Showing 87001 words to 90000 words out of 131263 words
me kwantar da zuciya. Flat Takalmi bakake Mami ta sata tasa sannan suka kama hannunta se mota inda Jawad ke mazaunin driver, suna shiga ya cillar mota zuwa orthopedic dake Dala!
Gabanta babu Abinda yake banda faduwa lokacin da Amma ta tura dakin suka shiga kanta na kasa ta kasa dagowa don batasan ganin Junaid a halinda ta barshi. Gefen gadon Amma ta aje ta sannan ta Ajiye mata wata jaka batareda tace da ita komai ba tasa kai ta fice, ta jima tana zaune yadda ta barta gashi ta kasa dago idanunta Balle ta kalli dakin dukda tasan gurin Junaid aka kawo ta, kenan ta zama matarshi da gaske an daura auren kenan! Allah kenan yana amsa addu'a ya bawa Bawa Abu lokacin da ya debe tsammani.
A hankali taji alamar an bude kofa an fito, tasan ba shigowa akai ba Daga toilet aka fito, to ko dai wani na ciki ne? Amma se kawai taji muryar da ko a ina take ko me takeyi ta jita tasan ta wacece, wannan karan a hargitse ta dago idonta ta dubi inda ta jiyo muryar shi, shi dinne her beloved, her everything, her world, her life yana tsaye jikinshi da jallabiya yayi haske amma akwai rama sosae tamkar bashi bane wanda ta bari jiya baisan waye a kanshi ba. Hannunsa ya bude mata Fuskarshi tamkar gonar auduga Don fara'a, babu musu ta Mike Tana sassarfa ta isa gareshi Tare da fadawa cikin kirjinshi ta saki kuka, a hankali ya zagaye hannuwansa a bayanta, ya rungumeta Tsam Yana jin wata nutsuwa wadda zai iya rantsewa bai taba jin makamancin hakan ba!
Shatuuu ♥️
[9/2, 9:38 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU*
40
✍️Shatuuu♥️
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
#⃣Shatuuu095@wattpad
Daga office din Musbahu Bata Kara zuwa ko ina ba ta biyo Kabir don ya kawota gida, Tunda yanzun ta samu abinda take so Tana ganin kamar yawace yawace ya Kare ya Kuma kamata ta zauna ta nutsu ta tsara yadda zatayi rayuwa tare da Musbahu.
Suna zuwa gida tayi sallama da Kabir akan se sun zo Washegari sannan ta shigo gida fuskarta dauke da wani madaukakin murmushi, murmushi ne daga kasan zuciya wanda yake nuni da burina ya cika. Babu kowa tsakar gida hakan yasa ta shige daki ta cire kayanta, tare da kurawa kanta ido jikin mudubi, bazata taba gajiya da yiwa Allah godiyar kyau da diri da yayi mata ba don tasan shi ne Abinda yake jawo hankulan Maza kanta, juyawa tayi ta shiga karewa kanta kallo tasan tana Hulda da Maza, tayi Hulda sosae dasu amma ko da wasa batayi Kuskuren bada kanta ba, zaayi romancing, smooching, fingering da duk wani abu amma bata yarda da penetration ba saboda tana ganin shi din shi ne pride dinta, shi ne darajarta ta 'Ya mace!
Katifa ta koma ta kwanta, ta janyo wayarta wadda tuni ta kashe da taje office din Musbahu, kunawa tayi babu tunanin komai ta Fara kiran Aimana, Bata dade tana ringing ba Aimana wadda mamakin kiran yasa tayi picking tace
Khul......
Katseta Khulthum tayi da fadin
Ba wannan na kiraki kiji ba, na kiraki na fada miki aure zanyi.
Aimana da bata fahimci inda maganar Khulthum ta dosa ba tayi ihun murna tace
Ke amma naji dadi Wallahi, Yusuf ne.
Wata harara Khulthum tayiwa wayar tamkar Aimana na gurin tace
Kina abu tamkar har zuciyarki bayan bakin ciki ne fal, Bari kiji na samu miji Wanda har ki mutu bazaki taba haduwa da Irinshi ba! Kince masu kudi ba'a haduwa dasu ina son kisan cewar na samu kuma zan aura.... Kije ki samu rijiyar da tafi kowacce zurfi cikin kano state ki fada don bakin ciki!!
Bakin cikin Aimana guda daya ne Bata samu ta rama ba, bata fadi Abinda take son fada ba, ba kuma ta samu ta mayar mata da martani ba ta kashe. Haka ta Bata kusan Mintina ashirin tana kiran Khulthum amma taki shiga kawai se ta kira Sulaim ita kuma wayarta a kashe. Tsaki tayi tana addu'ar Allah ya hada su itada Khulthum Koda cikin mafarki ne Wallahi se ta sha mamaki, ita har ta isa ayi mata bakin ciki, bakin cikin me talauci ko kuma rashin tarbiyya?
Da daddare wajen karfe Tara tana kwance tana kokarin hada wayarta da power bank, Amira ta leko tace
Yaya Khulthum kizo Baba yana kiranki.
Kanta ta gyada tace
Kice gani nan.
Amira ta fice ita kuma ta cigaba da Abinda take babu niyyar ma fitar, jin shiru yasa Baba ya kalli Mama yace
Kije ki Kira min ita Tunda ke Uwarta ce, ni kuwa kinga ba haifar ta Nayi ba.
Kai Mama ta girgixa ranta a bace saboda yadda Khulthum ke jawo mata magana. Tana zuwa ta sameta a kwance, kunnenta da earpiece ta lumshe idonta saboda yadda wakar ke ratsata, wani duka Mama ta kaiwa cinyar ta wadda ta bayyana saboda kwanciyar da tayi zaninta ya tattare, wani tsalle ta buga wadda yasa wayarta faduwa kan simintin dakin, idanunta ta bude idonta Cikeda masifa se taga Mama ce amma dukda haka tace
Mama ya haka?
Ubanki nace, tun dazun Baban A'isha ya turo kizo amma kika ki zuwa saboda kin shahara ko?
Tsaki ta saki tareda daukar wayarta wadda tuni ta fashe, gashi babu screen guard, ihu ta kwalla tace
Haba Mama Wallahi nidai Baki kyauta min ba.
Wani dukan Mama ta kai mata tace
Tashi muje.
Mikewa tayi tana kunkuni ta nufi inda Baba yake Zaune, ranshi a hade wai kar ma taga fuskar da zata kawo mishi wargi, itama bata ran tayi tamkar me shirin wata tsiyar. Yadda ta tsaya tsegege ta kama kugu yasa Mama Dalla mata harara, amma se ta dauke kanta tana Kara hade fuska tamau. Ba karamin bata ran Baba abin yayi ba yace
Ke!
Kin jiyowa tayi seda Mama tace
Khulthum bakyaji? Ba dake yake ba?
Juyowa tayi tace
Mama Ke yace fa! Bakiji ba?
Zauna
Ya furta Yana danne bakin cikin dake addabar zuciyarshi, yasan komai Khulthum ta zama har dashi , Tunda ya bata yarinyar bai hanata yin komai saboda tana bashi kudin cefane gashi yanzun babu Wanda ta kyale cikinsu. Kanshi ya girgixa Cikeda takaici kafin ya dubi Mama yace
Duk inda na wuce se anyimin magana akan Khulthum tana Tara maza don haka na gaji ko dai ta fitar da miji tayi aure ko kuma ta koma malumfashi.
Yana aje numfashi tace
Gobe zaa zo gaisheka.
Tana gama fadar haka ta mike zuwa Dakinsu ta kwanta, Mama ta biyota tana ta fada amma Khulthum ko kallonta Batayi ba, hakan yasa Mama ta dinga kuka Tana fadin
Wannan shi ne ladan haihuwa Khulthum, Kinyi daidai Yarinya wannan Itace sakayyar goyon da nayi miki!
Khulthum bata motsa ba har su A'isha suka dinga rarrashin Mama kafin ta tafi ta kwanta zuciyarta tana gobara!
Washegari ta kasance juma'a, kamar yadda Musbahu a ranar Bayan anyi sallar juma'a yazo shida Kabir ya gaishe da Baba Alkasim wanda ya gayyato abokinsa guda daya. Cikin mutunta juna suka gaisa, nan Musbahu ya sanar musu yana son Turon iyayenshi wani satin ayi finalizing komai. Anan Baba ya sanar mishi asalin Khulthum iyayenta na malumfashi Don haka zaiyi magana da babarta aji. Da haka aka tashi maganar bai nemi ganin Khulthum ba duk yadda Kabir Ke rokonsa Amma yace bai da wannan lokacin ya bada kudi a Bata ai kuwa tayi murna don Musbahu bata ga wani lokacin batawa tayi soyayya ba kudin dai.
Da daddare ya gabatar da kudirinshi ga Gwoggo.... Kuzo kuga murna gurin baiwar Allah, nan ta dauki waya ta Fara kiran uncles dinshi akan wani satin zaaje nema masa aure, yadda take murna yasa zuciyar Musbahu karyewa ya bar gurin yana jin ya tsani Abinda yake aikatawa.! Sede wani kuskure daya da aka tafka Gwoggo bata saka an bincika wacece Khulthum ba Tunda tana ganin a nutsuwar Musbahu bazai kawo abin kunya ba, su kuma dangin Khulthum Dana ubanta Musbahu yayi musu girman da zasu bincike shi! Tirkashi
_Just a smile and the rain is gone, can hardly believe it... Yeah! There's an angel standing next to me reaching for my heart!_
Sun jima sosae a tsaye a gurin yana rungume da ita, yana bubbuga bayanta ita kuma tana ta hawaye a jikinshi. Kasa yayi da kanshi saitin kunnenta ya hura mata iska wadda tasa babu shiri ta saki ajiyar zuciya tareda kankame shi. A hankali ya kamo hannunta zuwa kan gadon da ta baro, seda ya zaunar da ita tukun ya janyo farar kujerar dake gefen gadon ya zauna Yana dubanta da idanunshi wanda Lokaci daya tayi Kasa da nata saboda bazata taba iya jurar abubuwan dake fita daga nashi idanun suna shiga cikin nata.
Dove! Kinsan how your tears are piercing my heart, inda Kinsan yadda nake jin kukanki tunanin zaki iya yin fushi balle kuka.
Hannunta tasa Wanda yasha lallai ta goge fuskarta tare da sakar mishi tattausan murmushi, lokacin ya lura da zanen henna hakan yasa ya riko hannyenta ya kura musu ido kafin ya fara shafa su cikin wani Irin salo da Hannunsa Wanda yasa su jin tamkar electrical current ake passing jikinsu, a hankali ta janye hannunta saboda abin affecting dinta yake sosae, langwabar da Kai yayi shima ya turo bakinshi yace
Rowa ba kyau!
Murmushi tayi ta rufe fuska da hannayenta, Tana jin mahaukacin farin ciki da bata taba mafarkin shiga Irinshi ba, hannun ta Mika mishi a hankali tace
How does it happened?
Tashi yayi ya dawo gefenta ya zauna, baki dayansu suna jin numfashin junansu, lafayar ya fara warewa har ya cire ta gaba daya sannan ya ajeta a gefe ya dago fuskarta ya kalleta yace
Dove! Kinsan me yasa nake kiranki Dove?
Kanta ta girgixa, ajiyar zuciya ya sauke yace
Doves are beautiful and very gentle, gentility dinki da kyau da Allah ya baki shi yasa kikai suiting da Wannan sunan..... I love you my Dove so much, na miki alkawarin kasancewa a tare dake Duk runtsi duk wuya, ba lallai ki samu farin cikin da kike tunani ba ko kuma kike mafarkin samunshi ba amma Inshaaa Allah xanyi iya bakin kokari na!
Hawaye ne suka gangaro mata tayi saurin kauda su, Tana jin dukkan damuwarta ta yaye dukkan wani kuncin ta Yana yayewa kamar evaporation na steam.
Lokacinda muka gama magana da Mami nace mata na hakura, I was shattered, I threatened her inason Tace min nazo ta bani ke amma haka raina a mugun bace na taho Kano, I was lucky duk yadda hanyar batada kyau amma haka Allah yasa na iso kano, se a cikin gari sannan bansan yadda akai ba kawai nasan munyi Karo shikenan. Se jiya Mami tace kin fita da yan Mintina na farka, I was lucky kaina ne kawai ya bugu amma brain din is OK, bacin rai da nake ciki yasa na zama unconscious. Gashi at least Bayan accident I was able to have you! I love you baby.
Hawayen dake mata zarya a kumatu ta goge ta bude Baki don yin magana ya hanata maganar ta hanyar hade bakinsu waje daya.
Washegari Misalin karfe takwas da rabi, akazo handing over, Junaid na zaune kan carpet yayinda Sulaim ke kwance kan gadon ta kudundune tamkar ita ce marar lapiyar a cikin duvet. Hirar da nurses din keyi da Junaid yasa ta farka ta yaye bargon Zuwa wuyanta tana binsu da kallo. Daya daga cikin nurses din tace
Amarya Anya jinya kike kuwa? Kin wullo mana patient kasa kin hau gado.
Dariya sukai Junaid yace
A'a sister Karki takura mata fa.
Dariya suka kuma Yi sister tace
Dariya take kamar ba ranar take ta kuka ba kamar ranta zai fita.
Haka dai aka gama sukai mishi Allah ya sanya alkhairi da fatan Karin lapiya. Suna fita ya rufe dakin da key sanann ya dubeta yace
Sakko Kije kiyi wanka.
Mika tayi bbau musu ta sakko ta nade blanket din ta gyara gadon sannan ta nufi bayi, ta jima tana wankan sannan ta fito da hijabi jikinta lokacin baya dakin, hakan yasa tayi saurin ciro kaya a jakar da Amma ta kawo mata, wata simple gown ce baka se inner wears dinta, Seda ta saka sannan ta shirya tayi shafe shafenta kafin ta gyara gurin, tayi kyau kamar ba ita ba, kofar ta nufa daidai lokacin Junaid ya sako kai ya bigeta tayi baya zata fadi yayi saurin tarota jikinshi. Ajiyar zuciya ta sauke ta biyo bayanshi suka Fara breakfast. Seda suka gama tsaf yace
Dove are you happy ko tursasa ki nayi kika aureni?
Da sauri ta girgixa kanta tace
I'm so happy that I can't express exactly how I feel, Amma nasan zaka fahimci how exactly I feel, felt and feeling and I love you so much!
Hannunsa ya bude mata babu musu tayiwa kanta masauki jikinshi!!!
*I lay my love on you, it's all I wanna do, every time I breathe I feel brand new, you open up my heart show me all your love and walk right through......*
Shatuuu ♥️
[9/2, 9:38 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU*
✍️SHATUUU♥️
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
#⃣shatuuu095@wattpad
Assalamu alaikum Sweerie pies..... how's Sallah fatan kowa yayi sallah lapiya? Amin.... Allah ya maimaita mana Dearies.
Inshaaa Allah zaku iya jina anytime from now, Allah ya karba ibadunmu. I've seen your comments and votes, Wallahi I can't ask for more... You guys are the best, I love you so very much.... Allah ya bar mu tare. Aci nama lapiya!
Shatuuu ♥️
[9/2, 9:38 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU*
41
✍️shatuuu♥️
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
#⃣shatuuu095@wattpad
Monday Morning
Mikewa yayi daga kan carpet din da yake Zaune akai Tun bayan Idar da sallar asuba yake Zaune a gurin yana tilawa, gaba daya a takure yake jin kanshi tamkar anyi chaining dinshi haka yakeji, ya gaji zaman asibitin nan Tunda shidai yanzun yasan lapiyarshi kalau babu Abinda Ke damunshi, amman baya son ya nemi discharge din Tunda su suka kwantar dashi suka San Meye matsalarshi.
Inda Dove dinsa take ya isa, ta kudundune cikin Duvet cover abinta se sharar baccinta take, Tunda sukai sallar asuba ta koma ta kwanta, gefenta ya zauna ya yaye cover din hakan yasa tayi juyi ta turo mishi karamin bakinta, murmushi yayi yace
Dove makaranta fa, is already six.
Bata fuska tayi ba tareda ta dago ba tace
Ni ba zanje ba gaskiya.
Idanunshi ya dan zaro Yana murmushi yace
Why?
Ni ba patient relative ba ce.
Wannan karan seda yayi dariya yace
Kinji ki da me kikeyi min? Come on tashi Kada ki makara.
Zumbura Baki tayi ta Mike Daga gadon Tana ta Bata rai tana fadin
Dama ba sona ake ba, if not me yasa zaace se naje school.
Dariya yayi kasakasa Yana shafa kanshi, shikam Allah ba karamin so yake mishi ba da ya bashi Sulaim, Tunda Mami da Baba suka mishi albishir bai kara daina murmushi ba, she gave him every reason to smile, she never cease to amuse him. Yarinyar tana tafiyar da soyayyar ta kamar yadda ta fada mishi xai gani gashi kuma yana gani. Seda ya linke Duvet din sannan ya fita don yasan bazata iya shiryawa ba idan yana nan. Masifar kunya ce da ita don common peck ya bata se tafi 10 minutes idonta a kasa. Balle kwanciya dama se ya bari tayi bacci sannan yake hawowa gadon ya kwanta idan ba haka ba ta dinga mutsu mutsu kenan.
Zama yayi Yana ta kallon yadda ake hadahada cikin asibitin, ita kuwa seda ta leko taga baya nan sannan ta fito ta shafa manta na Jergens ta fesa turarruka a jikinta sannan ta dakko wani lace zata saka ta tuna Monday ce yau black and white, hakan yasa ta maida ta dakko Bakar abaya Fara tas da Polk dots na baki a jikinta, powder ta shafa hade da balm ta kalla kanta tayi murmushi ganin yadda ta fito tayi kyau. Kanta ta taje ta gyara zaman ribbon din sannan tasa hula baka ta Fara gyaran dakin lokacin bakwai ta buga. Kafin ta leka kiranshi taji ya bude kofar ya shigo a nutse bakinsa dauke da sallama haka idanunshi kur a kanta yana jin wani sonta na fuzgar shi hade da nutsuwa cikin zuciyar shi.
Kan carpet ya zauna lokacin tana tsiyayo ruwan zafi Daga flask zata hada tea, tayi kicinkicin da fuska ita a dole fushi take. Tana gama hadawa ta zauna gefen gado ta Fara sha tana ciccin magani tare da kawar da kanta Duk kuwa da tasan kallonta yake, shima share ta yayi Yana murmushi ya maida hankalinshi kan newspaper da aka kawo mishi.
Seda ta gama ta dauki madaidaicin veil Baki me Polk dots farare mahadin Abayar jikinta tai rolling sannan ne ta dubeshi tace
Yaya zan tafi.
Kanshi ya dago tareda zare glasses din idonsa yace
Zo kiji.
Babu musu ta nufi inda yake ta sunkuyo, hannunta ya kamo ya zaunar da ita yace
Yayan akewa fushi? Da fushi zaki tafi school?
Kanta ta girgixa, kallonta yayi yace
To Kiyi min murmushi na gani mana tawan!
Murmushin ta sakar mishi hakan yasa ya janyota jikinshi tareda rada mata abu cikin kunne, kwace jikinta tayi tana dariya shuma yanayi yace
Kin yadda?
Kanta ta girgixa tace
No!
Zaki sani
Ya bata amsa kafin ya Mike ya dakko wata Leda me kyau yace
Amma tazo jiya Kina bacci tace na baki.
Karba tayi ba tareda ta bude ba ta Mika mishi tace
Ka aje min idan na dawo zan duba.
Kanshi ya girgixa yace
A'a kije kya duba a school.
Babu musu ta karba suka fito tare Yana ta tsokanar ta wai amaryar Asibiti, itama tana ce mishi angon Asibiti, a haka suka zo station din nurses ya dan tsaya yace zai rakata gate zata tafi makaranta. Sallama sukai suma suna ta tsokanar ta, har gate ya rakata inda Jawad ke jiranta cikin mota, Seda yaga ta shiga kafin ya juya yana jin kawarta cikin jikinshi da zuciyarshi, hakika Sulaim tanada kaso mafi girma cikin zuciyar shi.
Tana