaaaa Allah very pointed me kyau Wanda yayi fitting fuskarta, bakinta ba me girma bane daidai yake, lebenta sirara masu taushi, Tana da wushirya me Dan girma sannan da both side dimples. Sulaim ba gajeriya bace doguwa ce saboda ta gaji tsayi daga gurin Daddy da Mummy Baki daya, jikinta me kyau ne well shaped Sede tsayinta ke boye kirar ta ta. Sulaim mutum ce very gentle, Tana da nutsuwa sosae, Tana da addini sauran kunfi kowa sanin su!


A hankali ta cigaba da takawa zuwa parlon, fuskarta babu walwala ga gajiya da tarin kunci da suka mata kakanakayi, sede gabanta babu Abinda yake banda faduwa sosae, zuciyarta ta tsananta bugawa ga dauki. Tana yin sallama sassanyan kamshin Fierce cologne by Abercrombie and Fitch yayi mata sallama wanda ya tabbatar mata mamallakin turaren na gurin, cikin nitsuwa ta dago idonta ta dubi kujerun parlour, Yana zaune idanunshi a kanta Wanda ko kyafta idon ya kasa samu yayi, tamkar an canza ta haka yake kallonta ko kuma bai taba ganinta ba se ranar. Tayi mishi haske dukda rama da tayi amma idanunta kadai shows farin cikin da Bata taba tunanin zata tsinci kanta a ciki ba Wanda ganinshi ya Kore tarin kuncin da take ciki na abubuwan da suka mata yawa. Idanunta ta kyafta se hawaye Sharrrrrrr! Ya fara mata zarya kuma ta kasa daina kallonshi, hawayen yaki daina zuba mata. A hankali ya mike ya nufi inda take tsaye hannunshi cikin pocket dinshi, sede murmushin dake fuskar shi ya dauke se tarin damuwar ganin hawayen da take yi.


Menene kuma? Are you not happy?


Ya fada a hankali wanda I'm sure ba kowa bane zaiji se itan da dukkan hankalinta ke kanshi taji, da sauri ta girgixa kanta tace


A'a.


Then why kike kuka?


Hannunta tasa ta goge fuskarta tace


Banida lapiya.


Da sauri ya kalleta yace


Je canza kaya kizo muje asibiti, me yasa baki fada min ba? Why will you stay with sickness haka.


Kanta ta girgixa ganin yadda ya rikice tace


Kaina ne kawai yake ciwo kuma ina tunanin stress ne.


Wata ajiyar zuciya me nauyi ya saki wanda Sulaim ta Lura sakamaakon kirjinshi da ya bude sannan yayi relaxing.


Duk da haka jekiyi changing I'm waiting for you.


Ya fada Yana kallon wrist watch dinsa, babu musu ta wuce dakinta kamar tana taka iska haka take ji saboda wani abu me sanyi da yabi ya mamaye jini, tsoka da jiki. Tana shiga ta wuce bayi ta cire kayanta ta saki ruwa, ta kasa tantance me takeji farin ciki takeji wanda babu kamar shi, Yaya ya dawo me take nema kuma? Baki daya ta manta da Khulthum, Hanan, Ja'afar da Salim. Junaid ne kawai a duniyarta a Wannan lokacin.


Tana fitowa fuskarta tayi fayau ga wani lallausan murmushi akai wanda yaki tafiya se ajiyar zuciya datake saukewa akai akai, sau uku tana dakko kaya Tana mayarwa a karshe ta samu wani Lace off white an mishi ratsin pink dinkin gown me kyau ta saka. Ita yanzun ta Riga ta sawa ranta Duk yadda za'ai Duk me zai faru da izinin Allah se ta karkato hankalin Junaid kanta Koda kuwa duniya zata zageta amma a ganinta Lokaci yayi da zata kwatar wa kanta 'yanci, ta gaji da yadda kullum zuciyarta take wahalar tuwa akan maza a karshe ta tashi da heartbreak, wannan karan tabbas kida zai canza.


Kusan Lokaci guda suka fito, shi yayi changing Zuwa mark and Spencer trousers Baki se tummy Hilfiger top ash, hannunsa ya daura bakin agogo wanda ya zauna daidai akan hannun nashi. Yayi kyau na fitina har Khulthum taji inama shi din nata ne da sun fasa fitar nan don tasan dole Za'a kalleshi, ita kuma Abinda bazata iya withstanding ba kenan.


Are you set?


Ya fada Yana kare mata kallo, a ranshi Yana tasbihi ga Allah saboda kyakykyawar halittar da yayiwa abu mafi soyuwa cikin zuciyar shi, son sulaim ya mishi shigar ba zata, ya kainanye shi bashida katabis se yadda tayi dashi. murmushi tayi tace


Eh.


Martani ya mayar mata wanda seda ta lumshe idonta saboda yadda murmushin ya wanke mata zuciya.


Je ki tayar da motar gani nan.


Kanta ta gyada ta fice yayinda ya nufi parlour Subay'a don yaji shigowarta yana dakinshi. Tana zaune ta zabga tagumi deep in thought, kana kallon ta kasan akwai abinda take so amma ta kasa furtawa. Sallamarshi yasa tayi firgigit tare da dubanshi ta ganshi da alamun fita zaiyi saboda shigar jikinshi.


Zan kai Sulaim Asibiti.


Bata da lapiya?


Ta tambaya Tana tsatsare shi da ido tana ganin hakan zai girgiza shi, murmushi yayi yace


Eh.


Banga alama ba


Ta bashi amsa Tana duban idanunshi, shima kallonta yayi yace


Ke baki gani ba, ni na gani.


Daga haka ya juya ya fice ya barta a gurin Tana bacin rai, ita yanzun Sulaim Bata gabanta abinda yake gabanta gobe shi ne damuwarta a hankali zata dawo kanta.


Tana hangoshi ta matsa mishi drivers side ya shiga sannan suka fita, zuciyoyinsu cike da farin ciki da nishadi, suna jin tamkar su biyu kadai suka rage cikin duniyar. Dukda bawai magana suke ba amma yanayin kawai ya isa ya nutsar da zuciya, balle su da suka kusan shafe wata basu tare ai wannan ranar is memorable. Duk tunaninta asibiti zasuje Amma se taga sunyi hanyar grand square, dagowa tayi ta dubeshi, kallonta yake yace


Ba kan ya daina ciwo ba? Dama ba kukan an ganni bane?


Dagowa tayi ta turo Baki Cikeda shagwaba ta Harare shi. Daidai lokacin yayi parking kawai se ya tsaya Yana murmushi yace


Sulaim like serious harara ta kikayi?


Da sauri ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta tana murmushi. Kallonta ya kuma Yi yana ganin inama kada ta Kara kuka saboda yadda sanyi ke ratsa shi ganin dariyar da takeyi.


Muje.


Ya furta cikin wata husky voice wadda ta ratsa ta har cikin kanta, ta bude side dinta ta fito Tana sake gyara zaman Veil dinta.


Tamkar couples haka suka jera ciki fuskokinsu kawai ka kalla will tell you how happy they are been by each others company.


*We could build up a universe, right here all the world could disappear would it notice*


Ice-cream kawai yayi mata order, triple treat chocolate, vanilla da strawberry kowanne scoop dinshi cikin cup, Mika mata yayi sannan ya zauna opposite dinta tareda tsare ta da ido wanda suke Kara ninka soyayyar shi cikin zuciyar ta. Hannunshi ya mata alaman ta sha. Babu musu tasa spoon din Cikeda nutsuwa ta fara kaiwa bakinta, Duk wani move dinta akan idanunshi amma a zahiri wayarshi yake dubawa kafin kuma ya shiga amsa call. Yana dawowa ta mika mishi cup din da sauran ice-cream a ciki tace


Gashi Kasha.


Kanshi ya girgixa yace


A'a wannan maganin Ciwon Kai ne, kinga ni kuma lapiyata kalau ko?


Ya fada Yana kashe mata ido wanda yasa zuciyar ta harbawa da sauri, a ranta tana tunanin me Junaid ke nufi da ita ne? So yake ya fasa mata zuciya?.


Seda ta gama sannan ya kaita wani Pizza joint dake kan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login