Showing 9001 words to 12000 words out of 131263 words
skirt da riga wanda yayi mata kyau tayi kwalliya a fuskar ta, dankwalin ta daura shi yadda ya dace gashi se kamshi take hakan se ya saukar masa da nutsuwa yaji duk ya zubar da makaman yakin nashi, amma a ranshi Yana Raya idan suka cigaba da haka lallai zai zama kullum shi ke cutuwa amma yau Tasha. Kamar tasan me yake tunani tana isa gun da yake zaune ta riko Fuskarshi ta Fara bashi wani hot kiss wanda ko minti bai cika ba ta kashe masa dukkan jikinsa tasa ya manta da wanzuwar wata mace Bayan ita. Subay'a kenan.
A dining kowa ya hallara banda uwar gayya Sulaim har lokancin tana iya hango tsagoran bacin rai idanun Junaid ta kasa manta hararar da ya zabga mata dazu hakan yasa taga gwara tayi zamanta idan suka gama cin abincin ta fito taci nata, amma hakan bata samu ba Don kuwa aiko Ahmad yayi akan tazo abinci is ready. Turo Baki tayi kamar Junaid dinne yazo da kanshi tace
Kace na koshi
Shikuwa ya juya Yaje ya isar da saqon shi, share maganar yayi ya fara cin abincinshi, Subay'a na mishi hira, Sede ya kasa jurewa don ya Saba da ganinta gefensu tana tauna abinci da wannan mitsitsin bakin nata, wayarshi ya janyo ya tura mata
_Come on fito Kici abinci _
Tana jin shigowar message din tasa hannunta ta janyo wayar Don tunaninta Ja'afar ne ashe me gayya me aiki ne, baki ta Kara turowa tareda buga kafa Cikeda shagwaba kamar yana gabanta tace
Mhm Mhm Bazanci ba.
Shikam bawan Allah gaba daya hankalinsa Yana kofar dakinta ita kadai yake da muradin gani amma taki fitowa ita kuma Subay'a bata Lura ba, a haka ya kara tura Mata wani text din
_Don't let me come and meet you a dakinnan, ranki zaiyi mugun baci wallahi_
Yadda text din ya nuna mata seriousness dinsa yasa ta fito Tana ta cin magani, da idanun shi ta Fara arba yayinda ya lumshe idanun shi Yana jin yadda sanyi ke zagaye jikinshi, haka Kuma ya sauke ajiyar zuciya wadda har Seda Subay'a ta dubeshi.
Zama tayi ta janyo plate ta bude abincin, baki daya daga shinkafa, macaroni se salad. Abincin kenan kullum su ake sarrafawa ita kuma ta gaji, ga abinda ya faru daxu ga tursasawar Junaid akan taxo taci abinci ga yanzu idanunshi da suka hanata sakat, kawai se ta kifa kanta ta Fara kuka.... A'a abin mamaki duka suka bita da ido, wani mugun tsaki Subay'a taja tareda mikewa tace
Jimana bataciyyar Yarinya, zaki samu a gaba da kuka.
Daki ta wuce abinta yaranta suka bita dukda son su lallashi Antynsu amma Subay'a ta buga ta tsare. Shikam Junaid Daga kukan yasan tsantsar shagwaba ce amma dukda haka se kukanta ke sukar mishi Vena cava. Fork din hannunshi ya aje yace
Sulaim
Kanta ta dago Baki daya fuskarta ta baci da hawaye, kallonta yayi yace
Ya akai, don nace Kici abinci?
Pouting face dinta tayi tace
Ni bashi nake so ba.
Murmushi yayi wanda yasa yayi kyau sannan ya zaro ido a ranshi yace Anzo gurin
Me kike so.
Seda ta gama share fuskarta sannan tace
Tuwo!
Kuma yadda ta fada irin seriously dinnan, wani kallo yake binta dashi with full of mamaki sannan ya dubi wall clock din karfe Tara ta gota, kallon fuskarta yayi yaga yadda take kallonshi kuma da alama jira take yace a'a ta sake Daga mishi hankali.
Atika!
Ya Kira a nutse, within seconds Atika ta iso Cikeda mamaki Don shi baya saka aiki, yana kallon fuskar Sulaim yace
Tuwo nake so yanzu
Kallon time tayi tace
To Yallabai!
Daga haka ta wuce kitchen dake sunada miya cikin fridge. Daga haka bai kara magana ba ya bar mata dining din ya koma kan cushion tareda maida channel din zuwa aljazira yana kallon news. Itama share shi tayi ta cigaba da zamanta Tana jiran abinci, to 10 Atika ta kawo tuwon da miyar ogun wadda a ido ma kawai cewa take "eat me" ajewa tayi ta juya yayinda ya dawo da dukkan hankalinshi kanta hakan yasa ta ji duk ya takurata se ta turo Baki, kanshi ya dauke Yana shafawa a ranshi yace "Sulaim case" ita dama haka take rasuwar su Daddy yasa ta rage shagwabar amma Bayan ta gama secondary se abun ya fara dawowa kuma indai tanayi dole Se ta dauki hankalinka wasu lokutan ko magana take se Junaid yaji kamar don tasan tana rikitashi Shiyasa take amma ina haka take normalcy dinta kenan.
Seda ta koshi ta tattare Kwanukan kafin yace
Babu Abinda kike so kuma?
Kanta ta gyada tana murmushi, shima martani ya mayar mata kafin yace
To your bed.
Haka ta wuceshi zuwa dakinta, haka kawae se ta tsinci kanta Cikeda farin ciki, ta dinga hango murmushin Junaid se kuma ta saki murmushi ta kankame pillow, ko Ja'afar bata tuna ba bacci ya dauketa.
Shima a nashi bangaren se goma da Rabi ya kashe komai ya nufi dakin Subay'a, tuni ta dade da bacci, a hankali yake ta kallonta yana mamakin yadda take ita babu ruwanta batada damuwa, bata wani daga hankalinta akanshi, duk lokacinda ya kwanta kanshi sede idan tana bukatarshi idan yayi magana tace ita a gajiye take dawowa kuma shi babba ne so yake Abinda zata yiwa Ahmad da Muhammad tayi mishi. Kanshi ya girgixa yace "Subay'a " se kuma ya wuce dakinshi inda yayi Alwala sannan ya kashe wutar dakin amma duk yadda yaso bacci yace no tunanin Sulaim zaayi, hakan ce ta faru ya dinga tunanin ta yana tariyo abinda tayi mishi dazu a dining a haka barawo ya lallabo ya sace mana babban yaya Junaid!
To fa people of Allah! Have seen your comments so far nasha dariya amma naji dadi, Kada Ku damu yadda kukeso haka zaayi. Gaisuwar girma zuwaga yan SHATUUU KINGDOM...... 🤝🏻🤝🏻🤝🏻
Shatuuu ♥️
[6/23, 5:20 PM] Shatuuu😍: *MACE A YAU*
6
✍️Shatuuu♥️
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
#⃣Shatuuu095@wattpad
LLB1 yayi shiru saboda wata zazzafar test da akeyi ta philosophy, gaba daya kowa hankalinshi yana kan paper dayake rubuta test dinshi, inda Sulaim take naje abin mamaki Tana zaune gefen Khulthum wadda itama dukkan hankalinta ya ta'alaka wajen test din. Baifi minti goma ba daya daga cikin malamin yace
Pens up.
Aje pen din Sulaim tayi tareda sakin ajiyar zuciya, yayinda ta gefenta ma hakance ta kasance, a hankali suka dinga bi suna tattara papers din kafin suka fice. Khulthum ce ta Fara kallon inda Sulaim take wadda hankalinta yana kan wayarta tana karanta text din Junaid akan idan ta tashi ta sameshi a office dinshi, se ta tsinkayi muryar Khulthum tace
Ya test din?
Murmushi tayi Wanda ya fito da gapped teeth dinta ta dago tace
Alhamdulillah, tayi sauki not as expected.
Yadda tayi magana shi ya fara jan hankalin Sulaim, itama martanin murmushin ta mayar mata tace
Gaskiya kam amma......
Kafin ta karasa class rep dinsu ya bayyana gaban class inda ya bada announcement din Logic class baxaiyi taking place ba don haka kowa is free now. Kowa murna yayi mussaman yan nesa da suke son barin kano ranar don an tafi mid semester break, tare suka mike suka jero har wajen class, Sulaim tace
Bari na tafi ana jirana se Bayan break.
Murmushi Khulthum tayi tace
Allah ya kiyaye nima na tafi ayi Hutu lapiya.
Kanta ta gyada mata kafin kuma tace
Bansan sunanki ba fa.
Nima haka, Sunana Ummu_Khulthum
Ido Sulaim ta dan zaro kafin tace
Ummu_Sulaim
Tare da mika mata hannu sukai musabaha, basu bar gurin ba seda sukai exchanging phone digits, Khulthum na fito da wayarta wata Infinix note ce hannunta ta zama babbar yarinya don a cewarta dole a dama dasu, shi kanshi kayan dake jikinta ba karamin amsar ta sukai ba, hardly ka hasaso cewar ga daga gidan data fito, yadda take tafiya a hankali kamar bazata taka kasa ba shi ya fara janyo hankalin Huzaifa dake tsaye gaban motarsu da dukkan alamu wani abun yake jira, ita bata Lura da shi ba hankalinta Baki daya ya tafi tunanin Sulaim, yarinyar ta burge ta she's simple yet classy, kuma kana kallon yanayinta kasan Daga gidan data fito don wani zobe na gold data lura dashi hannun Sulaim din, fatarta ma is flawless. Tana ta wannan tunanin taji alamar anyi parking gefenta, amma da yake Khulthum is Khulthum ko daga idonta Batayi ba balle ta kalli gefenta inda motar take haka ta cigaba da tafiyarta, Huzaifa dake ciki yayi murmushi sannan ya bude motar ya iso inda ta tsaya ita a dole napep take nema nan kuwa addu'a take a ranta Kada ya tafi. Abinda ya fara futawa shi ne
Kin burge ni.... Kizo Nayi dropping dinki dan kyakyawa kamarki bai dace rana ta doke ta ba.
A hankali ta juyo da fuskarta ta sauke Kan tashi, bashida tsayi don idan ya fita da kadan zai fita, kana kallonshi kasan dan Hutu ne kuma dan gayu, naira tana kuka hannunsu.
Nagode
Ta bashi amsa kafin ta kara matsawa gefe don tarar napep, shima juyawa yayi ya Daga kafada alamar Kinyi missing yaja motarshi ya barta a gurin Cikeda mamaki Don bata taba tunanin hakan zai faru ba, tabbas ta bar opportunity dinnan ya wuce ta, a haka a kufule ta samu napep shima ya dinga raina mata hankali dayake ya sameta a Bagas se bata kulashi ba, haka ta isa gida abin Yana ta damunta.
Sulaim na zuwa kofar office din Junaid tasa hannunta tayi knocking, cikin deep voice din nan tashi yace
Come in.
Hannu tasa ta bude kofar, bakinta dauke da sallama ta shiga, yana zaune kan kujerar, yayinda wani wanda ta saba ganinsu tare kuma take tunanin shima lecturer ne Yana zaune opposite him.
Yaya barka da Rana
Ta furta lokacinda ta iso tsakiyar office din, kafin ya amsa ta dubi bakon nashi shima ta gaisheshi maimakon amsawa se yace
Sulaim right?
Kanta ta gyada, shi kuma Junaid ya zabga mishi harara wanda yasa ya kwashe da dariya cikin kankan da murya yadda Sulaim ba zataji ba yace
Se na fada mata Wallahi.
Itadai tana tsaye ta dauke kanta daga kallonsuu taji Junaid yace
Auta koma kan cushion ki zauna kafin na gama.
Babu musu tayiwa kanta masauki tareda tunanin Yaushe rabon da yace mata auta ita kanta ta manta last time din. Wayarta ta ciro ta Fara abubuwa da bansan me takeyi ba, wajen Mintina talatin ta dago idonta cikin sa'a shima kallonta yake se suka hade cikin na juna, dauke kanta tayi shi kuma ya bata rai Wanda kadan ne Ridwan dake gefe baiyi dariya ba haka suka karayi wajen sau uku sannan Junaid ya gyara murya yace
Ya akai ne?
Bakinta ta turo tace
Tafiyan fa?
Idonshi ya kura mata yace
Zuwa ina kenan?
Kaduna mana, yau fa an tafi mid semester break.
Kanshi ya dauke don kwatakwata bayada niyyar ta tafi wani gurin better ta zauna don shi se yanzu yake ganin Tun tuni me ye dalilin da Tunda su Daddy suka rasu bai dakko ta ba ya bari su Mami suka dauketa. Ganin yayi shiru yasa tace
Yaya flight din fa 6pm zai tashi
Da sauri ya dago Cikeda mamaki yace
Waye yayi miki booking, you didn't even let me know.
Tun last week Ja'afar yayi mata booking ko Mami bata sani ba, to yanxu tasan inhar yasan Ja'afar ne tafiyar sede a fasa,
Mami tayi booking fa,
Junaid baice komai ba ya mike shida Ridwan suka fita, suna fita ta Mike kafafuwanta. Acan Ridwan yace
Ka kyaleta ta tafi, kada kana takura mata idan ba haka ba Abinda muke nema bazamu samu ba.
dafa kanshi Junaid yayi ya sake jinginar da jikinshi a jikin mota yace
I don't want her to go, nafi son kullum ina ganinta by my side.
Kallonshi Ridwan yayi yace
Kada ka zama me son kanka, to me yasa bazaka fada mata ba.
Da sauri Junaid ya dubeshi Yana zaro ido kafin kuma ya fara girgiza kanshi yace
Is not yet time and kasan yanzun haka tare suke da Ja'afar, ni ina tunanin shi yayi booking flight dinnan Don there's no way Mami zatayi batareda sani na ba.
Tabdi! Ja'afar Yana son ta?
Ridwan ya fada Yana kara jinjina abin kafin yace
Abokina ka hakura mana.
Murmushin takaici yayi yace
Da zan iya da tuni na hakura, bazan iya bane na kasa dangana.
To idan bazaka iya hakura ba is better you let her know, yarinyar da alama bazatayi wahalar shawo Kai ba.
Dariya Junaid yayi yace
Ba haka bane, shi ne kawai Abinda mutane Ke gani a tattare da ita amma ni nasan taurin kan Sulaim se addu'a.
Sun dade suna tsaye har Sulaim ta gaji da jiranshi zata kirashi ya turo kofar ya shigo, tashi tayi ta zauna Tana kallonshi, shima kallonta yake har ya zauna inda Ridwan ya tashi yace
Kinyi sallah?
Kanta ta gyada yace
Mu tafi kenan?
Take wani murmushi ya subuce mata, bai kulata ba suka fito Zuwa mota, lokacin awa daya ta rage flight dinsu, kallonshi tayi yadda yake tuki kamar bayaso tace
Yaya zanyi missing flight din fa
Baice da ita komai ba ya cigaba da takunshi itama tayi iskar kare dashi tareda daukar wayarta tana ta danne danne taji muryar shi yace
Zaki dauki abu a gida ne?
Dago kanta tayi tace
A'a na saka a booth Tun safe
Seriously? Kin gaji da ganina ne har haka?
Kawai abinda yaji bakinsa ya furta kenan, lumshe idonsa yayi a ransa Yana fadin you messed up Junaid. Itakam kallonshi tayi tace
A'a Yaya, ina son kawai zuwa ne.
Kanshi ya gyada bai kuma fadar komai ba saboda gudun kwafsawa haka ya kaita airport seda aka gama komai kafin suka rabu, tana ta murna wadda ta kasa boyuwa shi abin har mamaki yake bashi ma.
A airport tana sauka ta fito a departure hall ta hangoshi a tsaye ya harde hannayensa Kan kirjinsa, Yana cikin Kaftan coffee da hula a kanshi yayi kyau har ya gaji da kyau, Kada Ku manta Duk yaran Mami Ja'afar Yafi kowa kyau, idanunshi Yana cikin eyeglasses fari tas, sede yana tsaye da wata azabbabiyar kyakyawar Yarinya Irin lousy kyau dinnan wanda abinda zaka fara hangowa kenan, suna tsaye Sunata dariya Irin abinda ake fada yayi dadi, gaba daya se Sulaim taji tamkar karta karasa gurin amma se ta dake ta isa inda suke fuskarta babu walwala ta zagaya Dayan kofar ta bude ba tareda tace komai ba ta shiga ta zauna amma ko bata fada ba kunsan how it feels kaga Abinda kake fadi tashi a kanshi, kake fatan ya zama naka na har abada yake tsaye da wata, abinda taji yace shi ya sake dugunzuma ta
Bari na wuce Kada baby sis tayi ta jira.
Seda ta zagayo inda Sulaim ke Zaune tace
Baby Sis ki kulamin da baby na naga Yana ji dake.
Kamar an buga mata guduma haka taji "Baby sis" like serious, shiru tayi ta sunkuyar da kanta Tana ta battling da hawayen dake son zubo mata se taji ta wulakanta.... Yes wulakanci ne. Shima jiki a sanyaye ya shigo but being the Ja'afar se cewa yayi
Sweetm se ki bani tsoro yadda kika Bata rai dinnan.
Ko kallonshi Batayi ba ta bata rai Haka ya aje wayar shi saman cinyarta ya fara driving sede yadda yake driving kawai will tell you cewar baiji dadi ba. Haka suka tafi shiru kamar anyi rasuwa Duk Surutun Ja'afar kasa magana yayi se can yace
Susu ba fushi zakiyi ba at least let me explain.
Ban tambayeka ba.
Come on Susu why you behaving like this.
Mtsssssssw
Taja tsaki wanda ba Ja'afar ba hatta ni Seda nayi mamaki, yadda take kada kafarta da kuma fuskarta ya nuna bacin rai sosae. A haka bai sake magana ba har aka bude gate din gidan, wani sharp breath tayi inhaling at least she's home. Yana gama parking ta aje masa wayoyinsa ta fice, tana bude parlon Mami ta fito daga kitchen hannunta rike da katon tray, a guje ta nufe ta itama aje tray din tayi ta rungume abarta, wani Irin farin ciki ya dinga shigarsu a hankali Mami tace
Haka unexpected Autar Mami?
Murmushinta tayi daidai shigowar Ja'afar, bai kulasu ba ya wuce inda zai kai shi dakinsu iatakam Mami tabi Zuwa sama rikeda tray din, ganin yanayin ta yasa Mami tace
Auta kamar ranki a bace yake?
Boye fuskata tayi cikin hannunta tace
Babu komai na gaji ne Mami, Ina Baba ?
Yaje massallaci jekiyi wanka kafin ya dawo.
Babu musu tayi dakinta, se lokacin da ta shiga bayi Abinda ya faru daxu ya fara dawo mata, wannan shi ne Karo na uku da suna Irin haka itada Yaya Ja'afar se take ganin kamar ta sake mishi da yawa ne, a haka tayi wanka tana ta tufka da warwara. Seda ta shirya sannan ta dauki wayarta Don duk expecting dinta Junaid ya kirata amma ko message babu hakan yasa ta kirashi, yana zaune kan sofa a parlonshi Ahmad yana ta damunshi akan se sunje siyo chocolate yayinda Subay'a ke dakinta kannenta sunzo, kiran Sulaim ya shigo, kawai murmushi ne ya kwace masa tareda jin sanyi cikin zuciyarshi. Shi kanshi mamakin yadda son Sulaim yayi masa Illa har haka yake, gashi ita bata wani damu dashi ba a yadda take abubuwan ta, a haka dai kiran ya katse. Kamar tana gabanshi tayi pouting lips dinta Wanda har ya zama jikinta tace
He'll not pick shima.
Tana shirin fita taji yayi returning call din, wani murmushi ta saki ta dauki wayar ta kara a kunnenta Sede kafin tayi magana ta Fara tuhumar kanta dalilin da yasa ta kirashi, meye take jinta special saboda yayi returning call dinta.......
Sulaim are you there?
Idan tayi Rantsuwa cewar babu mahalukin da duk duniya ya iya kiran sunanta Irin yadda Junaid ya ke kira Batayi karya ba, Harda gunna, kalkala sufra, madda da komai yake kira, kowanne harafi se ya bashi hakkinsa.....
Mhm
Mhm
Shima ya furta Yana rike wayar sosae, itakam jikinta duk yayi wani yum hakan yasa ta kwanta
Talk to me, ya kika je?
A hankali in a whisper tace
Lapiya lau, Mami na gaisheka
Dan