Showing 90001 words to 93000 words out of 131263 words
zuwa school sukai sallama da Jawad ta nufi class, inda suka saba zama taje ta zauna babu jimawa Aimana da Khairi suka iso kamar wanda suke Daga guri daya. Cikeda farin ciki suka zauna suka sata a tsakiya. Khairi ta dubeta tace
Sulaim wannan kyau haka, ga kamshin amare da kike fitarwa.
Aimana tayi saurin fadin
Wallahi, kinga sati biyu kawai ta zama very matured se kyalli take.
Gyara zamanta tayi tana jin ta inda zata Fara su fahimce ta, cikin nitsuwa tace
Kuyi hakuri nasan kuna ta nemana a waya baku sameni ba, Wallahi Yaya yayi accident I some how fainted..... Idanu suka zaro.... To muka taho Kano na bar wayata a Kaduna. Tohm kuma yau Kwana biu aka daura mana aure ni dashi.
Maimakon ganin bacin rai saboda bata fada musu ba, se gani tayi suna ihun murna har hankulan mutanen class ya fara dawowa kansu, Salma kwalam, Hidaya da Halimatou suka zo jin kwakwafi Aimana ta Mika musu invitation da Sulaim ta karbo hannun Junaid ashe shi ne sakon Amma din, su Mami sun yanke zaayi biki in a week time don ta tare basu son a ja abin, event din Kamu ne se dinner da friends din Junaid suka hada mishi anan Kano.
Aimana ce ta dinga raba invitation card Khairi tana harhada yadda abin zai kasance da yadda zasu fitarda anko a samu a sati daya. Ranar gaba daya haka ta kare sun manta da wata Khulthum Seda Sulaim tace da Aimana
Bani Aron Wayarki na kira Khulthum na fada mata.
Nan Khairi ta Fara dariya tana bawa Sulaim yadda Aimana sukai da Khulthum, Aimana Cikeda bacin rai tace
Ki bar shegiya kawai, Allah naji haushi Allah ya hadani da ita.
Sulaim tace
A'a ai ya wuce ki rabu da ita kawai, bani number idan naje na Kira da wayar Friend (Jawad).
Rubuta mata akai jikin paper sannan kowa ta kama hanyarta, ta dan jima tana jiran Friend amma bai zo ba gashi bata da waya kuma, batayi azancin dakko kudi ba. Mikewa tayi ta nufi office din Ridwan daidai sun fito shida Sagay, da Mai Sogha da Dr Halliru, gaishesu tayi Ridwan Yana musu bayanin ita ce amaryar Junaid, gaba daya sukai mata Allah sanya alkhairi suka basu guri, anan ta samu ta fada mishi Abinda Ke faruwa,
Muje na kaiki dama can zanje.
Godiya tayi mishi tabi bayanshi suka tafi a motarshi, maimakon Asibiti se suka nufi gida, kamar zatayi magana se ta kyaleshi har suka iso yayi parking yace
Ki fadawa Junaid ina waje ina jiranshi.
Kanta ta gyada ta sake godiya sannan ta shiga ciki, Tunda ta bar gidan ranar jumaa da daddare bata kuma dawawa ba se yau, cikin nitsuwa ta Koda Yaushe ta shiga gidan daidai Jawad zai fito Yana ganinta ya fara fadin
Dan Allah Friend Kiyi hakuri Wallahi Mami ta aikeni.
Hararashi tayi tace
Ba ruwana da Kai.
Dariya yayi yace
Se Amaryar babban yaya!
Dariyar ta Kara saki tayi ciki tana jin farin ciki sosae a ranta. Koda ta shiga da Muhammad ta Fara cin Karo yana kuka yana kiran sunanta, take taji gabanta ya fadi tuna cewar Ashe akwai uwarsu fa, ita Wallahi ta manta ma gaba daya ta manta da rayuwar wata Subay'a don idan Suna tare manta wa take da wata Subay'a.
Tsugunnawa tayi ta daukeshi tana lallashi suka shigo ciki, Mami ce a Zaune Kan kujera se Junaid a gefenta yana nuna mata abu cikin wayarta, sallamar ta yasa baki daya suka dago idonsu suna kallonta, zama tayi akan carpet tace
Mami ina yini?
Lapiya lau Sulaimi ya makaranta?
Alhamdulillah.
Ta fada sannan ta dubi Junaid wanda ke kallonta tace
Yaya ina yini?
Hararar ta yayi, sannan ya amsa, kanta ta dauke don ta fahimci Abinda yake nufi tace
Yaya Ridwan Yana waje Yana jiranka.
Da sauri ya mike yayiwa Mami sallama ya fice, kallon Mami tayi tace
Mami zanyi wanka.
Jeki se kin fito.
Kwanaki haka suka cigaba da ja sosae ana ta shirye shiryen gagarumin bikin Ya'yan gata, ranar alhamis suka wuce kaduna gaba dayansu, sun tarar gidan ya cika da mutane, Tunda sukaje Mami ta dakko su Aliyah suka shiga Kara kimtsa Amarya, ranar jumaa Aimana, Khairi, Khulthum wadda ta shammace su Taxo don basu taba tunanin zata zo ba, don da Sulaim ta fada mata cewa tayi itama shirin nata bikin take. Ranar Friday akai Kamu na idon duniya wanda ya amshi sunanshi kamu, Amarya tayi kyau kamar babu gobe, yan class dinsu Hidaya sani Lawan, Halima Ahmad Ya'u da Salma Hassan Kwalam suka halarta, Yan SHATUUU's KINGDOM kamar kasa sunyi kyau kuma sun kayata gurin haka mutanen Maman mama novels da Kainuwa Fans group duka sun bayyana cikin ankonsu me kyau.
Dab da zaa gama komai Junaid yazo da tashi tawagar, akai pictures sannan aka kamasu tare. Washegari ya tashi Saturday ranar Mami tayi yini, gidan ya cika sosae anci an sha anyi biki.
Ranar Sunday da safe Mami da Baba, Junaid da Sulaim suna zaune Baba yayi musu nasiha sosae akan aure da kuma hakkokin junansu, Mami tayi nata sannan aka rufe taro da addu'a, da yamma suka isa Kano inda ta tare dakin Junaid akan zai karasa ginin shi, ita Sulaim batayi kuka ba saboda bataga dalilin kuka ba tunda jinta take tamkar taje yawo kaduna ne ta dawo kano.
Karfe Tara aka fara kayattaciyar dinner wadda ta samu dubban mutane suka halarta, sunyi kyau Sulaim da Junaid kafin wani Lokaci hotunansu ya baza media.
Shatuu ♥️
[9/2, 9:38 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU*
42
✍️Shatuuu♥️
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
#⃣Shatuuu095@wattpad
_Assalamu alaikum warahmatullah wa barakatuhu gorgeous damsels! Barka da sallah! Allah ya maimaita mana many years to come. Ga barka da sallah na hope you guys will like it?_
Hannunshi cikin nata suka iso kofar parlon, takan tuna lokacin da suke dawowa daga school, kaduna a matsayin cousins to yau gashi ta dawo a matsayin mata, matar aure kuma matarshi. Wani sanyi taji Yana ratsa mata jiki har ya kai hannu ya bude parlon, shi dinne dai, yasha gyara an canza kujeru da carpets din. Saman kujera suka zauna a gajiye saboda yadda suka gaji. Idanunta ta daga ta dubi agogon parlon, karfe goma Harda rabi kallonshi tayi taga ya zuba mata dukkan idanunshi, sunkuyar da kanta tayi taji wani nauyin shi ya kamata. Hannunta da har lokancin ke cikin nashi ya matsa yace
Bacci?
Kanta ta gyada, Mikar da ita tsaye yayi, suka nufi parlonshi, wani niimantaccen kamshi ne gauraye da sanyi suka dokesu, komai na ciki an canza zuwa sababbi, parlon yayi kyau sosae bedroom dinshi ya nufa da ita har lokancin bai sake mata hannun nata ba. Shima komai an canza yayi kyau, Daga can lungu ta hango jerin trollies Kala wajen hudu da yake Wannan ne Karo na biyu da ta taba shigowa bedroom dinsa.
Kallonta yayi yace
Jeki wanka kinji?
Kanta ta gyada ta Mike ta nufi toilet ya dakatar da ita ta hanyar fadin
Da kayan zaki shiga? Bazaki cire ba?
Bakinta ta turo tace
Mhmmm.
Kanshi ya shafa saboda yadda yake samun mugun effect a jikinshi duk lokacinda ta turo wannan karamin bakin nata, ji yake tamkar an jona mishi electric current cikin jininshi. Juyawa yayi ya fita don ya manta ya Bar abinci cikin mota. Tunda ta shiga take bin ko ina da kallo, toilet din very neat and tidy, komai in place. Kayan ta cire cikin dabara don karsu jike, ajesu tayi a tsanake ta Fara wanka, seda ta kammalla sannan ta dauro Alwala ta fito Tana jin tamkar tafi kowacce mace sa'a.
Bathrobe ne jikinta se towel ta rufo saman kanta, yana shigowa tana fitowa, kallonta yayi yaga ta Bata rai yasan kada yayi mata magana ne hakan yasa ya shareta ya fara cire kayan jikinshi, seda ya kammalla sannan ya shige toilet, zama tayi ta Fara tunanin abinda zata saka a jikinta, nan ba dakinta bane tasan bata aje komai ba. Mikewa tayi ta bude kofa ta fice Zuwa Tsohon dakinta, Tana tura dakin taji ya bude Sede babu komai nata, gadaje ne biyu blue da coffee se wardrobes biyu, shelf da study tables babu tantama na Ahmad ne da Muhammad, don gasu a kwance abinsu suna shan bacci, Atika a kwance kan karamar katifa. Ciki ta shiga ta tsugunna kan Muhammad tayi kissing dinsu sanann ta juya bayan ta kashe wutar dakin a ranta tana tunanin ina ya kai mata kayanta? A parlor ta tarar dashi ya shimfida praying carpet daya a gaba daya a baya da hijab saman ta. Tana shigowa ya bita da kallo har ta zauna baice mata komai ba seda tace
Kayana?
Tashi yayi ya shige bedroom din ita kuma tabi bayanshi har gaban trollies din yace
Ga lefenki I hope you will like them,
Ya bude wardrobe dake can karshe jikin bango se ga kayanta sun bayyana, ya cigaba da fadin
Is that all.
Murmushi kan fuskarta ta gyada Kai. Seda ta saka sleeping dress sukai sallah kafin brain din Sulaim ta dawo aiki, Aure fa tayi kuma idan zata tuna ba ana having affairs ba, gabanta taji yayi mummunan faduwa har ta furzo yoghurt din da ta Riga ta kai baki sakamaakon fara cin kaza da suka Fara, da sauri Junaid ya matso kusa da ita tare da kokarin kama hannunta Amma ta matsa baya idanunta taf da hawaye tace
A'a!
Kallonta yayi cikin rashin fahimtar Abinda take fada yace
Menene
Kanta ta hada cikin cinyoyinta ta Fara kuka ilahirin jikinta na rawa saboda fargaba da tsoron yadda zata kasance, ta tuna Auren Afra cousin dinsu, Washegari sukaje tamkar ruwa haka suka sameta a kwance, to ita ta yaya zata amince ayi mata haka. Tasowa yayi ya nufo inda take ya rungume ta batareda ta farga ba, kuka ta kara saki tana son kwace jikinta amma ina bai bata wannan damar ba se ma Kara kusantata da jikinshi da yayi, seda ya tabbatar ta nutsu kafin ya sake ta yace
Muje ki kwanta.
Binshi tayi a baya har suka iso daki yace
Ki kwantar da hankalinki kiyi baccinki, Abinda kike tsoro bazan yi miki shi ba.... Matsoraciya rigimammiya kawai.
Turo bakinta tayi ta haura gadon ta kwanta yayinda Junaid ya fice a ranshi Yana fadin "perks of marrying a baby" dama tuntuni ya shirya ma hakan don yasan za'ai hakan. Shima shirin kwanciya yayi ya nufi dakin inda tuntuni bacci yayi awon gaba da ita. Gyara mata kwanciya yayi cikin jikinshi amma bata farka ba, dariyar yarintar Sulaim yayi ganin Tunda aka daura aure tare suke Kwana banda zuwanta kaduna amma se yanzun hankalinta ya dawo jikinta. Sake rungume ta yayi Yana karewa fuskarta kallo yadda take bacci peacefully and innocently. Murmushi yayi Yana jin abu me karfi Yana sake bin jikinshi game da Sulaim. Inda yayi niyyar yi mata wani abun da yi zaiyi yadda take wannan baccin.
Gyara kwanciyarshi yayi lokaci daya Subay'a ta fado mishi, Allah babu yadda baya tsara abinshi, Subay'a ta tafi ta bashi space ya auri love of his life Sulaim. Runtse idonshi yayi yana tunanin yadda sukai da Mami jiya da take tambayarshi ko Subay'a tasan zancen auren yace Bata sani ba, Mami ta dinga fada sannan tace ya tabbatar ya sanar da ita idan ba haka ba ranshi zai baci! Shi dariya Mami ta bashi wai ya fada mata? Lallai! Kamar yadda tayi surprising dinshi da tafiya Cyprus haka zai surprising dinta da Sulaim.
Bayan ta Idar da sallar asuba ta gyara dakin sannan ta fito dakin su Ahmad, har lokancin basu tashi ba amma Atika Bata nan wanda ya tabbatar mata tana kitchen, da sauri ta juya kitchen din saboda gargadi sosae Mami tayi mata akan barwa me aiki girkin miji. Tana shiga Atika har ta Fara kokarin Fara soya Irish wanda ta Riga ta Fere itada Laraba. Kallonsu tayi suma suna kallonta dauke da murmushi wanda ya tabbatar mata suna farin cikin kasancewar ta uwar dakinsu. Cikeda ladabi suka gaisheta tana ta dariya ta kullum sannan tace
Atika jeki shirya su Ahmad, Bari na karasa girkin.
To
Atika ta fada Tana ficewa sannan Sulaim ta dubi Laraba Tace ita taje ta Fara gyara gida. Seda suka fice ta dukufa sosae tana girki Cikeda nutsuwa da kwarewa. Kamshin turarenshi ya fara sanar mata ya shigo. Gas din ta kashe sannan ta juyo fuskarta Cikeda murmushi tana kallonshi kamar yadda yake kallonta, ita ta Fara fadin
Ina Kwana?
Ciki ya karaso ya bude mata hannayenshi alamar ta rungumeshi ai kuwa babu musu ta shige jikin shi, Lokaci daya suka sauke ajiyar sannan ya karkato kanshi saitin kunnenta yace
Wannan ce gaisuwar! How's your night ina fatan ba Za'a Kara kukan jiya ba?
Ya karasa fada Yana dariya, tureshi tayi ta nufi kofa ya bi bayanta yana dariya, dakinsu Ahmad ta nufa hakan yasa ya wuce nashi Cikeda jin dadin yadda take kula dasu Ahmad din.
Karfe bakwai duka suka iso dining, suka zazzauna ta Fara serving din yaran kafin ta hade nata da na Junaid, he was impressed Don Abinda yake shirin fada mata kenan se gashi tayi. Suna kammalawa yace
Mu wuce Kada kuyi latti.
Kallonshi tayi tana Kara gyara zama tace
Se next week zanyi resuming.
Idanunshi ya zaro yace
Kidding right?
Maida fuskar ta tayi very serious tace
Nifa gaskiya na gaji da karatun.
Kanshi ya girgixa yace
That will never happen kinji? Tashi school zaki tafi so kike Baba yace na Hana yar shi karatu ko?
Turo bakinta tayi tana fadin
Dama ba sona ake ba zaace se naje school!
Yana dariya yace
Naji indai akan school ne na yadda.
Daki ta nufa Don gyara kanta, har zuciyarta bata son Zuwa saboda bacci take ji Tunda Kwana biu duk a Wahale take. Skirt da riga tasa white and black sannan ta daura suit a sama ta yafa veil ta dakko books dinta ta fito sukai kicibis zai shigo, seda ya kare mata kallo kafin ya ja hannunta suka koma ciki ba tareda ya furta komai ba. Daya daga cikin trollies din ya bude take Abaya different designs cike fal amma Daga Fara, baka se mixed white and black. Kallonta yayi yace
Ga sunan, sukadai nayi approving Kisa.
Ita din ba Mai musu bace hakan yasa ta ciro daya daga ciki Fara heavily adorned with sparkling stones and sequence bakake, tayi mata kyau. Kallonta yayi yace
It fits you Dove. Kinyi kyau.
Lagwanbar da kanta tayi tana murmushi a haka suka fice don kiris ya rage su Ahmad su makara, iyayensu sun zauna soyayya. Yau kam har cikin class ya rakata kusan a cike class din yake saboda 8 har ta dan gota donma wanda suke dashi bai samu zuwa da wuri ba. Tunda suka shigo ajin yayi shiru idon kowa na kansu musamman ma Junaid kowa na mamakin shi ne mijin dama? Seda ta zauna sannan ya Mika mata handbag dinta bayan ya amsa gaisuwar su Khairi. Yana fita Aimana ta Fara dariya tana fadin
Kaga love birds, bazai iya barin ki shigo ke daya ba se an rako ki. Ta Yayan ba!
Itakam grinning take ear to ear kamar bakinta zai yage, kafin ta bada amsa lecturern Y shigo majestically hakan yasa sukai focussing akan lectures din, seda ya kammalla ya fice sannan suka Fara zolayarta ita dai murmushi kawai take saboda babu baki Tun asali ita bamai magana bace dalilin da yasa bata fiye sakewa cikin cousins dinta ba saboda ireiren wasan, Mami Tasha nuna mata tana mayarwa amma Sede murmushi kamar sokuwa. Sunanan zaune suna revising books dinsu Junaid ya aiko messenger shi akan tazo. Aimana ta dubeta ganin bata da niyyar tashi tace
Ke bazaki tashi kije kiran miji ba?
Hararar ta tayi tace
Ke ina ruwanki? Sa ido kawai.
Khairi tayi tsaki tace
Wannan munafukar wai kunyar wa takeji? Allah yasa bamu ba, Allah kadai yasan abinda ku ka gama a gida shi ne xakixo kina susunke kai.
Duka ta kai mata ta Mike Don Zuwa gareshi. Lokacinda ta isa office dinshi shi daya ta tarar har yayi Alwala zaije masjid don yin sallar axahar, kallonta yayi yace
Se yanzun ko?
Langwabar da kanta tayi a shagwabe ta hade hannayenta alamun ban hakuri , ruwan hannunshi ya fatsa mata ya fice yana fadin
Naje sallah.
Kanta ta girgixa a ranta farin ciki ne fal tana jin ya isheta rayuwa idan kuma ya wuce haka kila kwakwalwar kanta ta zauce. Aje handbag dinta tayi, tayi Alwala tayi sallah sannan ta zauna jiranshi. Shi daya ya dawo bayanshi dasu Ahmad da yasa aka dakko su, suna ganinta suka yo kanta suna fadin
Ammiey!
Kansu ta shiga shafawa tana tambayarsu school da komai, yana tsaye Yana kallonta taji kaifin kallon hakan yasa ta dago fuska dauke da murmushi, gefenta ya dawo ya zauna tareda sauke ajiyar zuciya me nauyi yace
Your only concern is Ahmad and Muhammad. Papansu fa? Kin manta Mami tace ki kula Dani.
Bata fuska tayi tana shafa kan Muhammad dake cinyarta tace
Bakajin tausayinsu, Mamansu bata nan, kai kuma kanada Mami sannan kana Dani ko?
Janyota jikinshi yayi gaba daya tausayin yaran na Kara ratsa shi, basu ma tambayar Mamansu ko sun manta da ita ne oho!
Wasawasa haka rayuwa ta mika, soyayya me tsayawa a zuciya, kwanciyar hankali Marar misaltuwa haka Sulaim da Junaid suka samu, matsalarsu daya duk dare se Sulaim ta birkice mishi ta dinga fushi ko kuma yana kusantar inda take ta bare baki tana kuka, se kawai ya biye mata yadda take so hakan yasa take ganin ta fishi wayo. A haka sukai Kwana hudu, a ranar ya kai gejin da hakurinshi ya Kare, he wants her Amma yasan Za'ai rigima ba karama ba amman ya shirya wa koma me zatayi.
Tunda ya fita sallar maghrib bai dawo ba dama yace mata se anyi isha'i zai shigo, dakinsu ta wuce tayi wanka tazo ta shirya bayan ta barar da turarruka jikinta, trollies dinnan ta nufa Don dakko kaya, English wears take so don ta gaji da saka native. Budewa tayi da wani bakin trouser ta Fara cin Karo hakan yasa ta dakko shi sannan ta hado da silk shoulder off half gown kalar milk, sakawa tayi ta kalla jikin mirror yadda kayan suka amshe ta sukai mata kyau tamkar bakuwar foreigner,