Showing 18001 words to 21000 words out of 131263 words
Baki kuma yayi kyau kan shiny caramel skin dinta ta duba. Tare suka fito su hudun Ummu_Sulaim, Ummu_Khulthum, Ummu_Aimana da Ummul_khairi.....the 4 Ummu's. Khairi tace
Kuzo mu fara yin sallah kafin muje neman abinci.
Khulthum ta bata rai tace
Gaskiya ni yunwa nakeji, mu fara cin abincin kawai.
Ke kullum yunwa kikeji baki cin abinci daga gidan ku ne?
Harara ta watsa mata Wanda yasa Khairi yin dariya itakuma Aimana tace
To meye abin hararar tawa, ba gaskiya na fada ba, malama sallah zamu Fara yi.
Itakam Sulaim jinsu kawai take don bawai tayi wani sabo bane ita dasu last week suka dawo Daga mid semester break, ranar da ta dawo ta nemi Khulthum saboda zaman ita daya baya mata dadi to ita kuma Khulthum already tanada su Aimana hakan yasa sukai jamming baki dayansu. Amma har yanxu bata fiya sakewa ba sosae. Massalacin suka Fara zuwa suka bada farali Khulthum tana ta bacin rai wai ba'a girmama opinion dinta ba. Sulaim kam murmushi kawai take musu. Wani joint sukaje nanma kafin aje seda aka bata Lokaci kan ayi deciding gurin da Za'a ci abinci Se sulaim taji tarayyar batada amfani don lokacin tana ita kadai yanxun ta kammalla komai ta koma class amma ya zatayi Tunda ta Riga ta biyosu. A joint din sukai order fried rice da salad se Beef akai da drink. Dama se an gama ake biya kuma kana shiga gurin kasan na manyan yara ne ya'yan masu kudi don hardly kaje baka hadu da wani lecturer ba a gurin, sunsan takan iya girki. Suna fara cin abincin wayar Khulthum ta Fara ringing gaba daya suka kalleta itakam tana kokarin picking tana sakin wani lallausan murmushi
Kina ina ne?
Shi ne tambayar da Hu ya Fara mata, cikin daidaita muryarta ta fada masa joint din da suke. Tana aje wayar Aimana tace
Wa zaki rakito mana?
Khairi wadda wasu abubuwan nata na shige Dana Khulthum tace
Batta yazo dama yau purse dita babu nauyi, Dan kun nace Keda Sulaim ne amman yau banyi niyyar Zuwa gurinnan ba.
Dariya Sulaim tayi ta cigaba da cin abincinta saboda itama yau yunwar takeji Don Junaid Nada class din safe yau hakan yasa ya figo ta bata wani Yi breakfast din kirki ba. Suna tsaka da cin abinci Hu ya shigo shida abokansa kusan zan ce muku babu Wanda a gurin bai san lucky Hu ba, har wani kirari ake mishi Kaga yaro me kudi kana gudu luck na binka, yaro me tashe. Kusan bawai a faculty dinsu yayi suna ba entire new site ansan Lucky Hu saboda yadda yake da yanmata idan baiyi dating dinki ba to yayi flirting kawarki haka abin yake Shiyasa ko award night ake shi ke daukan most popular a cikin faculty. Abokansa uku suna bayanshi, Tunda ya shigo Khulthum baki daya ta rasa nutsuwarta, ta gyara nan ta matsa can har Aimana tace
Dallah ki nutsu se kace tsutsa kin kasa zama guri daya Bari naga waye wannan saurayin.
Me zasuyi banda dariya Don Aimana ita ke maganin rawar kan Khairi da Khulthum. Gefenta ya tsaya tareda dubansu Sulaim yace musu
Sannunku!
Suma sannu sukai mishi daidai lokacin gama cin abincinsu Aimana wadda tana kallon Hu ta ganeshi kasancewar faculty dinsu daya da yayanta kuma yana yawan bata labarinsa, mamaki sosae tayi haka yake kamar me charm indai yace yana so to dole ne mutum ya amince dukuwa da sanin halinshi da sukai, mikewa sukai Don biyan bill ya dakatar dasu yace
Paid! Kuna kawayen Her Majesty ta yaya zaku biya kudin abinci.
A'a Khulthum se aka Fara blushing Irin taji kunyar nan, itakam Sulaim shiru tayi tana jiran jin Abinda sauran zasu fada. Aimana ce tace
No Dan Allah Karka Kara biya mana , zamu biya namu ita se ka dinga biya mata. For today thank you!
Tana fadin haka taja hannun Sulaim suka fito ita kuma Khairi ta zauna godiya, yayinda Huzaifa ya bisu da kallo saboda bai taba katari da irinsu ba, kawayen yan matanshi shishige masa suke amma wannan har akan Fuskarshi take fada masa bata bukatar payment dinsa.
A class Khulthum ta shigo lokacin already Ridwan was in class, dayake period dinsa ce yana taking dinsu wani course shima banashi bane mutumin bazai samu Zuwa bane Shiyasa ya turoshi, so ranar ne ranar farko da ya Fara shiga class dinsu. Tana ta yauki ta shigo class din itada Khairi, bai ce musu komai ba seda t
Suka zo tsakiyar aji yace
Hey! Get out of my class, irresponsible ones.
Simsim kamar an dakesu haka suka fito Khulthum tana ta Balai yaci musu mutunci, se bayan La'asar ya fita kowa ya tashi ya fito, tunanin Aimana da Sulaim Khulthum tuni ta tafi dake Khairi a hostel take su uku suna day. Tana hangosu ta nufo su, Sulaim ce ta Fara fadin
Me yasa kuka zo late gashi yayi yabbing dinku.
Tsaki Khairi tayi tace
Rabu da shege, ya dauki tsayi kamar Daren bakin ciki.
Dukda maganar batayiwa Sulaim dadi ba ganin laifinsu ne for coming late, banging into the class without permission seda tayi dariya wai tsayi kamar Daren bakin ciki. Khulthum ce ta Fara magana ranta a bace tace
Aimana ni banji dadin Abinda kikayiwa Huzaifa ba, har zakice wai ya rike kudinshi, don kin samu ya kalleki ma.
Baki sake Aimana take kallon Khulthum kafin tace
Ya kalleni? Na rokeshi ne? Ke nifa Bana son wani kato ya biya min abu har idan zan wuce yana tunanin favor yayimin, kuma Inace cewa nayi ya biya muku nida Sulaim Bama bukata.... Ke bana son nonsense stuffs kinji.
Ganin ta dauki zafi yasa Sulaim tace
Kai friends basa fada, Dan Allah kui hakuri meye a ciki.
Khulthum dai batace komai ba se juyawa tayi ta nufi inda yake jiranta kullum ta bi bayanshi ta fada mota suka tafi, Khairi ma sallama tayi musu ta tafi hostel itada wani gaye dan class dinsu. Se ya rage Aimana da Sulaim wadda har lokancin mitar abin take, suna tsaye Sega kiran Oga Junaid ya shigo gabanta ya fadi don ta rasa me ya hanata kiranshi tace ta gama kamar yadda suka Saba bare yau tasan har ta gama lectures bai tashi ba Balle tace ko Yana gida. A hankali kamar me tsoro ta Kara a kunne tace
Yaya na gama.
Ki samu napep ya kawoki na wuce Tun dazu, zamuje shopping da Subay'a
Zaro idanta tayi don bai taba barinta ba ko ya tafi se ya dawo ya dauketa hakan ya kular da ita ba tareda ta amsa ba ta kashe wayar, kallon Aimana tayi tace
Bari na tafi me daukan nawa baya kusa.
Kai ta girgixa mata tace
Yanzu Yaya Nu'uman zai zo se mu Baki lift.
Itama kanta ta girgixa tace
A'a gaskiya ki......
Bata karasa ba Se gashi yayi parking a gefen su hakan yasa taja hannunta suka isa bakin motar, baya ta budewa Sulaim ta shiga ita kuma tayiwa kanta masauki a gaba, waya yake Don haka ko gaisuwarsu bai amsa ba in fact baisan Sulaim na ciki ba a haka suka fito Daga BUK, kafin su karaso AA Marmaro inda nan ne kwanan gidan Junaid Aimana tace
Sulaim kiyi mishi kwatance.
Aje wayar yayi yace
Keda waye.
Kafin ta bashi amsa ya hango Sulaim ta jikin mirror, bai kalla fuskarta da kyau ba se side view dinta dake gefen window take kalla, gabanshi yaji ya fadi take zuciya ta kwadaitu, muryata yaji a hankali tace
Kwana ta gaba zan sauka.
Kasa furta komai yayi saboda yadda ilahirin jikinshi ya amsa Daga Wannan furucin da tayi, seda Aimana tace
Yaya Nu'uman magana ake maka
Naji
Ya fada suna zuwa Kwanar Tace zata sauka se ta karasa tunda babu Nisa, godiya tayi musu a lokacin ya samu damar kare mata kallo, itama kuma haka, fari ne sosae kamar yadda Aimana take babu laifi yanada kyau. Suna amsa mata godiyar ta nufi layinsu, tafiya kadan ta isa gidan, tura karamar kofar tayi ta shiga ta gaida maigadin sannan ta nufi parlourn, kafin ta kai ga budewa aka bude, Junaid ne shida Subay'a wadda ta dawo tun Kwana hudu da haihuwar Sulma ta bashi hakuri sosae tareda nuna nadamar ta, shi bashida matsala hakan yasa ya manta da abin suka cigaba da rayuwarsu. Bayansu Ahmad da Muhammad ne da dukkan alamu fita zasuyi, seda ta Fara gaida Subay'a sannan ta tsaya Seda suka fito sannna Junaid ya dubeta yace
Ya akai se yanzu kika dawo.
Kanta ta dan dauke Daga kanshi tana jin yadda yake ke beating wanda ta rasa dalilinshi kuma abin is only idan tana tareda Junaid ne tace
Babu komai.
Tana fadin haka ta Kara da fadin
Allah ya kiyaye
Tayi ciki abinta, shiru yayi a gurin ya bita da kallo se yaji kamar bataji dadi ba, se zuciyarshi take tuhumar shi akan ya bata mata rai ne? Kallon Subay'a yayi wadda tuni ta isa gefen motarshi ya Dan Daga murya yace
Nayi mantuwa Bari yanxu zan fito
Kanta ta gyada mishi, shikuma ya koma cikin parlour, straight dakinta ya nufa ya kwankwasa kofar. Itakam Tunda ta shiga kujera ta fada ta zauna tayi shiru haka kurum taji ranta a tsananin bace kuma babu abinda take bukata tayi irin kuka, kafin ta gama tunanin aka Fara knocking tasan su Atika ne a ranta tana mitar Daga dawowar mutum Za'a isheshi, kofar ta bude se taga Junaid a tsaye Yana kallonta, kanta ta dauke tareda pouting face dinta, se yaga tayi mishi wani kyau yaji if to say it's okay he'll hug definitely hug her dan fuskarta ta nuna ranta a bace yake amma babu dama hakan yasa yace
Shopping zamuje kiyi min text din abinda kike so kinji?
Unconsciously ta buga mishi Harara wadda tayi cikin sa'a ya gani hakan yasa ya zaro ido da mamaki amma se ta dauke kanta tamkar ba ita tayi ba tace
Tohm.
Tana fadar haka ta tura kofar ta shige, kanshi ya shafa saboda ba haka zuciyarshi ta aiko shi yayi ba, ta aiko shi yaji damuwar abinda take so sannan ya fada mata abu me dadi, who knows he will mess up but he couldn't! Bazai iya ba he lacks wannan courage din.
Fita yayi suka tafi Yana ta mamakin shi Sulaim ta harara, yayinda take kwance har aka kusa kiran maghrib sannan tayi wanka ta bada farali, Tana idarwa wayarta ta Fara ringing, Bro ta gani hakan ya tabbatar mata Junaid ne se ta samu kanta da kin picking, sau biyu yana kira Tana kin dauka shima se ya hakura. Can Sega kiran Ja'afar ya shigo, Kwana biu nan se taji yau tana daukin jin muryarshi, cikin silvery voice dinsa yace
Ina gate gidanku fito mu gaisa.
Da gaske!
Ta tambaya Tana jin wani nishadi from no where
Come and see for your eyes.
Kit! Ya yanke call din, Cikeda zumudi ta Mike ta zaro wani plain lace peach zani da riga, se kuma ta mayar ,ta janyo Abaya ash da silver stones se off white lace da aka saka a edge din hannun da kasan Riga... Rolling tayi da veil din kayan ta fesa turare sannna ta dauki wayarta ta fito anan sukaci Karo da Atika
Uwardakina Kinyi kyau, ina zuwa haka?
Sa ido yanxu zan dawo
Har ta tafi ta isa bakin parlour Se ta tsaya da gaske Ja'afar take wa wannan zumudin ko kuwa? What if idan Junaid ya dawo suka hadu Don ta dan Lura baisan tarrayar su? Tayi kusan 7 minutes kafin zuciyarta tace mata go shi matarsa Ya dauka suka fita, se ke xa'ayi caging a hanaki. Da Wannan ta samu karfin gwiwa ta fita, megadi na zaune Tace dashi
Baba Bari na karba sako
Bata jira me zaice mata ba ta fice, Itakanta bata taba ganin motar ba tana tunanin ya sake mota ne, Tana isa inda yake ya bude mata ta fada Ciki ,tana rufewa ya ja motar with full speed ya bar layin. Da mamaki tace
Yaya Ja'afar what are you doing?
Dariya yayi mata yace
Kin manta a kd kika ki bina kisha ice cream shi zan kaiki kisha yanzu.
Dan Allah don't do this kaga yaya bai sani ba Kada ya dawo bananan.
Bai kara kulata ba itakuma Bata fasa Yi masa magiya ba amma yayi iskar kare da ita, hakan ya tayar mata da hankali.
A gida Junaid da Subay'a sun dawo, yana gama parking megadi ya sanar mishi Sulaim anzo an dauke ta a mota kuma baisan waye ba.
Bakasan waye ba? Ni Kake cewa baka san waye ba?
Ya fada Yana nuna kanshi tareda nuna kanshi wanda hakan seda yasa megadin firgita, hatta Subay'a mamaki tayi yadda ya Daga murya ashe basuga komai ba.
Gidan ubanwa ka barta ta fita? Wayace ka barta ta fita?
Subay'a ta matso zata rike hannunshi ya juya kanta
Don't you dare touch me.
Se taja baya saboda yadda ta tsorata da yanayinshi, Ya dinga masifa wadda tasa baki daya veins din kanshi suka tashi, yayi yayi se kuma yayi shiru ya dinga safa da marwa yana karkada kanshi, baki daya kwakwalwar kanshi ta cushe waye ya fita da ita? Ina kuma taje?
Ganin yanayinsa yasa na aje wayar haka kada nima yar rahoto ya make ni! Lol...... Waye zai bawa Junaid ansa NE? Ya haduwar Sulaim da Junaid zata kasance? Me Ja'afar ke planning yi kadafa yayi!
Shatuuu♥️
[6/23, 5:20 PM] Shatuuu😍: *MACE A YAU*
6
✍️Shatuuu♥️
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
#⃣Shatuuu095@wattpad
LLB1 yayi shiru saboda wata zazzafar test da akeyi ta philosophy, gaba daya kowa hankalinshi yana kan paper dayake rubuta test dinshi, inda Sulaim take naje abin mamaki Tana zaune gefen Khulthum wadda itama dukkan hankalinta ya ta'alaka wajen test din. Baifi minti goma ba daya daga cikin malamin yace
Pens up.
Aje pen din Sulaim tayi tareda sakin ajiyar zuciya, yayinda ta gefenta ma hakance ta kasance, a hankali suka dinga bi suna tattara papers din kafin suka fice. Khulthum ce ta Fara kallon inda Sulaim take wadda hankalinta yana kan wayarta tana karanta text din Junaid akan idan ta tashi ta sameshi a office dinshi, se ta tsinkayi muryar Khulthum tace
Ya test din?
Murmushi tayi Wanda ya fito da gapped teeth dinta ta dago tace
Alhamdulillah, tayi sauki not as expected.
Yadda tayi magana shi ya fara jan hankalin Sulaim, itama martanin murmushin ta mayar mata tace
Gaskiya kam amma......
Kafin ta karasa class rep dinsu ya bayyana gaban class inda ya bada announcement din Logic class baxaiyi taking place ba don haka kowa is free now. Kowa murna yayi mussaman yan nesa da suke son barin kano ranar don an tafi mid semester break, tare suka mike suka jero har wajen class, Sulaim tace
Bari na tafi ana jirana se Bayan break.
Murmushi Khulthum tayi tace
Allah ya kiyaye nima na tafi ayi Hutu lapiya.
Kanta ta gyada mata kafin kuma tace
Bansan sunanki ba fa.
Nima haka, Sunana Ummu_Khulthum
Ido Sulaim ta dan zaro kafin tace
Ummu_Sulaim
Tare da mika mata hannu sukai musabaha, basu bar gurin ba seda sukai exchanging phone digits, Khulthum na fito da wayarta wata Infinix note ce hannunta ta zama babbar yarinya don a cewarta dole a dama dasu, shi kanshi kayan dake jikinta ba karamin amsar ta sukai ba, hardly ka hasaso cewar ga daga gidan data fito, yadda take tafiya a hankali kamar bazata taka kasa ba shi ya fara janyo hankalin Huzaifa dake tsaye gaban motarsu da dukkan alamu wani abun yake jira, ita bata Lura da shi ba hankalinta Baki daya ya tafi tunanin Sulaim, yarinyar ta burge ta she's simple yet classy, kuma kana kallon yanayinta kasan Daga gidan data fito don wani zobe na gold data lura dashi hannun Sulaim din, fatarta ma is flawless. Tana ta wannan tunanin taji alamar anyi parking gefenta, amma da yake Khulthum is Khulthum ko daga idonta Batayi ba balle ta kalli gefenta inda motar take haka ta cigaba da tafiyarta, Huzaifa dake ciki yayi murmushi sannan ya bude motar ya iso inda ta tsaya ita a dole napep take nema nan kuwa addu'a take a ranta Kada ya tafi. Abinda ya fara futawa shi ne
Kin burge ni.... Kizo Nayi dropping dinki dan kyakyawa kamarki bai dace rana ta doke ta ba.
A hankali ta juyo da fuskarta ta sauke Kan tashi, bashida tsayi don idan ya fita da kadan zai fita, kana kallonshi kasan dan Hutu ne kuma dan gayu, naira tana kuka hannunsu.
Nagode
Ta bashi amsa kafin ta kara matsawa gefe don tarar napep, shima juyawa yayi ya Daga kafada alamar Kinyi missing yaja motarshi ya barta a gurin Cikeda mamaki Don bata taba tunanin hakan zai faru ba, tabbas ta bar opportunity dinnan ya wuce ta, a haka a kufule ta samu napep shima ya dinga raina mata hankali dayake ya sameta a Bagas se bata kulashi ba, haka ta isa gida abin Yana ta damunta.
Sulaim na zuwa kofar office din Junaid tasa hannunta tayi knocking, cikin deep voice din nan tashi yace
Come in.
Hannu tasa ta bude kofar, bakinta dauke da sallama ta shiga, yana zaune kan kujerar, yayinda wani wanda ta saba ganinsu tare kuma take tunanin shima lecturer ne Yana zaune opposite him.
Yaya barka da Rana
Ta furta lokacinda ta iso tsakiyar office din, kafin ya amsa ta dubi bakon nashi shima ta gaisheshi maimakon amsawa se yace
Sulaim right?
Kanta ta gyada, shi kuma Junaid ya zabga mishi harara wanda yasa ya kwashe da dariya cikin kankan da murya yadda Sulaim ba zataji ba yace
Se na fada mata Wallahi.
Itadai tana tsaye ta dauke kanta daga kallonsuu taji Junaid yace
Auta koma kan cushion ki zauna kafin na gama.
Babu musu tayiwa kanta masauki tareda tunanin Yaushe rabon da yace mata auta ita kanta ta manta last time din. Wayarta ta ciro ta Fara abubuwa da bansan me takeyi ba, wajen Mintina talatin ta dago idonta cikin sa'a shima kallonta yake se suka hade cikin na juna, dauke kanta tayi shi kuma ya bata rai Wanda kadan ne Ridwan dake gefe baiyi dariya ba haka suka karayi wajen