Showing 84001 words to 87000 words out of 131263 words

Chapter 29 - MACE A YAU Document from Sulaim .txt

24 Nov 2024

4829

Ja'afar yana fadin


Mami ta farka!


A hankali Baba ya durkusa ya riko hannunta, idanunshi sunyi ja yace


Ummu_Sulaim me ya faru dake.


Wani numfashi taja me karfi, ta kalli Mami wadda take kuka cikin karyewar zuciya, Ahmad da Muhammad, ga Ja'afar sannan Baba, ga ma'aikatan gidan kowa hankalinshi a matsanancin tashe, kuka ta saki ta damke hannun Baba tace


Baba Yaya ya rasu da gaske? Ya tafi ya Barni? Bayan ya min alkawarin bazan Kara kuka ba shine ya tafi....... Me yasa? Me yasa?


Ko ya ka kai da danne zuciyarka se kayi kuka, saboda yadda take kuka from the bottom of her heart, how's that feeling Irin abu kike jira all your life se kuma yazo lokacin kike gaf da samu abin ya barki..... That's shattered dreams!!!


Juyawa Baba yayi ya dubi Ja'afar yace


Nayi booking tickets Tun kafin na shigo gidan, ka wuce airport yanzun Zamu karaso.


Wani kuka Sulaim ta Kara saki cikin matsanacin tashin hankali tace


Shi kenan I'm shattered, na zama marainiya Baba, banida gata kuma a duniya.


A takaice Seda Sulaim tasa Baba ya zubarda hawaye Balle Mami wadda da kyar ta debo kayanta da na Baba, haka suka fito with a heavy heart Zuwa Airport. Sulaim Tunda suka shiga jirgi ta rungume Ahmad da Muhammad a jikinta tana zubar da hawaye wanda ta rasa a yananyin da take ciki, yaran sunyi shiru se kallon kowa suke.


Tunda Sulaim take bata taba ganin most dreadful journey Irin wannan ba, tamkar da kafa take tafiya haka take ji, a haka ya kare bazai kare ba suka sauka a cikin Aminu Kano international airport. Ana Fara fitowa, Ja'afar ya dakko Muhammad a kafada, yana jan hannun Ahmad, Baba hannun Sulaim ya kama wadda take ta kallonshi yasan bayani take bukata amma yasan bazata taba fahimta ba Yafi son taga komi da idanunta.


Basu jira wani yazo daukarsu suka samu cab ta daukesu zuwa National orthopedic hospital dake Dala a birnin Kano. Tun a gate suka so hanasu shiga amma kallon Sulaim kadai bazai barka kayi Abinda kayi niyyar ba. Ta lalace Lokaci guda ta rame, idanu sunyi jawur tamkar garwashi ko jikinta ka kalla kasan akwai damuwa. Jeans ne jikinta se top Fara iya gwiwa da karamin veil wanda babu inda ya rufe mata, haka kuma babu Wanda ya lura da shigar dake jikinta Don babu me wannan nutsuwar.


Dr. Halliru suka Fara hangowa me Family law da Ridwan suna tsaye suna jiran isowar su, Tunda ta hada idanu da Ridwan ta saki hannun Baba ta nufeshi kamar zata kifa tareda ruko hannun shi tace


Ka fadamin Yayana ya tafi ya barni? Na zama marainiya ko? Bai cika alkawari ba, he said he'll be my home, my shelter, the shoulders I'll cry on.......


Ja'afar ne ya ruko ta dan baki daya Ridwan da Halliru sun kame a gurin tamkar gunki, me Zasu ce mata? Ya mutu? Ko kuma he's battling with his breathing.


Kuka sosae take har suka isa building din SOPD inda Tanan suka hau sama zuwa new Aminity. Hannunta ta fixge Daga hannun Ja'afar tana kokawa da numfashinta, so yake ya fita amma hanashi take ta fison ko zai fita ya fita bayan ta ga Rabin rayuwarta, taga better half dinta. Tayi nasara cigaba da tafiya sede kawai kafar take wullawa batasan inda take zuwa ba.


Suna isa kofar room din, doctors wajen ashirin suka fito Daga ciki, Blue Team, Pink Team, White team da Green Team kowanne yana son ganin Team din da zaa aje Junaid din ciki.


Dukansu Suka tsaya suna kallon Sulaim wadda ta taryi babban consultant din Pink Team dake gaba, ta rike hannunshi me rikeda waya da stethoscope da bai samu ya makala a wuyanshi ba tace


Doctor tell me is he truly dead? How is he? Tell me he's waiting for me inside.


Gaba daya gurin yayi tsit ana jiran amsar bakinshi.


Your husband is OK, yana jiranki kije gareshi.


Babu jira ta kutsa ciki lokacin nurses biyu na kanshi, daya yana sa mishi blood daya kuma yana daidai ta dakin. Baki daya tsayawa sukai suna kallonta babu Wanda yayi mata magana har ta dira gwiwarta a kasa ta ruko hannunshi hakan yasa ya saki karamar kara, da sauri ta sake shi hawaye na bin idanunta, ta kalli Fuskarshi babu ciwo a jikinta amma tana iya hango jini Yana fitowa daga kunnenshi da hancinshi. Kifar da kanta tayi tana wani Irin kuka me zafi wadda yake Marar dadi ga kunnuwan me saurare.


A station na nurses doctor ya zauna shi da Baba don yi mishi bayanin halin da Junaid din yake ciki.


Sir! Bayan accident din da yayi bamu samu ganin karaya ko daya ba sede ya bugu wanda ya taba kanshi shi ne muke kira "Head injury" shima mild ne saboda gashi yana bleeding ba ta ciki yake ba. Se dislocation a hannunsa da karan hancinsa. To matsalar he's unconscious amma Inshaaa Allah Zamu ga Duk yadda zamui da izinin Allah ya dawo hayyacinsa.


Kai Baba ya gyada yace


Nagode kwarai, Allah ya Baku saa.


Daga haka suka tattauna da nurses din akan bills da zai yi depositing a account office dinsu. Daga haka ya wuce dakin da Junaid lokacin kowa ya shiga ya ganshi kuma koke koken ya ragu sosae don hatta Sulaim tayi shiru sede bata magana haka Mami wadda ta kasa daina blaming kanta as cause of everything. Tunda Ridwan yace Accident yayi Bayan ya shigo Kano dayake shi ne last call dinshi yasa bayan abin ya faru shi aka Fara kira shi kuma ya kira Baba Wanda bai iso gida ba Yana hanyarshi ta dawowa daga Abuja. Yadda ya shigo gidan hankali a tashe yasa Mami tayi tunanin mutuwa Junaid din yayi!!!


Basufi awa a gurin ba Imratu da Jabir Harda Jawad suka iso hankalinsu a matukar tashe Amma ganin yana raye yasa suka nutsu aka Fara jajantawa. Kafin isha'i labarin accident din ya kai Birnin kudu, Jega, Kebbi da Birnin Kebbi se kira suke a waya don jin jikin na Junaid amma magana daya ce he's still unconscious.


Karfe goma Baba ya tattara Mami, Ahmad, Muhammad, Imratu, Jawad da Sulaim don su tafi, aka bar Ja'afar da Jabir a gurin shi, Sulaim kuka akan ita bazata tafi ba a gurinshi zata Kwana, seda lallashi kafin ta yadda ta bisu shima ta dinga kuka tamkar ranta zai fita saboda gani take idan bata kusa dashi mutuwa zaiyi.


A gidan Junaid driver din Baba ya ajesu Sulaim, Baba yana tayiwa Imratu kashedin ta kula da Sulaim, su kuma suka wuce zuwa hotel don su Kwana. Daren ranar ba sai na fada ba babu Wanda yayi baccin arziki Balle Sulaim me gayya me aiki!


Washegari tun da sassafe ta shirya amma Baba da yazo yace mata ai basu Bari aje gurin patient se karfe uku na yamma.... Hey pipu tamkar sokuwa haka ta dinga kuka tamkar don shi Allah ya halicce ta, babu Wanda ya lalashe ta don bazatayi shiru ba, Baki daya tausayi Take bawa Baba, ji yake idan yana da halin tashin Junaid da se ya tashe shi kodan Sulaim kodan hankalinta ya kwanta amma bashida wannan halin.


Wajen karfe biyu Mami ta karaso ita dasu Mama Sauda, Umma Fatima, Neneh ta birnin kudu da Hajiya ta Jega, suka saka Sulaim a gaba Sunata mata nasiha amma ina a ranta fada take bazaku gane ba, dukkanku da aurenku, iyayenku na da rai Nikam banida kowa ban kama komi ba. Haka suka dunguma Zuwa Dala sede Alhamdulillah yau ya fara responding ba dai kamar jiya ba. Hakan ya kwantar musu da hankali suka kara samun hope.


Da daddare Bayan Mami sun kwanta itada Baba ta matso jikinshi ta daura hannunta a Fuskarshi tace


General!


Dagowa yayi yace


Nafisatou!


Haka yake fada idan soyayyar ta motsa.


Nasan ban kyauta ba Abinda nayiwa Junaid amma Allah ya sani inada dalili na....


Hannunta ya riqo gam yace


I know and I understand you Shiyasa kikaga ban saka baki ba kwata kwata nasan duk Abinda kikayi kina da dalili. Rest well please.


Hawayenta ta goge tace


Inada abu daya da zan rokeka kuma Dan Allah gobe juma'a ka daura auren Sulaim da Junaid!


Da sauri ya kalleta yace


No! Nafisatou mu Bari ya tashi tukunna.


Kanta ta girgixa Tana kuka a hankali tace


Dan Allah Baba just do this for me please !


Ta fada hawaye na Kara wanke mata fuska, hannunta ya Kama yace


Is ok gobe kike so right?


Kanta ta gyada yace


Inshaaa Allah .


Daga haka ya sauka a gadon ya dauki wayarshi ya koma can gefe yana waya, ya jima yanayi ba da mutum daya ba sannan ya dawo ya kwanta.




Shatuuu ♥️[9/2, 9:38 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU*
39


✍️Shatuuu ♥️


🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION


#⃣Shatuuu095@wattpad




Ranar ta kasance juma'a, jumaatu babbar rana, Tunda Junaid ya fara rashin lapiya wannan shi ne Karo na farko da Sulaim ta samu tayi bacci shima bawai niyya tayi ba a'a taci bashi da yawa dole ta biya, hakan yasa bayan ta Idar da sallar Asuba tana zaune kan praying mat wadda tun ranar da ta iso gidan ta shimfida ta, wanka da Alwala kawai ke tada ita se idan zasu tafi Asibiti amma dama abinci ta dade da daina ci, yoghurt kadai take iya sha shima se wani na tsaye a kanta. Ta rame ta lalace tayi baki tamkar ba Sulaim ba, babu komai ya rage fuskarta banda kwalakwalan idanu da suke a warwaje kamar na owl. Suna zaune Bayan sunyi sallar Imratu ta dube ta tace


Sulaim bazaki sawa zuciyarki salama ba ki rungumi kaddarar da Allah ya aiko miki ba. Duk wannan damuwar da kike ciki bazata Hana Kun Fayakun aiki ba. Ki kwantar da hankalinki kiyi mishi addu'a gwargwado iko.


Hannunta tasa ta share hawayenta tace


Anty Imratu, kina ganin Yaya zai tashi? Kina ganin zai samu sauki bazai mutu ba? Wallahi ya mutu mutuwa zanyi.


Ta fada Tana fashewa da matsanancin kuka me cin rai, me taba zuciya. Rungumota Imratu tayi tana bubbuga bayanta alamun rarrashi Don gaba daya tausayin Sulaim din take sosae, yarinyar tana cikin mawuyacin hali tana bukatar dauki. To daga nan ne bacci me nauyi ya dauketa wanda Bata farka ba se karfe goma da rabi shima hayaniyar da ta cika gidan ita ta farkar da ita. Gabanta na wani Irin bugawa, tsoro Yana kara shigarta ta mike jikinta a matukar sanyaye tamkar an watsa mata ruwa haka ta fito amma se ranta yayi matukar baci saboda at first tayi tunanin Junaid ne ya rasu Amma tana fitowa se tayi kicibis da su Mami anata hada Hada tamkar wanda suke shirin yin biki. Fasa fitowar tayi ta koma daki ta kwanta tareda kifa kanta ta saki kuka me ban tausayi, bakin ciki sosae takeji cikin zuciyar ta, wato yaya Yana can a kwance unconscious su kuma saboda basu damu ba yasa suka zo Harda hada Hadar biki lallai ma!


Yaya Maryam wadda ta kasance first born din Umma Fatima ta shigo don duba ko Sulaim ta tashi ta ganta a wannan halin. Gefenta taje ta dago ta, tare da fadim


Haba Sulaim kin dinga kuka kenan? Se Yaushe zaki hutawa zuciyarki, Allah zai yayewa Junaid ko.


Kanta ta girgixa tace


Amma kuna kallo Yaya Yana Asibiti unconscious, shi ne zakuzo kui ta hayaniya.


Murmushi Maryam tayi tace


Kiyi shiru mun daina, taso muje Umma na kiranki.


Babu musu ta Mike tabi bayanta, parlon daya kasance na Junaid anan Mami da 'yan uwanta suke da kuma 'yan uwan Baba, Tana shiga ta tsugunna ta gaeshesu Sede farin cikin da take hangowa akan fuskarsu yasa ta Fara tunanin kodai Junaid ya farka ne amma ai da Za'a Fada mata. Zama tayi inda Amma ta nuna mata. Wata budurwa me Kimanin shekaru ashirin ta dubi Amma tace


A fara?


Kanta Amma ta gyada tare da duban Sulaim tace


Duk Abinda yazo cikin rayuwarki, ki karbeshi hannu bibibyu kinji?


Hawaye na zuba daga idanunta ta gyada Kai, zuciyarta na son sanin dalilin da yasa ake mata wannan Mulken mulken Amma ba Wannan ne a gabanta ba, karfe uku kawai take jira tayi ta tsallake koma Menene taje ga yayanta.


Tamkar an dade da sanar da mutane wannan daurin Auren haka massalacin na Alfurqan dake cikin Alu avenue ya cika da dumbin mutanen dake zaune don shaida auren na Junaid da Sulaim. Ja'afar shi ne Wanda ya wakilci Junaid, yasha manyan kaya tamkar aurenshi, Fuskarshi babu yabo babu fallasa cikin zuciyar shi Yana gwada Irin asarar da yayi amma ko babu komai dan uwanshi ya samu, yasan it was all his fault ba laifin kowa.


Karfe daya da Rabi, Bayan an kammalla sallar juma'a babban Limamin massalacin Wanda Baba ya bashi wallicin Junaid don abokinshi ne Tun school days, Baba Abdul Aziz wanda abokin Daddyn Sulaim ne shi Baba ya bawa wallicin Sulaim. Babu bata Lokaci dubban jama'ar dake ciki da harabar massalacin suka shaida daurin Auren Muhammad Junaid Lukman Birnin kudu da Ummu_Sulaim Aminu Birnin kudu akan sadaki Dubu Dari Biyu. A take aka shafa fatiha kafin aka ja doguwar addu'ar rokawa Junaid lapiya.


A gidan Junaid kam Sulaim Tasha gyara na gani na fada, within hours ta canza Baki daya tamkar ba ita ba, tayi kyau sosae tamkar an Bare ta sabuwa. Ga wani kamshi da takeyi kamar an mata barin turare. Seda suka gama pampering jikinta kafin suka Fara zana mata lalle ja. Lokacin daga ita se Najaatu wadda Ke kunshin, sauran biyun Aliyah wadda gyaran Kai tayi mata se Mamaaa wadda Itace head din ita tayi gyaran jiki.


Cikin sanyin murya Sulaim tace


Me yasa ake min wannan abin, Yayana yana Asibiti amma har nake da lokacin kunshi.


Murmushi tayi tace


Kede ki Bari na karasa miki kinji.


Kanta ta gyada kawai, ta cigaba da ambaton sunan Allah tareda lumshe idonta Wanda ya fara washewa Daga jan da yayi. A hankali taji tamkar ana zubawa zuciyarta ruwan sanyi, Lokaci daya taji wata nutsuwa Tana shigarta, taji wani bakon yanayi me dadi wanda ta manta rabon da ta shiga Irinshi, ajiyar zuciya ta dinga saukewa har lokancin idanunta a lumshe suke. Seda Najaatu ta kammalla kafin ta bude idonta tace


Dan Allah idan kin fita ki tambaya Wace Imratu ki Turon ita.


Inshaaa Allah ta fada haka kurum take jin tausayin Sulaim din a zuciyara saboda kana kallonta zakaga tana cikin damuwa. . Kafin Imratu ta shigo taji gidan ya kuma kacamewa da guda da ihun murna a'a nanma kanta ya kara shiga duhu tana tunanin abinda yake faruwa?


Tun tana zuba idon ganin Imratu har ta hakura ta cigaba da zama, can Sega Najaatu Taxo ta cire kunshin, subhannalllah! Kwaai zaka iya fada saboda masifar kyau da yayi. Wasu abubuwa ta shafa mata sannan ta hada bakin lalle ta Fara mata shima me kyau. Shi bai dade ba aka cire kuma har lokancin babu Wanda ya shigo gurinta hakan yasa taji Duk ta damu tana son sanin abinda yake faruwa da ita, don tasan ko Meye dole it has to do with her, amma ko a ranta bata kawo ta auri Junaid bane.


Har dakinta Mamaaa ta kaita lokacin babu mutane da yawa a gidan ya dan sarara, kowa ta kalla Fuskarshi annuri ne kawai ke fita amma da idan ta nufesu se taga babu fuakar ta Tambayesu. Ita ta hada mata ruwan wanka me hade haden kamshi da stuffs dinsu wanda Bata San meye ba, tayi wanka da kyau dama tana son Ruwa hakan yasa duk dadewar da tayi a ciki bai dameta ba. Amma hankalinta gaba daya yana kan Junaid don har hudu tayi tasan yanzun Duk anje an ganshi ita daya ce kawai.


Tana fitowa aka barta tayi sallah Sega Mami ta shigo hakan yasa duka suka fita, Mami ta zauna Tana ta kallon Sulaim din wadda tayi kasa da kanta, gabanta na tsanan ta faduwa don batasan me Mami zatace da ita ba. Sun kusa Mintina talatin in awkward silence kafin Mami tayi breaking silence din da fadin


Ummu_Sulaim!


A hankali Cikeda nutsuwa ta dago idanunta da sukai haske kamar an diga zaiba a ciki ta kalli Mami kafin ta dauke kanta don haka kurum taji kunyarta take ji.


Yau Friday, juma'a kenan babbar rana ga Dukkanmu. Wani barin na zuciyarta yana fada min Nayi shishigi amma wani barin na fadamin daidai kenan. Bayan mun rabu jiya mun yanke shawarar aura miki junai......


Da sauri Sulaim ta dago Tana kallon Mami wadda kallon yasa ta kasa karasawa, wasu Irin mixed emotions ne cikin idanunta da kan fuskarta, lokaci daya madaukakin farin ciki ya mamaye mata zuciya da dukkan jikinta! Amaryar Junaid! Oh Allah ta ayyana cikin ranta kafin kuma ta saki kuka a hankali wanda yasa Mami tace


Bakya murna ne?


Da sauri ta girgixa kanta Tana share hawayenta kuma ta kasa furta komai banda hailala da kirari da take yiwa Allah daya cika mata barinta ko tace burinsu, Allah ya tayar mata kafadun Junaid ta gaya mishi ta zama mallakinshi, inama yana nan tasan murmushin nan zaiyi wanda ko fushi take yayi se taji ya tarwatsa fushin, ta tuno idanunshi masu kaifi da Hana mutum sakat! Kuka ta dinga Yi tana Shesheka wanda Mami ta tabbatar na tunanin halinda Junaid yake ciki don tasan Sulaim ko abinda tayi a wannan jinyar tashi ya isa ya tabbatar wa da kowa son da take mishi.


Bayan sallar isha'i Mami da Umma da Amma suka shirya Sulaim cikin zani na soft cotton material Baki da long sleeve top Fara kal, kanta da Aliyah tayi mata parking gashinta in an assemble bun ya tashi yayi kyau aka saka mata bakar hula me kyau, sannan amma ta ciro wata lafaya me tsananin kyau Fara tas da sequence bakake a jiki se edge dinta wani black lacy ne aka mishi ado. Haka suka shirya ta tayi kyau Tana fitarda kamshi na musamman

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login