Showing 81001 words to 84000 words out of 131263 words

Chapter 28 - MACE A YAU Document from Sulaim .txt

24 Nov 2024

4869

tsauri da yawa bata isa ta kwace ba. Seda ya kaita gefen parlon inda babu me ganinsu sannan ya hada ta da bango yace


Sulaim me kikeyi? Me ye hadinki da baban Ahmad?


Wata harara ta watsa mishi tace


Me idanunka suka gane maka? Sonshi nake.


Wata dariya ya saki yace


Amma you're insane ko, that's completely impossible Yarinya.


Tureshi tayi har Seda tayi mamakin inda ya samu karfin don yadda yayi taga taga tamkar zai kai kasa amma ya daure ya tsaya, a hankali tace


Shi kanshi impossible fada yake I'mpossible ka gane.


Ke mayaudariya ce, deceiver, heart breaker.....


Dariya tayi tace


They all fit you Yaya,


Daga haka ta wuce tana dariya amma ya sake janyo hannunta hakan yasa ta doke hannun ta juyo a fusace ta ce


Kada ka sake, don't ever.....


Bata karasa ba ta bar gurin tamkar zata kifa saboda bacin rai. Kitchen ta wuce ranta dukka a jagule tana mamakin har kura ce zatace da kare Maye? Lallai Ja'afar!


Seda ta Daidaita nutsuwarta kafin ta dauki tray din ta hau dashi, parlon is tensed saboda yanayin fuskokinsu, jikinta a sanyaye ta aje mishi abincin sannan tace


Yanzun zaka ci?


Kanshi ya girgixa yana kakaro murmushi wanda tasan baikai yadda ake so ba yace


Se Anjima,


Kanta ta gyada ta nufi ciki don kwanciya Bayan ta tambayi Mami ko Tana bukatar wani abun. Tunda ta kwanta take juyi tana jin better half dinta baya cikin nitsuwarshi, inama zata iya ta tunkareshi taji meye yake damun shi, meye taji Yana fadin


Mami kina ja min rai da Yawa!


Ko me yake so Mami ta hanashi? Kanta ta kwantar kan pillow ta runtse idonta tareda janyo Muhammad jikinta ta rungume a haka bacci ya dauketa me nauyin gaske wanda har Junaid ya kirata yana son fada mata ta gayawa Mami tana sonshi amma batai picking ba. Shikam hankalinshi baki daya ya tashi don ya rasa me Mami take so kuma? Me zaiyi yayi proving da gaske son yarta yake? Taki yarda taki fahimta. Idanunshi ya runtse se yaji vib da sauri ya bude idanunshi amma yaga Subay'a ce wadda duk tunaninshi Sulaim ce, tsaki yayi ya maida idanunshi ya rufe can aka kuma kira ya bude idon ya janyo wayar yayi blocking duk wani call Daga Cyprus don bai shirya jin rubbish Daga bakinta ba.


Washegari Bayan sunyi breakfast Mami ta wuce daki ta bar Junaid da Ja'afar da Sulaim, parlon yayi shiru se Lokaci zuwa Lokaci biyun Kan dago su dubu junansu saboda chatting suke ta whatsapp.


Junaid: Mami tace bata yadda na aureki ba saboda wai bana sonki.


Juanid: kije ki fahimtar da ita ina sonki Kema haka.


Kanta ta girgixa ta dago ta kalleshi se taji jikinta yayi sanyi tayi replying


Sulaim: I can't, kunyarta nake ji.


Dagowa yayi ya dubeta da pleading look sannan yayi typing


Jumaid: Kema haka kike gani Bana sonki ko?


Sulaim: no I'm sure of the love, amma bazan iya tunkarar ta da maganar ba.


Kanshi ya dafe tareda mikewa ya nufi dakin Mamin, Tana ganin hakan ta bar parlon Zuwa dakinta. Yana shiga ya sameta Zaune Kan cushion idanunta cikin fararen medical glasses hannunta rike da wani littafi na judges tana dubawa. Tunda yayi sallama ta amsa, ta aje littafin ta bishi da kallo har ya zauna gefen gadon ta yace


Mami sannu da hutawa.


Hutu yana gurinku Baban Ahmad.


Dan murmushi yayi sannan yace


Mami dan Allah badan na isa ba Mami ki taimaka min ki yadda da proposal dina.


Junaid! Ka bar Wannan maganar kawai dan Allah.


Kanshi ya dafe saboda yadda yake kokarin tsagewa gida buyu saboda azabar Sara mishi da yakeyi yace


Kiyi hakuri Mami amma idan kika fada min dalilinki ni kuma na miki alkawarin zan hakura.


Kanta ta girgixa don tasan bazai taba hakura ba tace


Kasan Ja'afar na sonta? Jiya bayan Kaje ka kwanta yazo yana min kuka akan na aura mishi Sulaim, bana son tarwatsa gidana da hannuna, idan na aura maka ita zaice na soka, idan na aura ma Ja'afar banyi maka adalci ba!


Hatta itama Sulaim din Mami, maganar akan wa ake ba Sulaim bace? Ki kirata ki tambayeta wa take so cikinmu inhar ta Ja'afar shikenan magana ta wuce Mami. Amma inason kisan cewar Ja'afar bashi bane right choice ga sulaim ba.


Inda ace Jabir ko Jawad ke sonta, bazaki taba jin nace ina sonta ba amma Ja'afar no Mami! Kuma ki tuna ranar da Daddy ya cika Kwana bakwai da rasuwa kika cemin idan lokacin auren Sulaim yayi ni zan zaba mata miji.....


Wannan ya Junaid, kayi hakuri ka manta da sulaim nafi son ta kawo bare na aura mishi ita.


Mikewa yayi a hankali idanunshi sunyi ja, veins en kansa sun tashi, ya kalli Mami sannan ya tsugunna gwaiwowinshi a kasa ya kama hannunta yace


Nagode Mami amma NA HAKURA DA SULAIM


Abinda Mami bata taba kawowa ba kenan, maganar tayi mugun bugunta amma ta kasa tabuka komai. Hakan baikai yadda maganar ta sauka kunnuwan Sulaim ba wadda ta zo niyyar kawowa Mami wayarta da Baba ke kira taji NA HAKURA DA SULAIM. Bata Gama shiga tashin hankali ba seda Junaid ya fito ko kallonta baiyi ba, uwa uba yanayin da yake ciki. Wani kuka ne ya taho mata hakan yasa ta koma daki Tana jin kamar zatayi hauka, Tana jin bakin ciki, radadi da zafi Marar misaltuwa cikin zuciyar ta! Window taje ta tsaya daidai lokacin ya bude motarshi ya shiga!


*When you feel alone I'll be your shoulders, with the tender touch you know so well. Somebody once said is the soul that matters, Baby who can really tell when two hearts belong so well, may be the walls will tumble and sun may refuse to shine.... When I say I love you...*


Shatuuu ♥️ *MACE A YAU*
37


✍️Shatuuu♥️


🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION


#⃣Shatuuu095@wattpad






Tun tana zuba idon ganin kiran Kabir a wayarta har ta hakura amma ranta tana tunanin Irin rashin mutuncin da zatayi mishi shi da Salim. Ta tsani rashin cika alkawari no matter what indai tayi alkawari ko alkhairi ko sharri se tayi kokarin ganin ta cika shi.


Misalin karfe Sha biyu na dare har bacci ya fara awan gaba da ita taji ringing din wayarta, hakan yasa ta bude idonta a hankali ta janyo wayar, new number ce hakan yasa tayi tunanin Kabir ne. Tashi tayi ta zauna sannan tayi picking call din, muryar kabir din taji Yana fadin


Ran gimbiya ya dade !


Gyara zamanta tayi tace


Tare da naka.


Muryarshi ya gyara yace


Naso tun dazun na kiraki amma hakan bai samu ba saboda wata yar hidima da ta tsayar dani. Ina fata baki damu ba.


Ko daya Don na manta mun hadu da Kai!


Dariya kabir yayi yana mamakin halin Khulthum, shi bai mata bayanin kanshi ba amma gashi har ta gane shi kuma tana gaya mishi hakan.


Ayya! Lemme get straight to the point, wato Khulthum tun da na ganki naga kin dace da wani friend dina Musbahu, saboda yadda yake fadar features din matarshi da yake so, se naga kina dashi.


Abokin ka kuma?


Ta fada da mamaki, Bama kanshi yake yiwa kamu ba abokinshi yake yiwa to fa? Kuma ma aure ta! Jin tayi shiru yasa Kabir yace


Ko dai wani ya Riga mu ne? Mu nemi wata.


Kanta ta girgixa kamar yana kallonta tace


Ni yanzun babu aure cikin tsarina kwatakwata, ban shirya committing suicide ba.


Suicide!?


Ya tambaya idanu a warwaje


Of course haka nake daukar aure suicide, tunanin yin aure kawai is suicidal attempt, saboda tamkar ka dinga cin jollof rice ne kullum na shekaru babu adadi, babu free life komai an take ka anyi caging dinka.


Kanshi ya girgixa yana Kara tabbatar da Khulthum tayi fitting position din matar me titαΦ.


Kada ki damu gobe da karfe Tara na safe zanzo na kaiki inda yake, idan har mukaje kika ji Baki son aurenshi kada ki damu bazan Kara takura miki ba. Seda safe.


Daga haka ta kashe wayar ta kwanta ta rufe idonta zuciyar ta fal tunanin wanene Musbahu? Meye aikinshi? Dan wanene?


Washegari da wuri ta tashi ta gyara dakin tayi wanka, ta Nemo kayan da take son sakawa, yau shadda ta dakko wadda Tasha embroidery design me kyau, shaddar coffee ce akai aikin milk a jiki don haka tayi amfani da milk accessories, dinkin skirt da Riga da yayi fitting dinta. Karfe Tara daidai ta kammalla komai da takeyi ta fito Tana fitar da kanshi me kashe jiki. Mama dake zaune tsakar gida Tana zuzzuba abinci taga fitowar Khulthum, itafa yarinyar nan ta Fara tsorata ta, ta Fara bata tsoro ina yarinyar take zuwa da Wannan uwar kwalliyar kamar me zuwa dakin miji?


Ina zakije da Safiyar nan? Wai ina tukunna kike Zuwa kike kaiwa dare Baki dawo ba. Anya Khulthum hanyar da kika dauka zata bulle miki?


Murmushi tayi tace


Mama gidansu Sulaim zanje wadda nake Baki ku gaisa a waya.


Take bakin Mama ya washe Tace


Yarinyar arziki Sulaim ki gaida min ita sosae, bari na baki kuka da Daddawa ki kaiwa babarta.


Bata fuska tayi tace


Haba Mama Duk Wannan kwalliyar na kare da daukar kuka? Zan dai ce Kina gaisheta .


Daga haka ta fice Don tuni taji kiran kabir tasan yazo, Tunda ta nufoshi yake Raya Irin kyau da Allah ya bawa Khulthum inda ace Musbahu is Musbahu da yayi Saar mace, komai daya dace mace tana dashi Bata rasa ba.


A kofar tangamemen company TitαΦ Flours anan yayi parking tare da kallon Khulthum wadda take bin ko ina da kallo, idanunta kawai zaka kalla kasan abubuwa ne fal ciki, mamaki, tsoro. Tare suka jera anata gaishe dashi har suka isa inda lift yake suka shiga ya danna 3rd floor inda anan office din Musbahu yake. Duk yadda taso daurewa kar kauyancinta ya fito seda ya fito tun ba a wajen lift ba, ji take kamar ta kankame Kabir, shi kuwa hankalinshi Yana kan wayar da yake bai lura da yanayinta. Tana tsayawa suka fito Yana gaba tana bayanshi cikin nitsuwa tana satar kallon gurin se taga first floor ba kawai bane compared to Wannan don hadasu ma bai taso ba. Seda secretary dinsa ya sanar dashi shigowar su Kabir ya bada izini kafin suka shiga ciki.


Lokacinda ta hango cikin office din seda numfashinta ya kusa daukewa, wata nannauyar ajiyar zuciya ta aje har Seda kabir ya juyo tareda kallonta yace


Bismillah.


Cikin takun jan hankali ta shigo ta zauna kan kujerar da Kabir ya nuna mata, Seda ta zauna sannan yace


Se kin fito.


Kafin ta bude Baki tayi magana har ya fice, yayinda Musbahu ya juyo da Fuskarshi Baki daya yana facing Khulthum wadda tayi mutuwar zaune, wannan kyakyawan me kudin shi ke sonta? Gira ya daga mata yana binta da kallo sosae sannan ya tako a hankali yazo ya zauna cushion din dake opposite din inda take. Ya jima yana kallonta haka kurum taji ba zata iya kallonshi cikin idanu ba, idanun sun mata kwarjini da yawa, taji tsoro Yana shigarta sannan tana ayyana Anya kuwa kamar wannan yace yana sonta, Anya line dinnan intact yake ko wani abu yayi breaking?


Khulthum right?


Ya fada Yana kawar da kanshi cikin siriryar murya wadda zaka rantse mace ce. Kanta ta gyada a hankali ta kasa dago idonta balle ta kalleshi, murmushi ya danyi yace


Nasan Kabir ya miki bayani a kaina, Abinda bai fada ba zaki fahimta with time, zan aureki Inshaaa Allah nan da sati biyu zan turo gidanku sede akwai wasu dokoki da nake dasu kuma duk Wacce ta aureni se tasan da Wannan. Na farko in kika aureni na miki murna Keda kishiya har abada, bazan Kara kallon wata mace ba da sunan ta birgeni ba, na biyu namiji ya haifeni, cikin maza na tashi, Maza ne Abokaina idan kin ganni dasu bana son tambaya. Na karshe ni kaina bansan iya dukiyar da na makalla ba, babu Abinda zaki nema ki rasa don haka inason ki tsaya a matsayinki. Idan kikayi haka we're good.


Dago idonta tayi wanda ta lumshe saboda yadda words dinsa ke sinking cikin kwakwalwar ta sede bawai auna su take ba, a'a greed ya dibe ta saboda furucin karshe, me take so kudi, me kudin gaske, me kyau gashi yazo! Ina Aimana da Tace masu kudin Nigeria duniyarsu daban take? Gashi ta cin musu cikin kano batareda ta wahala ba. Kanta ta dago tace


Na amince!


Kanshi ya gyada yace


Jibi juma'a zanzo na gaida babanki.


Daga haka ya koma inda ya tashi, Sega Kabir ya shigo suka danyi maganganu wanda ba jinsu take ba hankalinta yana wata duniyar. Suna gamawa ya Mika mata sabuwar iPhone X! da envelope sannan ya maida kanshi kan Abinda yake yana jin hankalinshi Yana kwanciya saboda zai cikawa gwoggo daddan barinta shima ya samu hankalinshi ya kwanta.




Gado ta zauna ta saki kuka me ciwo, me radadi, shi kenan ya daina sonta, ya hakura bazai aure ta ba kenan? Mikewa tayi ta dakko wayarta ta Fara kiran Imratu wadda take kitchen, Tana ganin kiran ta dauka amma jin kukan Sulaim yasa jikinta yayi sanyi, hankalinta ya tashi tace


Sulaimi Menene


Yaya yace ma Mami ya fasa aurena, ya zanyi?


Shi ne kike wannan kukan Sulaim?


Yaya fa Anty! Yaya!!


Idanunta ta runtse hakan ya kara bawa hawaye damar gangarowa, sunanshi kawai da take fada ji take dukkan jikinta na amsawa, zuciyarta na harbawa da sauri da sauri! Oh Allah what will life be without Junaid?! Shi ne kawai Abinda ayyanawa.


Sulaim ki nutsu kina jina, Mami tana da dalilin Hana papan Ahmad aurenki, duk inda akaje aka dawo Kece a Wahale. Mami bata san Junaid na sonki ba seda matarshi ta tafi sannan ya gabatar da bukatar shi, Ta yaya kike tunanin baza tayi tunanin amfani yake son yi dake wajen hukunta subay'a ba? Wannan abinda take threat ne tafi kowa farin ciki kuma shima Yayan bazai taba hakura dake ba, fada kawai yake don haka kiyi shiru ki nutsu Kada kiyi abinda zaki koma jin kunyar Mami har abada. Kin gane?


A hankali taji zuciyrta tana sanyi, taji ta gamsu da maganganun Imratu hakan yasa ta share hawayenta Tace


Nagode Anty.


Kanta ta gyada tace


Allah ya zaba muku mafi alkhairi.


Amin ta furta da dusashiyar muryarta. Suna sallama ta kwanta gefen gadon hawaye na Mata zarya, ita dai soyayya bata karbeta ba, da zarar ta saki jikinta da mutum se wani abu yazo ya datsa tsakiyarsu, yanzun dukkan hope dinta yana kan Junaid gashi yanzun abubuwan da suke kunno kai. Ta dade a gurin bata daina kukan ba seda bacci yayi gaba da ita bayan Azahar ta Mike kanta nayi mata azababben ciwo kamar zai fado amma a haka tayo wanka da Alwala tazo tayi sallah sannan ta Fara neman layin Junaid sede har ta gama ringing ba'ayi picking ba, hawayenta ta share ta aje wayar akan gado ta fito parlour Don neman su Ahmad ko taji saukin abin dake damunta.


Tana fitowa taji mummunan labarin da har duniya ta nade bazata taba mantawa dashi ba, ba zata taba daina kuka akan wannan abin ba haka........ Muryar Mami ce cikin kuka take fadin


Junaid ya rasu......?!


Shi ne kadai abinda Sulaim ta jiyo taji tamkar an saka Rodi an caka a kahon zuciyarta, hakan yasa ta rike kirjinta wanda yayi mata nauyi, se baki da ya gifta daga idanunta ta zube sumammiya a gurin.




_Innalillahi wa Inna ilahil rajiun! Kui hakuri haka labarin yake, dole haka xa'ayi!!!_




*If only you could see the tears in the world you left behind, if only you could heal my heart just one more time, even when I close my eyes there's an image of your face and once again I come to realize you are a loss I can't replace......*






Shatuuu ♥️ *MACE A YAU*
38


✍️Shatuuu♥️


🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION


#⃣Shatuuu095@wattpad








*I've seen your comments all Wanda nake in touch dasu, kuyi hakuri Amma akwai abu da nake son ku fahimta ko a rayuwa ta dan Adam akan samu irin wannan abubuwan suna faruwa, ina son kusan cewar ba kowanne so ne yake zama samu ba... Haka rayuwar take ko kuma Kaga dole Se ka bi rough hanya kafin ka wuce ta smooth one. To haka rayuwar take is not everything that's at our disposal, akwai abubuwan da dole Se Kasha wahala kafin ka samu.... Nagode sosae Allah ya bar zumunci naga comments dinku nima ina baku hakuri, nasan Wanda suka fadi wasu abubuwan is out of anger banyi fushi ba ina fatan wanda sukai fushi su sakko.*








Wata razanannen ihu Ja'afar yayi wanda ta janyo hankalin Mami da Baba dake parlon, da gudu ya isa Kan sulaim din ya fara jijjiga ta Yana kiran sunanta amma ko motsi ba tayi balle asaka ran zata farfado, Ahmad da Muhammad da suke wasa suka taho kanta suna kukan AMMIEY don Junaid yace musu sunanta kenan baya son anything like Anty. Sosae Mami take kuka kamar ranta zai fita hakan ya janyo hankulan ma'aikata dake gidan suka hayo saman. Mama talatu me aikin Mami ta dakko ruwa ta zubawa Sulaim wanda Daga Baban har su Ja'afar saboda tashin hankali Babu Wanda yayi tunanin hakan, wata ajiyar zuciya me nauyin gaske ta saki kafin ta Fara bude idonta a hankali har tayi adjusting da hasken gurin, murmushi ta saki don ta tabbatar mafarki tayi, mummunan mafarki ma kuwa, wai yayanta mahadin rayuwarta ya rasu, yabi Daddy da Mummy Kai ai kuwa da ta cika marainiya Don tana ganin farin ciki sede a lahira kuma!


A hankali ta gyara kwanciyarta amma se taji muryar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login