Showing 69001 words to 72000 words out of 131263 words

Chapter 24 - MACE A YAU Document from Sulaim .txt

24 Nov 2024

4836

new hospital road ya kaita yayi mata order pizza slice biyu, Dakyar ta cinye Daga nan yace mata


Ina kike son Zuwa kuma?


Shiru tayi tana tunani kafin tace


Cinema!


Kanshi ya shafa yace


Shi ne inda kike son Zuwa?


Kanta ta gyada tana murmushi, agogon hannunsa ya kalla lokacin hudu tayi hakan yasa ya tsaya yayi sallah batace zatayi ba shima bai ce mata ba don Abinda yayi believing ba yadda za'ai ka cewa mace tayi sallah kilan tana off.


A cinema shoprite sukaje ya tambayeta na wanne kasa tace India. Can sukaje bayan ya karba mata popcorn se tace


Kai kuma fa?


A'a na Ciwon Kai ne wannan ai, Ke kadai zaki ci abinki.


Murmushi tayi ta cigaba da bin bayanshi har suka karba ticket ana shooting Goliyinka Ram Leela Ras Leela. Bata taba kallon film din ba amma tasan famous wakar film din, suna ta kallo ko ita kadai takeyi don shi hankalinshi Yana kan wayarshi seda aka kusa yaji alamar sheahekar kuka, da sauri yace


Oh God! Meye kuma na kukan?


Hannunta tasa ta goge fuskarta tace


Sun kashe kansu fa?


Su waye?


Ram da Leela na film din.


Tsaki yayi yace


Tashi mu tafi.


Mikewa tayi ta bi bayanshi ba tareda ta ce komai ba, gaba daya se yaji ranshi ya baci if at all yasan cewar ranta zai baci Wallahi bazata kalla film din ba. Duk kokarin ganin ya faranta mata rai haka kurum wani fiction yazo ya bata mishi komai.


Basu suka koma gida ba se bayan sallar ishai seda ya tabbatar ta samu farin cikin da yake son ganinta a ciki, babu ko digon damuwa cikin kwayar idanunta kafin suka nufi gida amma abin mamaki duk wannan abin ya kasa Furta "L" word din.


A parlor Subay'a na zaune da Ahmad se Muhammad da ya sata a gaba yana kukan shi Anty zaije, Tun tana lallashinshi har ranta ya baci ta daddake shi, nan Kuwa ya kara Sautin kukanshi, abin ya dameta ga Junaid bai dawo ba, ga tsanar sulaim dake kara nunkuwa cikin zuciyar ta, ga tsoron yadda zata tunkareshi da maganar nan. A haka suka shigo gidan, rigerigen taro Sulaim Ahmad da Muhammad sukai, ta tsugunna ta rungumesu jikinta tareda daga Muhammad sama ya fara dariya sannan ta riko hannun Ahmad zuwa cikin parlour. Zama tayi ta dubi Subay'a dake kallonta tace


Kun dawo lapiya?


Lapiya.


Ta bata amsa Tana bin bayan Junaid, tabe Baki tayi ta dauki yaran zuwa dakinta, seda ta shirya su tsaf kafin ta shirya itama don bacci amma taji an turo kofar, fitila ta kunna da mamakim ganin Subay'a tsaye Tana kallonta, itama kallanta tayi batace mata uffan ba, se dan kanta tace


Yarana fa.


Gasu


Sulaim ta bata amsa, aikuwa ta karaso da nufin daukar Muhammad Yana bude ido ya fara ihun shi gurin Anty zai Kwana haka Ahmad dole ta hakura ta koma gurin Junaid wanda tuni yana gado yana aiki da system gefenshi ruwa ne kan table Yana Sha time to time tareda murmushin tuno Outing dinsu, se yakejin tamkar they went for a date. Gefenshi ta zauna tareda mika mishi envelope tace


Papa gashi.


Ture system din yayi ya bude envelope din, visa dinta ce ta zuwa Cyprus se wasu takaddu na makarantar da zataje masters din. Glasses dinshi ya cire yace......




Shatuuu ♥️


*MACE A YAU*
31 nd 32
Double page




✍Shatuuu♥


🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION


#⃣Shatuuu095@wattpad


Zare glasses din idonsa yayi ya aje papers din kan table din sannan ya dago ya aje maida hankalinshi kanta, ya kusan minti biyar Yana kallonta tareda nazarin yanayin da take ciki wanda hakan Ke Kara mata uneasiness a tattare da ita, kafin yace


Explain yourself


Dago idonta tayi rashin gaskiya da tsoro karara a idonta, tamkar ba Subay'a ba haka ta koma.


Hajiya ta aiko min jiya akan gobe da safe zamu wuce Abuja mu tashi zuwa Cyprus. Two years ne program din, zan na dawowa every six months. Kuma ni, Sulma, ya Suhaila da Yaya Salima Zamu tafi.


Ta fada Tana kawar da kanta , kanshi ya girgixa yana Kara mamakin Subay'a, da gaske ita hankalinta ya bata ta tafi ta barsu kenan. Ya dade bakinshi a rufe yana harhado kalamun da suka fi sauki ya mata magana dasu domin already cikin ranshi ya fara baci, baisan me Subay'a ke nufi dashi ba, baisan me ta dauki aure ba gaba daya.


Idan kika tafi, a hannun wa kika barwa ni da su Ahmad? Ko marayu kike son mu zama?


Ya fada Yana kara kallonta, inda baisan wacece Subay'a ba da zaice tana da gaskiya Amma Subay'a crook ce, kasa bashi amsa tayi ita dama Abinda bata so kenan a Junaid tambaya, idan ya tsareka da ido ko kana da gaskiya se ka duburburce hakan yasa indai zasui irin wannan maganar tafi son se ta shirya kafin ta sameshi. To Amma yau abin is different and seems difficult, kuma tun safe take harhada abubuwa da zata fada mishi.


Bakida amsa right? Kinsan dalilin da yasa nake daga miki kafa akan abubuwan da kikeyi?


Bai jira amsarta ba ya cigaba da fadin


Saboda wasu lokutan tursasa ki ake akan Kiyi abu, ke kuma babu yadda zakiyi tunda haka kika tashi kika tarar anayi a gidanku. Wannan karan nasan kin raina ni Baki dauke ni a bakin komai ba don ina tantamar idan kinsan me kalmar aure take nufi, me kuma ta kunsa.......


Da sauri ta katse shi da fadin


Nace maka fa yau suka kawo min, bansan da maganar ba kwatakwata.


Dago kanshi yayi yana dubanta Cikeda mamaki yace


Se Yaushe xaki daina karya a rayuwarki? Duk Abinda kike babu Wanda bansani ba, maganar masters dinku ke kika Fara bawa Hajiya shawara akan kuje Cyprus ko ba haka akai ba? itama ta biyeku tayi. Saboda kin raina ni for more than four months da maganar se ana gobe zaku tashi sannan zaki fada min? Kece mijin ko ni?


Shiru yayi ya dafe kanshi saboda zuwa lokacin ranshi ya gama baci, mijin Sulma ya kirashi ya sanar dashi abinda ya faru, tun lokacin yake jiran ta fada mishi don yayi niyyar barinta inda ta fada mishi a lokacin amma serves her right, don yana son nuna mata wannan karan tayi karya shike aurenta ba ita ba.


Papa Dan Allah na amshi laifi na, amma kar ka hanani tafiya asarar kudi zaayi kuma hajiya.....


Shi yasa bazaku taba zama gidan miji ba, ni Nake aurenki ba hajiya ba, a yanzun I've every right over hajiya a kanki, zancen asara I promise to refund abinda ta kashe buri na kawai ki zauna a gidanki.


Kanta ta girgixa tace


Papa please


Murmushin takaici yayi ya zame Daga Zaunen da yake ya kwanta tare da juya mata baya yace


Idan kin tashi fita Kunna min AC, ki sani in har nine mijin, ni na aureki, ni Allah yace na shygabance ki ban amince ba amma zaki iya tafiya sede.....


Bai karasa ba ya saki murmushi. Itama Ta sani Tunda ya fadi haka to bazai sake magana ba, to zaman me zatayi? Ita tana cikin tsaka me wuya Don kuwa Hajiya tayi rantsuwa akan kowa se Yaje yanzun ita kadai ce matsala haka ta mike jikinta a sanyaye ta fita zuwa dakinta. Ta dade a tsaye Tana kallon kayan da tayi parking cikin trolleys, kayansu Ahmad da ta hada musu. Zama tayi gefen kujera tana tunano zancen su itada Junaid tasan gaskiya ya fada bata taba zama matar kirki ba ko uwar arziki, ita a duniya aikinta shi ne priority dinta not her family amma tasan tafiyar ta Zuwa Cyprus dole ce, tasan halinshi da ta tafi zuciyarshi zata huce babu Abinda zai iya mata Don sabonta ne ya hanata Abu ta tsallake amma wani bari na zuciyar ta gargadi yake mata da babbar murya akan Kada ta tafi.


Junaid Na kwance idanunshi rub a rufe amma ba bacci yake ba, haushin kanshi yake ji yana jin duk Abinda Subay'a takeyi kamar dukka laifinshi ne, ya tuna yadda Tun yana nemanta Mami ta nuna kin amincewa saboda ance uwarta tana juya ubanta Amma lokacin ba karamin so yake ma Subay'a ba haka Daddy Aminu yayi fadi tashin ganin kowa ya amince sunyi aure saboda yana yawan fadawa Junaid "Tarbiyyar da nayi maka, inason ka zama tsayayyen namiji wanda son mace bazai Kada shi ba, ya zamana kai ke ruling gidanka ba matarka ba" amma gashi yayi failing to the extreme kuwa. Yasan Matar da ya aura, mutane ne dukkansu masu son duniya hakan yasa duk tafiyar da zaiyi zai tafi da ita don ta kashe kishirwar da takeji amma bai tsira ba, shi kuma in har ta tafi se yayi mata hukuncin da yasan har ta mutu bazata taba mantawa ba.


Washegari, babu Wanda ya fito a cikin su biyun, Sulaim ce kadai take ta kokarin shirya su Ahmad da kanta zuwa makaranta. Tana gama shiryasu tace


Kuje ku gaida Mimi da Papa.


Suka fice ita kuma ta karasa gyara dakin ta fitar da kayan wanki sannan ta hada abinci Se Gasu sun fito dukkansu har Junaid da Subay'a, gaisheku tayi sannan suka Fara cin abincin. Suna gamawa Junaid ya koma daki don ya dakko key da briefcase su tafi, itakam Subay'a zama tayi ta janyo yaran ta rungume wannan tayi kissing wancan idanunta taf da kwalla. Sulaim ce ta Fara fitowa suka hada ido da Subay'a kowacce seda gabanta ya fadi, sulaim ta Fara dauke kanta yayinda Subay'a ta kura mata ido zuciyarta na fada mata tafiya zatayi ta bar mijinta da yarinyar nan? Bayan Abinda take zargi tsakaninsu. Se tayi murmushi kawai saboda ta tuna waye Junaid, meye matsayinta a zuciyarshi.


Yana fitowa ya mikawa Sulaim briefcase dinshi da key din motar yace


Ku jirani gani nan Zuwa.


Amsa tayi ta ja yaran waje yayinda ya dubi Subay'a yace mata


Zan wuce office, na bar miki kudi akan decoder na cefane, bazaki je office ba?


Kanta ta girgixa ta taso ta rungumeshi tare da furta


I'm so sorry and I love you.


Shima rungumeta yayi Yana murmushi yace


Is ok ya wuce, I've to go.


Sakinshi tayi Bayan ta bashi peck a kumatu ya fice saboda kukanta na karyar mishi da zuciya. Yana Zuwa suka wuce, kamar ko da Yaushe seda suka kai su Ahmad school kafin suka wuce,


Sulaim


Ya fada cikin muryar daukar hankali, Dago kanta tayi ta dubeshi tace


Na'am.


Kallonta yayi Yana tantamar Abinda zai fada mata amma yana ganin is high time ya kamata ya fada mata. Jin yayi shiru yasa ta maida kanta gefe Sede abinda kunnuwanta suka jiyo mata yasa cikin hanzari ta dubeshi daidai lokacin da yayi parking don tabbatar da furucin daga bakinshi ne ko kuwa, kallonshi take kamar yadda yake kallonta, Sede kowa da Irin wanda ke cikin idanunshi. idanunta sunyi haske gashi ta bude su wanda hakan yasa yaji ilahirin jikinshi ya mutu, a hankali ya bude Baki yace


Ba se kin amsa ni yanzun ba, I want to you to think over it. Amma ki dauke kasancewa ta cousin dinki ki dauka ni Baki sanni ba kawai na ganki ne nace *INA SONKI, ZAKI AURENI?*


Da sauri ta kalleshi mamaki fal fuskarta, a take wani murmushi ya kwace mata, idanunta cikin nashi tana jin wani nishadi na daukarta se kuma ta sauke idonta a hankali kafin ta lalubi murfin motar ta bude ta fice dukkan jikinta a sanyaye. Yaya Yana sonta? Tambayarta yake zata aureshi? Yana son ta completing puzzle din da ya kasa? farin ciki se take jin tsoro Yana shigar ta, Me yasa bata amsa mishi ba. Tafiya take a hankali Cikeda nutsuwa ta isa class zuciyarta cunkushe haka kanta yayi mata nauyi Tana son tayi tunanin dalilin da zaice yana sonta.


Can bayan class ta zauna ita daya saboda yau bata da raayin jin lecture din gaba daya, Tana nan Zaune taga shigowar Aimana hakan yasa tayi saurin Dukar da kanta dan kar ta ganta, Seda ta zauna sannan ta dago kanta Sega Khairi sun shigo itada roommate dinta wata Amina, bata ga shigowar Khulthum ba kawai ta hango ta acan gefe itada wata Maimuna suna hira. Hakan ya tabbatar mata Khulthum tayi nisa Tunda ta Fara ma'amula da yarinyar saboda tayi kaurin suna cikin faculty akan iskanci kuma yarinyar ta samu kyakyawan backing na lecturers din da take bi, to dama idan Khairi na basu labarin yadda yarinyar take abu a hostel se Khulthum tana kareta OK gashi yanzun tayi joining dinsu.


Sagay ne dasu kuma very strict mutumin yake Tunda ya shigo class din yayi tsit, itama shiru tayi hankalinta Baki daya baya cikin class din tayi nisa sosae gurin tunani tabbas Tasan tana son Junaid so kwaya daya tak nashi ne amma bata taba tunanin he feels the same way ba, bata taba wannan tunanin ba. Ji tayi an buga table din dake gabanta hakan yasa ta dago da sauri, Sagay ne a gabanta ita bata san yazo ba ma kwatakwata ba she was deep in thought. Cikin karaji yace


Stand up and get out of my class !


Babu musu ta mike bata ma ce mishi ko yayi hakuri ba saboda tasan shi office din Junaid, suna yawan haduwa. Jakarta ta dauka ta fice baki daya daga class din sede tana fitowa sukai kicibis da Junaid wanda yake kokarin wucewa. Tsayawa tayi kanta a kasa gabanta nata faduwa, shima kallonta yayi yace


Ina zakije?


Kanta ta girgixa tace


Koro ni yayi?


Me kika Yi?


To anan tayi shiru don batasan me zatace mishi ba, bata concentrating ko kuwa? Ajin ya nufa hakan yasa tabi bayanshi suna zuwa yayi knocking dan ya Riga ya kulle kofar. Budewa Junaid yayi ya tako har gaban Me Sagay, da sauri ya sakko ya mikawa Junaid hannu suka gaisa Cikeda girmamawa don he seniors him. Kallon kofar yayi ya yiwa Sulaim alamar ta shigo, aikuwa ta shigo tayi kicinkicin da fuska, kallonta Junaid yayi yace


I'm sorry na shigar maka abin class dinka.


Kanshi ya girgixa yace


Ba damuwa sir, she wasn't concentrating that's why na Kore ta amma taje ta zauna.


Kallon Sulaim yayi yace


Go and sit down.


Kanta ta gyada tace


Thank you sir


Batareda ta kalli Junaid ba ta wuce gefen Aimana ta zauna amma da ta Fara kokarin concentrating se ta koma tunanin Junaid haka period din ta kare bata tsinci komai ba. Ita a karan kanta tayi tunanin idan Junaid yace yana sonta wanne irin farin ciki zata shiga amma se gashi tsoro ya hanata sakat, ta kuma rasa tsoron da take amma tana jin kada shima ayi irin ta sauran mazan. Babu yadda Aimana batayi ba akan taji abinda Ke damun Sulaim din amma fir taki, suna nan Zaune junairu ya kirata, seda taji gabanta ya fadi kamar bazata dauka ba se ta dauka ta kasa magana se shi ne yace


Kizo office Ina jiranki.


Sauke wayar tayi tace da


Kuzo muje office din Yaya.


Mikewa sukai dama tuntuni Khairi ke mitar dama Dr Junaid ne Yayan amma ita ba'a fada mata ba. Dariya kawai Sulaim tayi tace


Gashi yanzun kin sani.


Suna tafe Aimana tace


Wai ni Khairi ya akai kika san tsakanin Khulthum da Salim ne?


Tabe Baki Khairi tayi tace


Rabu da yan iska, kinga ta bi Sahun su Maimuna ko?


Sulaim tayi dariya tace


Ke Khairi ina ruwanki? Meye naki haka ta zabarwa kanta, nima fa na gansu a see sweet am sure ranar da ya bata lift suka hade.


Kai Aimana ta girgixa Cikeda mamakin Khulthum tace


Ban taba kawowa zata iya abinda tayi ba, Allah ya shirya kawai.


Daga haka suka rufe shafinta suka fada hirar idanun Sulaim lokacinda Sagay ya koreta,


Kinsan yadda na tsorata kuwa? Har cikin kaina Seda naji ihunshi.


Aimana tace


Tambaya ya dinga jero miki Ke kuma se murmushi kike kamar wani yayi proposing.


Dariya suka sakeyi hakan yasa Sulaim jin dadi dadi a ranta, suna isa suka shiga dukkansu suka gaisheshi ta nuna musu kujerun suka zauna, Inda yake ta nufa ta zauna kujerar dake facing dinsa tace cikin sanyin murya Tace


Yaya ina yini.


Aje pen din hannunshi yayi yace


Zauna mana.


Zama tayi cikin nutsuwa wanda yake burgeshi yace


Se 4 zaku tashi?


Kanta ta gyada tace


Eh.


Key din motar ya mika mata yace


Gida zan tafi, ki taho kawai.


Kafada ta girgixa tace


Kaje da ita ni zan biyo Aimana.


Sure?


Ya tambaya murmushi kwance a Fuskarshi yau Yana jin shi daban da kowa Yana jin tamkar babu Wanda ya tashi da saa kamar shi a wannan ranar. Itama ganin yadda yake ta murmushi yasa ta sake jikinta, ranta fal farin ciki duk wannan fear da take ciki dazu yanzun babu kuma in dai zata cigaba da ganin tarin farin ciki a Fuskarshi tana ganin babu abinda zai hana ta kasance tare dashi har abada.


Junaid Suna fita ya shafa kanshi tareda mikewa ya dauki abinda zai dauka ya cewa messenger dinshi duk wanda yazo yace dashi ya wuce gida. Yana shiga motarshi ya fice Seda ya biya ya dakko yaran kafin ya nufi gida haka kurum yake jin something is not in place Amma ya kasa figuring me Nene. Haka suka isa gida sunata tsalle shikuma Yana dariya, yaran kansu are happy Amma a haka Subay'a ke son tafiya ta Barsu.


Bai tarar da ita a parlor ba, se kawai ya wuce daki, Dama suna shigowa Laraba ta karbesu Don Yi musu wanka, seda yayi wanka yayi sallah kafin ya nufi dakin subay'a amma Tun Daga parlor gabanshi ya fadi, ta canza curtain Zuwa wanda idan zata yi tafiya take sawa, sofas dinta ta rufe da ledojinsu, da sauri ya shiga bedroom dinta not wanting to believe abinda zuciyarshi ke fada mishi, babu bedsheet kan gadon,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login