Showing 117001 words to 120000 words out of 131263 words

Chapter 40 - MACE A YAU Document from Sulaim .txt

24 Nov 2024

4837

ba fa, Ehen yau class din Dr. Ammar kuke dashi ko?"


Kanta ta gyada tana maida hankalinta Kan gyara mishi link din da kuma collar rigar tashi,


"He's not coming, so ina ganin ba se Kinje ba"


Wani karamin ihu ta saki tana fadin


"At least someone can rest"


Bakinshi ya tabe yana Mika mata wayarshi yace


"Lazy fellow! "


Kafadarta tayi shrugging Irin Kara fada dinnan, sannan suka fito Zuwa parlourn inda ya zauna suma su Ahmad da Muhammad an shiryasu cikin uniform. Seda ta gama shirya breakfast din kan dining mat dake ba kowanne Lokaci bane suke ci kan table ba, suna kamalla breakfast din suka Mike kowannensu na kokarin fita inda ya dace, kallonta yayi bayan ta rakasu bakin mota yace


"Dove Anjima zaki fitan? "


Kanta ta gyada tace


"Eh Inshaaa Allah Zamu fita tareda su Aimana "


Kanshi ya gyada yace


"Na bar miki sako kan gado, Allah ya kiyaye hanya"


Godiya tayi mishi yana harar ta Daga haka sukai sallama ya wuce ita kuma ta koma ciki ta Fara gyara inda ya dace da taemakon Nanny su Muhammad. Parlor ta dawo ta zauna Tana kurbar tea tareda kurawa wani frame dake kan center table din ido, hoto ne Daddynta da Mummynta, Junaid da ita, idan zata iya tunawa wannan hoton anyi shi lokacinda ta gama primary ne akai mata graduation party, tana ta dariya dukkan wushiryar ta siririya me kyau ta bayyana haka dimples dinta masu matukar daukar hankali sun lotsa, hannunta cikin na Junaid wanda yake dariya da sauran iyayensu, a hankali ta kai hannunta ta dauki hoton wasu abubuwa na tsirga mata, hakika tayi kewar wannan fuskokin da ace suna da rai ko wanne irin farin ciki zasu kasance ganin sun auri junansu. Allah kadai ya san Irin murnar da zasui, Allah dai ya jikansu ya rahmushe su yasa sun huta, Tana fatan su kasance tare a Aljannah don ko bata fada ba tana kewarsu dukda bata rasa komai ba amma iyaye daban suke.


Wajen karfe Sha biyu ta kammalla abincin Rana ta sake wanka ta shirya cikin Farar Abaya me bakaken stones tayi mata kyau kamar me, a ranta tana ta mitar rashin zuwansu Khairi tare da tunanin Irin rashin mutuncin da zatayi musu. Ai bata gama wannan tunanin ba taji sallamar Aimana da Khairi, hade fuska tayi yayinda su ma suka Bata rai suka zazzauna, se kuma Aimana ta Mike ta debo musu ruwa da lemu daga fridge wanda ke aje a corridor da zai kaika kitchen, Tana zama Sulaim tace


"Lallai Bakuda mutunci har wani ku bata min Lokaci sannan kuzo Ku fini fushi"


Aimana ta zabga mata harara Tana sauke gwangwanin Shani din da ta daddaka saboda rana da suka kwaso tace


"Babbar Marar mutunci ai Kece, har wani yau Dr Ammar ba zai zo ba mijinki ya fada miki kika barmu rana ta Kare a kanmu"


"Duba wayoyinku Allah yana fadamin na muku text"


Duka suka dakko aikuwa ga text dinta tun safe, borin kunya yasa aka Fara hira ta Mike don zubo musu abinci Khairi tace


"Karki fara, yau gidan Amarya Khulthum Zamu ci lunch, Kede tashi kawai mu tafi"


Haka kuwa akai babu jimawa suka yiwa Lodge road tsinke, da taemakon text din address din Khulthum da tayiwa Sulaim, a bakin gate Sulaim tayi parking Baki daya suka fito suna karewa gate din kallo, shi kanshi abin kallo ne, seda akai formalities kafin suka samu suka shiga inda kowacce ta jinjina alamarin Khulthum, Aimana da bata iya shiru tace


"Ikon Allah! Khulthum ta auri me kudi ina taya ta murnar cikar buri "


Duka suka jinjina abin lokacinda kafafunsu suka taka parlon, ya hadu karshe kamar wani palace, babu kowa se karar plasma da AC dake ta aiki babu kakautawa, Khairi ta ciro wayarta tayi dialing number Khulthum din bugu daya ta dauka tamkar wadda take bacci tacr


"Inata jiranku....."


Katse ta tayi da fadin


"Muna parlor to uwar complaint"


Ta manta wani ciwo da kasanta da bayanta yake mata tayi saurin Durowa daga gado wanda taji wani sharp pain ya soketa se kuma abu yana bin kafarta, da sauri ta daga rigar dake jikinta, wani muguwar faduwar gaba ta ziyarce ta ganin Kashi ne ya biyo kafarta, hannunta na hagu tasa ta lakato tare da kaiwa hancinta, wani wari taji wanda ya tabbatar mata Kashin ne, tayi shiru Tana tunanin abinda yake faruwa da rayuwar ta, toilet ta shige cikin sauri ta gyara jikinta tareda sake feshe jikinta da turarruka sanann ta fito jikinta kamar an zare mata laka haka ta fito, ganinsu yasa ta danji sanyi tareda tuno da, school days dinsu, lokutan fada da suke itada Aimana, kurara Maza itada Khairi, secrecy dinsu itada Sulaim, Gasu nan duk tsiyar da tayi musu sun amsa gayyatar ta sunxo gareta basui fushi ba. Idanunta suka ciciko da kwalla tana tunano yadda Aimana ta dinga hanata auren me kudi, yadda Sulaim ta dinga mata fada akan yadda take treating Ashir, Gashinan ita ke kuka Su they've moved on already, hawaye ya sakko mata duk yadda tayi kokarin hana hakan amma ta gagara, ta tuna yadda Khairi ta dinga binta akan ta dawo makaranta tayi kunnen uwar shegu dasu, gashi tun ba'a je ko ina ba komai ya lalace, Abinda take neman ta samu amma babu amfani.


Gaba daya jikinsu yayi mugun sanyin ganin yadda Ummu_Khulthum ta zama, yadda ta lalace ta kare musamman ganin yadda hawaye Ke yi mata zarya a kumatunta, duk se sukai shiru kowa da Abinda yake tunani, Seda tayi kuka me isarta wanda yake me ciwo da karawa zuciyarta zugi a yanzun kam bata da wani buri na rayuwa komai ya fitar mata akanta bata jin akwai Abinda yake burgeta kuma, to meye zai burgeta, me zaayi da mata'ul hayat... Kyalekyalen rayuwa? Basuda amfani, kuma bahaushe yayi gaskiya da yace son zuciya bacinta.


Sulaim ce ta Fara bude bakinta da yayi mata nauyi tace


"Khulthum Kiyi hakuri ki bar kukan haka, komai da yake faruwa da dan Adam Kaddara ce.... Kiyi hakuri kilan ribar ki na gaba"


Hawayenta ta share tace


"Kayya Sister ina wata riba? Babu da ne naci riba yanzun gashi ina girbar abinda na shuka. Kaddara kuma da kike magana na yadda komai na rayuwa MUQQADARI NE daga Allah, amma everything in life is predestined.... Bai gama zama kaddarar ba Shiyasa Allah da manzonshi sukace kayi addu'a it can change it, ni meye banyi ba, meye baku fada min ba naki yadda nace Se na auri me kudi, gashi na samu na aura here I'm and only God knows where I'm leading my life to"


Se kuka ya kara kwace mata hakan ya kara saka su cikin tashin hankali gaba daya suka shiga rarrashinta har tayi shiru ta daina kukan kuma babu Wanda ya tambayeta halin da take ciki, a haka ta wanko fuskarta suka hadu suka ci abinci aka tuna baya. Tunda Sulaim tace bata son kamshin ketchup suka saka ta a gaba wai ta harbu hakan yasa Khulthum ta ware ana ta hira inda take jin yanzun suna level 3 second semester tayi kukan zuciya yadda ta rusa rayuwarta da hannunta.


Seda sukai La'asar sannan suka shirin tafiya nan ta Kara jin tamkar ta bisu Amma babu Hali Don Tana tunanin tabbas akwai abinda Musbahu yayi mata, ya cuceta amma tana ganin babban azzalumi shi ne Kabir wanda yayi hooking dinsu kuma Tunda aka kawo ta gidan Bata kuma ganinshi ba se wancan satin yazo kamar an jefo shi lokacin fitar Musbahu kenan daga dakinta ta gama azzabtuwa Don yanxun maza sun fita kan Musbahu ya rage Hulda dasu sosae se kan Khulthum kuma har lokancin Anal sex din yake, kullum da Ciwon baya da kasa take Kwana, kullum dare Tana jin tamkar ba zata kai Washegari ba, ta tsani rayuwar da Abinda Ke cikinta amma ya zatayi haka zatai managing Tunda ita ta jawa kanta.


Kuka sosae ta dinga yiwa Kabir Tana fadin ya cuceta shi kanshi yayi mamakin ganin Khulthum yadda ta rame tamkar ana tsotse ta, ya dinga bata hakuri shi Wallahi baisan hakan ce zata kasance ba amma zai San yadda zaayi da haka suka rabu.


Har a mota babu Wanda ya bude Baki yayi maganar halinda Khulthum ke ciki bawai don sun manta ba sedan babu abin fadar ma, kome zasu fada bayada amfani. Jiki a sanyaye Sulaim ta karasa gida, babu kowa yaran sun tafi islamiyya shi kuma oga ya fada mata se dare zai shigo. Har maghariba tana zaune yaran suna ta tambayarta me yake damunta amma ta kasa cewa komai a haka a daddafe ta yi girkin dare, ta tsalo wanka ta shirya cikin cotton lace Red da farin zare da akai designing manyan flowers a jiki, tayi kyau babu karya ta dawo parlour ta zauna tareda kurawa agogo ido, wayarta dake hannun Muhammad ta Fara ringing hakan yasa ya miko mata, wani yanayi Marar dadi ta tsinci kanta a ciki saboda ganin sunan Khulthum na yawo a kan screen din, har zuciyarta take jin tausayin ta don fuskarta kadai zai fada maka Bata da nutsuwa.


"Kunje gida lapiya? Nagode Allah ya bar zumunci "


Murmushi Sulaim tayi tacr


"Lapiya lau babu komai ai"


Se kuma sukai shiru, Khulthum tana tunanin daga inda zata Fara haka ta daure cikin sarkakkiyar murya ta fayyacewa Sulaim halin da take ciki, tamkar ruwa ya cinye ta haka Sulaim tayi Bayan Khulthum tayi shiru, ta rasa me zatace mata, Wacce shawara zata bata a karshe nasiha kawai tayi mata sannan ta tuna mata laifufukan da tayiwa Mama ya kamata ta gyara, ta nemi gafarar wanda ta batawa. sannan tayi addu'a Allah, ta nema gurin ubangiji shi ka
dai kadai zai gyara Musbahu ba mutum ba!






Shatuuu ♥️[9/7, 6:28 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU*
56


✍️Shatuuu♥️


🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION


#⃣Shatuuu095@wattpad


Washegari aka tashi da kwalleliyar rana kasancewar a watan April muke ga kuma ranar juma'a ce don haka rana ta haska wanda zakai tunanin Irin sha biyun ranar nan ne, a firgice Sulaim ta Mike Daga kan couch din data kwanta bayan tayi sallar asuba bacci yayi gaba da ita, mikewa tayi ta zauna ta daga kanta zuwa kallon agogon dake manne a bangon parlour, ajiyar zuciya ta sauke ganin shida da yan Mintina, kitchen ta wuce ta jona toaster tareda farke sardine ta hada da Attaruhu, albasa da seasonings tasa spoon ta farfasa sannan ta zuzzuba a sliced bread tayi toasting ta jera a plate, custard ta dama ta hada Tea black kawai me kayan kamshi sannan ta fito dasu ta Dora Kan dining Table din sannan ta nufi dakinshi, yana zaune kan sofa yana kallon news, gefenshi ta zauna tareda kwantar da kanta akan kafadar shi tace


"Morning heartthrob"


"Morning Dove, Kinada son jiki dama Cat nake ce miki"


Murmushi tayi tareda kokarin dauke kanta daga kafadarshi amma ya hana hakan,


"Munada lecture fa ko baza kije ba? "


Fuskarta ta bata Tace


"Bacci nake ji kar naje nayi ka Kore ni"


Dariya yayi yace


"Wannan dole ne, tashi mu shirya yau bazan koreki ba"


Haka suka shiga wanka sannan suka shirya akai breakfast a daddafe saboda makara, tare suka fito dukkansu har yaran seda suka ajesu kafin suka wuce makaranta.


Misalin karfe daya na Rana Subay'a ta dauki handbag dinta tareda tattare komai nata tayiwa makotanta sallama, gaba daya ilahirin jikinta a tsorace take saboda wannan kiran gaggawar da Alhajinsu yayi mata dole haka ta je gurin manager yayi excusing dinta don zazzabi take fama dashi.


Tana isa kofar gidan taji wata mummunar faduwar gaba saboda ganin motar Junaid yayi parking a kofar gidan, hawaye masu zafi suka shiga sakko mata don tasan takardar sakinta ya kawo mata, ta dade cikin motar tana kuka sosae ko ta samu zafin da zuciyar ta take ya ragu, kuka tayi har fuskarta tayi ja haka idanunta, tayi tunanin kukan zai rage wasu abubuwan amma ko daya se kara tayar mata da hankali da yayi, ita a yanzun duk ta fahimci Abinda Sulma ke fada mata cewar Allah idan yace kayi abu to idan ka kiyi se ya saka dole ka yishi ko baka so Bayan ka gama shan wahala, itakam gadhi ta gani akan kanta.


Babu yadda ta iya haka ta fito jikinta a sanyaye ta shigo parlon part din Hajiya anan ta ta tarar Samina na kwance tana kallo yayinda take watsa popcorn a bakinta. Gefenta ta samu ta zauna Tana fadin


"Samina Alhaji Yana ina? "


Dagowa tayi tace


"Yana part din Amaryarshi mana"


Daga haka ta Mike zuwa daki ta canza kaya kafin ta nufi part din Asiya, Tun Daga kofa take jin fadan Alhaji Yana fadin


"Dan ubanta! Ai da sakinta kayi idan yaso ta Kara hankali ai"


Wata ajiyar zuciya ta sauke ta yi sallama sannan ta saka kai ta shiga, idanunshi ya dago Yana kallanta, Yana kallon yadda matarshi ta koma, wani sanyi yake gani a tattare da ita, itama kallonshi tayi jikinta ya kara sanyi don wani kyau Taga yayi, ga nutswa a tattare dashi lokaci guda she felt humiliated saboda tasan her presence is same as her absence, ta tuna ranar da suka maida Suhaila gidanta yadda babansu Fannah ya rame, gidan gaba daya ya lalace saboda Suhaila Bata nan Amma kalli yadda mijinta ya koma bata tunanin ta taba ganin kwanciyar hankali a kwayar idanunshi kamar yadda ta gani a yanzun, hawaye masu dumi fresh suka zubo mata.


Gefe ta zauna kanta a kasa tana jin yadda Alhaji ke sirfa mata masifa Har yana fadin duk Abinda tayi ya saketa itakam kuka kawai take kasan zuciyarta wani sanyi taji don tasan mijinta ya dawo gareta ne. Alhaji na fita kukanta ya tsananta wanda yake damun Junaid




🎶_Baby give me one more chance to be the one to hold your hands, maybe we could learn to love again.... Yeah yeah_


hakan yasa ya Mike zuwa inda take Zaune ya tsugunna akan gwiwarshi ya dago fuskarta wadda tayi kaca kaca da hawaye, da sauri ta Fada jikinshi ta rungumeshi tamkar zaa kwace mata shi,


🎤_I don't deserve it, I know I don't deserve it but stay with me a minute, I swear I'll make it worth it, I failed you, feel like a failure I know that she gave you everything! One last time I need to be the one to take you home, one more time I need to be the one to hold your hands_


Seda ta nutsu kafin ta dago Daga jikinshi kanta a kasa saboda masifaffiyar kunyarshi da take ji. Zama ya gyara tare da kallonta a tsanake kafin yace


"Duk lokacinda a aure aka Fara yaji, ko kuma ace kije gidanku to Abu na gaba da zai biyo baya saki ne...... "


Da sauri ta dago idonta ta kalleshi don tunaninta lallashinta zaiyi, ko gezau baiyi ba se ya cigaba da fadin


".....Saboda tuntuni darajar da dignity sun Fara zama weak, bazan tuna miki abubuwan da suka faru ba don they're already in the past, Amma ina son zanyi miki albishir cewar inada mata yanzun wadda bata taba sabamin ba, she pampered me kamar jariri, tana girmama ni ta daukeni shugaba kuma Bata taba ketare umarnin da na bata, Bata min musu tana da juriyah......and many more ke kuma hakan sune lapses dinki kinga duk Abinda nake nema na samu Amma ina daraja ki saboda abu guda biyu na farko saboda ina sonki na aureki, na biyu 'ya'yan mu da muka Haifa. Inason idan kin koma ki gyara mistakes dinki Amma idan hakan yaki komai zai iya faruwa"


"Batun aurena da Sulaim ina son ki sawa zuciyarki ina sonta ina kaunarta shi yasa na aureta, ban aureta don na huce haushi ba, ina son kisan Sulaim din wata aba ce me daraja cikin rayuwarta, Karki ce na miki wulakanci ko daya Kema ina sonki Amma ina son ki daraja kanki, ki martaba kanki sannan ki nuna mata Kece uwargidan kuma ran gidan idan ba haka ba kina zaune zaki zama yar kallo. After Asr zan dawo mu tafi"


Mikewa yayi ya fice yana jin wani bakon yanayi a tattareda shi, yasan Za'a ga rashin kyakyawar shi Amma hakane kadai zaisa Subay'a ta dawo hankalinta.


Sulaim ta gama lectures tana ta jiran Junaid dan taje office ance ya fita ga wayarshi bata shiga, hostel ta tafi wajen Khairi wadda take gyaran Kwana, sunayi suna hira har bacci ya dauke Sulaim. Se wajen biyu ta farka tayi sallah sannan taga missed call din Junaid, cikin hanzari tayi returning call din


"Kina ina ne? "


"Ina hostel gurin Khairi "


"On my way"


Kashe wayar yayi Itama ta Mike Tana kwallawa Khairi kira, tana shigowa tace


"Yaxo zan tafi"


Harararta Khairi tayi tace


"Custard din fa "


"Hada zan sha a mota"


Aikuwa ta dakko madara ta hada mata ta rufe cikin wani mug me murfi yayi kyau sannan suka fito Khairi na ta tsokanar ta. Bata kulata ba don Duk hankalinta yana kan mijinta, suna zuwa suka gaisa ta Mika mata handbag dinta da cup din sannan sukai sallama, Yana fara driving ta Fara shan custard dinta, kallonta yayi yace


"Wai ni baby akwai sirri ne a shan custard kullum se Kinsha ko sanmin bakya yi, kin koyi rowa ma "


"Kai Heartthrob har rowa kuma, ni din ko?"


Dariya yayi yace


"Wasa nake miki 'Yar albarka my honey"


Spoon daya tasa mishi a baki ya amshe haka har suka cigaba da tafiya yana mata hira, suna zuwa gida ta wuce kitchen Don tasan kowa yunwa yake ji, biyo ta yayi lokacin tana kwashe macaroni and cheese din data hada, kwantar da kanshi yayi a jikinta, tureshi tayi yana binta har ta hakura, cikin nitsuwa yace


"Dove anjima Mimin su Ahmad zata dawo, ina fatan zaki kasance kamar yadda kike, ina fatan zaki goya min baya, ki cigaba da supporting dina Kina min addu'a na samu Nayi adalci a gareku"


Shi kanshi ya sani kuma he felt yadda jikinta ya saki yayi sanyi Amma a haka ta daure saboda wani kishin shi dake ratsa ta tace


"I'll always

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login