Showing 96001 words to 99000 words out of 131263 words
sukai ayau sunje shan ice cream Yana Sanye da black trouser da white top itakuma tana cikin black plain Voil na gown anyi mata ado da farin lace a wuya da hannu, kana kallonsu kaga Wanda hankalunsu yake a kwance wanda soyayya ke gara musu, gabansu bowl ne an saka scoop din ice cream guda uku, hannunsu rikeda spatula karama sun kai bakinsu suna murmushi me tsayawa a rai.
A hankali taji wayar ta sulale Daga hannunta se kan tiles, kanta a take ya fara juyawa tamkar zata fado a gadon, zuciyarta tamkar zata balle kirjinta ta fito hakan yasa ta bude Baki ta saki ihu me karfi da ya janyo hankulan Samiha da Salima dake cin abinci a parlor!
Hohohoho! Rate the page on a scale of 10
One word for the love birds #JUNSU#
One word for the couples to be #MUSKHU#
One word for the defeated #Subay'a#
To me for the love birds #Allah ya bar kauna# for couples to be #mute# for defeated Subay'a #sorry#
Does Subay'a still have a chance? Let's talk people, next chappy depenads on your comments.
Shatuuu ♥️ *MACE A YAU*
44
✍️Shatuuu♥️
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
#⃣Shatuuu095@wattpad
_Hip Hip Hip hooray!!! My hearty congratulations goes to all the Writers of kainuwa, for marking our 2 years anniversary.... I pray Allah Azzawajal continue to guide us, lighten our path and may he forgive all of our shortcomings. Anty Fauzar mu 'yar amanah and others take this page as we celebrate together_
Babu Wanda yayi sallama cikinsu suka turo kofar suka shigo, a kwance suka sameta gwanin tausayi tana kuka Riris Tun karfinta, wanne irin masifa ce ta shigo rayuwarta? Baki daya suka tsaya turus tamkar gumaka saboda ganin halin da take ciki, Salima ce tayi karfin halin karasawa gefen gadon ta zauna Tana fadin
Haba Subay'a! Me yake damunki? Shikenan ke kullum cikin Daga mana hankali kike, idan da Kinsan mijinki haka yake me yasa zaki ketare umarnin shi!
Fada mata dai Yaya Salima, batada aikin da ya wuce tayar mana da hankali kamar ke daya ce me miji.
Itakam ko fahimtar Abinda suke fadi batayi, ina ruwanta ma dasu, babu me fahimtar halin da take ciki idan ba ita kanta ba. Kishiya! Junaid aure! Shi ne kadai abinda take maimatawa cikin zuciyar ta, kuka kawai take don gani take shi ne abu mafi muhimmanci a wannan lokacin, shi kadai zaiyi wiping mata dukkan kuncin da take ciki. Ganin bata kulasu ba yasa Samiha tace
Tunda bazata Yi magana ba, let her be.
Suka fice ransu a bace suna mitar halayen subay'a, ita kuwa tashi tayi ta zauna tareda hada kanta da gwiwarta tana sakin kuka me Cikeda tashin hankali, da tafasar zuciya. idanunta sunyi jawur a lokacin Abu daya take bukata shi ne someone to talk to and that someone is none but Sulma. Mikewa tayi ta dauka abayar da ta cire ta mayar jikinta, mayafin abayar ta yafa sannan ta tsugunna ta dakko wayar da ta fadi, ko lapiyarta Bata tsaya dubawa ba ta fito, ilahirin jikinta a sanyaye yake tana jin tamkar an sassare mata gabban jikinta, ga hawaye dake mata zarya cikin idanunta zuciyarta nayi mata zafi tamkar garwashi haka takeji. Suna Zazzaune ta fito babu Wanda ta kula haka suma se rakiyar tsaki da ta samu daga gurin Samiha.
Sulma na zaune tana kallon wani TV show a Arabian channel, gefenta Amna ce rike da feeding bottle Tana shan tea a ciki, Daddynta baya gari sunje field trip cikin wani gari hakan yasa ita kadai ta rage a gidan. Tunda ta jiyo sallamar Subay'a ta Mike don kuwa tasan babu lapiya ko daga amon Sautin muryarta, kanta ta dafe tana tunanin Anya ta Taba ganin mutum me masifar matsala Irin 'yar uwarta. Tun suna yara haka take, mutum ce da bata daukar shawara in zatayi Abu se ya kwabe mata sannan zata zo ta daga muku hankali haka take kuma har suka Girma babu Abinda ya canza zani.
Gefenta ta zauna ta hade fuskarta da tafukan hannayenta tana kuka me cin rai, Wanda yake tabbatar maka wanda yake ba karamar tashin hankali da walagigin rayuwa yake ciki ba, kuka ne wanda Subay'a keyi na rashin sanin makomarta, na tashun hankali Cikeda nadamar da bata da amfani a wannan lokacin. Sulma Bata ce mata uffan ba dukda she's disturbed da kukan amma ya ta iya? Me zatayi? Kyaleta tayi taci kukanta me isarta wanda tasan ko babu komai she'll shed away some of her pains. Kowa yasan kuka is a powerful pain reliever, just try it.
Seda tayi ta koshi tayi to her satisfaction kafin kuma ta goge fuskarta tare da kallon Sulma wadda fuskarta kawai zaka kalla ka hango tsantsar damuwar da take ciki, hannunta Subay'a ta kama Tana sakin murmushi wanda babu komai cikinshi banda zallar pain wanda dashi gwara tayi wani sabon kukan amma ya zatayi,
Kiyi hakuri sister, inajin inama ina da wanda zan kawo wa kukana bayanki at least na daina tayar miki da hankali, I'm not good to myself balle to be good to others. Bana neman shawara ina yin duk Abinda zuciya ta taji ya kwanta mata don Nayi satisfying ego dina. Inama ace ni ce ke, inama ace Nayi kwaikwayon kyawawan halayenki da wasu abubuwan sun zo min da sauki.
Hannunta Sulma ta rike bakinta ya kasa furta komai saboda abubuwan da take hangowa cikin idanun Subay'a wanda Bata taba gani ba. Wayarta ta dauka ta bude mata pictures din idanunta na zubar da hawaye ta Mika mata. Jiki a sanyaye ta karba sede biyu kadai ta iya kalla jikinta ya fara rawa, ta aje wayar tareda runtse idonta. Wasu hawaye masu zafi a Karo na barkatai suka shiga zubowa Subay'a, kuka sosae ta kuma fashewa dashi tana fadin
Kinga ni ko? Junaid yayi aure, ya auri yarinyar da tafi kowa sanin flaws dina! Yarinyar da duk duniya bana fatan na bude ido Naga tana numfashi! Nayi kuskure babba na gasken gaske kuwa! Na tafi na baro mijina under the care of abinda nake ganin sonshi cikin idanunshi. I deserve it......
Toshe mata Baki tayi tareda janyota jikinta tana lallashinta, har Seda tayi shiru kafin Sulma tace
He punished you da aurenta.
Kanta ta girgixa tace
A'a Sister kin tuna Abinda nake zargi? Na zargi yana sonta zamana ya zama kamar barrier tsakaninsu, I never in my life taught barin gurin zai basu space din cika burinsu, se gashi ya cika burinshi. Ya zanyi I destroyed myself with my hands.... My very own hands Sister.
Shiru tayi ta Mike Kara dawowa ta zauna idanunta basu daina barin hawayen da suke ba, bata taba mafarkin akwai ranar da zata wayi gari taji makamancin wannan kuncin ba, kai ko ce mata akai a duniya irin wannan feelings din does exist to tabbas zata karyata mutum, yau gashi Itace ta tsinduma kanta a ciki. A yanzun ta fahimci maanar zaman lapiya shine kabi Abinda Allah da manzonsa suka ce, ta tuna wata levtures da ta taba attending akan biyayyar aure, manzon Allah SWA yace Idan da zansa ayiwa wani sujjadda Bayan Allah to miji ne! This is to show how manzon Allah SWA yake son nuna girma da kuma daraja ta miji amma a yanxun ta take Nata tayi yadda take so.
Zan tafi Nayi booking next flight to Nigeria.
Ta fada Bayan ta koma ta zauna, Sulma Cikeda damuwa tace
Hakan yayi amma zaki dawo ko?
Kanta ta girgixa tace
Not necessary, zan koma na gyara Abinda na bata, Kede Kiyi min addu'a na dace.
Dafa kafadarta tayi tareda fadin
Duk Abinda zaki tarar ina fata zaki rufe idanunki, kiyi hakuri kada ki tada hankalin ki me faruwa ta faru.
Dariya Subay'a tayi tace
Life has taught me so much, ba se kin dora ni a hanya ba sister. Yanzun bana bukatar kowa yace min ga yadda zanyi.
Kanta ta gyada mata kafin suka Mike ta rako ta har bakin kofa, daga nan sukai sallama ta koma ciki jikinta a matukar sanyaye, Tana fatan hakan ya zama babbar shiriya gareta.
Bangaren Subay'a kam tunda ta shiga dakinta ta kwanta tare da fara booking flight sede next flight to Nigeria is in a week time. Tasha kuka kuwa saboda tana ganin hakan yana Kara nisanta ta da kudinrinta. Tundaga wannan ranar ta daina fita, Ta kashe wayar ta. Hakan yasa ta zama very lonely and bored.
Ranar da sati ya cika ranar ta kammalla shirinta tsaf, an hour to the time ta fito da kayanta tsaf ta nufi airport don ko Sulma Bata fadawa ba Balle su Suhaila wanda basa gidan Baki daya sun tafi lecture. Tana zuwa babu bata Lokaci akai screening da komai sukai boarding jirgin da ya Lula zuwa Nigeria.
KADUNA.
Mami na Zaune itada Baba Wanda ya dawo shekaranjiya daga umra, suna kallo jefi jefi suna hira akan matsalolin da suke addabar Nigeria.
Nikam matar Junaid har yanzun bata dawo ba?
Baba ya tambaya idanunshi kan Mami, gyara zamanta tayi tareda fadin
Inafa bata dawo ba, don bance tasan da zancen Auren ba.
Kai Baba ya kada yace
Junaid baiyi Saar uwar 'ya'ya ba, kwatakwata yarinyar tafi kama da yaran da basuda uba Amma bansan abinda mahaifinta yake ba har uwarsu Ke wannan hidimar.
Tsakin takaici Mami ta saki tace
Ka manta Ance shima haka yake fama, kawai kaddarar Junaid ce hakan, Shiyasa bazan saka baki ba akan hukuncin da zai yanke mata ba, kawai bazan Bari ya saketa ba amma lokaci yayi da zai daidaita gidanshi.
Hakane Nafisa, Amma ya kike ganin zaman Ummu_Sulaim da Junaid zai kasance?
Dariya Mami tayi don ta fahimci me Baba yake nufi, Kada yarshi tayi bora.
Wannan is sort already, yanxun yace Malta zasuje early next month, kafin su dawo ginin da yake ya kammalla, Kaga kowacce da gidanta.
Sallamar Ja'afar yasa Baba bai bada amsa ba, sema wani muhimmin zance da ya fado mishi ganin Ja'afar din, shima ya kara kyau dukda yayi rama a fuska amma kana kallonshi zaka San Hutu yana aiki a gurin. Zama yayi kan carpet ya gaishesu, suka amsa sannan Baba yace
Ja'afar Babanka Ibrahim dazun ya kirani akan maganar ku kaida Haulat!
Haulat? Haulat kuma
Ja'afar ya fada a birkice, Wacce Irin magana kuma
Eh Haulat dai, babanta yace ta fito da miji zai mata aure tace Kai kuke tare.
Da sauri yace
Wallahi karya take Baba, Mami......
Karka sake ka kira Sunana, Haulat kake denying, sau nawa ina ganin pictures din ta cikin wayarka, Mamanta Tace min har Abuja Kake Zuwa zance.
Baba yana kallon Ja'afar yadda yayi kicin kicin da fuska Cikeda tashin hankalin jin inda yake neman afkawa. Haulat ita daya Allah ya bawa Alhaji Ibrahim Kasim kanin Mami da Anty Batuul wanda suke Zaune a Abuja, Haulat babu laifi tana da kyau kuma tanada tarbiyya Sede yarinya ce shakwaf da batafi 16 years ba amma tanada girman jiki, kuma tana daya daga cikin yan matan Junaid sede Itace me least wadda yake ganin zai iya aura se gashi an rikeshi rum a hannu!
Kai Ja'afar yimin bayani, ya zancen Maminku yake?
Da gaske ne Baba, amma ni ba sonta nake ba.....
Yaudarar ta kake, kasan duk Abinda kake ina sane dashi, kasan haka kayiwa sulaim ko?
Sulaim kuma Mami? Ni nace miki
Bakace ba, I read it a diary dinta, Hanan fa?
Kanshi ya dafe wanda yake Sara mishi kamar zai fadi, waye ya mishi wannan ta'asa, Baba kasa magana yayi saboda mamaki, ranshi a bace yace
Wallahi ko baka sonta Ja'afar Seka aureta, kuma wannan shi ne magana ta karshe. Ki zama cikin shiri next week zamu tura a bamu Haulat a Karo na biyu Bayan Sulaim!
Subay'a na hanya, who will volunteer to sweep her room for her, ya haduwar zatayi da Junaid da Sulaim matafiyan Malta? Ina labarin mutanen Texas da A'isha? Ga Ja'afar ya ballo aiki, Ina TitαΦ da Amaryarshi.
Tell me your opinion about this page and what might happen next.
Shatuuu ♥️[8/26, 5:03 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU*
45
✍️Shatuuu♥️
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
#⃣Shatuuu095@wattpad
*Ina masoya Anty Sumayya Abdulkadir Takori? Ga dama ta samu cikin sauki da kudi kalilan zaki karanta littafinta na _A BARI YA HUCE...._*
Jirgin daya taso Daga Murtala Muhammad INT'L Airport dake Lagos ya sauka a Aminu Kano INT'L Airport dake birnin Kano. A hankali passengers ke fitowa kowanne da yanayin da Fuskarshi ke ciki, wasu gajiya, wasu yunwa, wasu excitement, wasu tsoro ne karara kwance akan fuskar tasu kamar Hajiya Subay'a wadda tamkar kace mata kett ta zura a guje saboda tsabar yadda take a firgice batasan abinda zata tarar ba a wajen Junaid don ita a halinda take ciki bata Sulaim take ba so take ta fara kashe kurar kafin ta koma kan Sulaim din.
Bata expecting kowa ya zo daukarta ba Tunda babu Wanda yasan tazo din haka ta tari napep wanda if she can remember vividly bata tunanin ta taba hawa commercial ride Tunda take a rayuwarta. Kwatance tayi mishi yana ta basarwa tareda ciccin magani ya amsa zaije, seda ya kalleta tsaf yaga yadda kudi ya samu gurin zama yace 600 zai karba, bata ja ba haka ta hau suka nufi gida, gabanta Yana ta faduwa lokaci lokaci tana share hawayen da yake bin kuncinta. A kofar gate din ya ajeta tareda nade hannunshi Yana jiran ta fito amma ina tayi nisa sosae cikin duniyar tunanin da take akan abinda zata tarar idan ta shiga, ko wanne irin tarba zata samu, tasan bazai taba sakinta ba amma zai iya hukuntata da mafi munun hukunci shi ne Silent treatment halin Junaid ne ya kyaleka akan laifinka Sede ya barka da guilty tension haka yake.
Juyowa me napep din yayi ganin yana ta mata magana Bata bashi amsa ba, ya juyo yace
Hajiya ki sauka ki bani kudina ina ta miki magana kinyi min banza.
Dagowa Subay'a tayi ta share hawayenta tace
Yi hakuri Malam.
Tsaki yayi ya ciro cigar daga pocket dinshi yayi lightning tareda Fara zuka, Jakarta ta bude ta ciro purse Amma babu Nigerian currency se na can inda ta baro, jikinta har rawa yake tace
Bari na shiga na dakko maka kudin dan Allah anan babu.
Wata ashar ya saki tareda bule ta da hayakin bakinshi wanda yasa ta fara tari babu kakautawa don idan akwai Abinda Subay'a ta tsana shi ne warin cigar
Amma Kinci uwar rainin hankali, da Kinsan bakida kudi xakixo ki shigar min napep na kawo ki!
Subay'a ta kullu take Hali ya motsa ganin yadda kankanin yaro yake mata rashin kunya, Amma a hankali ta dinga petting kanta tana fadawa kanta yanxun is not the right time tayi haka, kawai ta lallabashi ta samu ta bashi kudin taje taga yadda gidan yake ciki.
Kayi hakuri mana shiga kawai zanyi na kawo maka.
Tsaki yayi hakan ya kara bata mata rai amma ya zatayi, yau tana jin tamkar ba Subay'a bace, kamar ba ita ba wadda fuskar wargi mutum bai samu Balle Ya kawo mata hauka amma imagine Yau Itace wannan kanin bayan nata yake mawa haka. Trolley dinta taja ta Fara knocking wabda shima ta kusan shafe Mintina goma kafin me gadin yazo, ranta a matukar bace tace
Bakasan aikin ka ba kenan wawa kawai!
Shi baima bi ta kanta ba yayi ciki abinshi hakan ba karamin mamaki ya bata ba, to Meke faruwa? Her remaining dignity is lost also? Ta tuna yadda jiki na rawa ma'aikatan gidan ke mata biyayya amma yau Itace ko matsayin gaisuwa Bata samu ba. Kanta ta girgixa Tana jin wani daci cikin ranta wanda har bakinta take iya jin dacin. Ciki ta shiga gabanta Yana dukan uku uku, lokacinda ta tura kofar parlour ta shiga Seda ta runtse idonta saboda wani yanayi da ya ratsa ta, gidan da ta bari ba tareda izinin Junaid ba, Ta tsallake yaranta wanda take jin duk duniya ba abin da takeso tamkarsu Amma a haka ta tsallakesu ta tafi biyawa zuciyarta bukatarta. Da sallama dauke a bakinta ta karasa cikin tsakiyar parlour, ko ina tsit se kamshi wanda ya zama bakonta da take iya shaka, komai ya canja an canza komai in just 3 months kawai, se taji ta tamkar bakuwa, tamkar is the first time of her being a gidan.
Jin shiru yasa ta nufi kofar dakinta don shiga Sede Tana rike kofar taji Atika na fadin
Wacece?
Idanunta ta dan runtse tare da aro jarumta ta juyo Tana facing Atika wadda ta fito Daga dakin Sulaim, Tana kallon Atika Bata wani canja yanayin fuskarta ba da ta ganta, hakan ya ruguza mata lissafi tareda sakar mata da gwiwa. Amma haka ta dake tace da Atika wadda take Mata wani kallo wanda Subay'a ta kasa fassara manufar kallon Amma yafi kama da you lose!
Ina mutanen gidan?
Daidaita kanta tayi ta tsugunna kamar yadda ta Saba Don kuwa Subay'a na nan matsayinta Koda sakinta Junaid yayi Balle da aurenshi har yanzun a kanta.
Tun shekaranjiya suka tafi kaduna.
An fadi Yaushe Zasu dawo?
Kanta ta girgixa tace
A'a Ammiey bata fada ba.
Cikin rashin fahimta Tace
Wacece Ammiey?
Anty Sulaim!
Ta Bata amsa take taji Wani abu ya tokare mata makoshi Jin Sulaim ce Ammiey! Juyowar da kanta tayi tana murda kofar amma a rufe hakan ya tabbatar mata Junaid ya tafi da key din, purse dinta ta bude don neman spare key Amma fit babu shi don kuwa ta barshi anan tana sauri bata dauka ba. Kallon Atika tayi da take rurrufe kujerun parlour da ledarsu hakan yasa tasan mutanen gidan ba yanzun Zasu dawo ba