Showing 129001 words to 131263 words out of 131263 words

Chapter 44 - MACE A YAU Document from Sulaim .txt

24 Nov 2024

4835

Kingdom damsels
Ladies of Maman Mama Novels
Kainuwa writers association group
Kainuwa fans club 1 to 12
Zauren Sadeeya novel
Ummu hanash novel group
Mace tauraruwa
Ummu Safwan novel group
Taskar Marubuta group






_My gratitude also goes to Anty Sumayya Takori, Anty Nafisa Tafida, Anty Fauza 'yar amanah..... You guys are my personal persons♥️_








Bayan Watanni Uku


Shigowar Musbahu cikin bedroom din Khulthum din yasa ta rufe Wardrobe din da take sake gyarawa saboda kayanta da aka kawo daga gurin guga, zama yayi gefen gadon idanunshi na kanta har ta karaso ta zauna a gefenshi tareda fadin


"Yanzun nan zan taho"


Hararar ta yayi yace


"Shiyasa naga kina gyaran wardrobe"


Dariya ta danyi tareda mikewa ta Kama hannunshi Tana fadin


"Oooo gashi na tashi muje na shirya ka"


Kafadarshi ya noke yace


"Goyo nake so"


Baki ta bude tareda sakin dariya tace


"Tabdijam, Too Big fa! "


Rankwashi ya kai mata akanta tayi saurin kaucewa tareda barin gurin Tana yi mishi gwalo, kanshi ya gyada yace


"Ni ko?"


Dariya tayi mishi ta bude kofar ta fice, hannunshi ya ware ya biyo bayanta a ranshi Yana Raya present situation dinshi, ko cikin mafarki bai taba kawowa cewar akwai rana da zai zauna da mace haka ba bai taba kawowa ba, bai ma taba tunanin cewar a mace akwai abin burgewar da har zaisa yana aiki Yana tunanin dawowar gida, har yana jin dokin dawowa gida, har yana jin tamkar yafi kowanne saa a rayuwarshi.


A farkon dawowarsu daga India yasha wahala kafin yayi coping da rashin Abinda yake, ya kasa tunkarar Khulthum don gani yake Yana Zuwa tabbas zai cigaba da Anal sex dinne da ita amma haka ya kaurace mata sede kira kawai a waya yaji yadda take, ya jima a Wannan halin idan ya hadu da maza se yaji Yana son komawa ruwa ga yadda suke kawo mishi attack ta ko ina Seda ya tsaya a tsaye akan addu'a da neman gafarar Allah sannan ya samu ya dace har ya fara hango abubuwa a tareda Khulthum na burgewa hakan yasa ya fara shiga jikinta itama ta saki jikinta dashi ta Fara bashi kulawar da ya kamata shima baya taba wofantar da Al'amuran ta a haka shakuwa da sabo suka shigesu har basu san soyayya ta samu guri a zukatansu ba a haka rayuwar ta cigaba da tafiyar musu har ta mallaka mishi kanta Wanda wanann taste din yasa yaji tabbas ya cuci kanshi da ya zauna Yana biye ma zuciyarshi akan wanda suke jinsi daya, tundaga ranar suka bude shafin soyayya tayi kiba ta murmure hankalinta a kwance, Duk Saturday a gidan Gwoggo suke yini.


Iskar bakinta ta hura mishi hakan yasa ya saki murmushi tareda zama ta Fara serving dinshi ya nutsu yana ci suna hira har ya kammalla ya goge bakinshi tareda mikewa Yana gyara rigar jikinshi, itama mikewa tayi tana fadin


"Har ka koshi? "


"Cikina kike so ya fashe? "


Dariya ta danyi ta dauki briefcase dinshi tayi gaba yana bayanta har ta iso bakin motar da driver ke jiranshi, bude mishi back seat tayi seda ya shiga kafin ta rike marfin motar tana kallonshi kamar yadda yake kallonta yace


"Ki fita da wuri ki dawo da wuri bansan na dawo bakya gida "


Salute tayi mishi tace


"Angama Yallabai"


Murmushi yayi sannan yaja hancinta suka saki dariya gaba daya Cikeda farin ciki da nishadi, rufe motar tayi ta daga mishi hannu sannan ta wuce cikin gida Bayan ta ga ficewarsu Daga gate din. Tana shiga ta tarar komai an gyara hakan yasa ta wuce dakinta ta shirya cikin milk din Voile lace da red flowers tayi kyau sannan ta harhada abinda take bukata ta fito Tana jin sanyi cikin zuciyarta, gaba daya rayuwar tayi mata rangwami Allah Yana sonta da ya hukuntata kuma ya maida ta akan hanya, gashi ta fahimci kudi ba komai bane farin ciki da kwanciyar hankali shi ne jigon rayuwa wanda yanzun haka ta samu batada matsala da kowa don a yanzun renovating gidansu Mama take wanda Musbahu ya bata kudin duk wanann rowar ta daina Don ta rigada ta samu kawa ya rabeta se ya jiku.


Tana fitowa driver dake kaita Duk inda zataje ya taso dama tuni ta sanar dashi inda zataje, aikuwa bai sauke ta ko ina ba se gidan Aminiyarta Sulaimi, Sulaim ta kammalla dukkan abinda zatayi na tarbar su tana kwance kan carpet se Su'ad da ta Fara wayo tana gefenta tana mata wasa yarinyar kamar an ciro fuskar Jabir an saka mata saboda yadda take masifar Kama dashi. Sallamar Khulthum yasa Sulaim tashi ta zauna fuskarta dauke da murmushi, shigowa Khulthum tayi ta zauna suka gaisa tana rikeda Su'ad


"Allah sarki Sulaim wayo Su'ad take karawa kullum"


Murmushi Sulaim tayi tace


"Gata nan kam, Matar nan kin ganki kuwa Musbahu ya dage fa"


Dariya sosae Khulthum tayi suka Fara hira yawancin Khulthum ce ma me maganar Tana Kara bata labarin yadda komai ya koma normal tsakaninsu a lokacin ma ciki gareta na watanni biyu, Sulaim murna tayi sosae a haka su Aimana suka karaso kafin wani Lokacin tuni hira ta barke ta Yaushe gamo.


Karfe hudu na yamma Jabir yayi parking kofar gidan su Junaid, dake yawanci nan yake wuni idan bashida aiki hakan na kara kwantar mishi da hankali, Tundaga kofar parlon yaga takalma yasan tayi Baki amma haka ya shigo da sallama bakinshi lokacin Su'ad na hannun Aimana tana canja mata diaper da kaya, Sulaim na gefenta tana waya da Junaid wanda ya tafi Kwara attending wani conference. Sulaim ce ta Fara amsawa sannan Aimana dake Khairi da Khulthum sun fita wani guri zasu karbo sako, zama yayi kujerar dake gefen Sulaim tana facing Aimana, seda suka gaisa da Sulaim kafin Aimana ta gaisheshi haka kurum ya kura mata idanu ba tareda ya amsa gaisuwar ba har Seda Sulaim ta buga handle din kujerar sannan ya ja numfashi tareda dauke kanshi ba tareda ya amsa ba, itama mikewa tayi ta nufi bedroom din Sulaim hannunta rikeda Su'ad ga idanun Jabir da sukai mata rakiya har ta kule cikin corridor din, zamanshi ya gyara tareda kallon bangaren Sulaim ashe kallonshi take hakan yasa ya saki dariya tareda daga hannun, itama dariyar tayi tace


"Zaka shiga ne? "


Murmushi kawai yayi yace


"Zan samu abinci? "


Kanta ta gyada Bata Kara cewa komai ba ta hada mishi a dining sannan ta dawo parlour tana lissafi cikin ranta, yana gamawa ya kalli corridor da Aimana tabi sannan ya dubi Sulaim wadda ta tsareshi da idanunta masu kaifi


"Yaushe kika zama yar sa ido ne wai? "


Kanta ta girgixa tace


"Ni na isa baka dauki Su'ad ba"


Tsaki yayi don yasan Jan magana take ya fice baice mata komai ba. Wasawasa se karamar magana ta zama babba tun Jabir Yana dauke idanu amma picture Aimana da akai storing a kanshi ya kasa barin kanshi hakan yasa ranar wata Thursday da daddare kamar yadda ya saba ya shiryo ya taho gidan. Suna parlor suna kallo yayi sallama inda Ahmad ya taroshi suka shigo ciki, Seda suka gaisa kafin suka ci abinci sannan Sulaim ta kwashi yaran suka tafi Dakinsu don tayasu homework anan ta bar Su'ad hannun Junaid suna hira shida Jabir. Har ta gama yaran suka kwanta ta dawo ta tarar Jabir bai tafi ba, gefen Junaid ta zauna tareda daura kanta a kafadarshi ta kalli Junaid tace


"Bacci nake ji fa! "


Ya gane me take nufi hakan yasa ya saki dariya tareda kallon Jabir yace


"Gwauro Zamu rufe kofa dare yayi"


Fuskarshi ya yamutsa yace


"Ni Abu ne ya kawoni kuma specifically gurinki Ammin Su'ad"


Kanta ta dago tace


"Ni kuma?"


Kanshi ya gyada tareda gyara zama yana shafa kanshi yace


"Wannan friend din taki, kina ganin zan iya aurenta? "


Gaba daya mamaki ya daskarar dasu don babu Wanda yayi tunanin Jabir Zai nemi aure a Kwana kusa Amma se gashi ya basu mamaki, sun kansu basu sha wahala ba Aimana ta amince a hankali abubuwa suna tafiya har iyaye suka shiga cikin abin suna shiga level 4 akai Auren se ya rage Khairi ce kawai batai aure ba itama kuma wanda zai aureta dan jaligon ne yana jira ta kammalla sannan ayi abin.


A hankali kwanaki suka shude kowacce dakika na zama Mintina haka mintina na zama awanni har cikin Khulthum ya tsufa Gwoggo ta takura dole Musbahu ya maida ita can shima kuma ya tare acan din, ko sati bata rufa ba ta haihu danta namiji me kama da Musbahu, ranar suna aka Sakawa yaron Muhammad anyi shagali Irin na gasken gaske kuwa, Tana arbain ta wuce gidansu inda suka samu afuwar rayuwa suka zama tamkar basu ba yadda haihuwa tayi rana ba Daga Khulthum ba, ba Daga A'isha ba haka Amir kowanne na iya bakin kokarinshi. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya inda Musbahu ya nema mata admission a wata university dake Michigan State inda take Law din Don ya wanke kanshi ya kafata ta kamu kafu sosae.


Bangaren uwar dakin su walida Hajiya Subay'a kam ta yadda ubanta shi ne Alhaji don seda taji tamkar ta bar gidan ya muzgunawa rayuwarta yasa ta bar aikin bank din da take ya hanata fita ko ina Tana gida kullum tsamannin ganin anzo bikonta take amma shiru gashi hajiyar ma bawani dadi takeji Daga gurin ta ba haka yan uwan, Seda tayi shekara daya cif a gida ta gane batada wayo, ta gane Junaid shi ne rufin asirin ta sannan ya maida aurensu inda ta zage damtse sosae ta zage ta shiga taitayinta yaranta duka suka dawo gurinta. Watanta biyar da dawowa ta samu ciki lokacin ita kuma Sulaim ta yaye Su'ad yarinyar ta girma sosae tana yawonta amma ciki shiru babu labari tun abin bai dameta ba har ya fara damunta amma bata taba nunawa ba haka Subay'a ta haihu Sede babyn kwananshi biyu ya rasu, a wannan haihuwar anan Hulda ta Fara hada Subay'a da Sulaim kullum se taje gidan an gyara gidan ta wuce school ana gama lectures ta dawo se dare ta koma gidanta haka har akai Kwana bakwai sannan ta daina Zuwa. Bayan sati biyu Subay'a ta Fara fita tazo tayiwa Sulaim godiya shikenan zaman lafiya ya kara wanxuwa cikin rayuwarsu har Su'ad na Zuwa tayi weekend abinta.


Five Years Leap


A wannan lokacin tuni su Sulaim sun Gama Law har Law school inda a shekarar da suka shiga suka kammala anan ta zama cikakiyyar Barrister, buri ya cika se lokacin hankalinta ya dawo jikinta ta dawo gida ta gina sabuwar rayuwa itada mijinta da yarta Su'ad wadda a lokacin Aimana ta Haifa Namiji me sunan Baba ana kiranshi Abid, itama Subay'a ta kara haifar namiji Mahmud.


Tun Sulaim na damuwa akan ciki har ta hakura saboda yadda Junaid dasu Mami ke Kwantar mata da hankali akan ai Mummynta ma Seda tayi shekara bakwai da aure kafin ta haihu hakan yasa ta hakura bawai Dan bata son haihuwar ba sedan kwantarwa mijinta hankali.


Ranar ta kasance Monday Tun sassafe ta tashi ta shirya breakfast Don a ranar Haulat matar Ja'afar zata koma kaduna tazo tayi Kwana biu kuma da sassafe zata tafi ga Junaid zaije office haka Su'ad dake primary one zataje school. Seda ta kammalla komai sannan ta nufi dakin Junaid tabar Su'ad Haulat zata shirya mata ita, wanda dawawarshi kenan daga massalacin asuba inda ya biya gidan Subay'a sannan ya dawo.


Zama tayi gefenshi tareda fadin


"Heartthrob Ina Kwana? "


Kanta ya shafa yace


"Lafiya lau Dove dita, how was your night baby "


Murmushi tayi tace


"It was...... "


Ta fada kusada kunnenshi, mikewa tayi ganin yana son rama cizon da tayi mishi a kunne ta fada toilet ya biyota suka kammalla wanka anata watsin ruwa sannan ta fito mishi da kayan da zaisa Itama ta shirya cikin plain material baki me kyau dinkin Bubu style yayi mata cif sakamaakon cikowar da jikinta yayi, turare ya dauka nashi na kullum fierce cologne by Abercrombie and Fitch, hancinta tayi saurin toshewa jin yadda zuciyarta ta tashi lokaci daya ga hautsinawar da cikinta yayi, kafin tayi yunkurin wani abu se amai hakan yasa ya nufo ta da sauri amma yana karasowa ta Kara rikicewa ta dinga amai wanda ya tayar mishi da hankali, kafin wani Lokaci ko tsayuwa kirki bata iyawa dole ya kira Jabir akan ya hada yaran duka ya kaisu school akan zaikai ta Asibiti. Kafin suje wani Asibiti dake kusa dasu private akan gwarzo road har zazzabi ya rufeta tana ta surutai, Junaid iya rikicewa kam yayi a haka suka isa aka Fara bata taemakon gaggawa har bacci ya dauke ta sannnan aka tura jininta screening, result din na fitowa ya nuna tana dauke da ciki, murna understatement ce, farin ciki kamar zasu hadiye junansu, kafin wani Lokaci Mami ta iso inda ta tarar Aimana da Subay'a suna gurinta ana ta Faman pampering dinta.


Da daddare Junaid ya shigo lokacin ita daya ce tana Zaune Akan carpet ta Idar da sallah saboda jikin nata yayi sauki sosae Alhamdulillah, gefenta ya zauna tareda janyo wani farin flask wanda ya shigo dashi, yana budewa yawunta ya tsinke dama zaman da tayi so take ta Kira Mami taji abincin ba a kawo ba, plate ya janyo ya fara xuba mata pepper chicken wanda akai garnishing da Irish potatoes, sosae ta nutsu taci dukda akwai yaji amma ko a jikinta haka ta gama ci ta goge bakinta da hannunta Tasha zobo sannan ta kwantar da kanta kan kafadarshi, a hankali yasa hannunshi Yana shafa fuskarta yace


"Precious babynmu na hanya, I can't wait to hold the baby in my arms"


Murmushi tayi tareda sake shigewa jikinshi tace


"Thank you for the love, thank you for everything and thank you for the baby and..... "


Bai bata damar karasa maganar ba ya shiga bata wani sassanyan kiss me tsayawa a zuciya wanda yasa suka manta cewar a asibiti suke!!!




Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!




Shatuuu ♥️

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login