Showing 60001 words to 63000 words out of 131263 words
Daki ta koma lokacin Atika ta gama shirya mata su Muhammad suna zaune kowanne rikeda madara cikin glass cup, Tana shigowa ta kallesu Ahmad yace
Anty morning
Kanshi ta shafa tace
Morning Boy.
Ahmad ta dauka Wanda idanunshi suka cicciko da kwalla it's normal kullum se yayi kukan Papa da Mimi har ta Saba. Jijjiga shi tayi a ranta tana fadin
Inama ace inada wanda zan kwanta a jikinshi nima nayi kukan rashin Papan naku da nayi baku kadai kuke missing dinshi ba.
Seda yayi shiru kafin ta ajeshi ta nemi Abaya fuschia pink ta saka sannan ta daukesu suka fito dining, serving dinsu tayi sannan ta Fara cin Nata tana duba time don Kada suyi latti. Suna gamawa ta dakko lunch boxes dinsu, school bags dinsu da Nata suka fito parlour anan wayarta ta Fara ringing, Duk tunaninta ma Salim ne don rashin Ja'afar, rashin Junaid yasa ta saki jikinta sosae da Salim sukai wani Irin sabo sosae me wuyar faduwa Dan hausawa sunce a rashin uwa akanyi uwar daki. A rashin wannan gwarzon mazajen guda biyu da zuciya ta kasa kankare su tayi Abota da Salim.
Yaya ina Kwana
Ta fada Bayan tayi picking, muryarshi deep da dadin saurare yace
Yakuke gaba daya.
Lapiya lau
Ta bashi amsa Tana zura key cikin handbag dinta,
Megadi yace min baki fita da motar napep kuke Hawa me yasa?
Kanta ta girgixa tace
Babu komai.
Kyautar Batayi miki ba?
Da sauri tace
A'a Yaya dama I was planning yau mu fita da ita.
Sounds better, se munyi waya Anjima ki gaida yaran.
Kafin ta bashi amsa ya kashe, ajiyar zuciya me nauyin gaske ta saki gaba daya wani yanayi ya mamaye mata jikinta. A hankali ta taka zuwa wani couch dake parlon ta ciro key din motarshi da Tun ranarda zai tafi Estonia ya bata akan suna zuwa ko ina Tunda yasan ta iya driving don dawowarta Nigeria lokacin rasuwarsu daddynta Tana cikin mental breakdown Baba yasa Jawad ya ke koya mata don hakan ya dauke mata hankali da kewa amma ko kadan a lokacin umarni kawai take bi Don ba yadda xatayi amma Lokaci gani take meye sauran farin ciki Bayan rashin iyayenta babu wani abu da ya rage Amma dake Allah Allah ne se gashi ba'a shekara ba ta koma normal self dinta.
Tare suka fito ta shiga mazaunin driver Muhammad da Ahmad suna baya Sunata wasa a haka ta ajesu a makaranta kafin ta wuce BUK, Tana parking idanunta suka sauka akan Khulthum wadda wata flashy car ta ajiyeta, cikin wani Hadadden lace take kallonshi will give you insight akan tsadarshi color din ash da baki kasancewar ta Fara yasa ya mata kyau sosae sede dinkin da akai ma kayan an kacaccala shi, sun mata gyam a jikinta tamkar idan tayi nishi kamar zai tsage. Ita ta Fara nufo inda Sulaim din take wadda take kokarin rufe motar, kallonta Khulthum take da mamaki tace
Sulaimi wannan motar fa?
Harara ta maka mata tace
Almost a month bamu tare amma Abinda kika fara tambaya shi ne mota, gaskiya kina da matsala.
Dariya Khulthum tayi tace
Don't mind me kawata mamaki nayi ne, kodan babu mamaki kuna da saa a rayuwarku komai naku me kyau na 'yan gayu masu kudi.
Bata ce mata komai ba suka nufi lecture room a haka aka kammalla ta farko babu khairi babu Aimana hakan yasa koda ya fito sukai zamansu cikin class din nasu aka Fara hira can Sulaim tace
Meyasa through out last week baki zo school ba?
Kai Khulthum ta girgixa tace
Ni fa Kinsan yanzun karatun ya fara isata.
Isarki fa?
Sulaim ta tambaya da mamaki, kanta ta gyada tace
Ki Bari kawae na samu abinda Yafi karatu, Kede ki Bari kawae, ke bazaki gane ba.
Dariya Sulaim tayi karo na farko tun tafiyar Junaid don ko hira tsakaninta da Salim karkari tayi murmushi, idanunta kawai zaka kalla kasan tana cikin damuwa me tarin yawa sede ko an tambayeta amsar daya ce banajin dadi.
Yanzu muke level 2 har kika gaji ko dan kince bazan gane ba ai, by the way Ashir ya kirani yana min wasu maganganun da na kasa fahimta Meke faruwa ne?
Wayarta ta janyo tana fadin
Ki rabu da wawa kawai!
A'a Khulthum kiji tsoron Allah gaba daya kin canja ba kamar farkon Sanina dake ba, Kinsan Maza da kika saka a gaba Bbu inda zasu kaiki se halaka.
Ya isheki malama, wai nawa Ashir ya biya ki gurin Yi masa campaign ne. Na fada maki uncountable times Wallahi bazan auri talaka ba, me yaci me ya bani.
Kafin ta bata amsa khairi ta shigo itada Aimana nan aka bar Wannan maganar suka dauki sabo har malamin ya shigo kafin suka tattara hankalinsu kanta.
Dadinta daya ranar lecture Zuwa 12pm ne hakan yasa ana tashi ta yi musu sallama dan tafiya gida sede suna fitowa dukkansu ta hango Salim tsaye jikin motarshi, ya sakale hannunshi Yana jiranta. Kallonsu tayi tace
Finally yau kowa zai hadu da Salim.
Khulthum da sauri tace
Shi ne Salim din?
Kanta ta gyada suka nufi inda yake tsaye Yana sakin murmushi me kayatarwa, Tana zuwa ta saki masa murmushi tace
Kazo kenan?
Kinyi tunanin bazan zo ba ko? Wane ni nazo banga princess ba.
Murmushi tayi Don Salim ya iya zance, kallon su Aimana tayi tace
Ga friends dina ku gaisa.
Kallonsu yayi suka gaisa sannan yace
Mu wuce?
Girgiza Kai tayi tace
Nazo da mota se wani lokacin.
Khairi tayi musu sallama yayinda Khulthum tace
Sulaimi Bari na bishi ya ajeni Tunda zaku wuce da Aimana.
Hannunta ta karkada tare da kallon Salim wanda yake danne danne a waya tace
In bazaka damu ba ka aje ta please.
Hannunshi ya zura cikin pocket dinshi yace
Babu damuwa, se munyi waya.
Sallama sukai da Khulthum wadda Allah kadai yasan me ye cikin zuciyarta. Aimana ta shiga suka tafi tunda kusan hanya daya ce.
Acan Khulthum tana ta tunanin yadda zata Dana tarkonta Don wannan guy din Irinshi take burin samu, sun kusa Mintina goma suna tafiya cikin wani salo Khulthum tace
Baka tambayi inda Zamu je ba.
Kallonta yayi saboda yadda muryarta ta ratsa shi har kwakwalwar kanshi
Na manta fa.
Murmushi tayi ta Fara bashi address daga nan sukai shiru har ya kaita inda take sauka ta dubeshi tana wani murmushi wanda a iya rayuwar Salim baa taba masa makamancin Irinshi ba hakan yasa ya sake baki da hanci yana kallonta. Dariya ta danyi wanda yasa hakoranta farare tas suka bayyana tace
Nagode.
Ta kama handle zata bude a ranta tana addu'ar Allah ya sa ya tsaidata, addu'a ta karbu dan ji tayi ya riko hannunta idanunshi cikin nata shima yana sakar mata murmushi me tsayawa cikin zuciyar wanda ya gani.
Can I have your number!?
Ya furta a hankali, murmushi tayi tace
Ni kawar Sulaim ce fa!
Kallonta yayi ya Sosa kanshi yace
Then? Come on Baby Wallahi kin birgeni ban taba tunanin a Nigeria akwai wayayyun mata irinki ba, Sulaim din me? She's just a friend and nothing more!!
Gbam! Gbam!! Gbam!!! Who saw this coming ne?
Seda ta dakko su Ahmad kafin ta sauke Aimana bayan ta shiga sun gaisa da Maman Aimana kafin ta nufi gida. Wanka suka Fara yi sannan sukaci abinci ta shiryasu Zuwa islamiyya da yake tare ake kaisu da yaran makotansu yasa Bata kuma fita ba se kallo da ta zauna yi Lokaci Lokaci tana tsamannin kiran Salim zai shigo amma har su Ahmad suka shigo sukai dinner bai kira ba itama bata wani bata Lokacinta ba tayi shirin bacci.
ESTONIA
Kwanaki sun shude har sati yayi da barowarshi Nigeria. Tunda suka zo bai fiya samun wasu time na kanshi ba saboda conference din da gaske akeyi, abin Yana mishi dadi sosae amma yana kewar wani Bangare na jikinshi, lokuta da dama yakan ayyana me sulaimi take Yi yanzun? Ko taci abinci? Ko tana missing dinshi? Shi bai fiye damuwa dasu Ahmad ba Don yasan they are safe amma ita abar tunani ce. Idan yana tareda ita babu nutsuwa yanzun sunyi nisa da juna zuciya taki hutawa yana ganin mallakar sulaim Shi ne kadai abinda zai sa yaji nutsuwa da kuma kwanciyar hankali to ta yaya?
Hannunsa yasa ya kashe shower dake zuba a jikinshi gajiyar tana ta wartsakewa a hankali sannan ya dauki towel ya goge jikinshi tas sannan ya dauki farar bathrobe me flowers purple a jiki, fitowa yayi anan ya samu Subay'a tuntuni tayi bacci, shikam Yana mamakin Yawon Subay'a Tunda suka shigo kasar nan baki daya Bata zauna ta hutawa ranta ba kullum tana cikin yawo ga Kawaye da ta yiwa kanta dasu kullum suna waje se yanzu yake ganin rashin amfanin zuwa da ita Tunda babu Abinda take mishi se gaisuwa, kafin ya fita tana bacci ya dawo bata dakin se bayan maghrib itakuma ta gaji likis bazata moru ba hakan yasa ya kyaleta ya zuba mata ido.
Farin wando ya saka 3 quarter se Riga fara itama ya dauki wayarshi ya fita zuwa balcony Don kiran Sulaim, karfe Sha daya da Rabi anan gurinsu yasan Nigeria karfe Tara ne da rabi. Dab da zata katse Sulaim ta dauka bakinta dauke da sallama Cikeda nutsuwa ta gaisheshi
Inasu Ahmad?
Kallon inda suke kwance tayi tace
Sunyi bacci tun dazu, ya conference din?
Kanshi ya shafa yana jin sanyi na ratsa ilahirin jikinshi yace
Alhamdulillah! Gashi mun shigo second week.
Kanta ta gyada se kuma sukai shiru har na kusan minti biyar kafin tace
Seda safe?
More like a question, rausayar da kai yayi yace
OK, goodnight!
A hankali ta sauke numfashi Don ba haka ta so ba, taso Sui ta kira amma ya ta iya? Haka sukai sallama kowa cikinsu zuciya na axabtuwa da rashin dan uwanta!
Shatuuu ♥️
[7/28, 2:52 PM] Ayshatuuuu: *MACE A YAU*
28
✍️Shatuuu♥️
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
#⃣Shatuuu095@wattpad
Daga labulen dakin da Khulthum ke Zaune Mama tayi ta bita da kallo sosae amma da yake hankalin Khulthum din yayi kan film din da take kallo cikin system dinta. Shigowa Mama tayi da kyau tareda zama Kan katifar da A'isha take kwance, yau ta tashi da zazzabi hakan yasa ko kofar daki bata iya Zuwa ba Tana nan a kwance ta rame sosae saboda ko babu zazzabi A'isha na cikin damuwar hadin da Baba yayi mata da Ashir saboda kullum tana kallon Ashir a matsayin brother dinta Wanda zai auri yayarta and nothing more abin ya buge ta da yawa donma ita bata kula samari saboda past experience da ta samu, don kuwa kowa yazo gunta idan har Khulthum ta fito to se ya koma kanta bata taba mantawa akwai wani da take so sosae Khulthum ta fahimci yadda take son gayen se idan yazo se Khulthum ta fito a haka har hankalin gayen ya fara karkata kanshi what she saw at last was sun dinke da Khulthum hakan yasa ta daina kula kowa Tunda tana ganin inhar Khulthum na nan she's nothing fa ce background wadda take shining in the absence of Khulthum.
Amma abinda ya Bata mamaki Kwana biyu da akai abin, Kwana biu da maida kudin Khulthum kanta Sega Maman Ashir da kanta tazo ganinta, Allah ya taimaka Khulthum bata nan. Matar me kirki wadda tasan darajar mutane wayayyiya ta dinga jadaddawa Aisha cewar haka Allah ya tsara ta karbi kaddarar ta da hannu bibibyu Allah shi kadai yasan sauyin me yake nufi. Da daddare sega Ashir yazo shida abokinshi da farko kamar bazata fita ba amma Amir ya dinga balbala mata masifa akan ta fita Mama kuwa ko kallonsu Batayi ba a cewarta Aisha ta bata mamaki da ta karbi abinda yake na Khulthum ta manta lokuta Nawa Khulthum tana snatching samarin Aishar. Tun tana Dari Dari dashi taga shi ya saki jikinshi da ita tamkar bai da damuwa but deep down inside him he's having an internal battle na karbar wannan canjin saboda zuciya ta ginu ne akan soyayyar Khulthum, Lokaci daya yayi receiving shockest blow daga gurin ta. Da farko kin amincewa yayi da canjin Seda Babanshi ya nuna mishi maida hannun kyauta baya shedan ne kawai ke yin hakan.
Ya jera kwanaki yana zuwa gurinta har ta Fara sakin jiki dashi Amma basu taba haduwa da Khulthum ba se kwatsam ranar bai tafi da wuri ba Daga gurinta har Khulthum ta dawo Daga yawonta. Ranar wani Alhaji me naira a kasan layinsu wanda Khulthum taje yiwa matarshi kunshi suka hadu mutumin Yana da kudi, irin arziki na fada fa sede Irin azzaluman nan ne wanda kudinsu yake iya waje amma banda gidanshi bai wadata dasu ba arzikinshi bashi da amfani garesu, ya jima da sanin Khulthum Sede wancan sanin da yayi mata a nutse take iyakarta tara samari, idanunshi Yana kanta yana watching moves dinta ta hanyar ya ranshi se kuma ya samu labarin ta zama yar hannu saboda yadda Maza dabandaban suke direta cikin saa suka hadu a gidanshi shi kenan aka kulla kullaliya.
Tunda ta hango ta tabbatar Ashir ne da A'isha tace da Alhaji
Yiwa wayancan na tsayen full light.
Murmushi yayi yace
An gama gimbiya
Da haka ya dalle fuskokinsu , wata mummunar faduwar gaba ce ta ziyarci Khulthum saboda yadda taga suna dariya baki dayansu, wani abu taji ya dirar mata a kirji saboda haukan karya take Ashir zuciya zaiyi wahala ta samu madadinshi. Jikinta na rawa ta bude motar tareda daukar handbag dinta ta fito ko kiran da Alhaji keyi mata bata saurara ba shima se yayi reverse kawai ya fice. Tamkar lioness ko tigeress haka ta nufesu idanunta sun kankance saboda kishi wanda bata san tanayi ba, Tana zuwa ta dauke Aisha da mari tare da fadin
Macuciya har dariya kike kin kwaci abinda ya.....
Tas taji akan nata kuncin wanda yasa maganar katsewa ta juyo Ashir ne! Ashir ne!! Ashir ne!!! Shi ne ya mare ta Yana huci yace
Kada ki sake ko da wasa hannunki ya Kai kanta shashasha kawai.
Ashir ni ka mara? Ni Ummu_Khulthum? Ni?
Ta fada mamaki da tsoro da kuma bakin ciki suna sake shigarta
An mareki din do your worst.
Hannunta ta shiga Tafawa tana kallon A'isha wadda idanunta sunyi ja saboda bacin rai,
Lallai na yadda duk inda namiji yake munafiki ne, se kace min Khulthum tuntuni bake nake so ba Aisha nake so basai kayi putting drama ba. Matsiyaci kuma ka sani nafi karfinka ke kuma
Se tayi dariya kawai wadda gwara ace kuka take kafin ta shige cikin gida, straight daki ta wuce ta fada gado ta saki kuka me ciwo na haushin Har yanzun bata daina son Ashir ba. Daga Wannan ranar gaba me tsanani ta shiga tsananin Khulthum da sauran yaran Mama hatta Amira ta daina kulata itama dama bawai shiga sabgarsu take ba hakan yasa ta manta dasu ko abinci akai ta daina ci a cewarta takamarsu tana cin abincin da ubansu ya kawo Shiyasa suke iskanci Mama ita nata kallo ta rasa abinda zata fada hatta Baba kallonshi take don yabi bayan ya'yanshi Tunda yaga Mama akwai saura.
Aisha ya jikin?
Bude idonta tayi a hankali ta kalli Mama tace
Da sauki Mama kina ta aiki ko?
Se hawaye ya fara mata zarya, she hate been sick saboda aiki a jinin jikinta yake idan ba tayi ba bata jin dadi Balle tana son Mama sosae Bata son ganinta tana aiki ko kadan.
To meye abin kukan Allah ya baki lapiya.
Amin ta furta Tana maida idanunta ta rufe. Se lokacin Khulthum ta ankare Mama ta shigo hakan yasa ta tashi ta xauna tana kallon Mama tace
Yaushe kika shigo?
Yanzun nan
Kanta ta gyada zata maida earpiece din kunnenta Mama ta dakatar da ita ta hanyar fadin
Zauna magana Zamuyi.
Dan tsaki tayi tace
Dan Allah ki Bari se anjima Wallahi kallo nake.
Cikeda rashin jin dadi Mama tace
Ki tsaya mana me yasa kike haka ne?
System din ta tura gefe sannan ta zauna ranta a bace tace
Ina jinki.
Kallonta Mama tayi, Tana son Khulthum gaba da kowa da komai a Rayuwarta amma halayen Khulthum ta rasa inda ta kwaso su baki daya tarbiyya tayi mata karanci.
Ina kike Zuwa ne Kwana biu bakya dawowa da wuri.
Cikin ko in kula tace
Ina nake zuwa banda makaranta, kiji Mama da wata magana.
Kai Mama ta girgixa tace
Me yasa baki san Irin maganar da zaki na fada ba, ni mahaifiyarki ce fa.
Allah Kece Mama da wata tambaya wai ina nake zuwa? Zargina Kema kikeyi
Da sauri Mama ta girgixa Kai tace
Haba dai ya ma zakiyi wannan tunanin naga dai yaron hasiya karfe hudu ya dawo gida amma ke se bayan isha'i.
Kai ta girgixa don ta gane wa take nufi wani Rabiu makocinsu yana level 4 same faculty.
Mama Nifa Bayero nake zuwa shi kuma Kinsan legal me kallon kofar gadon kaya wannan yake Zuwa fa.
Aisha na jinsu a ranta tace jahilci baiyi ba gashi dai ta ninke mama a baibai.
Tana fitowa daga wanka ta hango wayarta na haske da sauri ta karasa kan couch din, Tana zuwa taga hajiya ce me kiran Dammm! Taji faduwar gaba ga Junaid Yana zaune kan gado yana aiki a system dinshi kasancewar weekends ne baije ko ina ba kuma itama ya hanata fita. Aje wayar tayi ta Fara shiryawa cikin sassaukan kaya. Seda ta gama tazo ta zauna har lokancin bai daina aikin da yake ba.
Inason magana dasu Ahmad.
Dagowa yayi ya dubeta kafin ya maida kallonshi ga system din yace
Kira Sulaim mana suna tare ai.
Banida number dinta.
Kallonta ya kuma Yi sannan ya janyo wayarshi ya fara dialing sulaim bugu biyu ta dauka lokacin tana kitchen tana aiki
Sulaim how are you?
I'm fine Alhmdllh.
Ta bashi amsa Tana tattara dukkan nutsuwarta ta mayar kanshi.
Inasu Ahmad Mamansu zatayi magana dasu.
Seda gabanta ya fadi jin ya ambaci Subay'a, ajiyar zuciya ta sauke tace
Jiya kakarsu tazo ta gansu ta tafi dasu.
Idonshi ya zaro yace
You let them? Me yasa baki kirani ba.