Showing 105001 words to 108000 words out of 131263 words

Chapter 36 - MACE A YAU Document from Sulaim .txt

24 Nov 2024

4830

tensed and not favorable kwatakwata hakan yasa taji ta gundura har Seda Hajiya ta iso idanunta a warwaje ganin Suhaila, Sulma da Kuma Salima mutanen Cyprus, ga kuma Surayya, Samina, Samiha da Sakina. Gabanta Yana bugawa da sauri sauri tamkar zai fito tazo ta zauna Tana fadin


Meye ne kuka dawo kuma? Meye kukazo kuka zazzauna kamar marasa......


A makogaro maganar ta makale ganin Abinda idanunta Ke hangowa, Alhaji ne Sanye da trouser na kamfanin Zara se top wadda ta amshe shi, kanshi anyi masa saisaye hatta Fuskarshi an rage kasumbar da ta cikata, yayi kyau tamkar lokacin yana ganiyar 20s dinsa, Baki daya tsufan ya wuce se yarinta karara da ta bayyana a tare dashi. Duk wannan bashi bane damuwar Hajiya ba a'a kyakyawar Yarinyar da shekarunta bazasu wuce sha Tara ba tana Sanye da pencil trouser Baki da top ja kanta babu dankwali ta zubar da gashin kanta Wanda ya sauka har ya dan wuce dokin wuyanta Baki sidik Yana sheki, ita kanta yarinyar tamkar anyi barin perf jikinta saboda tsabar yadda take fitar da fitinannen kamshi, kyakyawa ce ta gasken gaske don kallo daya zakai mata ka gaskata hakan. Fuskarta ta nuna tsantsar yarinta ga kuma kyabe fuska da tayi kamar me shirin yin kuka, se kara shigewa jikinshi take. Surayya ce ta Fara mikewa idanunta tamkar xasu fado kasa ta bude bakinta Dan magana Alhaji yace


Duk Wacce tayi magana se nayi mugun saba mata.


Jagwab ta koma ta zauna, Sulma hawaye ta Fara itada Subay'a Bayan sun kankame hannayen junansu, Samina kuwa kana kallonta itada Suhaila kasan a cike suke taf da masifa don fuskarsu har tayi jawur saboda tsabar Abinda yake cinsu basu fitar dashi ba. Salima tafin hannayenta tasa ta rufe fuskarta, yayinda Samiha da Salima suka kurawa Alhaji da yarinyar idanu tamkar basu taba ganin Alhajin ba ko kuma ya zama wani bako, Surayya ta Mike tareda kamo Hajiya wadda ta rigada ta daskare a wajen saboda tsabar yadda ta fita a hayyacinta ta zama tamkar statue wadda aka dasa ta a gurin! Tsoron Surayya kada hajiyar ta fadi ta samu stroke su shiga ukunsu!


Na Tara ku anan saboda na gabatar muku da Matata, amaryata, sabuwar uwarku Asiya! Ina.......


Alhaji....


Hajiya ta katse shi mid sentence shima ya katse ta da fadin


Mistakenly kika Kara saka min baki Se na sauke igiyar aurenki.


Jin wannan furucin ba karamin dukansu yayi baki daya ba, itakam Asiya ba su bane a gabanta don ko kallon arziki babu wadda ta yiwa hasalima tana jin an takurata Zuwa gurin nan hakan yasa ta dubeshi a shagwabe tace


Honey mu tafi mana.


Mikewa yayi ya kama hannunta baice dasu komai ba ya nufi wajen part din zuwa na gefen inda anan ne zata zauna. Kamar hadin baki gabaki daya Suka fashe da matsanancin kuka saboda a ganinsu an tozarta su, sun manta tozarcin da saukai yiwa wasu, sun manta rashin arzikin da sukai a nasu gidajen. Hajiya kam tamkar fool haka ta koma Ta rasa me zatace se binsu take da ido tana jin inama ita ke kukan da suke at least ta samu sassauci. Basu gama wannan tunanin ba Alhaji ya dawo shi daya, ya hadasu ya wanke su tas har uwarsu, yace yayi cancelling Cyprus kowacce ta koma dakinta, kada su sake Zuwa mishi gida weekly kamar yadda suke sede Bayan wata dai dai, sanann ya basu awa daya suci abinci kada ya samu mutum daya a gidan!


Who saw this coming? Ina Subay'a zataje? How will everything be? Let's continue d journey to its end!!!


Shatuuu ♥️[9/2, 9:38 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU*


49


✍️Shatuuu♥️


🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION


#⃣shatuuu095@wattpad




*Of course, today is a special day, my beautiful, elegant favorite sister has clicked 12 years today. Maman moon, Oum Abdallah are all a year older... I pray Allah continue to shower his endless blessings, mercies and support upon them. Be blessed dearies!*




Kowanne ka kalla cikin su takwas din kasan ba karamin duka maganar Alhaji tayi musu ba, tamkar saukar aradu haka Maganganunshi suka isa kunnuwansu, Baki daya ba kansu suke tausayawa ba Illa Hajiyarsu da zata kwashi bakin ciki cikin gidan, gaba daya Asiyar Nawa take ba zata wuce shekaru goma Sha Tara ba, to Samina ita ce autarsu wadda ta dade da bawa shekaru ashirin baya, yanzun haka shekarar ta ashirin da uku. Amma Alhaji ya rasa wadda zai aura matsayin matarshi se wannan mitsitsiyar yarinyar da Fannah 'yar Suhaila kadan ne Bata girme mata ba. Yanzun duk wannan cika bakin da suke na su basu zama da kishiya, nasu su kadai ne mata gidajensu se gashi Anyiwa uwarsu da jikarta. Kuka sosae suke wannan karan har ita kanta Hajiyar, gaba ki daya jinta take tamkar ba ita ba, Tunda take bata taba jin Irin wannan wulakncin ba ko a labari se gashi ya faru a karan kanta.


Samina ce ta Fara mikewa tayi hanyar fita ko dankwali babu a kanta, cikin sauri Surayya ta Mike tareda fadin


"Ke samina ina zaki je? "


Juyowa Samina tayi idanunta sunyi jawur, ga hawaye da yayi mata kacakaca a fuskarta tace


"Zanje gurin waccan yarinyar da Alhaji ke kiranta Uwarmu, Wallahi se na targada mata kashin ta"


"Idan baki targada ta ba, ni na karairaya ki shashashar wofi! "


Haka ta tsinkayi muryar Alhaji Yana fada a bayanta da yake ya dawo Dan ganin ko sun tafi, da sauri jiki na rawa Samina ta shigo tayi Bayan Hajiya jikinta na rawa saboda tsabar tsoro, ita dama haihuwarta an gama asirce Alhajin don haka a laushinshi tubus ta sameshi amma dukda haka basa kawo mishi wargi, bar su dai da basu bin takanshi idan zasui abu idan hajiya ta amince shi kenan. Su Surayya su suka san waye Alhaji Alkasim, su suka san true definition dinsa, Shiyasa suka hango wautar Samina da take tunanin ketare umarnin shi.


"Uban me kuke har yanzun Baku tafi ba? Kun manta Abinda na fada kenan? "


A rikice duka suka Mike kowacce ta Fara maida mayafinta da tazo dashi, Hajiya ganin hakan yasa tayi ta maza tareda kallon Alhajin tace


"Babu inda zasu je Kasimu, babu inda zasuje nace, ku koma ku zauna nace gidan ubanku ne babu Wanda ya isa ya koreku Daga ciki. Idan banda asara da lalacewa Irin taka tsofe tsofe da Kai Kaje ka auro yarinya Saar jikarka, ai Wallahi kaji kunya ka bani mamaki, kuma tsakani na da kai Allah ya isa! 'ya'ya babu inda zasuje na fada"


Maimakon yayi fada se yayi murmushi tareda fadin


"Kika ce babu inda zasuje?"


Kanta ta gyada ta kallesu dukkansu sunyi tsaye kamar zakaru tace


"Babu inda zakuje, gidan ubanku ne"


Bai ce mata komai ba ya ficewarshi , dariya tayi tana tunanin aiki ya fara dawowa, dukkansu suka zauna amma a tsorace banda Sulma da tace


"Hajiya ki Bari mu tafi kawai, wannan fadi in fada da kuke ke da Alhaji, bashi da amfani, aure ya riga yayi, hakuri ne kawai namu. Dama ai munsan ranar nan dole Se tazo ranar da komai zai kwabe mana"


"To Muslim Sister, Assheikh, Malama. Naji nace naji idan ke bazaki zauna ki tayani kukan abinda ubanku yayi min ba, kije Allah ya kiyaye dadin abin ba ke daya bace 'yata da tuni takaicin ki ya kasheni"


Sumsum Sulma ta samu guri ta zauna tunda ta rasa Wanda zai Goya mata baya, dukkansu sunyi shiru masu sharar hawaye Nayi, Masu kulle kulle cikin zuciya sunai dukda sunji maganganun Sulma kuma gaskiya ta fada amma furucin Hajiya bazaisa su Goya mata baya ba, don idan aka bi salsala duk saboda su waye ta shiga wannan halin? Saboda su dinne, don su samu soyayyar uba ba tareda an raba ta zuwa ga wasu yaran ba amma a karshe abinda ake gudun shi ya faru!


Dawowa alhajin yayi, mamaki kwance a Fuskarshi ganin yaran suna zaune, a ranshi ya Raya dole ne ma yayi abinda yayi niyyar, Seda ya tsaya gaban Hajiya kafin ya ciro farar takarda Daga aljihunshi ya Mika mata tareda fadin


"kije na sake ki! "


Dif parlon yayi saboda wani abu da ya ratsa dukkansu, Subay'a ta lumshe idonta a hankali tana jin ita ce next person da hakan zata faru a kanta, Hajiya was dazed and confused ta kasa Koda kwakwaran numfashi me tsawo, tunaninta Baki daya ya dauke se harbawa da zuciyarta Ke yi tsabar firgici. Juyawa Alhaji yayi Bayan yace


"Duk tsawon rayuwar ku Baku taba kallona a matsayin uba mahaifi ba, se shashasha da kuke daukata. Mahaifiyar ku ita ce mutum a idonku Don haka nake son ku tattara har ita ku tafi duk inda zakuje amma ku manta na haifeku"


Yana gama fada ya juya don ficewa amma ya gagara hakan sakamaakon Sulma da ta tsugunna ta rike mishi kafafunsa kamar zata balla su, kuka take wanda me saurarenta ma dole zuciyarshi ta karye, kallonta yayi a ranshi Yana jin tausayin ta da ta kasance Yarinyar Hajiya, Yarinya me hankali da hangen nesa wadda ita daya take binshi bata manta cewar shi din uba ne a gareta ba, yana sonta a kaf cikin yaranshi babu Wanda ya ke da gurbin da take dashi, Amma bazai bari ta karya masa Abinda yayi niyya ba, hakan yasa ya janye kafafunshi ya fice baki daya. Ta jima tana kuka kafin ta Mike ta koma ciki inda ta samesu suna hadawa Hajiya kayan ta wadda ko uhm ta kasa furtawa se hawaye da take tana binsu da idanun ta.


Wasu cikinsu kuka suke, wasu kuma sun shiga taitayin su kamar Subay'a, Salima da Sakina. Suna gamawa Surayya ta dafo Hajiya suka fito tareda kulle sashen gaba daya Bayan Subay'a ta fito da nata kayan zuciyar ta Cikeda zulumin inda zata nufa. Dukkansu da motarsu suka zo hakan yasa kowacce ta shiga tata se Subay'a ta shiga ta Sulma. Surayya ce a gaba hakan yasa suka mara mata baya zuwa Darmanawa inda anan gidan aurenta yake. Ita kadai ta shiga da motarta dukkansu a waje sukai parking sannan suka shiga kayataccen parlon gidan Wanda ya sha gyara ga dukiya da aka narkar a ciki. Yaran ta basu nan sunje gidan su mijinta suna Family meeting hakan yasa gidan masu aikinta kadai suka rage. Dakin dayake spare cikin gidan ta bude ta kai wa Hajiya kayanta se a sannan Hajiyar ta dinga kuka Tana karawa, a ganinta bata cancanci hakan Daga gurin Alhajin ba. Yaran dukka suka saka ta a gaba suna kuka wasu na lallashinta.


"Kaico ni! Haka Alhaji ya zaba yayi min, hakan ya ga yayi mishi daidai? Seda na gama mishi aiki na bauta mishi sannan zai sakeni? "


Kuka yaci karfinta, su kansu sunsan fada kawai take amma Babu abu guda daya da take yi cikin abinda ta lissafa, su a karan kansu sukan manta cewar wai suna da Uba, se suje gidan su yini amma ko sashen da yake basu kalla kasan ba. Gashi nan karshensu dukka yazo Allah se ya fara daga kan uwarsu wadda ta dorasu a hanyar!


"Surayya miko min wayata na kira Kubra dole a gaggauta aikin"


"Wacce Kubrar? "


Suka hada baki, Suhaila tace


"Hajiya Baki daddara ba, har tunanin sake komawa ga laifinka kike? Haba Hajiya ko ni nan na bar komai na tuba nabi Allah don ya nuna mana iyakarmu, ya nuna mana shi ya halicce mu"


Surayya tace


"Mufa tsakanin mu da Anty Kubra Allah ya isa! Saboda ita ta jefa mu cikin wannan rayuwar, Hajiya ki manta da komai ki rungumi Allah kilan hakan yasa Alhaji ya maida ki dakinki Amma ni dai yau na girgiza matuka "


Samina wadda se lokacin tayi magana tace


"Nufinku yarinyar can taci bulus? Shi kenan ta Kori Uwarmu Daga gidan ta, Wallahi ni nan se nasan yadda na Kwata mana 'yancin mu"


Hajiya wadda jikinta yayi matukar sanyi, kalaman yaranta suka shige ta farat daya tace


"Kaiyya auta, babu wata wadda ta koreni ni na Kori kaina, ina fatan hakan ya zame mana darasi gabaki daya, kowaccenku ta gyara gidan ta kafin Lokaci ya kure mata, Kawaye basuda amfani Don na gani a karan kaina. Subay'a ki tattara ki tafi Kaduna ki jira mijinki ya dawo sannan ki zauna da abokiyar zamanki lafiya don munyi sake babba. Haka nima bazan zauna anan ba akwai gidana dake tarauni can zan koma har Zuwa yadda Allah ya tsara! "


Tabbas sunga saurin nadamar Hajiya amma basu san Hajiya ta Fara laushi ba tun zuwansu gidan Junaid da sukaga yayi aure, Tun lokacin jikinta ya bata karshenta yazo Amma taki aminta da hakan ta cigaba da bin son zuciyarta gashinan ga inda ya kawota!!!




Amarya Kinsha kamshi Koda kin kashe dan masu gida! Haka abin yake, haka bahaushe yace Amma ga Khulthum zata iya karyata wannan popular saying din, zata iya Rantsuwa cewar ba gaske bane Don kuwa ta shaida hakan. Aure de gashi tayi shi, irin wadda take mafarkin yi kullum, ga dukiya nan ta samu kana kallonta kasan Hutu da jin dadi Ya samu guri Sede rashin kwanciyar hankalin da take ciki yasa idanunta suka Fada ciki sosae, kashinta na wuya ya bayyana. Tana zaune tayi wanka tayi kyau cikin wata Holland wax purple me kyau da tsari, dinkin plain zani da riga wanda yayi mata kyau da cifcif a jikinta, ko dankwali bata daura ba haka take Zaune tana tunanin yadda komai ya juye mata, aure kusan sati hudu amma sau biyu kadai tasa miji a idonta, ranar da aka kawo ta da ranar da taje gurin shi a part din shi.


Kwanciyarta ta gyara ta janyo wayar ta dake jikin socket tana caji ta Fara kiran Sulaim saboda tana bukatar wanda zatayi magana dashi Amma ta buga tafi a irga amsa daya ce a kashe se lokacin ta tuna Ashe lokacin kanta yana rawar aure ta fada mata zataje Malta. Kawai se ta Fara kiran Maimuna wadda kamar jira take ta dauka. Seda ta gama tsokananta


"Matar Manya amaryar TitαΦ uwar Magajin TitαΦoils, foods and flours!"


Da idan Maimuna tayi mata wannan kirarin Jinta take tamkar a saman gajimare amma yanzun se take jin wani banbarakwai kwatakwata Bata fitting da abin ba.


"Ki Bari kawae Maimuna, ina cikin matsala!"




"Wacce Irin matsala kuma? Haba dai mu a cikin matsala kuma a ciki"


A ranta cewa tayi nima haka na dauka amma gashi ba hakan bace ta kasance, ta dauka cewar idan ka auri me kudi ka gama dacewa cikin duniya, to gashi babu inda akaje abubuwa sun lalace! Cikin nitsuwa ta warwarewa Maimuna dukkan abinda yake damunta, dariya Maimuna tayi tace


"Amma kin bani Mamaki uwar Magaji, Karki manta lokutan da kike saka Maza dripping Amma gashi mijinki kin kasa juyashi, ni har ina tunanin gobe inzo da PT strip nayi gwaji. Yanzun har wata daya babu wani abu, ina tactics dinki suke? Kije kiyi seducing dinshi idan yaki zan kawo miki tablet kiyi mishi amfani dashi. Kiyi amfani da damar ki kafin ta kubce miki sannan ki yi amfani da damar ki ta mace ki janyo hankalinshi. "


Wannan magana ta shiga kunnuwan Khulthum hakan yasa ta Mike Bayan sunyi sallama ta nufi kitchen inda ta bada order plantain, porched egg da coffee, komawa tayi ta sake wanka ta shirya tsaf tayi barin turare sannan ta dora katon hijabi ta dauki tray din zuwa part dinshi.


Tana zuwa tsakiyar parlon Sega wani hadadden saurayi ya fito Daga wancan bedroom din da taga sauran sun shiga wancan karan, kallonta yayi Baice mata uffan ba ya fice abinshi. Jikinta a sanyaye ta nufi bedroom din gabanta Yana mugugun faduwa tare da fara tunanin Meye Musbahu yakeyi da Maza har haka???


Ku biyoni a next page dan jin yadda zata kaya tsakanin Musbahu Dan Gwoggo da Amaryarshi Ummu_Khulthum uwar magaji.




Shatuuu ♥️
[9/2, 9:38 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU*
50 to 51


✍️Shatuuu♥️


🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION


#⃣Shatuuu095@wattpad






*Its a long journey I know, yeah! I'm concluding the novel Inshaaa Allah on or before 1st September. So from now on Inshaaa Allah double in one page zamu Nayi. Thank you very much for all the support, prayers, love and comment..... That's what kept me going, that's what makes me update daily, I'm so much grateful for everything*




_My heart goes out to Salma Hassan Kwalam, Tee Zarewa, Anty yaya (Sadiya Lawan), Anty Fatima sadi, Yaya Baby, Anty Asma'u, A'isha, A'isha imam, Aisha kaagu, Aisha Akko, Aisha Ahmad, Aisha sheikh, Yaya Umma, Farida S maina, Abida Suleiman, Ammasheikh, Anty Hijja, Daughter Farida, Oum Annur, Maman Zarah, Amaryar yaya Mousa, my Najeeyba, Maman Hanif, leiymahs delicia, Sister Sadiya, Sister deejah, Sister Ummin D/batta , Fatima idris, Nanah ganuwa, Fatima ummi, Yaya Nana, Pyaule, heedaya Bunu, Aisha major, Jidda Hamisu, Fatyn zulayha, Hanifa, Khadeeyja DRB....including all and all the ghost readers in the SHATUUU's KINGDOM .....without you many things won't be possible thank you!_






Cikin dakiya da jarumta Uwar magaji ta Kai hannunta Kan handle din kofar, gabanta a lokacin ya kara bugun da yake amma haka ta murda kofar ta shiga, sanann ta maida kofar ta rufe tareda murda key din da yake jiki.... Kunji karfin Hali kamar dakinta. Zare key din tayi ta daura saman tray din dan yau ko Wacce aljana ce ta aure mata miji as they said, ko da bashi da lafiya yau se tayi yadda tayi. Tana juyowa idonta bai sauka a ko ina ba se makeken Italian bed din Musbahu, kafin cikar seconds jikinta ya fara bari tamkar mazari, idanunta Manya ta Kara ware su kirjinta tamkar zai balle, tamkar an ingiza hannunta tray din dake hannunta ya kubce jikake Tas! Tas! Ceramic plates, cups da bowls din dake kan tray din Baki daya sun fashe wanda a take yayi awakening Musbahu da partner dinshi Daga abinda idanun Khulthum dani na kaina suka gane min...... Khulthum kidimewa tayi ta juya da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login