Showing 126001 words to 129000 words out of 131263 words
Allah yayi lokaci yayi haka ta rasu ana kallo. Jabir kowa yasan yadda yake son Imratu babu Wanda yafi shi shiga tashin hankali haka ya rungume Mami Yana kuka kamar karamin yaro tamkar ba soja ba. Sede muce Allah yasa ta huta!
Mami da ta gama hada mata Madarar da akai musu prescribing ta mikowa Sulaim wadda ta Fara bata tana jin tausayin yarinyar a zuciyarta, tasan me ake kiran maraici tasan zafinshi dukda babu Abinda ta rasa amma iyaye daban suke ko me ka samu a rayuwa kuma ko mai ka zama dole iyaye daban suke amma tasan wannan ba zata rasa gata ba, bazata taba maraici ba kamar yadda itama ba tayi ba tasan wannan family bazasu barta haka ba, ita kanta she's covered with love, tasan Abinda suke mata ko Daddy da Mummy na raye ba Lallae suyi mata hakan ba.
"Sulaim ba zaki daina kuka ba, Imratu ta tafi addu'a kawai take bukata amma wannan kukan naki yayi yawa, Kema kinga yadda kike bazai helping condition dinki ba"
Haka ta tsinkayi muryar Mami a kanta, hakan yasa ta goge hawayen fuskarta tareda daura babyn akan kafadar ta don tayi gyatsa sannan tace
"Mami tausayin Baby nake ji, zata tashi batada uwa"
Karo na farko tun bayan rasuwar Imratu da Mami tayi murmushi tareda kama hannunta tace
"Kina nan zatayi rashin uwa? Nasan idan kina raye ba zata taba kukan maraici ba, inason ki rungume ta ki zame mata uwa kinji Auta ta? "
Da sauri Sulaim ta gyada kanta tare da kara kankame babyn daidai shigowar Baba da dukkan yaranshi. Idanunta cikin na Junaid wanda ya dan fada Balle kuma Baban baby idanunshi sunyi jawur ya rame sosae se ido da karan hanci. Kana kallonshi dole tausayinshi ya kama ka saboda yana cikin mawuyacin hali wanda shi kadai yasan yadda yake axabtuwa da rashin Imratu.
Dukkansu kan carpet din da Mami ta shimfida suka zazzauna, seda suka gaggaisa aka Kara jajantawa juna rashin Imratu da barin da Sulaim tayi kafin Baba yace
"Jabir bansan pain din mutuwar mata ba, amma nasan pain din rasa 'ya Dan a gidan aure kaine sirikina Imratu ce 'yata don haka dole a bawa kowa hakuri don munyi babban rashi, Allah ya jikanta ya bamu hakurin juriya, ya kyautata namu zuwan, Allah ya Raya mana babyn"
Baki daya suka amsa da Amin hawaye na bin kuncin Jabir wanda baisan har Yaushe ne zai fita daga kuncin rashin matarshi ba, yayinda Sulaim ke kuka sosae tana rikeda babyn wadda Ke baccinta hankali kwance.
"Babban yaya a kullum bana son nida Maminku mu zama mun saka idanu akan rayuwar gidanka amma halayen uwargidan ka Yana bani mamaki, kasan bata zo tayi mana ta'aziyya ba balle ta duba abokiyar zamanta dake jinya, Anya kuwa muna kan hanyar daidai? "
Maganar Baba tasa Junaid sunkuyar da kanshi kasa saboda azababben kunya da ta lullube shi baisan har wani Lokaci ne Subay'a zata shiryu ba don dazun da ya kirata ce mishi tayi Hajiya zata koma gidan Alhajinsu shi ne suke shirye shiryen tarewar he couldn't say a word Don takaici amma yanzun zuciyarshi ta Fara wasiwasin Anya zai iya jurewa halayen Subay'a da da yanzun akwai banbanci matuka.
"Baba........"
Katse shi Baba yayi da fadin
"Tuni nake maka akan gyaran gidanka to me ba dole Se tazo ba dubanta sunzo, Jabir wannan baiwar Allah wani hukunci ka yanke a kanta, she needs a mother"
Hawayen dake bin kuncinshi ya goge, Junaid ya dafa kafadarshi don ya samu karfin gwiwa hakan kuwa ya karfafa mishi gwiwa yace
"Munyi magana da Babanta yace na barta anan gurinmu Tunda shi baisan waye zai kula da ita ba, kayi mata huduba da Nafisa Sunan Mami haka Imratu tace sannan na Mika ta gaba daya hannun Sulaim ita ce uwarta! "
Idan nace kowa yaji dadin hukuncin Jabir understatement kenan, sosae Sulaim ta Kara kuka yayinda Junaid ke tayi mishi godiya, haka familyn nan suka yini Cikeda farin ciki da kuma alhini da yamma aka sallamesu suka koma gida nan Jabir ya tattaro komai na Nafisa Su'ad ya kawowa Sulaim inda ta dauki shawarwarin Nurses din don kula da yarinyar.
Washegarin Ranar sadakar bakwai ranar gidan ya koma daidai kowa ya koma bakin aikinshi har shi Jabir din wanda aka mishi transfer ya koma Kano hakan yasa yaji dadi don Yana tunanin komawa Delta ya rayu babu Imratu, Junaid da Sulaim Harda Subay'a wadda tazo ranar sadakar bakwai suka juya kano, babu alamar rashin jin dadin Abinda tayi don gani take ai babu dole ace se ta zo Tun ranar da akai rasuwar, Junaid kam baice mata komai ba se kallonta da yake Yana tunanin yadda zaiyi da ita.
Sulaim suka Fara saukewa wadda ta gaji sosae, Tana zuwa ta Kwantar da Su'ad yarinyar me hakuri Sede tasa yatsanta cikin baki tana tsotsa, seda tayi wanka sannan tazo tayi mata ta goya ta ta Fara gyaran gidan, tana kammalawa ta janyo kayan Su'ad ta shirya cikin abin kayanta wanda shima lokacin ta hada, wayarta ta bude nan text na gaisuwa da tambayar lafiya ba tazo makaranta ba Daga gurinsu khairi, zama tayi ta dinga bi tana replying har tazo kan Aimana anan ta kirata tana fada mata Abinda ya faru sosae Aimana mutuwar Imratu ta dake ta don sunyi sabo sosae lokacin bikin Sulaim din. Hakan yasa mutuwar ta bigeta sosae, suna kashewa ta kira Mami ta sanar mata ta iso nan ta Kara mata nasiha sosae sannan sukai sallama.
Junaid na isa gida kowannensu ya wuce dakinshi don yin wanka, zuciyarshi Sam babu dadi a yanzun kam dole ya aiwatar da abinda ke ranshi, fitowa yayi ya shirya cikin kanan kaya sannan ya fito parlour, Subay'a na fitowa ta shirya cikin bakin high waist skirt ta daura farar top akan blue din skirt din, kanta ta daura blue din scarf wanda ya kayatar da ita tayi kyau sosae kamar matashiyar budurwa, ga kamshi dake tashi Daga jikinta me sanyaya zuciya da nutsuwa. Tana fitowa Atika na kokarin jera abinci a dining gaisheta tayi cike da girmamawa tareda Yi mata gaisuwa don ita kanta rasuwar ta bige ta ba kadan ba, samasama ta amsa daidai shigowar su Muhammad wanda ta kaisu gidan Suhaila, hannunta tasa a bakinta alamun suyi shiru sannan ta bisu daidai ta manna musu peck a goshi tace
"Welcome home boys din Mimi? Ina Amma (Suhaila)"
A tare suka Fara bata labarin Kwana Dayan da sukai gidan Suhaila gaba daya ta tattara hankalinta Zuwa kansu tana ta murmushi a wannan lokacin taji wayar ta ta Fara ringing tana dagowa taga My Everything tasan nemanta yake amma a haka tayi picking tace
"Na'am "
"Ina jiranki a bedroom dina yanzun"
Bai jira amsarta ba yayi hanging wayar, tsaki tayi ta cigaba da sauraron 'ya'yanta, shikam Yana daki Ya zubawa kofar shigowa ido yaga ta inda zata shigo amma shiru har ya dauki waya zai sake kira se ya fasa ya janyo wayarshi ya fara surfing internet a haka har ya gama amma babu ko keyar Subay'a, me son kuka se aka jefashi da kashin awaki inaga Ya samu dalilin kukan, haka zuciyarshi ta Kara baci se huci kawai yake amma Junaid been Junaid a lokacin yayi calming kanshi se gashi ta shigo fuskarta a hade ita a dole batasan raini, zama tayi gefen kafafunshi tace
"Muna tareda su Muhammad Shiyasa ban zo ba"
Kallonta yayi a tsanake wanda har Seda ta zama uncomfortable sannan ya daga pillow din da yake kwance akai ya zaro wata farar takarda ya mika mata, Lokaci daya jikin Subay'a ya fara karkawa ta kasa dago hannun balle ta karba, kallonta yayi yace
"Ki karba mana!"
Ya fada Yana buga mata tsawa, hannunta, bakinta Kai ilahirin jikinta rawa yake tsabar yadda ta tsorata take cikin tsoro, wata tsawa ya daka mata batasan lokacinda tasa hannu ta karba paper ba Sede tuni hawaye ya wanke mata fuska ta kasa bude paper shikam yadda ranshi yake a matukar bace ce mata yayi
"You can't read right? Lemme help you "
Ya karba takardar ya bude tareda kafe ta da idanu kamar yadda take kallonshi cikin wani yanayi Wanda bai taba ganin Irinshi ba, he's sure da idanu na iya yin magana to tabbas nata zasuyi, all he saw was ban hakuri, roko da Dana sani amma a wannan lokacin bazasu taba tasiri cikin zuciyarshi a wannan lokacin sede next time
*NI MUHAMMAD JUNAID LUKMAN na saki Matata SUBAY'A YUNUS saki biyu bisa wasu dalilai*
Tamkar jini ya daina gudu a jikinta haka taji, take fuskarta tayi wani Irin Fari ,Mika mata takardar yayi tareda mikewa Don bar mata dakin saboda wani kuka da ta saki Don wannan shi ne last thing da ta taba tunanin Junaid zaiyi mata, da sauri ta sakko kasa tareda rike kafafunshi tace
"Papa na tuba nabi Allah na bika, Kada kayi min haka, kada ka wulakanta soyayyar mu, nasan I was never good amma give me another chance"
Baiso yin magana ba amma dole yayi saboda yaga she needs clarification akan abin
"Da Nayi hakuri lokacin ke daya ce amma yanzun bazan iya ba, ke idan banda butulu irinki har Imratu zata rasu kiki Zuwa gaisuwa ai ko banda ni taci albarkacin 'ya'yanki da ta rike miki, sannan har yanzun baki san me ake nufi da aure ba har yanxu Bakiyi hanakali ba, kije me tsautsayi ya dauka! "
Kuka sosae Subay'a take amma ko kallon inda take baiyi ba yayi wucewarshi Zuwa Dakinsu Ahmad inda ya tarar dasu suna cin pringles suna tsomawa cikin mayonnaise wadda aka hada da Venigar, suna ganinshi suka rungumeahi, shafa kansu yayi sannan ya zauna kan Mini cushion din dake aje a dakin yace
"Waye zaije gurin Ammiey"
In chorus sukace
"Ni! "
Kanshi ya gyada yace
"Kowa zaije"
Mikewa yayi ya hada musu kayan da ya zama basic yasa a katuwar trolley sannan yace suje su jirashi a mota, dakinshi ya koma har lokancin tana durkushe inda ya barta ko kallonta baiyi ba ya shige dressing room dinshi ya hado kayan da zai bukata ya fito lokacin hawaye kawai take don tasan ta makara lallai Junaid ya shammace ta don Bata taba kawowa zai iya rabuwa da ita ba se gashi ya bata unexpected blow!
Tana kallo ya fice ya barta a gurin ganin haka yasa taji karfi yazo mata ta fito a daki ta nufi nata, ta tsaya tsakiyar dakin tana tunano Irin halin da ta shiga wancan komawarta gidan amma me yasa tayi repeating same mistakes gashi ta kare a babu, sosae ta shiga kuka babu kakautawa haka ta shirya kayanta ta fito bayan ta daura Abaya saman kayan sede har lokancin kuka take sannan tayi clutching takardar sakin Tana jin yadda zuciyarta Ke zafi da radadi anma Lokaci ya kure.
Hajiya na Zaune Kan sofa gefenta Fannah ce wadda tazo Hutu, kanta babu dankwali Tana ta bawa Hajiya labari suka ji shigowar Subay'a, seda gaban hajiya ya fadi saboda ko ba'a fada ba tasan aure ya Kare, Fannah daki ta wuce ranta babu dadi, Hajiya ta ruko Subay'a wadda ta sake wani kukan tace
"Hajiya ya sakeni, na kashe auren na cuci kaina, na shiga uku! "
Wani wawan mari taji da Bayan hannu Wanda yasa ta gigice hatta Hajiya batasan Alhaji ya shigo ba se saukar Marin ne ya sanar mata da zuwanshi,
"Se kizo mu zauna Tunda haka kika zaba jaka Marar hankali, kuma Wallahi Keda farin ciki har abada "
Alhaji ya fada sannan ya fara kiran sauran yaranshi akan a Daren yau suje su kwashe kayanta kada su bar komai, hajiya ta dinga rokonshi akan ya bari a sasanta wani mugun kallo yayi mata yace
"Kin cuci Rayuwar yaranki haka zasui ta fitowa daya bayan daya, kuma Wallahi Subay'a se kinyi dana sanin kashe aurenki se na nuna miki ni ne ubanki! "
Kuka sosae take haka ya fice kuma kamar yadda ya fada haka aka kwaso kayanta kowannensu mamaki yake don sunyi tunanin a cikinsu babu Wanda zai kuma wannan saken se gashi Subay'a tayi. Sulma da tazo kasa magana tayi jin Abinda ya faru tace
"Dama nasan hankalinki bazai taba kwanciya ba har se kin kashe auren, congratulations Sister kinyi kokari you've succeeded se ki jira hukuncin Alhaji"
Sosae Subay'a Tun ba a je ko ina ba ta fara nadama wadda Lokaci ya riga ya wuce!
Sulaim na kitchen ta kammalla hada miyar kifi se farar shinkafa da ta dafa, gefe ta hada salad sannan ta samu guri a kitchen din ta kunce su'ad Daga bayanta ta Fara bata Madarar dake cikin feeding bottle din, Seda ta koshi kafin ta sabo ta a kafada ta shiga daki inda ta gyara kanta sosae kamar tasan mijinta na hanya, pencil skirt tasa Wanda ya wuce gwiwa amma bai Kai idon sawunta ba baki me wasu glitters da suke ta haskawa, tasa top gold wanda kamata kadan sannan ta bude wani dan kit ta ciro chain na gold da dan karamin pendant ta daura a wayanta tasa dan kunnenshi tareda shafa maroon paint lip, kafin wani Lokaci tayi kyau kamar Mamie water.... Beautiful Oyinye. Bakar ribbon tasa ta hade kanta in a Bun sannan tasa hula baka da golden ribbon a gaban, turarruka masu sanyi tasa ta dakko karamin Cot din Su'ad ta kaita parlo ta kwantar sannan ta dakko system dinta ta Fara karatu wasu slides da Aimana ta turo mata na lecture din da tayi missing.
Sallamarsu Muhammad yasa ta aje System din gefenta tareda nufarsu ta rungumesu tana jin yadda tayi kewarsu har cikin zuciyar ta, ganin zasu fara ihu yasa tace
"Kui shiru kuzo Ku gani"
Gabaki daya sukai tsit suka biyo bayanta har inda Cot din Su'ad yake tace
"Ga kanwarku nan "
Gaba daya suka tsira mata idanu suka Fara murna hakan yasa ta Fara motsi Sulaim ta matsar dasu don kada su tashi, tana dagowa ta hangeshi yana tsaye ya harde hannayensa Kan kirjinsa ya zuba mata ido, murmushi tayi tareda yi mishi wink, kanshi ya kawar ya bude mata hannayenshi alamar ta rungumeshi, kanta ta girgixa Tana zumbura Baki, shigowa yayi ya Daga ta sama hakan yasa ta kankameshi tana dariya Wanda ya kwantar mishi da hankali tareda saukar masa da nutsuwa, juyawa tayi taga Ashe yaran sun shige ciki, tare suka ci abinci yana ta zolayarta da tsokana tana dariya, dake bai shigo da kayan ba yasa bata kawo komai a ranta ba tayi tunanin yaran ya kawo mata Tunda sun jima basu hadu ba, amma ga mamakinta har dare bai ko Yi alamun tafiya ba, wanka tayi ta gyara su'ad tasa Nighties dinta ta kwantar da ita sannan ta fito Yana zaune Yana kallon news ta zauna gefenshi tareda fadin
"Zamu kulle gida fa!"
Juyowa yayi yace
"Kora kuma Dove, anan zamu Kwana ga yaranki sun Fara bacci"
Idanu ta tsura mishi kamar tana son karanto wani abu tace
"Be serious Heartthrob bacci nake ji"
Dariya ya danyi tareda gyara zamanshi yace
"I'm sorry Amma ina sake neman alfarma akan ki rike su Muhammad a gurinki har Zuwa lokacinda ni bansani ba, nasan Kinyi kankanta da wannan burden din amma inason ki daure Kimin wannan taemakon"
Kanta ta girgixa tace
"I can't gaskiya su koma gurin Miminsu "
Idonshi ya zaro Don wannan ne Karo na farko da Sulaim tayi mishi musu hakan yasa yace
"Dove ni ne fa"
Kanta ta gyada tace
"Me yasa zaka yanke hukunci kana cikin fushi, why will you do that, nace maka kayi hakuri ka zauna da ita ko albarkacin ya'yanta amma ka nuna min banda mukamin baka shawara, then babu Wanda zan rike I'm sorry!"
Shiru yayi saboda tsabar mamakin furucin Sulaim akan bazata riskesu ba, Daga karshe tashi tayi ta wuce dakinta bawai don komai ta fadi hakan ba sedan tana son su Muhammad su tashi suna daraja mahaifinsu amma inhar suka tashi babu uwa lallai zasu zargeahi akan wulakanta babarsu.
Da kanshi ya kai yaran suka kwanta sannan ya biyo ta daki ya samu tana kwance gefen yarta, hannunsa yasa ya dauke Su'ad sannan ya matso da uwar wadda ta Fara kokarin kwacewa ita a dole fushi take dashi Seda ta gama ture turenta kafin ya fara zuba mata ruwan kisses kamar zai haukata ta daga karshe ya kashe ta da soyayyarshi me tsada, Seda suka nutsu sukai wanka sannan ya kwanta kan cinyarta tana wasa da gashinshi tareda kallon Baby Su'ad dake baccinta hankali kwance
"Nayi tunanin a yadda kika sanni bazaki zargeni da rashin adalci ba, Sulaim ya zanyi this is the last thing da zan iya dauka Daga gurin Subay'a na bata dukkan chances da take bukata amma har cemin tayi idan na gadama na saketa, to na nuna mata sakinta is the simplest thing da zan iya nidai kawai I need your support plz Kada ki barni no matter the hardship kinji"
Sunkuyowa tayi ta manna mishi peck sannan tace
"Allah ya daidaita komai and I will forever remain yours till death do us apart, I'm sorry for dazun"
Mikewa yayi ya hade bakinsu guri daya........... Tired I need a break...... Gobe Inshaaa Allah I'll post the final episode fadan karshe kenan!
Shatuuu ♥️
[9/13, 6:29 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU*
60
_FINAL CHAPPY_
✍️Shatuuu♥️
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
#⃣Shatuuu095@wattpad
*I've seen the critics akan sakin Subay'a, of course Subay'a need to go she need to learn her lesson, Kada Ku manta tayi amfani da son da Junaid ke mata take iskancinta amma ga page ne se ku gani ko hukuncin yayi muku. This mark the end of MACE A YAU I hope you guys liked it, ina fatan zaku cire lessons din ciki kui amfani dasu kubar sauran. I love each and every person who was, is and will be with me through this journey.... May Allah shower his endless blessings upon you.....nagode sosae Allah ya bar zumunci da kauna.... One Love💕*
_GODIYA TA MUSSAMAN_
My wattpad follwers
SHATUUU's