Showing 93001 words to 96000 words out of 131263 words

Chapter 32 - MACE A YAU Document from Sulaim .txt

24 Nov 2024

4831

tayi masifar kyau. Gashinta tayi combing ta daura scarf baki sannan ta maida trolley ta rufe tana mitar rashin inda zata jeresu don yace mata zamanta gidan is temporary wannan gidan Subay'a ne, ai fadar Subay'a da yayi Harda kukanta hakan ya tabbatar mishi tsananin kishin da take dashi.


Ammiey!


Ta jiyo jin Ahmad na kiranta, da sauri ta zura flat milk vine ta fito don jin dalilin kiran da yake mata. Cikeda nutsuwa ta bude kofar parlon ta fito bakinta na fadin


Yaron Ammiey......


She couldn't finish the sentence saboda mutanen da ta gani a tsaye suma fuskokinsu tsoro, mamaki da tsana, Hajiya ce yes Hajiyan Subay'a! Surayya da Samina Sun sakata tsakiya. Wata muguwar faduwar gaba ta ziyarce ta amma haka ta hadiye mugun yawu ta nufo inda suke, Bata kai ga karasowa ba taji knocking a kofa, ba tareda ta zauna kamar yadda tayi niyya ba ta wuce don bude kofar, Junaid ne tsaye hannunsa rike da ledoji, kallonta ya tsaya yi saboda masifar kyau da tayi mishi don wannan ne Karo na farko da ya ganta cikin ireiren kayan, kayan ya aje ya rungume ta tsam tareda Daga ta sama yana juyi da ita, ita kanta yadda taga sonta me tsanani cikin idanunshi sam ta manta da ruwansu Hajiya cikin gidan. Se dan kanshi ya ajeta sannan ya jawo ta ciki, shima da fuskokinsu yayi arba wanda kana kalla zakaga tashin hankali da tsoro ya karu akan tsanar, mamakin da da suke ciki. Hannunta ta zare Tare da jansu Ahmad don kaisu daki Samina tayi saurin shan gabanta tace


Ina zaki kaisu? Karuwa ka......


Don't! Don't!! Don't you ever call my WIFE with that name, Matata ce aurenta Nayi kamar yadda na auri 'yar uwarku.


Kutmar uba kenan!


Fadin Samina wadda kirjinta har ya fara sama da kasa saboda yadda masifa ke Cinta dama copy din Suhaila ce idan bata nan to Samina ce substitute dinta.
Juyawa Junaid yayi ya dubi Sulaim wadda idanunta kamar su fado saboda firgici se ta bashi dariya saboda he has never in his life cikin wannan tsoron.


Kuje daki Dove Keda yaran.


Kanta ta gyada ta ja yaran suka wuce shi kuma ya zauna tareda Fara gaida Hajiya amma bata ansa ba tace


Junaid abinda idanuna da kunnuwana suka jiye min gaske ne ko kuwa? Aure kayi?


Kanshi ya gyada yace


Eh gaskiya ne Hajiya.


Wata ashar Surayya ta saki tace


Amma Junaid Bakada hankali! Wa kake tunanin a cikinmu zai zauna da kishiya? Subay'a Wallahi baka isa ba se ka saki waccen matsiyaciyar!


Har cikin ranshi yaji zagin da Surayya tayiwa Sulaim hakan yasa ya dago idonsa da suka Fara canza kala yace da Hajiya


Ki ja musu kunne kada wadda ta kara zagin Matata, yadda sukejin Subay'a 'yar uwarsu ce nima haka nake jin SULAIM








To fa people kunji wannan? Tun kafin Subay'a uwar Boko taji labari kenan! Inhar Samina zata iya haka on behalf of Subay'a then wanne mataki Subay'a zata dauka a karan kanta? Let's go people.....




shatuuu ♥️ *MACE A YAU*
43


✍️Shatuuu♥️


🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION


#⃣Shatuuu095@wattpad






Hajiya ta riga ta sanya wa zuciyarta duk yadda takai da takatsantsan akan abu to se ya faru musamman kan Subay'a wadda duk cikin 'ya'yanta ita ce me bata matsala saboda son da takewa Junaid. Numfashi ta fizga tare da duban Junaid tace


Amma ka taba ganin anyi aure ba'a sanar da Matar gida ba, me yasa gaba daya maza Bakuda adalci? Bakuda alkawari? To Wallahi 'yata bazata zauna da kishiya ba, ban zauna da ita ba haka babu Wacce a cikinsu zata zauna da ita!


Kallonta yayi a ranshi Yana bakin cikin kasancewar yaranshi sun fito daga tsatsonta, bai taba ganin sallamamiyyar uwa ba Irin hajiya ba, kallonta ya karayi har bazai bata amsa ba se kuma yace


Wanda bai yiwa wani adalci ba, Hajiya ta ina yake tsammatar ayi mishi adalci. Aure na riga nayi shi, idan zata zauna kanta idan ba zata zauna ba aure mutum biyu ke yinshi zata iya tafiya babu damuwa! Zancen baki zauna da kishiya ba wannan tsarin Alhaji ne ni kuma nawa tsarin shi ne aje mata biyu a gidana.


Idanu waje Hajiya take kallon Junaid kamar taji yace Subay'a can go, itakam Tunda ta Fara haduwa da Junaid matsayin siriki abubuwata ke lalacewa.


Mu zuba mu gani!


Murmushi yayi yace


Allah ya kiyaye hanya, gashi ko ruwa baku sha ba.


Yana sane yayi furucin don ya kara tunzurasu, aikuwa Surayya ta juyo Tana fadin


Bazaa sha ba, Kaga mun zo maka a tsiyace, Allah ya kiyaye Wallahi.


Dakyar ya iya controlling dariyar da tazo mishi, hajiya haka jikinta a sanyaye ta fito suka mara mata baya, suna shiga mota Samina ta dakko waya don sanar da Subay'a halin da ake ciki, hajiya ta kwace wayar ranta a mugun bace tace


Kada wanda ya sanar mata halinda ake ciki, taje ta dawo ta samu abinda ta bari, ba ita mai biyayya Ba? Tafi kowa bin miji se ta dawo ta tarar da sakamaakon abinda ta bari.


Surayya hankali tashe tace


Haba Hajiya ta yaya? Babu Abinda zamui mata kenan?


Me zaki mata? Mijinki ne? Duk yarinyar da na aurar se nayi mata kokarin da babu macen da zata kara burgeshi amma bansan inda subay'a take Kai Nata ba.


Wani abu da Hajiya bata sani ba, itafa Subay'a su kadai take nunawa tana bin miji sau da kafa hatta Abinda suke bata na kayan gyaran mata ba sha take ba wasu lokutan idan suka taru flushing dinsu take, kuma se ranar da ta ga dama sannan take Zuwa turaka wasu lokutan se tafi sati bata je ba.


Ina ganin lokaci yayi da zanbi shawarar Hansa'u.


Wacece Hansa'u?


Surayya ta tambayi Samina wadda a lokacin mafita kawai take nema.


She's a neighbor, wajen wani malami da take Zuwa nan zamuje a raba auren, don indai ina numfashi cikinmu babu Mai zama da kishiya.


Kada na sake Naji, ko by mistake wata taje gurin boka to ban yafe mata ba, boka idan yana maganin matsala shi yayiwa kanshi mana.


Turo Baki Samina tayi jin furucin Hajiya, tace


Bafa boka bane hajiya Malam ne.


Ubanki nace kinji! Akan duniya zaki salwantar da lahirar ki, ni dai Allah ya sani ban taba kai kukana wajen wani ba kuma ban yadda wata takai ba, idan har kissa da kisisina ba zata zaunar daku ba, to duk Ku kashe Auren kuzo mu hada kafada. Kuma na maimaita Kada wanda ya fada mata halinda ake ciki!


Tunda ta furta hakan kowa yayi shiru har suka isa gida. Acan gidan Junaid ya jima Zaune a parlour yana mamakin zuri'ar su Subay'a, gabaki daya babu hankali a cikin su, dukkansu taron tsintsiya ne babu Shara.


Sulaim na zaune kan kujera ta kammalla koyawa Ahmad homework dukda hankalinta baya jikinta, ko kallonta kayi kasan a tsorace take, a haka Junaid yayi sallama ya shigo, idanunta ta dago Tana kallon shi kamar yadda yake kallonta, Yana Zuwa inda take Zaune yasa hannunshi ya rankwashi kanta, da sauri ta Mike hannunta akai Tana turo Baki tare da kwabe fuskarta saboda zafin rankwashin har brain dinta. Bata fuska yayi yace


Wuce muje ki bamu abinci Tunda ke matsoraciya ce, kin tsaya Kina zazzare ido saboda su samu gut din Yi muki abu ko?


Banza tayi mishi ta kamo hannun yaran Don fita ya fuzgo ta, ta fado jikinshi, rungumeta yayi ta Fara kokarin kwacewa har tayi nasara don kuwa bai saka karfi ba, kallonshi tayi tace


Ahmad fa suna nan.


Bakinshi ya tabe Irin who cares dinnan ya wuce ya barta a wajen tana zumbure zumbure. Tunda ta dawo daga kwantar da yaran take fushi kamar yadda ya zame mata alaada, ko kallonta baiyi ba don abu biyu ne zai hanashi having dinta that's if she's on period se kuma wani kadari daga Allah amma yau night dinnan is all about him and her.


Agogo ya kalla yaga Tara tayi hakan yasa ya dubeta yace


Dove bacci zanyi.


Kallon time tayi sannan tace


Ni kuma kallo zanyi.


Harara ya maka mata yace


Get up muje, wayace miki ana barin miji ya kwanta shi kadai? Ko dan yi zamanki Kiyi kallonki zanyi waya da Matata.


Wani Dam taji a kirjinta saboda ambatar matarshi da tayi, da sauri ta Mike ta kashe komai sannan tayi gaba, shi kuwa me zaiyi banda dariya, lallai Sulaim at 19years har ta iya kishi. Yana Zuwa ya tarar har ta canja kaya Zuwa na bacci, wata silk Riga ce me hannun vest iya cinya se tight da ta saka a ciki Zuwa gwiwarta ranta a bace ta haye gado, shi ya rasa hadin Sulaim da bacin rai. Seda ya kammalla komai da ya saba kafin ya hayo gadon lokacin tana waya da Mami, yana zuwa ya jayota jikinshi tareda Fara zuba mata kiss wanda yasa ta saki wayar babu shiri saboda wani moan da keson escaping Daga bakinta saboda kiss din ba na wasa bane, bakinta ta bude da niyyar protesting kawai taji ya hada bakinsu ya fara bata wani kiss wanda Lokaci daya ya rikita jikinta da kwakwalwar kanta, Ta manta ita wacece, me take so da Maye bata so, what exist lokacin a duniyarta is only Junaid and nothing else. Seda ya tabbatar ta gama fadawa trap dinshi kafin akai me gaba daya.


Wayyo wayaga bakin kuka.... Lol.... Tasha kuka kamar ranta zai fita, Seda ya nutsu don kuwan ita babu nutsuwa a tattare da ita kafin ya fara lallashinta amma ina se kara birkice mishi take tana kara rikita mishi lissafi. Kawai jikinshi ya sakata ya rungume Yana patting bayanta don duk yadda yaso bude bakinshi he couldn't bazai iya ba, Abu daya ya sani he will never let go of her, she'll forever remain in his embrace till death do them apart!


Washegari fuskarta tayi jajawur ga wani wahallen zazzabi da ya rufe mata jikinta, ga bacci da take ji tamkar idanunta zasu rufe, ga jikinta ciwo yake mata amma haka ta mike a daddafe Bayan taji fitar Junaid massallaci saboda bai tashe ta ba dan ta huta. Bandaki ta shiga ta tara ruwa kamar yadda Yaya Imratu ta sanar mata lokacin har wani dariya takeyi saboda tana ganin babu amfanin hakan. Sitbath tayi sosae taji dan karfi ya dawo mata kafin tayi wanka tayo Alwala ta fito ta tada sallah. Tana idarwa wani bacci ya fara fizgarta amma haka ta daure ta Mike ta Nemo wata Abaya coffee me karamin hannu tasa hula sannan ta fito jinta take tamkar wata sabuwa, wani nauyi ya hau kanta, zuciyarta wasai babu wani kunci idan ka dauke bacci da Ciwon jikin dake damunta. Tana isa kofar Dakinsu Ahmad Junaid na shigowa Fuskarshi kadai zaka kalla kasan yana cikin madaukakin farin ciki wanda yaki boyuwa saboda yadda Junaid din ke ta murmushi.


Tana jin sallamar shi tayi saurin tura dakin ta shige saboda azababben kunyar shi da take ji, binta ciki yayi ya tadda ta Tana tsaye Tana lallashin Muhammad dake kukan da ya saba na duk safiya. Gadon Ahmad ya zauna akai yana kashe Sulaim da wani kyakyawan kallo wanda Seda taji butterflies suna yawo cikin cikinta, dauke kanta tayi don Bata son tuna Abinda ya faru jiyannan. Yana nan Zaune har ta gama Abinda zatayi batace dashi komai ba haka shima Sede duk inda tayi to zai bita da idanunshi, kuma yana iya hango yanayin da take ciki.


Tana barin dakin ya mara mata baya, se yaga ta nufi kitchen hannunta ya riqo hakan yasa ta dago a wahalce tace


Yaya girkin su Ahmad fa!


Your only concern is Ahmad and Muhammad, what about yourself? You need a break Bana son musu.


Babu yadda zatayi haka ta bishi ya kwantar da ita bayan ya bata tea Tasha, aikuwa bacci me nauyi ya dauketa, bata farka ba se 12pm sannan ta Mike Tana jinta wasai, fayau tamkar iska zata dauke ta. Babu kowa dakin hatta gidan yayi shiru, wanka taje tayi a ranta tana jin son Junaid Yana bin dukkan jikinta, Tana jin tamkar task ne daya kamata tayi completing yanzun ta Gama, dukda Tasha wahala jiyan nan Amma bataji komai na takaaicin Junaid ba se ma sonshi da yake kara huhhuda jikinta yana zagaye cikin blood dinta.


Wannan ranar ta dauki alkawari me nauyi akan duk runtsi duk wuya da izinin Allah se ta kawo mishi farin ciki wanda bai taba mafarkin samu ba, tayi alkawarin biyayya matsawar ranta sannan kuma zata soshi no matter the hardship, the situation and the circumstances!


Lace ta dakko purple da peach me circle pattern dikin gown me kyau, dankwalin ta daura tayi kwalliyar ta daidai misali sannan ta zauna ta kira Mami suka gaisa kafin ta fito parlour, yana zaune kan kujera yana aiki cikin computer dinshi, gabanshi ya aje takaddu da ruwa an tsiyaya cikin tumbler. Dagowa yayi don ko batai magana ba yasan ta iso gurin, jikinshi ya fada mishi sannan kamshin turaren ta na Zahrat Banafsa ya isar da saqon. Shutting system din yayi tareda ture table din daga gabanshi ya miko mata hannunshi, babu musu ta Kama har lokancin idanunta a kasa. Rungume ta yayi sosae tamkar zaa kwace ta, bakinshi yakai kunnenta yana fada mata kalmomi masu tsananin tsada, ya fada mata yadda Daren jiya ya kasance. Ranar haka ta Kare suna tattalin juna, wata sabuwar chapter aka bude cikin gidan!


Bari mu leka muji yadda amaryar TitαΦ ke ciki, Hajiya Khulthum ikon Allah!


Cikin dankareriyar Prado baka wuluk Hajiya Nana da Hajiya Rafi'a wanda suka kasance kannen Gwoggon Musbahu ne. Su biyu kadai ta wakilta don suje kawo lefen Khulthum don Tunda ta samu labarin yarinyar yar talakawa ce yasa bata son hada mutane saboda zance da surutai, to suma a gurin nasu bata tsira ba. Nana ta Fara fadin


Nikam Yaya Rafi'a Bakiji abin so strange ace Musbahu ya rasa duk fadin duniya inda zai aure se cikin ghetto?


Tabe Baki Rafi'a tayi tace


Bari dai Nana, Nifa haka kurum ban yadda da Musbahu ba totally. Kinsan yanzun he's 36 Amma ko sau daya bai nuna alamun mace na burgeshi ba, kullum idanunshi cike suke fal da tsanar mata kuma yasha furta hakan coincidence inaji baisan ina gurin ba.


Hmmm Kede Bari Yaya, Wallahi the same thing da nake gani amma uwarshi tace aljana ta aureshi.


Dariya suka kwashe da ita tareda tafawa sannan Nana tace


Ai Allah ya hallici soyayya da feeling tsakanin mace da namiji so Duk yadda ka kai da kamewa ko kuma me zance dole ne saboda wannan is in blood!


Balle shi Mai kudi ba!


Haka sukai ta hira har suka iso gidan inda suka tarar mota da kyar take shiga layin. Haka driver ya kutsa ta Baya sannan suka samu ta wuce. Immediately suka Fada gidan don Nana fadi take Allah ka rabamu da ghetto! Rafi'a tace


Allah ya rabamu tuntuni se wanda suka debowa kansu.


Gidan cike yake dam da mutane da wanda aka gayyata da wanda sukazo ganin kwakwaf ai kuwa sun gani ba kadan ba, don kuwa anyi lefe har na rashin hankali, kudi sunyi kuka da idanunsu. Daxasu tafi suka ki karbar komai haka suka wuce, se ga uwar gayya tazo tayi wani Irin kyau tamkar ba ita ba saboda tuni ta Fara gyaran jiki don tasan inda zata shiga she doesn't mind Abinda ta kashe tasan zata fanshe. Ihu, habaici ranar tayi shi dakayar tayi bacci saboda kallon kaya bata taba tunanin zata samu haka ba. An saka ranar biki Nanda sati biyu masu Zuwa..... Se muce Allah yasa munada rai!!


Cyprus.


A hankali suke takowa saman titin da ya malale ko ina cikin makarantar. Subay'a tayi fari, tayi kyau kana kallonta kasan Hutu ya samu gurin zama. Somehow dai hankalinta a tashe yake dukda yawan kwantar mata da hankali da Sulma keyi saboda rashin daga call dinta da Junaid yake.


Inajin karshen month dinnan zan tafi nigeria gaba daya sati biyu nan inajin tamkar akwai Abinda akeyi acan, yanzun gaba daya Junaid nake son gani sister.


Sulma dake saurarenta tace


Haba dai, amma lokacin ai kun kusa exams a department dinku.


Tsaki tayi tace


Na gaji da karatun Wallahi, tunda naxo banida kwanciyar hankali karatun duk simplicity dinsa amma Wallahi bana ganewa, Meye amfanin shi? Is better na koma na daidaita gidana na daidaita rayuwar aurena Sister, I've messed so much, nasan nayi wasa da damata, Junaid yayi kokari yanzun haka zan koma na gyara Abinda na bata.


Ta fada with sincere repentance cikin muryar ta. Sulma dake saurarenta tace


Hakane kam amma Tunda har Munzo yanzun inaga kiyi hakuri Zuwa yadda aka tsara se mu koma duka ko?


Kanta ta girgixa tace


Bazaki gane ba Sister, alhakin Junaid, Ahmad da Muhammad Wallahi bazai barni ba, is better I go back and amend whatever I torn. Is never late sister.


Haka suka ta hira duk yawanci Subay'a ke tsare tsarenta har suka isa gida. Seda Subay'a tayi sallar ishai kafin ta kwanta yau batajin fita ko ina Tana son shiga social media taji me ake fada ne, meye latest. Data ta kunna ta kifar da wayar Don komai ya gama shigowa, seda ta kammalla kafin ta Daga wayar ta Fara da whatsapp inda tayi replying messages dinta kafin ta koma IG. Tana shiga da stories din Junaid ta Fara cin Karo, seda gabanta ya fadi don ita ta bude mishi IG kuma baya ma wani amfani dashi Amma what's so important daya daura. Daidaita kwanciyar ta tayi, ta rike wayar a hannunta tana jiran su bude Se idanunta suka sauka akan caption din dake rubuce


#My Dove# the love of my life.... The best thing that ever happens to me.... I so much love you habibty♥️


Tana karasa karantawa take hotunan suka bayyana, tamkar tashin bomb haka hotunan suka Dakar mata zuciya, hotunan biki ne na kowanne event se wanda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login