Showing 99001 words to 102000 words out of 131263 words

Chapter 34 - MACE A YAU Document from Sulaim .txt

24 Nov 2024

4828

kuma alamu sun nuna sun bawa ma'aikatan Hutu. Batare Tace komai ba ta dauki Jakarta da trolley ta koma don tasan anan gidan a yanxun she's not welcomed. Tana fita ta tarar me napep din ya gama shaka tana tsayawa yace


Amma Hajiya wannan rashin mutunci ne ko ki bar mutum a tsaye Yana jira.


Hakuri ta shiga bashi sannan ta lallaba shi ya kaita gidan hajiya, nanma Bata samu hajiyar ba amma ta aika mishi kudindhi kafin tyi wanka ta kwanta ta Fara kuka saboda bata taba wulakanta Irin na Wannan ranar ba, dole ranar ta shiga history dinta!


Meye kuke ganin makomar Subay'a a gidan Junaid?


Wayarta dake gefe tana faman ringing ta kai hannu Wanda yasha lallai Baki me azabar kyau, tafukan hannayenta Baki daya jan lallai ne tamkar a India. Ita kanta Khulthum kara kallon kanta take not believing Itace wannan, buri Yana daf da cika, Tana daf da zama mata, Amarya kuma uwargida uwar yaran Musbahu me TitαΦ! Tun ranar da aka kawo lefe bata kara fita ba idan ba ya zama dole ba, shiri kawai take don bata bukatar ace batai fitting ba a matarshi ba kamar yadda mutane suke fada, wasu na ganin kawai don wata manufa zai aureta yayinda wasu Ke ganin asirce shi tayi. Koma dai me nene Khulthum dai Kwana biu kacal ya rage ta shiga daga ciki.


Gidansu ya cika har makota don komai da zaaci Musbahu ya kawo kuma Tun ranar da ta iske shi office dinshi basu Kara haduwa ko jin muryar juna ba, wabda hakan ko a jikinta Don ko taso damuwa idan ya hankado mata uban kudin se taji ta manta dashi. Hakan yasa babu Abinda sukai na kananan mutane komai ya tafi yadda Khulthum Take so yadda kuma ta tsara. Su A'isha sun zama yan kallo don seda ta samu Mama take Mata korafi akan kudin Musbahu amma Mama tace bata son gulma aikuwa ta rufe bakinta ta cigaba da harkarta itada Ashir wanda ta riga ta damke shi a hannunta. Yana Texas inda ya fara karatu cikin nasara don yayi mata alkawarin komai na lafawa zai dawo ya aureta su samu yadda zasui.


Hello Sulaim


Sulaim dake zaune gefen Mami tana cin abinci tace


Khulthum longest time.


Idanunta ta dan lumshe tareda fadin


Ina nan. Dama zan fada miki gobe Za'a Fara bikin.


Wanne biki?


Sulaim ta tambaya don ita rabonta da Khulthum ma tun data kirata tayi mata godiya da bangajiya basu Kara communicating ba dukda Sulaim ta kikirata akan school, test da exams bata picking, tayi mata text se tayi replying da ta bar school tuntuni hakan yasa Sulaim Bata Kara komawa ta kanta ba, don Tana ganin tafi karfin wulakanci a gurin Khulthum din.


Bikina mana


Ta fada sounding serious. Idanu Sulaim ta zaro tace


Aurenki Khulthum amma se ana gobe kike fadamin? Anya Khulthum are we still friends.


Dariya Khulthum tayi tace


Ki manta kawai abubuwa suka hade min Kede se kinzo.


Kai Sulaim ta girgixa tamkar Khulthum na ganinta tace


Bazan samu damar Zua ba saboda anjima jirginmu zai tashi zuwa Malta Allah ya sanya alkhairi.


Daga haka bata jira amsarta ba ta kashe tareda kallon Mami wadda da dukkan alamu bayani take jira. Briefly tayi mata bayani tare da fadin


Ko ina gari Mami ba Zuwa zanyi ba Balle kuma bana ma garin


Mami batace komai ba se dariya da tayi sannan kuma tace


Kin gama hada komai na tafiyar? 7pm sharp jirginku zai tashi.


Turo Baki tayi tace


Ni Mami bana son tafiya na barki.


Ja'ira rufe min baki.


Dariya Sulaim tayi tana fadin


Kai Mami yanzun kin daina so na.


Ta fada Tana sake turo bakinta Cikeda shagwaba. Hararta Mami tayi ta maida fuskar ta serious I tace


Sulaim! Inason ki maida hankalinki ki rike mijinki, kiyi mishi biyayya sau da kafa kinji? Karki manta bake daya bace kuma komai Daren dadewa Subay'a zata dawo gida. Nasan Junaid Yana sonki nasan bazai wulakanta ki ba inason ki rike darajarki saboda duk yadda mace take ita Gem ce a priceless one ma kuwa. Yanzun Auren Duk ya koma wani iri amma dukda haka ba duka aka taru aka zama daya ba, inason kisan cewar idan maza suna da laifi a aure to mata ma akwai tasu problem din. Inason ki dage Kiyi ibada Koda hakan ne kawai zai sadaki da Aljannah......


Mami ta jima tana mata nasiha da bata dabarun zama wanda jikinta yayi sanyi tamkar an watsa mata ruwa. Suna gamawa ta wuce daki don biyar na yamma tayi tasan duk inda Junaid yake to yana hanya. Wanka ta Fara yi sannan ta shirya cikin Abaya fuschia pink da bakin heart pattern a jiki. A hankali ya bude kofar ya shigo jikinshi Sanye da trouser na kamfanin marks and Spencer se milk din top ta Zara se silver wrist watch a hannunshi na hagu me kyau na kamfanin Frank Miller. Yayi kyau sosae amma Sulaim bataji Shigowarshi ba saboda nisa da tayi wajen daura bakin wedge sandals a kafarta kuma ta kasa, se kawai taji hannunshi ya zura mata igiyar. Dagowa tayi ta dubi inda yake tsugunne ya maida dukkan hankalinshi kan Abinda yake, murmushi me kyau ta saki daidai lokacin da ya dago idonsa ya zube cikin nata wanda Lokaci daya ya shagaltar dasu Seda wayarshi dake cikin Aljihu ta Fara vibration kafin ya mika mata hannu ta Kama suka fito babu Wanda yayi magana.


Baba ke driving da kanshi se Junaid a gefenshi, Bayan seat kuma Mami ce da Sulaim wadda ta kwantar da kanta akan kafadar Mamin tana jin wata kewar Mamin na ziyartar ta kamar kada ta tafi amma Junaid is everything for her, he's her entire world that revolves around the globe, he mean everything, idan tace everything she mean komai da komai na duniyar nan a bayan Junaid yake a gurinta. Seda sukai sallama dasu Mami Sulaim Harda kukanta, Junaid Yana ta dariya sannan suka wuce aka gama screening komai ya kammalla kafin sukai boarding jirgin wanda ya tashi zuwa birnin Valletta dake kasar Republic of Malta!








Shatuuu ♥️
[8/26, 5:03 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU*
46


✍️Shatuuu♥️


🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION


#⃣Shatuuu095@wattpad


Halooooooooooo.... Pipul of wattpad here's a page for all the votes, comments and recommendations. thank you very much Jazakumullahu khairan!


Tun daga parlor yarinyar da keyiwa hajiya hidima a gidan ta sanar mata Subay'a ta dawo tun dazun, da hanzarin ta ta nufi dakin dan Zuwa ganin lafiya saboda tun shekaranjiya su Suhaila suka kirata suka sanar da ita sun dawo basu same ta ba, baki daya hankalinsu a tashe yake haka itama hajiyar hankalinta a matukar dunguzume yake. Koda aka tambayi Sulma itama cewa tayi bata fada mata ba don ta manta sunyi maganar haka wannan kwanaki biyun ya kasance cikin matsaltsalu kashi kashi.


A dakinta ta samu Subay'a kwance kan gado ta kudundune cikin bargon dake ninke gefen gadon , da sauri hajiya ta iso ciki har tana tuntube, bargon ta yaye wani dumi ya bugeta ta Hangi Subay'a kwance tana ta karkarwar sanyi, ajiyar zuciya ta sauke kafin ta zauna gefen Subay'a tareda yaye ilahirin bargon wanda yasa Subay'a bude idanunta wanda sukai ja ba idonta harta fuskarta tayi jawur tamkar tumatir saboda azabar kukan da tayi, Tana jin Duk duniyar ta ishe ta, ji take ta tsani komai don se yanzun wani azababben kishi ya dirar mata anyi mata kishiya? Mijin ya tafi da kishiyar tata? Hawaye masu dumi suka sake gangaro mata wanda ya tilasta mata lumshe idonta saboda barazanar tsagewa da kanta keyi, ita kanta tasan tunda tazo duniya bata taba kukan da tayi Yau ba, Kai ita totally ma bata taba tunanin zata tsinci kanta cikin wannan rayuwar ba, Bata taba kawowa a hankali ta cewar Junaid zai iya kallon wata mace da admiration Balle har zuciyarshi ta kwadaita aurenta, ta tuna dimbin son da ya nuna mata lokacin yana neman aurenta, ta tuna yadda ya dinga fadi tashin samo mata farin ciki amma ita ko sau daya she never reciprocate, Abinda take son gani shi ne Tana juyashi kamar muciyar tuwo to every direction she desires, Wanda hakan ya fara jefa rayuwarsu cikin matsaltsalu don sam Junaid yaki daukar wanann abin. She remembers maganganu na lallashi, fada, nasiha, threats da yayi mata Daren da taje mishi akan zata wuce Cyprus, har ce mata yayi he'll refund hajiya abu daya yake so ta zauna dukda babu tsiyar da take mishi Shida 'ya'yanshi don aikinta da family dinta is her number one priority amma haka ta tsallake komai ta wuce! Idan ba rashin adalci Irin nata ba, taya take expecting Junaid ya zauna tsawon watanni shida shi daya ba tareda mace cikin rayuwar shi ba? Duk kuwa da cewar mutum ne shi me kokarin masking ainahin Abinda zuciyar shi take ciki amma ina bata yi musu adalci ba so dole rayuwarta ba zata taba tafiya daidai ba!


"Oh ni! Uwar Mata Subay'a me zan gani haka? Meye ne yake damunki?"


Idanun Subay'a ta kara lumshewa a ranta tana fadin duk ke kika sani a halinda nake ciki don dai ke uwa ce!


"Subay'a tashi ki fada min Abinda Ke damunki"


Bude idonta tayi a hankali ta kalli Hajiya wadda hankalinta yake a tashe saboda yadda fuskarta ke a dugunzume, a hankali ta bude bakinta tace


"Hajiya ki bar ni kaina ciwo yake min kamar zai fashe"


"Assha, kwanta ki huta"


Kafin Subay'a ta kuma furta wani abu ladidi ta shigo bakinta dauke da sallama ta tsugunna tare da sanarwa Hajiya Alhaji Yana jiranta a parlor, mikewa tayi jikinta a sanyaye ta fito inda Alhaji ke tsaye Yana waya, tana fitowa ya maida wayar aljihun gaban shaddar jikin shi, ya jiyo yana fuskantar ta ran shi a bace fuskar shi a murtuke, abune da Hajiya a iya zamansu sama da shekaru talatin baza ta iya tuna ranar da taga Fuskarshi a haka ba, ga wani wulakantaccen kallo da yake binta dashi Irin Shekeke dinnan. Se kwarjini da taga ya kara, baki daya taji ya cika gurin har taji tsoronshi ya darsu cikin ranta.


Kut ta hadiye wani abu daya tokare mata tare da kirkiro murmushi zatayi magana amma yayi beating dinta yace


Bani keys din part dincan na gefe yanzu.


Idanunta ta sauke Kan shi, kawai se ta tsinci kanta da juyawa ba tareda tayi mishi musu ba ta wuce dakinta kamar sokuwa ta tattaro keys din Baki daya ta kawo mishi. Yana karba ya wuce abinshi babu wani bayani ko wata magana hakan ba karamin tayar mata da hankali yayi ba.


What's Alhaji up to?


Rana bata karya sede uwar diya taji kunya wannan shine popular Hausa proverb da muka sani, tabbas ya tabbata Ummu_Khulthum Suleiman Malumfashi ta zama mallakin Musbahu Suleiman Jimeta akan sadaki zunzurutun kudi naira dubu Dari bakwai. Mutane sun halarci wannan daurin Auren duniya ta shaida saboda yadda Musbahu ya daukaka a duniyar business da Entrepreneurship, the young billionaire kenan, Musbahu me TitαΦ Dan Gwoggo na Khulthum!


Anyi biki na Kece raini ba Daga bangaren Amarya Ba ba Daga bangaren Gwoggo ba, anyi harkar girma don kuwa Khulthum ta sakar ma Mama kudi Don ta fitarda da ita kunya aikuwa babu karya ta fitar da itan. Parties iri iri seda tayi kala biyar babu Wanda Ango ya halarta se wata English dinner da business partners dinshi suka hada mishi anan garin Abuja, haka yasa aka mishi booking flight ita dashi suka tafi karfe shida na yamma, anan aka shirya ta tayi kyau tamkar ba ita ba sannan driver yaxo ya dauketa ya kaita inda Musbahu yake, yayi kyau shima cikin grey tuxedo suit hannunsa daure da bakin agogo na kamfanin Boss, yayi kyau sosae kana kallonshi kaga fulanin usul, lokacinda ta isa gareshi waya yake, ya juya bayanshi a hankali ta kare mishi kallo Tana Kara godewa Allah mijin da ya bata wanda ko daya bata taba tunanin zata samu kamarshi ba. Amma here she's with mijin da duk duniya tasan ta auri mijin nunawa saa. Juyowa yayi Don Tun shigowarta yaji a jikinshi saboda turarenta da ya ziyarci kofofin hancinsa, kallonta yayi he has to admit the fact that Khulthum kyakyawa ce wadda bazai yi shayin shiga da ita kowanne guri ba, Sede yasan babu digon son shi cikin zuciyar ta, kudin shi take yiwa zai cika mata burinta kamar yadda zata zama protector ga rayuwarshi.


Kanshi ya dauke ganin sun hada idanu kar tayi tunanin ta burgeshi ne, itama kanta ta dauke a ranta tana fadin duk wannan girman kan naka se na sauke maka shi! Tare suka fito Zuwa wata lambhorgini baka wuluk da take tsaye Tana jiransu. Kunsan abin wayayyu, Manya wanda kudi ya zauna musu, dinner was great karfe Tara aka tashi Khulthum ta tafi da kyaututtuka iri iri.


A Daren suka dawo kano, Washegari ranar ta kasance lahadi tun safe yan uwa, munafukai, abokan arziki, Kawaye sukaje ganin daki kowa idan ya dawo banda zancen gidan babu Abinda suke, gida ne da suke ganin tamkar drawing ko kuma a film saboda yadda ya hadu.


Da daddare Misalin Tara Gwoggo da kanta tazo ta tafi da Khulthum, babu wata nasiha da akai mata don kowa tsoron magana yake ganin gidan da Khulthum din ke ciki waye zaiyi gigin barar da kujerarshi, hatta Mama bata wani Yi mata fada ba kawai tace mata tayi abinda ya dace.


Har daki Gwoggo ta kaita tazo itada Musbahu wanda gaba daya jikinshi a matsanancin sanyaye yake gefen ta ta sanya su ta shiga tsakiyarsu tare da kamo hannunsu cikin nata fuskarta kadai zaka kalla kasan tana cikin farin ciki Marar misaltuwa, furucinta kadai seda ya kara jefa zuciyar Musbahu cikin Anya kuwa?


"Allah ubangiji yau ya cika min burina da ya dade cikin zuciya ta, Allah yasa yau naga matar ka Musbahu, ina fata zaku zauna da junanku lapiya, zaku sauke dukkan hakkokin da ubangiji ya daura muku. Ina fatan kunsan cewar shi aure is for two parties babu yadda za'ai ace na mutum daya ne, kowannenku Yana da nashi role din dayake playing. Dukkanku babu yaro ina fatan zaku zauna lapiya!..... "


Ta dade tana tuna musu hakkonkinsu kafin ta hada hannayen su guri daya ta fice baki daya daga gidan, ta koma nata. Sun dade a haka kowannen su da Irin tunanin da yake har wasu mintuna suka shude kafin Musbahu ya cire lallausan Hannunsa Daga nata, ba tare da ya furta komai ba ya fice daga dakin.


Mikewa tayi itama, ta Fara kallon dakin da yake mallakinta, duriyar da aka dankara a ciki don ko cokali ba Taxo dashi ba anan ta samu. Touring part din Nata tayi, kana shigowa zakaga karamin parlor me dauke da cushions guda biyu se center table da carpet, ta gefe jikin bango akwai wani hadadden console a manne. Daga nan se siririn corridor wanda yasha ado da manyan frames da akai painting a jiki na flowers masu kyau, a karshen corridor akwai tafkeken parlor wanda ya kunshe kujeru set uku kowanne da kalarshi da kuma design dinshi. Parlon kadai abin kallo ne, anan wawakeken kitchen wanda ya kunshi kayan alatu na idon duniya electronics iri iri kusan duka ma batasan yadda zatayi amfani dasu ba. Bedrooms biyar ne, uku nata biyu na Baki. Gidan yayi kyau.


Dakinta ta koma ta shiga wanka zuciyarta Fara kal kamar shinkafar tuwo, shiryawa tayi cikin wata sexy sleeping wear iya gwiwa baka tayi kyau kamar ba ita ba Balle yadda Tasha gyara don ta durzu a wajen masu gyaran jiki Shiyasa ta Kara kyau sosae kamar ka tabata jini ya fito, kwanciya tayi idanunta a lumshe tana planning yadda abubuwa zasu tafar mata. Tun tana zuba idon ganin ta inda Musbahu zai bullo har wani nannauyan baccin gajiya yayi tafiyar ruwa da ita.


Washegari Bata tashi ba Se sha daya na safe, seda ta tsala wanka kafin ta fito tayi kyau cikin wani dankareren bakin lace wanda aka mishi ado da manyan flowers fuschia pink, parlor ta fito inda ta tarar komai in place, dining an shake shi da different dishes na gida dana waje. Can ta wuce tana bubbudewa amma ko abinci kwaya daya Bata san sunanshi ba. Tana kokarin zama Sega wata matashiyar budurwa Sanye da uniform tazo ta gaisheta cikin Pigin English, ta gabatar da kanta matsayin Linda Itace me kula da abinci.


Zama Khulthum tayi Cikeda isa Tana karkada kafa ta dubi Linda tace


"you're welcome here, inason duk lokacinda aka gama abinci kafin ayi serving dina se an fada min sunanshi da asalin dish din wanne kasa ne "


Da sauri Linda ta gyada Kai tareda fadin


"Noted Ma'am"


A hankali ta Fara bubbudewa tana mata bayanin komai, Khulthum tana saurare saboda ta rike don babu girma ace Bata san wannan abubuwan ba. Bata jima da kammalla cin abincin ba Maimuna da Safiyya wanda suka zama sababbin kawayenta suka zo gidan, Bedroom dinta suka baje ana tashan shafta Bayan ta saka an cika musu gaba da abubuwan tabawa. Maimuna tace


"Hajiya gidannan yayi kyau babu karya se Munji kin Fara laulayi "


Dariya tayi tana jin yadda sanyi ke zagaye ilahirin jikinta, tana jin burinta ya kammalla cika bata da sauran matsala kuma. Seda sukai La'asar sannan suka tafi, dake an ware mata driver da me kaita da kuma na bakinta, haka tasa ya kaisu har gida, suna ta fasa mata kai ita kuma tana Kara girman kai. Dama Tun kafin a kawo ta Tace da Mama kada wadda tazo mata gida Washegari Tunda duk sunga gidan to hakan ma yayi, Shiyasa yau Batayi Baki ba se zagayen gidan da ta karayi.


Har aka Idar da sallar isha'i bata ji shigowar Musbahu ba, mikewa tayi ta dauki wayarta da niyyar kiranshi ta tuna bata da contact din shi, abinma se ya bata dariya don ko a labari bata taba jin hakan ba. Duba kanta tayi tana cikin wata Indonesian Abaya beige

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login